Manchester United za ta ɗauki golan Antwerp, Senne Lammens
Published: 2nd, September 2025 GMT
Manchester United ta amince za ta ɗauki golan tawagar Belgium, Senne Lammens daga Royal Antwerp kan fam miliyan 18.1 har da karin tsarabe-tsarabe.
Sasashen wasanni na BBC ya ruwaito cewa hakan ya kawo karshen zawarcin golan Aston Villa, Emiliano Martinez da ta yi.
An kama uba da ɗansa kan yi wa ’yar shekara 13 fyaɗe a Gombe An kama ɗan shekara 60 kan yi wa mai shekara 24 fyaɗeLammens, mai shekara 23, zai saka hannu a ƙungiyar Old Trafford kan yarjejeniyar kaka biyar.
United na fatan ɗinke ɓarakar gurbin mai tsaron raga, bayan da Altay Bayindir ke kuskure a wasannin Firimiya, yayin da ake zargin Andre Onana da sakacin da ya janyo aka fitar da United a Carabao Cup a hannun Grimsby.
Lammens ya koma Antwerp a matakin mara ƙunshin yarjejeniya daga Club Brugge a 2023, wanda ya tsare raga karo 64 a Antwerp da lashe Belgian Super Cup a 2023.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Royal Antwerp
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
Ya ce ya sayi layin wayar ne daga hannun wani Audu, ɗan kungiyar Vikings wanda ya tsere yanzu.
A wani lamari kuma, ‘yansanda sun kama wasu mutum huɗu da suka shiga gonar wani mutum a Lapai Gwari, inda suka saci kifi da darajar kuɗinsu ta kai Naira 750,000.
Babban wanda ake zargi, Hussaini Garba, ya amsa laifi tare da bayyana Ahmed Yusuf, Ibrahim Musa da Abdulazeez Bawa a matsayin mutanen da suke sayen kifin idan ya sato.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp