An kama uba da ɗansa kan yi wa ’yar shekara 13 fyaɗe a Gombe
Published: 1st, September 2025 GMT
Jami’an Hukumar Sibil Difens (NSCDC) sun cafke wani mutum mai shekaru 48, Ibrahim Haruna, tare da ɗansa mai shekaru 15, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 13 fyaɗe a unguwar Jekadafari da ke Jihar Gombe.
Wakilinmu ya ruwaito cewa an gabatar da waɗanda ake zargin ne a hedikwatar hukumar a ranar Litinin.
Mai magana da yawun hukumar a jihar, SC Buhari Sa’ad, ya ce bisa binciken da suka gudanar, uban da ɗan sun aikata laifin ne a lokuta daban-daban.
A cewarsa, Ibrahim Haruna wanda tela ne ya yi aika-aika ne a shagonsa na ɗinki, yayin da ɗansa kuma ya aikata laifin a cikin gidan da suke zaune.
“Mun kammala binciken da muke gudanarwa, kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar hukunci,” in ji Sa’ad.
Sai dai Ibrahim Haruna, yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai, ya musanta zargin, inda ya bayyana cewa kawai ya taɓa yarinyar ya yi a cikin wasa, amma bai yi mata fyaɗe ba.
Hukumar ta ɓoye sunan yarinyar da abin ya shafa don kare mutuncinta da kuma ƙa’idojin kare haƙƙin yara da dokokin kare ‘yancin ɗan Adam suka tanadar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗa fyaɗe jihar Gombe yarinya
এছাড়াও পড়ুন:
Ana zargin ɗa da kashe mahaifinsa a Kano saboda hana shi ƙara aure
Babbar Kotun Kano mai lamba 7 da ke zama a cikin birni ta bayar da umarnin tsare Aminu Ismail, mazaunin Unguwar Bai a Karamar Hukumar Ajingi ta jihar, bisa zarginsa da kashe mahaifinsa, Malam Dahiru Ahmad, ta hanyar caka masa wuƙa har lahira.
Lamarin ya faru ne bayan samun sabani tsakaninsu kan aniyar Aminu ta ƙara aure, wadda mahaifinsa ya ƙi goyon baya saboda abin da ya kira halin tattalin arzikin da ake fama da shi a kasa.
Babu wani uzuri da za a yi wa sabbin hafsoshi kan matsalar tsaron Nijeriya — Tinubu Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – ZulumA cewar lauyan masu ƙara, Barrista Lamido Abba Sorondinki, wanda ake tuhuma ya shaida wa mahaifinsa niyyarsa ta kara mata ta biyu, amma mahaifinsa ya ba shi shawarar kada ya yi hakan, yana mai danganta matsalar da halin tattalin arzikin ƙasa ke ciki.
Wannan sabani ya rikide zuwa faɗa, inda ake zargin Aminu da caccaka wa mahaifin nasa wuƙa a ƙirji, lamarin da ya jawo masa rauni mai tsanani har ya rasa ransa.
An gurfanar da Aminu da laifin kisan kai, wanda ya saba da Sashe na 221 na kundin penal code.
Ana ci gaba da shari’ar, kuma kotu ta bayar da umarnin tsare shi har zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraron ƙarar.