Rahotanni da suke fitowa daga yankin ‘Sahalul-Khayam na kasar Lebanon sun ce, wasu ‘yan asalin kasar Syria su 2 sun yi shahada sanadiyyar harin da Isra’ila ta kai da jirgin sama maras matuki sa’o’i 2 da su ka wuce.

Da safiyar yau Litinin ma dai wani karamin jirigin ‘yan sahayoniya ya jefa bom akan wata mota da take tafiya a garin “Beit-Lif” a kudancin kasar da hakan ya yi sanadiyyar jikkatar wanda ke cikinta.

Hare-haren da HKI take kai wa a kudancin Lebanon din dai yana a karkashin keta hurumin kasar da kuma kin aiki da kudurin MDD mail amba 1701 na tsagaita wutar yakin da aka yi a ranar 27 ga watan Nuwamba na wannan shekara ta 2025.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Har Yanzun Ana Zaman Dar-Dar A Burkina Faso Bayan Kokarin Juyin Mulkin Da Bai SamiNasara Ba

Ana ci ga ba da zaman dar-dar a kasar Burkina faso, bayan da shugaban kasa mai ci Ibrahim traure ya sake tsallaka rijiya da baya, a wani kokarin juyin mulki wanda bai sami nasara ba a makon da ya gabata.

Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News’ya nakalto radiyo Faransa RFI yana fadar cewa an bankado juyin mulkin ne bayan da dukkan bakin da aka gayyata a ranar 22 ga watan Afrilu zuwa wani taro sun kasa halattan taron. Wanda ya nuna shakku kan abinda aka kulla a cikin taron.

Labarin ya kara da cewa a cikin yan kwanaki masu zuwa mutanen kasar zasu fito zanga-zanga don nuna goyon bayansu ga shugaban Traore.

Har’ila yau ana gudanar da bincike a cikin barikokin sojojin kasar a birnin Wagadugu a kokarin gano wadanda suke adawa da gwamnatin Traore, sannan suke aiki wa kasashen yamma musamman kasar Faransa wajen ganin bayan shugaba Ibrahim Traore.

Kafin haka dai an nakalto ministan tsaron kasar ta Burkina faso Muhammada Sana ya na wani bayani a tashar talabijin na kasar,  kan cewa kafin su gano shirin juyin mulki sun satar maganar wayar tarho tsakanin wani babban sojan kasar da shugaban wata kungiyar ta’addaci wanda aka shirya za su kashe shugaba Traore.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Munafunci Dodo Ya Kan Ci Mai Shi
  • Katafaren Jirgin Daukar Jiragen Yaki Na Kasar Amurka Harry Truman Zai Fice Daga Tekun Maliya
  •  Falasdinawa 40 Sun Yi Shahada A Cikin Sa’oi 24 A Gaza
  • Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Na Iran Ya Ce: Maganar ‘Yan Sahayoniyya Rudu Ne Maras Amfani
  • Sabbin Bayanai Kan Fashe-Fashe Wasu Abubuwa A Tashar Jiragen Ruwan Kasar Iran
  • Har Yanzun Ana Zaman Dar-Dar A Burkina Faso Bayan Kokarin Juyin Mulkin Da Bai SamiNasara Ba
  • Shugaban Kungiyar Hizbullah Ya Abbaci Abubuwa 3 Wadanda Yakamata Kasar Ta Maida Hankali A Kansu
  • Jiragen Yakin Amurka Sun Kashe Mutane Da Dama A lardin Sa’ada Na Kasar Yemen
  • Lebanon:  Isra’ila Ta Kai Hari Akan Unguwar Dhahiya A Birnin Beirut
  • Uganda Ta Sanar Da Kawo Karshen Ebola Da Ta Barke A Kasar