Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce za ta karfafa kyakkyawar alakar da ke tsakaninta da asusun horar da ma’aikata ITF.

Shugaban ma’aikata na jihar Alhaji Muhammad K Dagaceri ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban asusun horas da ma’aikata na yankin arewa maso yamma, Malam Aminu Abdu a ofishinsa.

A cewarsa, gwamnatin jihar tana sane da muhimmancin da asusun ke da shi,  musamman ga ma’aikatan da aka horas da su domin samun kwarewa a fanninsu.

Dagaceri, ya tabbatar wa shugaban asusun cewa, gwamnatin jihar za ta ci gaba da bayar da dukkan goyon baya da hadin kai ga sabon ofishin na ITF da aka kafa a yankin Jigawa.

Tun da farko, Shugaban Asusun na Arewa maso Yamma, Malam Aminu Abdu ya ce sun kawo ziyarar ne a madadin babban daraktan asusun, domin nuna jin dadinsu ga Gwamna Umar Namadi bisa yadda ya samar wa sabon ofishinsu da aka kafa a yankin na Jigawa.

Aminu Abdu ya kara da cewa, asusun ya horar da ma’aikata a fadin kasar nan, kuma kwalliya na biyan kudin sabulu.

Usman Muhammad Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

Kwamatin Tantance Ayyukan Kananan Hukumomi Na Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ya Isa Sule Tankarkar

Shugaban kwamitin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa, Alhaji Aminu Zakari, ya ce kwamatin ya jinkirta rangadin kananan hukumomin jihar 27 a Zango na uku na shekarar 2024 ne a sakamakon zaben kananan hukumomi, don haka akwai bukatar ba su damar gudanar da ayyuka kafin tantance kwazon su.

 

Alhaji Aminu Zakari ya yi wannan tsokaci ne a sakatariyar karamar hukumar Sule Tankarkar a ci gaba da rangadin kananan hukumomi da kwamatin yake yi.

 

A cewar sa, kwamatin zai tantance kasafin kudin karamar hukumar na shekarar 2024 da 2025 na ayyuka ta da jerin ayyukan raya kasa, da  takardun biyan kudaden ayyukan da littafin ta’ammalin kudaden na banki.

 

Yace kwamitin zai tantance takardun kudaden shiga tare da duba kudin tarukan bangaren zartaswa da na kansiloli domin tabbatar da bin ka’idojin kashe kudaden gwamnati.

 

Karamin kwamati na daya bisa jagorancin wakilin mazabar Kanya Babba Alhaji Ibrahim Hashim Kanya ya duba aikin masallacin kamsissalawati na Rugar Danqulili, da famfunan tuka tuka a Gabala/Dangwanki da Yanyawai da Fulanin Tagai da Rugar Hardo Daudu da gidan ungozoma a asibitin Jeke, da shirin noman rani a Maitsamiya.

 

Kazalika, kwamati na biyu bisa jagorancin wakilin mazabar Guri Alhaji Usman Abdullahi Tura Musari ya duba aikin gidan ruwa mai amfani da hasken rana a unguwar Sule Gabas da masallacin Juma’a na Hammado da makarantar Tsangaya a Danladi, da masallaci kamsissalawati na gidan mulki na Shugaban karamar hukumar da famfon tuka tuka na Gidan Idi Ruwa.

 

A nasa Jawabin, Shugaban karamar hukumar Sule Tankarkar Malam Tasi’u Adamu, Ya lura cewar, tantance sha’anin mulki da harkokin kudin kananan hukumomi ko shakka babu zai taimaka wajen kawo ci gaban yankunan karkara.

 

Malam Tasi’u Adamu ya kuma yi addu’ar samun nasarar ziyarar kwamatin domin ta yi tasiri wajen kawo cigaban rayuwar jama’ar yankin.

 

Usman Mohammed Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hukumar Kula da Da’ar Ma’aikata Za Ta Fara Daukar Bayanai Ta Yanar Gizo
  • Kwamatin Tantance Ayyukan Kananan Hukumomi Na Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ya Isa Sule Tankarkar
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar da Tallafin Miliyoyin Naira Ga Ƴan NURTW da Mahauta a Jigawa
  • Gwamnatin Jihar Kano Ta Kaddamar da Manufar Sauyin Yanayi
  • Gwamnatin Tinubu ta mayar da Arewa saniyar ware – ACF
  • Gwamnatin Sakkwato Ta Sayo Manyan Tan-tan 250 Na Sama Da Naira Biliyan 22
  • Gwamna Namadi Ya Naɗa Shugabannin Hukumar Hisbah Ta Jihar Jigawa
  • Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Na Da Kwamitoci 30 Da Ke Sa Ido Kan Ma’aikatun Gwamnati
  • Wani mutum ya mutu yayin raba faɗar ma’aurata 
  • Gwamna Namadi Ya Biya Sama Da Naira Biliyan Daya Ga Tsofaffin Ma’aikata