Aminiya:
2025-11-02@12:28:46 GMT

Manchester City ta ɗauki golan PSG, Gianluigi Donnarumma

Published: 2nd, September 2025 GMT

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City ta ɗauki mai tsaron ragar PSG, Gianluigi Donnarumma ɗan asalin ƙasar Italiya.

Donnarumma wanda tsohon mai tsaron ragar AC Milan ne ya sanya hannu kan kwantiragin shekara biyar a Etihad, inda zai zai ci gaba da tsare ragar ƙungiyar zuwa kakar 2030.

Ndume ya koka kan sabbin hare-haren Boko Haram a Borno Kemi Badenoch ta shiga tsaka mai wuya kan karatun likitanci

Golan zai riƙa amfani da riga mai lamba 99 domin ranar haihuwarsa ta 1999, kamar yadda ƙungiyar ta sanar.

A jawabin da ya yi dangane da komawa ƙungiyar, Donnarumma ya ce yana cike da farin ciki da jin daɗi.

“Na koma ƙungiya da ke cike da zaratan ’yan wasa, sannan kuma ƙungiya ce da ke samun horo daga ɗaya daga cikin zaratan masu horar da ’yan wasan ƙwallon ƙafa da aka yi a tarihin tamaula a duniya wato Pep Guardiola.

“Na daɗe ina sha’awar Manchester City. Don haka komawa ƙungiyar abin alfahari ne a gare ni. Buga ƙwallo a filin wasan Etihad zai zama abin alfahari ne a waje na.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gianluigi Donnarumma

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi

Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da fasinjoji a cikin wasu motocin bas Toyota guda biyu a titin Itobe zuwa Ajegwu-Anyigba a Ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kogi.

An samu rahoton cewa, lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 5 na asubahi a tsakanin ƙauyukan Ojiwo’-Ajengo da Mamereboh da ke kan babbar hanyar.

Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasa

An ce masu garkuwa da mutanen sun yi amfani da wata tirela da aka kama wajen tare hanyar bayan shingen binciken jami’an tsaro, da ke kusa da wurin da lamarin ya faru.

Shedun gani da ido sun ce ɗaya daga cikin motocin bas ɗin mai lamba KG: KPA 622LG na kan hanyarta zuwa Abuja, tare da fasinjoji daga wata tashar mota a unguwar Ankpa da ke yankin Kogi ta Gabas.

Har yanzu ba a iya gano adadin fasinjojin da aka yi garkuwa da su ba zuwa yanzu, sai dai mun iya tabbatar da cewa ɗaya daga cikin motocin na ɗauke da fasinjoji ne daga yankin Ankpa, kamar yadda aka gano wasu takardu da wasu kayayyaki a wurin da lamarin ya faru suka bayyana.

“Motocin bas ɗin guda biyu suna kan hanyar Abuja ne a lokacin da suka ci karo da shingayen ’yan bindiga a safiyar ranar Alhamis. Dukkanin fasinjojin, ciki har da direban motocin bas ɗin biyu an yi awon gaba da su cikin daji,” in ji Unubi Ademu, wani mazaunin Achigili, a ƙauyen da ke maƙwabta.

Al’ummar yankin sun ƙara da cewa, jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji da mafarauta da kuma ’yan banga suna ƙoƙarin magance lamarin.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Kogi (PPRO), CSP William Aya bai amsa kira da saƙo ba lokacin da aka tuntuɓe shi har zuwa lokacin tattatara wannan rahoto.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada
  • Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025?
  • Kofin kofi mafi tsada a duniya ya shiga kasuwa a kan Naira miliyan 1.5m
  • ’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
  • NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa
  • Allah Ya Kai Manzon Allah (SAW) Muƙami Na Babban Yabo A Cikin Komai
  • Juventus ta ɗauki tsohon kociyan Italiya, Luciano Spalleti
  • Barcelona Na Shirin Ɗauko Victor Osimhen Na Galatasaray
  • Ƙwallo ta kashe ɗan wasan Cricket
  • Ƙungiyar Rays Heaven ta Ƙarfafa Wayar da Kai kan Lafiyar Kwakwalwa a Kaduna