An kama buhun tabar wiwi 150 bayan hatsarin mota a Kano
Published: 13th, September 2025 GMT
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta kama buhu 150 maƙare da tabar wiwi a yayin da ake tsaka aikin ceto bayan wani hastarin mota da ya auku a kan babbar hanyar Zariya zuwa Kano.
Hukumar ta bayyana cewa hatsarin ya auku ne tsakanin wata mota ƙirar Volkswagen Golf da wata babbar mota a yankin Gadar Tamburawa da ke Jihar Kano.
Kakakin NDLEA na Jihar Kano, ASN Sadiq Mohammed Maigatari, ya bayyana cewa ɗaya daga cikin fasinjojin da aka ceto ya yi ƙoƙarin tserewa amma an yi nasarar kama shi.
Ya ce a yayin bincike ne aka gano buhuna 150 na tabar wiwin wanda nauyinsu ya kai kilogram 112.
Abba ya tarbi tagwayen da aka raba da juna bayan yi musu tiyata a SaudiyyaYa ƙara da cewa direban motar ya shaida musu cewa shi ne ya yiwo dakon tabar wiwin madadin mai ita, kuma ba wannan ne karon farko ba da ya yi safarar ta zuwa Kano da wasu wurare.
Direban ya bayyana cewa ya yi aron hannu ne domin kauce wa shingen binciken jami’an NDLEA, a garin haka aka samu hatsarin na ranar Asabar.
Ya ƙara da cewa direban babbar motar ya samu karaya, sauran mutum biyu da aka kama suke tsare.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gadar Tamburawa Hatsari hatsarin mota Tabar wiwi
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Tsare-tsaren Ci Gaban Kaduna a Taron Duniya a Dubai.
Daga Abdullahi Shettima
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya wakilci Nijeriya a taron ƙoli na biranen Asiya da ya gudana a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda ya gabatar da kudirorin sauyin ci gaban Kaduna.
Taron ya samu halartar manyan baki daga ƙasashe sama da 150, ciki har da gwamnoni, shugabannin birane da jagororin kasuwanci daga Asiya, Fasifik, Turai da Afirka. Taken taron shi ne “Haɗin Gwiwa. Ƙarfafawa. Sauyi.”
A jawabinsa mai taken “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa,” Gwamna Uba Sani ya bayyana yadda Kaduna ke samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma da tallafawa jama’a. Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne kan faɗaɗa damar tattalin arziki, kare marasa ƙarfi, da ƙarfafa jama’a su cim ma nasara a rayuwarsu.
Haka kuma, ya halarci baje kolin birnin Dubai mai taken “Sauya Arewa a Nijeriya: Jagoranci, Ƙirƙira da Tasirin Zamantakewa,” inda ya jaddada muhimmancin jagoranci mai nagarta da amfani da fasaha wajen buɗe damarmaki ga al’umma.
A yayin taron, Gwamnan ya gudanar da ganawa ta musamman da Marwan Bin Galita, Darakta-Janar na birnin Dubai, inda suka tattauna batutuwan kirkirar makamashin sharar gida, kula da sharar zamani, da tsare-tsaren gine-ginen birane na zamani.
Duk ɓangarorin biyu sun amince da zurfafa haɗin kai a fannin fasaha da musayar ƙwarewa domin tallafawa sauyin tattalin arzikin Kaduna zuwa mai ɗorewa.
Gwamna Sani ya bayyana cewa halartar Kaduna a taron (APCS 2025) na nuna shirin jihar na shiga sahun gaba wajen yin haɗin kai, ƙirƙira da zama abin koyi a fannin ci gaba mai ɗorewa — a Najeriya da duniya baki ɗaya.
Karshe.