HOTUNA: Yadda aka tarbi Shugaba Tinubu a Katsina
Published: 3rd, May 2025 GMT
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya isa Jihar Katsina domin ziyarar aiki ta kwana biyu, inda zai ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar ta yi.
Gwamnan Jihar Katsina Dikko Radda, da tsohon Gwamna jihar Bello Masari na cikin manyan mutanen da suka tarɓe shi tun daga filin jirgin Umaru Musa.
Tinubu zai yi shekara takwas yana mulki – Afenifere Yadda aka yi bikin yaye sabbin matuƙa jiragen Rundunar Sojin Saman NajeriyaBayan isarsa ne kuma ya yi wa rundunar sojin ƙasar jawabi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Asiwaju Bola Tinubu
এছাড়াও পড়ুন:
Rashin tsaro: ‘Ba za mu miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba’
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci sojoji da su ƙara ƙaimi wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke addabar Najeriya yana mai jaddada alkawarin cewa ƙasar ba za ta miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba.
Da yake jawabi ga sojojin a lokacin ziyararsa a Katsina, Shugaba Tinubu ya nuna damuwa game da ƙalubalen tsaron da ake fuskanta a ƙasar a halin yanzu, inda ya bayyana su a matsayin wani lokaci mai muhimmanci a tarihin Najeriya.
Tinubu ya yi kira da a nuna jajircewa wajen kare ikon Najeriya da kuma dawo da zaman lafiya a faɗin ƙasar.
Ya tabbatar wa sojojin da kudirinsa na kula da jin daɗinsu, inda ya yi alƙawarin biyan alawus-alawus a kan lokaci, tabbatar da kula da lafiya, da kuma tallafa wa iyalansu.
2027: Mene ne mafita ga ’yan adawa? Yadda sojoji suka kashe manyan ’yan bindiga 5 a ZamfaraYa jaddada jarumtaka da sadaukarwarsu, yana mai cewa su ne “garkuwar Najeriya.” Ya jaddada cewa yaƙin ba wai kawai na yankuna ba ne, har ma da yaƙin neman ran kasar.
Tinubu ya tabbatar da ƙudirin gwamnatinsa na tallafa wa sojoji da ayyuka da zuba jari, yana mai gargaɗin masu kawo cikas na cikin gida da na waje cewa Najeriya ba za ta miƙa wuya ba.
Ziyarar tasa ta kuma hada da ƙaddamar da titin mota mai hannu biyu mai tsawon kilomita 24 da cibiyar aikin gona ta zamani a Katsina.