Jami’in tsaron al’umma 6 sun mutu a artabu da ’yan bindiga a Sakkwato
Published: 20th, February 2025 GMT
Mutum shida daga cikin Jami’an Tsaron Al’umma na Jihar Sakkwato sun kwanta dama bayan wata musayar wuta da ’yan bindiga a Kamarar Hukumar Sabon Birni.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa jami’an tsaron sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suka kai ɗauki ga al’umma da ’yan bindiga suka kai wa hari. A hanyarsu ne ’yan bindiga suka yi musu kwanton ɓauna.
Wata majiya ta bayyana cewa abokin aikinsu ne ya kira ya sanar da cewa, ’yan bindiga suna hanyarsu ta kawo hari ƙauyensi da ke kusa da Unguwan Lalle.
“Jami’an tsaron sun nemi abin hawa daga hukumar karamar hukumar amma an hana su, saboda an hana su gudanar da ayyukan tsaro na yau da kullum su kaɗai ba tare da jami’an tsaron gwamnatin ba,” in ji majiyarmu
Da ba su samu abin hawa ba, sai suka hau baburansu suka tafi ƙauyen, amma aka yi rashin sa’a, ’yan bindigar suka yi musu kwanton ɓauna.
“Sna musayar wuta da ’yan ta’adda kafin a kashe mutum shida daga cikinsu, waɗanda daga bisani aka kawo gawarwakinsu an yi musu jana’iza,” in ji majiyar.
Lokacin da aka tuntube shi, kwamandan Rundunar Tsaro ta Jihar Sakkwato, Kanar Na-Allah Idris, ya ƙi cewa komai kan harin.
Haka nan, shugaban majalisa, Alhaji Ayuba Hashimu da memba mai wakiltar Sabon Aminu Boza sun kasa amsa kiran wayar wakilinmu.
Memba, wakiltar Sabon Birni gabas, ya tabbatar da lamarin amma ya ƙi yin ƙarin bayani saboda yankin ba a ƙarƙashinsa yake ba.
An tuntuɓi kakakin ’yan sanda na Jihar Sakkwato, ASP Ahmad Rafa’i, inda ya ce ba shi da rahoto kan lamarin.
Mai ba da shawara na musamman ga gwamna Ahmed Aliyu Ahmed kan sha’anin tsaro, Ahmed Usman ya tabbatar da harin, kuma ana ci gaba da bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Jami an Tsaro kwanton ɓauna yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
Daga Ali Muhammad Rabi’u
Gwamnatin Jihar Kwara ta kafa kwamitoci biyu domin tantance bayanan wadanda suka yi ritaya a matakin jiha da kananan hukumomi.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinar Kudi ta jihar, Dakta Hauwa Nuru ta fitar, ta bayyana cewa kwamitocin za su tantance tare da tabbatar da sahihancin bayanan wadanda suka yi ritaya, domin a biya su bisa lokacin da suka bar aikin gwamnati.
A cewarta, kwamitin mutum takwas da aka kafa don kula da kudaden ritaya na matakin jiha zai kasance karkashin jagorancin Mai Duba Asusun Jiha, wato (Auditor General), yayin da wanda ke kula da matakin kananan hukumomi zai kasance karkashin Mai Duba Asusun Kananan Hukumomi.
Sanarwar ta bayyana cewa babban burin kwamitocin shi ne tabbatar da cewa an tattara bayanan masu ritaya bisa gaskiya da adalci, tare da biyan su kai tsaye ta asusun ajiyar banki.
Ta kara da cewa, mambobin kwamitocin sun hada da wakilan tsofaffin manyan sakatarorin, kungiyar tsofaffin ma’aikata, Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), da kungiyar kwadago ta TUC, da sauransu.