’Yan bindiga sun sace matashiya bayan karɓar kuɗin fansa a Kano
Published: 26th, January 2025 GMT
’Yan bindiga sun kai hari garin Garo da ke Ƙaramar Hukumar Kabo a Jihar Kano cikin daren ranar Lahadi, inda suka sace wata budurwa mai suna Zainab Auwalu, bayan sun karɓi kuɗin fansa Naira miliyan takwas daga hannun mahaifinta.
Zainab, wadda ta kammala makarantar sakandare kwanan nan, an sace ta a gidan mahaifinta, Alhaji Auwalu.
Shaidu sun bayyana cewa ’yan bindigar, kimanin su 10, sun shiga garin da babura ɗauke da muggan makamai.
Sun shiga gidan Alhaji Auwalu da misalin ƙarfe 1:30 na dare, inda suka shafe awanni suna cin karensu ba babbaka, sannan suka tafi da kuɗin fansa tare da sacw ‘yarss.
Wani mazaunin garin, Haruna Muhammad, ya ce harin ya jefa al’ummar garin cikin firgici.
Mutane da yawa na zargin cewa wasu mazauna garin ne suka bai wa ’yan bindigar bayanai.
Kakakin ’yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa jami’an tsaro na ƙoƙarin bin sahun ’yan bindigar da kuma ceto matashiyar.
Ko da yake satar mutane da fashi ba su yawaita a Jihar Kano ba, garuruwa irin su Garo da sauran yankunan Arewacin Kano da ke kusa da jihohin Kaduna da Katsina, sun sha fuskantar hare-haren ’yan bindiga.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Mutuwar majinyata: Asibitin Aminu Kano na roƙon KEDCO ya dawo da wutar lantarki
Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya roƙi Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na KEDCO ya gaggauta dawo masa da wuta bayan rasuwar wasu marasa lafiya da ke samun kulawa ta ceton rayuwada na’ura.
Wata sanarwa da kakakin asibitin, Hauwa Inuwa Dutse ta fitar ta nuna takaici bisa rasuwar marasa lafiyan, tana mai cewa mace-macen waɗanda za a iya kauce wa ne idan akwai tsayayyiyar wutar lantarki.
Ta bayyana cewa Asibitin yana AKTH yakan biya kuɗin wuta akai-akai daga kuɗaɗen shigansa, kuma yana kashe kuɗaɗe wajen sanya mai a janareto domin amfani idan aka ɗauke wuta daga KEDCO.
Don haka, “Hukumar gudanarwar Asibitin AKTH na roƙon Kamfanin KEDCO da ya taimaka wa ayyukan asibitin ta hanyar dawo da wutar a yayin da muke ƙoƙarin biyan ragowar kuɗin wutar,” in ji sanarwar.
Ambaliya: An gano gawar ’yar shekara 3 da ruwa ya tafi da ita a Zariya Gwamnati ta gargaɗi jihohi 11 kan yiwuwar afkuwar ambaliya a wannan makonTa bayyana cewa a yayin da take ƙoƙarin biyan bashin da kamfanin ke bin sa, yana da muhimmanci a fahimci cewa yanke wutar lantarki daga muhimmiyar cibiyar lafiya babbar barazana ce ga majinyata da danginsu.