EFCC ta cafke tsohon shugaban NHIS, Usman Yusuf a Abuja
Published: 30th, January 2025 GMT
Jami’an Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), sun cafke Tsohon Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, bayan kai sumame a gidansa da ke Abuja.
Aminiya ta tabbatar da cewa jami’an EFCC ɗauke da makamai sun isa gidansa da misalin ƙarfe 4:46 na yammacin ranar Laraba, inda suka kama shi a gaban matarsa da ’ya’yansa.
Sai dai har yanzu ba su bayyana dalilin cafke shi ba.
Wata majiya ta bayyana cewa an kama tare da tafiya da Farfesa Yusuf zuwa wani waje da ba a bayyana ba.
Duk da cewa hukumomi ba su fitar da sanarwa kan tuhumar da ake yi masa ba, wasu majiyoyi sun ce kamun nasa yana da alaƙa da shugabancin da ya yi a hukumar NHIS.
Wani babban jami’in EFCC ya ce, “Ba za a iya bayyana dalilin kama shi a yanzu ba saboda har yanzu ana bincike.
“Amma yana hannunmu kuma zai taimaka wajen gudanar da bincike.”
An cire Yusuf daga muƙaminsa a shekarar 2019 a lokacin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari.
Wani kwamitin bincike na Ma’aikatar Lafiya ne, ya bayar da shawarar korarsa bisa zargin ɓatan-dabon Naira miliyan 919.
Da aka tuntuɓi kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya ce zai bincika batun sannan ya yi ƙarin haske daga baya.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, bai yi martani ba.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum
Rikicin jam’iyyar PDP ya ƙara tsananta bayan sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya sanar da dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Illiya Damagum.
Yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a Abuja, Anyanwu, wanda yake ɗan tsagin Nyesom Wike, ya ce an dakatar da Damagum da wasu manyan jami’an jam’iyyar guda biyar saboda zargin rashin ƙwarewa, almundahana, da ƙin bin hukuncin kotu.
Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike“Mun yanke shawarar dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Ilya Damagum, saboda rashin ƙwarewa, almundahana, da ƙin mutunta hukuncin kotu,” in ji Anyanwu.
“An dakatar da shi na tsawon wata guda, kuma dole ne ya gurfana gaban kwamitin ladabtarwa.”
Anyanwu, ya kuma yaba da hukuncin kotu wanda ya soke babban taron jam’iyyar na ƙasa, inda ya bayyana cewa wannan nasara ce ga mambobin PDP baki ɗaya.
“Muna jinjina wa ɓangaren shari’a bisa wannan hukunci da ya nuna adawa da zalunci da rashin bin doka. Wannan nasara ce ga kowane ɗan jam’iyyar PDP,” in ji shi.
Sauran da aka dakatar sun haɗa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba; mataimakin shugaban jam’iyyar na Kudu, Taofeek Arapaja.
Akwai kuma sakataren kuɗi na ƙasa, Daniel Woyenguikoro; jagoran matasan jam’iyyar, Sulaiman Kadade da mataimakin sakataren jam’iyyar na ƙasa, Setonji Koshoedo.
Sanarwar Anyanwu, na zuwa ne bayan ɓangaren Damagum ya dakatar da shi da wasu magoya bayan Wike, lamarin da ya ƙara ba tsananta rikicin shugabanci a jam’iyyar PDP.
Anyanwu, ya kuma sanar da naɗa Alhaji Abdulrahman Mohammed, mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin Arewa ta Tsakiya, a matsayin sabon muƙaddashin shugaban jam’iyyar.