Aminiya:
2025-08-01@15:19:09 GMT

An soma rigimar haraji tsakanin China da Amurka

Published: 5th, February 2025 GMT

A bayan nan ne Amurka ta sanya harajin kashi 25 a kan kayayyakin da ake shigar wa ƙasar daga Canada da Mexico da kuma kashi 10 kan kayayyakin makamashi na Canada, yayin da kayayyakin China za su fuskanci harajin kashi 10.

Sakatariyar yaɗa labaran Fadar White House, Karoline Leavitt, ce ta bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai a ranar Juma’a.

Dalilin da farashin citta ya yi tashin gwauron zabo Hausawa sun yi bikin cika shekara 153 da zama a garin Owerri

Ta bayyana cewa “Canada da Mexico suna ba da damar shigar da muguwar ƙwayar nan ta fentanyl da ke kashe Amurkawa da kuma baƙin haure ba bisa ka’ida ba zuwa kasar mu.”

Ta ce Shugaba Donald Trump ya ba da umarnin wanda zai soma aiki daga ranar Talata, domin magance matsalar shigar da maganin kashe raɗaɗi na fentanyl da matsalar ‘yan gudun hijira da ke shiga Amurka ba bisa ƙa’ida ba.

“Shugaba Donald Trump na ɗaukar ƙwararan matakai don kare Amurkawa daga matsalar maganin na fentanyl. Fentanyl shi ne kan gaba wajen sanadin mutuwar Amurkawa masu shekaru 18 zuwa 45,” in ji Leavitt.

Amurkan dai ta zargi masu safarar miyagun ƙwayoyi na Mexico da kasancewa “kan gaba a duniya wajen safarar” fentanyl da sauran ƙwayoyi, yana zargin akwai ƙawance tsakanin masu safarar da gwamnatin Mexico.

Game da Canada, Fadar White House ta yi ƙarin haske game da ƙaruwar samar da maganin na kashe raɗaɗi na fentanyl da kuma tsallaka wa da shi kan iyaka ba bisa ƙa’ida ba, tana mai cewa: “an kama fentanyl a kan iyakar Arewa a bara wanda zai iya kashe Amurkawa miliyan 9.8.”

An soki China saboda zargin tana taka rawa wajen bayar da tallafi ga kamfanonin sinadarai wajen fitar da fentanyl zuwa ƙasashen waje, inda Fadar White House ta yi iƙirarin cewa: “ba wai kawai China ta gaza wajen daƙile tushen haramtattun ƙwayoyi ba, har ma tana taimaka wa wannan kasuwanci.”

Martanin Canada da Mexico

Ƙasashen Canada da Mexico sun sanar da ɗaukar matakan ramuwar gayya kan harajin da Shugaba Trump ya ɗora wa kayayyakinsu.

A ranar Asabar, Firaminista Justin Trudeau ya ce Canada za ta sanya harajin kashi 25 kan kayayyakin Amurka da suka kai dala biliyan 106.5 a matsayin martani ga harajin Amurka.

Harajin dala biliyan 20 zai fara aiki daga ranar Talata, sannan na dala biliyan 86 zai fara aiki a cikin kwanaki 21, kamar yadda Trudeau ya shaida wa wani taron manema labarai.

Trudeau ya yi gargaɗin cewa harajin zai cutar da Amurka, wacce daɗaɗɗiyar ƙawar ƙasar ta Canada ce.

Ya nemi mutanen Canada su riƙa sayen kayayyakin da aka yi a ƙasar, kuma su riƙa gudanar da hutu a gida maimakon a Amurka.

Ya ce ana kuma duba wasu matakan da ba na haraji ba, da suka haɗa da wasu da suka shafi ma’adanai masu mahimmanci da sayen makamashi da sauran ɓangarorin haɗin gwiwa.

Trudeau ya kuma ƙara da cewa, ƙasashen Canada da Mexico suna aiki tare don fuskantar harajin da Washington ta ɗora wa kayayyakinsu.

Fadar White House ta ce manufar harajin ita ce matsa wa Mexico da Canada da China lamba su ƙara ba da haɗin kai kan daƙile shigar da miyagun ƙwayoyi da tsaron kan iyakoki da hana kwarar baƙin haure shiga ƙasar ta ɓarauniyar hanya.

China ta bi sahu

China a wani mataki na ramuwar gayya ta lafta wa Amurka harajin kaso 15 cikin 100 na kayayakin kwal da na makamashin gas da ake shigar da shi kasar daga Amurka.

Ƙarin harajin a cewar Ma’aikatar Kuɗin Beijing zai fara aiki ne a makon gobe.

A cikin sanarwar da ta fitar ta ɗaukar matakan ramuwa, China ta zargi Amurka a ƙarƙashin Donald Trump da karya ƙa’idojin kasuwanci na ƙasa da ƙasa.

“Gaban kai da Amurka ta yi ita kaɗai ta lafta haraji ya saɓa ƙa’idojin Hukumar Kasuwaci ta Duniya. Wannan ya saɓa wa yarjeniyoyin kasuwanci da tattalin arziƙi tsakanin China da Amurka.”

Bugu da ƙari China ta sanar matakin fara bincike a kan kamfanin fasaha na Google.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Fadar White House

এছাড়াও পড়ুন:

DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Wasu al’ummomi sun bayyana dalilan da suka sa suka karbi tsarin yin gwajin lafiyar ma’aurata kafin a daura musu aure.

A wasu lokutan, akan samu matsaloli sakamakon rashin gwajin jini kafin a hada mace da na miji aure. Matsalolin sun hada da yaduwar cututtuka, samun ‘ya’ya marasa lafiya da sauran wasu matsalolin.

NAJERIYA A YAU: Yadda Za A Dama Da Matan Arewa A Fannin Kimiyya DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makaranta

Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu alummomin suka rungumi yin gwajin jini kafin aure.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Afirka ta Kudu na shirin daukar matakan kauce wa tasirin harajin Amurka
  • Matsayar Bai Daya Da Sin Da Amurka Suka Cimma Ta Fuskar Haraji Na Da Babbar Ma’ana
  • Canada Zata Amince Da Samuwar Kasar Falasdinu A Taron MDD
  •  Shugaban Kasar Lebanon Aun Ya Ce Mun Aike Wa  Amurka Sakwanni Akan Dakatar Da Hare-haren HKI
  • Dalilan Da Suka Sa Canada Ta Goyi Bayan Kafa Kasar Falasɗinu
  • Sin Ta Dade Tana Aiki Tukuru Kan Kiyaye Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali Na Yanki
  • Amurka Ta Ce HKI Ba Zata Fice Daga Kasar Lebanon Ba Sai An Kwance Damarar Hizbullah
  • Gidauniyar ‘Ya’yan Sarakunan Arewa Sun Marawa Sarkin Musulmi A Matsayin Shugaban Majalisar Sarakuna
  • DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure
  • Fiye Da Kamfanoni 30,000 Masu Zuba Jari Daga Waje Aka Kafa A Sin A Rabin Farkon Bana