Aminiya:
2025-09-18@02:18:00 GMT

Ra’ayin Jama’a kan ziyarar Tinubu Katsina

Published: 2nd, May 2025 GMT

A yau Juma’a 2 ga watan Mayu, 2025 Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ke ziyartar Jihar Katsina a karon farko tun bayan hawansa kujerar mulki.

Kamar yadda gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umar Raɗɗa ta ce, shugaban zai duba wasu muhimman ayyukan da gwamnan ya aiwatar da waɗanda ake cikin yi.

Wakilin mu ya tuntuɓi wasu daga cikin al’ummar jihar domin jin ra’ayoyinsu akan wannan ziyara.

Ya zo ɗaurin auren ’yar gwamna ne — Sabo Musa

Alhaji Sabo Musa shi ne mai bai wa Gwamna Raɗɗa shawara a kan wayar da kan al’umma a harkokin gwamnati, ya bayyanawa wakilinmu cewar, Shugaba Tinubu zai zo Katsina ne domin halartar ɗaurin auren ’yar Gwamna Raɗɗa wanda za a yi a ranar Asabar, 3 ga watan Mayu, 2025.

Wulaƙancin da ake mana a Kudu ya yi yawa —Hausawan Legas Gobarar rumbum makamai Maiduguri da Matakan da ya kamata a ɗauka — Ƙwararru

Akan haka ne aka yi amfani da wannan dama wajen gayyatar shi da ya ƙaddamar da wasu ayyukan da Gwamna Raɗɗa ya aiwatar da waɗanda ake cikin yi.

“Ai ka ga mu a yanzu sai mu ce wani abin alfahari ne ga jama’ar Jihar Katsina domin tun hawan shi mulki ita ce jiha ta farko da ya fara zuwa a Arewa inda ya amsa goron gayyata. Shi ya sa aka yi amfani da damar domin ya ziyarci wuraren da shi Gwamna ya aiwatar da kuma inda ake cikin aiwatar da wasu muhimman aiyuka.”

“A kan haka ma har shi Gwamna ya ba mutanen da ke kusa da masallacin da za a yi wannan ɗaurin aure haƙuri a kan ɗan ƙuncin da za su gani a wannan lokacin. Sannan ya yi kira ga al’umma da su fito domin tarbar shugaban kamar yadda aka san Katsina ɗakin kara ce”, in ji Sabo Musa.

Mun yi zaton ziyarar aiki ce kawai

Mafi yawan mutanen da muka tuntuɓa a kan wannan ziyara sun ce sun yi zaton ziyarar aiki ce.

Malam Halliru ya ce, “farko na yi zaton zai zo duba aikin hanyar da ta tashi daga Katsina zuwa Kano ce da aikin ya tsaya, da kuma batun wutar lantarki mai aiki da iska ta hanyar Rimi wadda ita ma ta yi tsaye cik.

Amma sai kawai na ji an ce, zai zo wajen ɗaurin auren ɗiyar Gwamna ne. Ke nan, babu wani abin a zo a gani da za mu ce na Gwamnatin Tarayya ne wanda ya zo a kan shi”.

Shi kuwa Abu Ƙasim cewa ya yi, ko ba komai a iya cewa jihar ta kafa tarihi daga cikin jihohin Arewa domin a nan zai fara kawo ziyarar yini biyu.

“Ina kyautata zaton cewa, a wannan ɗan lokacin ba zai rasa ganin wasu daga cikin dattawan jihar ba, inda za su bayyana mashi wasu abubuwan da jahar take ciki musamman batun matsalar tsaron da ta addabe mu. Sannan tunda inda zai je wajen duba aikin waccan hanya da aka yi magana wurin da wannan hanyar da aka yi watsi da aikin ta ne, Katsina zuwa Kano, zai ga irin halin da ake ciki da kuma irin ayyukan da shi Gwamna ke yi wanda ko makamantan su ita gwamnatin ta Tarayya ba ta yi su ba.

“Ka ga akwai maganar aikin hanyar jirgin ƙasan da ake cewa wai an dakatar, nan ma ina zaton jama’a za su san irin halin da ake ciki. Na kuma san ƙila zai ɗan yi jawabi a wajen buɗe wancan aiki, ƙila ya faɗi wani abu mai muhimmanci da jahar zata amfana.”

Malama Rabi, wata mai sayar da abinci, ta ce, “ni ina zaton samun abokan ciniki kawai saboda shigowar baƙi, amma in baya ga haka sai in ce banga tasirin wannan ziyara ba. Shugaban da aka ce batun ɗaurin aure ne ke jigon zuwanshi, to me za ka yi zato daga gare shi? Amma muna fata ziyarar ta zamo wani mabuɗin alheri ne ga al’ummar jihar da Jihar baki ɗaya”, in ji ta.

Gwmnatin jahar ta sanar da ranar Juma’a a matsayin ranar hutu ga ma’aikata domin ba su damar tarbar shugaban ƙasa tare da halartar wajen da zai ƙaddamar da waɗannan ayyuka.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ɗaurin Aure

এছাড়াও পড়ুন:

NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Matakin hana malaman da ba su da rajista hawa mumbari a Neja yana ci gaba da yamutsa hazo a ciki da wajen jihar.

Yayin da wasu suke ganin wannan mataki bai dace ba, wasu kuwa gani suke faduwa ta zo daidai da zama, wato matakin ya zo a daidai lokacin da ake bukata.

NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Uku

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kan tanadin Dokar Kasa game da wannan batu.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Kammala Ziyarar Yini 3 A Ma’aikatar Kananan Hukumomin Jihar
  • Microsoft ya ƙwace shafukan wasu kamfanoni 340 a Najeriya
  • Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
  • Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Baje Kolin Sin Da ASEAN Ya Fadada Matsayar Bai Daya Ta Cudanyar Sassa Daban Daban
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima
  • Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo
  • DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya
  • NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba
  • An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar