HausaTv:
2025-05-04@00:04:19 GMT

Sojojin Isra’ila sun kaddamar da sabbin hare-hare kan Siriya

Published: 3rd, May 2025 GMT

Sojojin Isra’ila sun kaddamar da sabbin hare-hare ta sama kan yankuna daban-daban na kasar Siriya a yammacin Juma’a.

Rahotanni cikin gida sun ruwaito cewa jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare akalla 20 a wajen garuruwan Damascus, Daraa da Hama, inda suka auna wuraren sojoji da ma’ajiyar kaya.  

Hare-haren sun hada da wani sansanin sojojin Syria da ke kusa da kauyen Shatha da ke Hama, hedkwatar tsohuwar bataliyar sojojin Syria da ke arewacin Damascus, da kuma sansanonin soji a Dera.

Fashe-fashe sun afku a Damascus da kewaye, ciki har da Harasta, inda wani farar hula ya mutu.

Kafofin yada labaran Isra’ila sun ruwaito cewa an kai hari a wasu yankuna a babban birnin kasar a karon farko.

Tun bayan faduwar gwamnatin Bashar al-Assad a watan Disambar 2024, kasar Siriya ta kasance karkashin mamayar Isra’ila.

Da sanyin safiyar Juma’a ne jiragen yakin Isra’ila suka kai hari a yankin da ke kusa da fadar shugaban kasa a Damascus, wanda shi ne hari na biyu da sojojin gwamnatin sahyoniyawan suka kai a cikin wannan mako.

Hukumomin Isra’ila sun kare harin a matsayin goyon baya ga al’ummar Druze, wadanda ke fafatawa da wasu masu dauke da makamai da HTC ke marawa baya a kusa da Damascus a wani sabon tashin hankali na kabilanci a karkashin mulkin HTC.

Rikicin ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da jikkata.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Isra ila sun

এছাড়াও পড়ুন:

Masifar Gobara Tana Kara Bunkasa A Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tare Da Fara Raba Yahudawa Da Muhallinsu

Ana sa alamar tambayar cewa: Shin gobarar da ta tashi a birnin Kudus… shin sako ne na ranar tunawa da kafuwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya?

Gobarar da ta tashi a tsaunin Kudus da aka mamaye ta bazu zuwa manyan yankuna a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila, inda ta kewaye wani sansanin soji tare da cinye filayen masu girma da tsayi. Hakan ya sa hukumomin gwamnatin mamayar Isra’ila suka kafa dokar ta baci tare da neman taimakon kasashen duniya. Yayin da Ministan tsaron cikin gidan Isra’ila Itamar Ben-Gvir yake neman dora wa Falasdinawa, alhakin tashin gobarar.

Gobarar ta kunno kai ne a daidai lokacin da yahudawan sahayoniyya suka fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 77 da kafuwar gwamnatinsu ta mamaya a kasar Falasdinawa, gobara mai karfin gaske ta barke a tsaunukan birnin Kudus ta kuma bazu zuwa manyan yankuna masu girma.

Gobarar ta tashi ne a kusa da babbar hanyar da ke tsakanin Kudus da Tel Aviv, lamarin da ya kawo yawaitar cunkoson ababen hawa a manyan tituna. Gobarar ta yi sanadin jikkatar mutane masu yawa, kuma ta tilastawa hukumomin gwamnatin mamaya fara kwashe yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida daga gidajensu da ma marasa lafiya daga Asibitin Hadassah Ein Kerem da ke birnin Kudus saboda gobarar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ISWAP sun kai wa sojoji hari a Yobe 
  • Gaza : Kungiyar Euro-Med ta bukaci a binciki harin Isra’ila kan jirgin ruwan Freedom Flotilla
  • Yadda sojoji suka kashe manyan ’yan bindiga 5 a Zamfara
  • Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Yi Kakkausar Suka Kan Hare-Haren Jiragen Saman Amurka Kan Kasar Yemen
  • Jiragen Saman Yakin Sojojin Isra’ila Sun Kai Hare-Haren Wuce Gona Da Iri Kan Kasar Siriya
  • Falasdinawa 40 Ne suka Yi Shahada A Zirin Gaza Sakamakon Ta’addancin Sojojin Mamayar Isra’ila A Jiya Juma’a
  • Masifar Gobara Tana Kara Bunkasa A Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tare Da Fara Raba Yahudawa Da Muhallinsu
  • Ranar Ma’aikata: Gwamnan Kano Ya Biya Basussukan Fansho, Ya ƙirƙiro Sabbin Ma’aikatu
  • Amurka ta sake kai Hari a yankunan Saada da Hudaidah na Yemen