HKI Ta Yi Barazanar Shiga Rikicin Da Ya Barke A Garin Jarmana Na Kasar Syria
Published: 2nd, March 2025 GMT
Kafafen watsa labarun HKI sun sanar da cewa sojoji a shirye suke su shiga cikin rikicin da ya barke a garin Jarmana dake kusa da birnin Damascuss na kasar Syria domin kare ‘yan Duruz.
Ofishin Fira ministan HKI Benjemine Netanyahi ya fitar da sanarwa a jiya Asabar da marece, yana ce; Netanyahu da ministansa na yaki Yesra’il Kats sun bayar da umarni ga sojojin kasar da su kasance cikin shiri domin kare ‘yan Duruz a garin Jarmana dake bayan binin Damascuss.
Ofishin watsa labarai na ministan yakin na HKI ya ce; Nauyi ne a wuyanmu mu kare ‘yan’uwanmu Duruz a cikin Isra’ila, da kuma hana a cutar da su a cikin Syria, don haka za mu dauki duk wani mataki da ya dace domin kare tsaronsu.”
Bayan kashe jami’an tsaron kasar Syria biyu, jami’an tsaron sun shiga cikin garin domin neman masu laifi,lamarin da ya haddasa taho-mu gama da makamai.
Kamfanin dillancin labarun Reuters, ya bayyana cewa; HKI ta bukacin Amurka da ta daina yin matsin lamba ga Rasha ta bar Syria saboda ta kalubalanci kwadayin Turkiya na shimfida nata ikon a wannan kasa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Tarayyar Afirka ta dage takunkumin da ta kakabawa Gabon
Kungiyar Tarayyar Afirka ta dage takunkumin da ta kakabawa kasar Gabon tare da maida ta a cikin cibiyoyinta.
AU, ta sanar da hakan ne yayin taron kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar yau Laraba a Addis Ababa.
Hakan dai ya karshen dakatarwar da aka yi wa kasar ta Gaban daga kungiyar, watanni 20 bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Agustan 2023.
Kwamitin zaman lafiya da tsaro na AU, ya yi la’akari da mika mulki da ya hambarar da Ali Bongo “gaba daya cikin nasara,” saboda haka ya yanke shawarar dage takunkumin nan take.
‘’Tsarin siyasar Gabon yana da ” gamsarwa” inji sanarwar kungiyar.
Wannan matakin na AU ya zo ne kwanaki uku gabanin rantsar da Janar Brice Oligui Nguema, wanda aka zaba a matsayin shugaban kasar a ranar 12 ga Afrilu.