Aminiya:
2025-11-02@06:26:24 GMT

ACF ta yi Allah-wadai da rushe kasuwar Alaba Rago

Published: 28th, August 2025 GMT

Kungiyar Dattawan Arewacin Nijeriya (ACF) ta bayyana matuƙar damuwarta kan rushe kasuwar Alaba Rago mai ɗimbin tarihi a Legas, inda ta bayyana hakan a matsayin babban koma baya ga dubban ’yan kasuwa.

A cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Farfesa T. A. Muhammad-Baba, Ƙungiyar ta bayyana cewa duk da cewa ba a samu asarar rayuka ba, ɓarnata kasuwanci da dukiyoyi ya jefa wasu iyalai da dama cikin ƙunci.

Gwamnatin Gombe da Rotary sun yi shirin rage mutuwar mata da yara An kama Ɗan sanda kan harbe soja a Bauchi

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Rushe kasuwar mai ɗimbin tarihi ya haifar da asarar kasuwanci da dukiyoyi, tare da kawo cikas ga hanyoyin rayuwar jama’a da haifar da matsaloli ga dubban mutane, ba a bayyana asarar rai ba.

Kungiyar ta ACF ta jajanta wa waɗanda rusau ɗin ya rutsa da su, inda ta buƙace su dage wajen yin haƙurin lamarin.

“Da fatan, waɗanda lamarin ya shafa za su kasance masu juriya masu ƙwazo, za su zo su taka rawa wajen taimaka wa waɗanda abin ya shafa su jure asarar da aka yi musu sanadin rushewar,” in ji Farfesa Muhammad-Baba.

Kungiyar ta bayyana cewa tana neman ƙarin bayani kan lamarin don jawo hankalin gwamnatin Jihar Legas da kuma al’ummar da abin ya shafa don magance matsalar.

A halin da ake ciki, ACF ta buƙaci gwamnati ta sa baki cikin gaggawa don taimaka wa waɗanda abin ya shafa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kungiyar Dattawan Arewacin Nijeriya

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Tsare-tsaren Ci Gaban Kaduna a Taron Duniya a Dubai.

Daga Abdullahi Shettima

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya wakilci Nijeriya a taron ƙoli na biranen Asiya da ya gudana a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda ya gabatar da kudirorin sauyin ci gaban Kaduna.

Taron ya samu halartar manyan baki daga ƙasashe sama da 150, ciki har da gwamnoni, shugabannin birane da jagororin kasuwanci daga Asiya, Fasifik, Turai da Afirka. Taken taron shi ne “Haɗin Gwiwa. Ƙarfafawa. Sauyi.”

A jawabinsa mai taken “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa,” Gwamna Uba Sani ya bayyana yadda Kaduna ke samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma da tallafawa jama’a. Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne kan faɗaɗa damar tattalin arziki, kare marasa ƙarfi, da ƙarfafa jama’a su cim ma nasara a rayuwarsu.

Haka kuma, ya halarci baje kolin birnin Dubai mai taken “Sauya Arewa a Nijeriya: Jagoranci, Ƙirƙira da Tasirin Zamantakewa,” inda ya jaddada muhimmancin jagoranci mai nagarta da amfani da fasaha wajen buɗe damarmaki ga al’umma.

A yayin taron, Gwamnan ya gudanar da ganawa ta musamman da Marwan Bin Galita, Darakta-Janar na birnin Dubai, inda suka tattauna batutuwan kirkirar makamashin sharar gida, kula da sharar zamani, da tsare-tsaren gine-ginen birane na zamani.

Duk ɓangarorin biyu sun amince da zurfafa haɗin kai a fannin fasaha da musayar ƙwarewa domin tallafawa sauyin tattalin arzikin Kaduna zuwa mai ɗorewa.

Gwamna Sani ya bayyana cewa halartar Kaduna a taron (APCS 2025) na nuna shirin jihar na shiga sahun gaba wajen yin haɗin kai, ƙirƙira da zama abin koyi a fannin ci gaba mai ɗorewa — a Najeriya da duniya baki ɗaya.

Karshe.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Tsare-tsaren Ci Gaban Kaduna a Taron Duniya a Dubai.
  • Kofin kofi mafi tsada a duniya ya shiga kasuwa a kan Naira miliyan 1.5m
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • ’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
  • Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar
  • NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa
  • Allah Ya Kai Manzon Allah (SAW) Muƙami Na Babban Yabo A Cikin Komai
  • Babban Daraktan Sakatariyar APEC: Sin Tana Ba Da Gudummawar Ba Da Jagoranci A APEC
  • Sudan : Kasashen duniya na Allah wadai da cin zarafi a lokacin kama El-Fasher
  • Gobara ta tashi a babban kanti a Abuja