2025-11-03@12:25:39 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7527

«Kwasar man fetur»:

      Kwankwaso, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na NNPP a zaben 2023, ya fitar da wata sanarwa mai karfi yana gargadin cewa kalaman Trump na iya kara ruruta wutar rikicin addini da kuma kara ta’azzara rashin tsaro a kasar.   A shafinsa na X, tsohon gwamnan ya yi Allah-wadai da matakin Trump na...
    Daga Aminu Dalhatu Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa Shugaban Karamar Hukumar Gusau, Alhaji Abubakar Imam, bisa shirin tallafawa jama’a domin dogaro da kai da kuma inganta rayuwarsu. Ta yi wannan yabo ne yayin bikin kaddamar da kayan tallafi a Gusau, babban birnin jihar Zamfara. Hajiya Huriyya Dauda Lawal...
    Daga Usman Mohammed Zaria Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Injiniya (Dr.) Muhammad Uba, ya yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, bisa amincewa da sabbin ayyukan gina hanyoyi a fadin jihar, ciki har da na Birnin Kudu. Ya ce wannan mataki na cikin ajandar gwamnati 12, musamman wajen inganta ci gaban ababen more rayuwa....
    Ana ta ce-ce- ku-ce kan batun da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na kawo dakarun kasar sa Najeriya don taimakawa wajen yaki da matslar tsaro.   Yayin da wasu ke ganin hakan abun san barka ne, wasu kuwa tofin Ala tsine suka yi ga wannan batu. Shin ko me zai faru idan aka...
    Har ila yau, majalisar ta amince da Naira biliyan 3.3 don ayyukan samar da ruwa da makamashi domin inganta samar da ruwa mai tsafta da aminci a cikin al’ummomin birane da karkara.   Daga cikin ayyukan samar da ruwan, an amince da gina tashar tace ruwa ta zamani a Taliwaiwai da ke ƙaramar hukumar Rano,...
    Shugaba Donald Trump, ya jaddada cewa Amurka na iya tura sojoji ko ƙaddamar da hare-hare a kan Najeriya idan har kashe-kashen da ya ce ana yi wa Kiristoci suka ci gaba. A yayin tattaunawa da manema labarai da kuma saƙonnin da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Mista Trump ya ce ba zai zauna yana...
    Sabon rikici ya kunno kai a Jam’iyyar PDP yayin da ɓangarori biyu da ke taƙaddamar — na Umar Iliya Damagum, muƙaddashin shugaban jam’iyyar, da na Samuel Anyanwu, sakataren jam’iyyar na ƙasa — ke shirin mamaye hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja yau Litinin. A ranar Asabar, yayin da Damagum da wasu mambobin Kwamitin Ayyuka na Ƙasa...
    Wani magidanci, Malam Jibrin Rabi’u, ya bayyana yadda matarsa, Khadijat Ado, ta ɓace a gidansu da ke unguwar Life Camp a Abuja a ranar Alhamis da ta gabata, sannan kuma aka gano ta a Sakkwato washegari. Ya shaida wa wakilinmu da yammacin Lahadi, cewa ya dawo gida a ranar Alhamis, sai ya tarar da matarsa...
    Ministar Jin Dadin Jama’a ta Sudan, Salma Ishaq, ta bayyana cewa Mayakan (RSF) sun kashe mata kusan 300 tare da yi wa 25 fyade a El Fasher, babban birnin Jihar Darfur ta Arewa a yammacin Sudan, a matsayin wani bangare na ayyukan kisan kiyashin da suke aikatawa a yankin. A ranar 26 ga Oktoba, dakarun...
    Daga Yusuf Zubairu Kauru  Al’ummar Karamar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna sun shiga halin kaka-ni-ka-yi duba da yadda rayukansu ke kasancewa cikin hadari yayin da suke gonakinsu. A wata tattaunawa ta wayar tarho, wani jagoran matasa, Junaidu Ishaq, ya bayyana cewa kusan shekaru biyar ke nan da hare-haren ’yan bindiga ke ta faruwa akai-akai, wanda...
    Kwankwaso ya kuma buƙaci gwamnatin Tarayya da ta ƙarfafa hulɗar diflomasiyya da Amurka ta hanyar naɗa jakadu na musamman da kuma jakadun dindindin domin kare muradun Nijeriya a matakin ƙasa da ƙasa. “Ya kamata gwamnatin Nijeriya ta naɗa jakadu na musamman da kuma jakadun dindindin domin wakiltar muradunmu yadda ya kamata a kasashen waje,” in...
    Wani fursuna mai suna Abba Hassan, wanda aka yanke wa hukuncin kisa, ya tsere daga gidan gyaran hali na Potiskum da ke Jihar Yobe. Rundunar ’yan sanda ta Jihar, ta tabbatar da wannan lamari a cikin wata sanarwa da kakakinta, DSP Dungus Abdulkarim, ya fitar a ranar Asabar. Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai...
    Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya ɗauki mataki mai tsauri a kan Shugaban Amurka, Donald Trump, game da barazanar da ya yi na amfani da ƙarfin soja a kan Najeriya. Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, malamin ya bayyana cewa...
    Da yake kaddamar da shirin, Darakta Janar na IRM, Alhaji Anas Muhammad, ya ce an kirkiro da shirin ne domin karfafa zaman lafiya da hadin kai ta hanyar tallafa wa Musulmai da Kiristoci ta bangaren samar da kiwon lafiya da bayar da tallafin kayan abinci da jari.   Ya ce: “Kalubalen lafiya ba sa bambance...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya. Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci. Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya. Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci. Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran...
    Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Isra’ila ba za ta kai hari kan Iran ba sai da goyon bayan Amurka Ministan harkokin wajen Iran Seyyed Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ba za ta kaddamar da yaki kan Jamhuriyar Musulunci ba tare da samun wata kariya daga Amurka ba. Ya kara da...
    Sakataren Majalisar Tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Ba suna cewa ba za su gudanar da tattaunawa ba ne, amma tattaunawar dole ta kasance ta gaskiya Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran, Ali Larijani, ya tabbatar da cewa: Ba za a iya kwantar da hankalin makiya ta hanyar yin sassauci da rashin gindaya sharaɗi ba....
    Gwamnatin mamayar Isra’ila ta yanke hukuncin kisa kan masu fama da cutar kansa da kuma waɗanda suke fama da matsalar koda na mutuwa a Gaza domin hana fitar da su wata kasa don neman magani Cibiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Gaza ta bayyana matukar damuwarta game da tabarbarewar lafiyar marasa lafiya da ke fama...
    Wani sojan Ƙasar Amurka ɗan asalin Jihar Kano, Suleiman Isah, wanda yake aiki a rundunar sojin Amurka, ya ce ba zai yaƙi da ƙasarsa ta haihuwa ba saboda yaɗa labaran ƙarya game da yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya. Isah, wanda ya shiga rundunar sojin Amurka shekaru biyu da suka gabata, yana aiki ne...
    Shi ma wasan da ta yi nasara a kan kungiyar Sifaniya a daf da za a tashi ta ci kwallon a gasar Zakarun Turai da na Newcastle United a Premier League. Tun daga nan alamomi suka fara bayyana cewar akwai tarin matsaloli a Liberpool, wadda kowanne wasa kwallo ke shiga ragarta in ban da wanda...
      Duk da cewa suna da karfi a fannin aikin soja, amma harinsu zai zama tamkar amfani da igwa ne wajen kashe sauro. Duk wani fifikon da suke da shi ba zai dore ba. Saboda haka, a zahiri wannan tambayar da wani mai amfani da yanar gizo ya yi, ta nuna rashin hankali cikin kalaman...
    Manajar  ofishin na NIWA,  da ke a jihar ta Legas Injiniya Sarat Braimah ta bayyana cewa, tura ma’ikatan hukumar domin yin aikin, zai taimaka wajen gudanar da aikin a cikin inganci. Kazalika, ya sanar da cewa, hakan zai kuma bayar da damar yin safarar kaya a cikin sauki da kuma safarar matafiya da ke bin...
    A yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan kalaman Shugaban Amurka Donald Trump da ke zargin gwamnatin Nijeriya da watsi da batun kisan Kiristoci a ƙasar, Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta bayyana cewa ta fara shirin kai farmaki a Nijeriya. Sakataren Ma’aikatar, Pete Hegseth, ne ya tabbatar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa...
      Da yake mayar da martani ga wannan zargin na Amurka, Bwala ya ce gwamnatin Tinubu tana jajircewa wajen kare dukkan ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da addini ba, yana mai cewa Amurka da Nijeriya sun dade suna hadin gwiwa a yaki da ta’addanci.   “Shugaba Bola Tinubu da Shugaba Donald Trump suna da...
     Babban dakaktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta Duniya ya tabbatar da cewa Iran ba ta kera makaman nukiliya ba, yana mai jaddada cewa tana ci gaba da kasancewa cikin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT). Rafael Grossi, ya shaida wa manema labarai a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York cewa “Zan iya...
    Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya musanta zargin da y ace karce ce ” da rundunar sojin Amurka (CENTCOM) ta yi cewa Hamas ta sace wata babbar mota dauke da kayan agaji. “Mun tabbatar da cewa wannan zargin karya ne, kuma wani bangare ne na manufar kafofin watsa labarai da nufin bata sunan...
    Fadar Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa nan da wasu kwanaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gana da takwaransa na Amurka, Donald Trump, domin tattaunawa kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya. Mai ba wa Shugaba Tinubu shawara na musamman kan yaɗa manufofi, Daniel Bwala, ne ya tabbatar da hakan a cikin wani saƙo da ya wallafa...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar amfani da ƙarfin soji kan Najeriya matuƙar gwamnatin ƙasar ba ta dakatar da kisan da ’yan ta’adda masu iƙirarin jihadi ke yi wa Kiristoci ba. A yammacin jiya Asabar ne Trump ya umarci Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta Pentagon da ta soma tsara yadda za a kai hari Nijeriya...
    Taron kaddamar da rabar da taraktocin noman, ya gudana ne a Shalkwatar Ma’aikatar Kula da Aikin noma da kuma yin Noman Rani da ke garin Kalaba.   Kazalika, taron ya samu halartar ‘yan Majalisa da Sarakunan Gargajiya da kungiyoyin manoma mata da masu ruwa da tsaki a fannin aikin noma da ke jihar da abokan...
    Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi a wata hira da yayi da gidan talabijin din Aljazeera ya gargadi isra’ila kuma yayi cikakkan bayani kan shirin nukiliyar iran na zaman lafiya , da kuma halin da yankin ke ciki da yi yuwar sake komawa teburin  tattaunawa da kasar Amurka. Wannan bayani yazo ne adaidai lokacin...
    Bug da kari Tinubu ya jinjina wa Shugaban jami’ar, Farfesa Wahab Olasupo Egbewole (SAN)da ‘yan tawagarsa wajen maida hankalin da suka yi na bunkasa Jami’ar da kumna kudurinta na muradun ci gaban da ake bukata. Shi ma anashi jawabin Shugaban Jami’ar Sarkin Katsina, Alhaji. Abdulmumin Kabir Usman, wanda Wazirin Katsina, Sanata Ibrahim Idah ya wakilta,...
    Shugaba Bola Tinubu ya mayar wa da Shugaban Amurka, Donald Trump martani cewa Najeriya ba ta yadda da duk wani nau’in zarafin addini. Tinubu, ya yi wannan bayani ne bayan Trump ya sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake kiran “Ƙasashen da ke da Babbar Matsala wajen ’Yancin Addini.” PDP ta dakatar da Anyanwu...
    An gudanar da taron tattaunawa na duniya kan kirkire-kirkire da bude kofa da ci gaba na bai daya, jiya Juma’a a birnin Lagos na Nijeriya. Yayin taron wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG da karamin ofishin jakadancin Sin dake Lagos suka shirya, ministan kula da harkokin matasa na Nijeriya Ayodele Olawande...
    Rikici a babbar jam’iyyar adawa ta PDP, na ƙara ƙamari, bayan da jam’iyyar ta dakatar da sakatarenta na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, da wasu da ake ganin ’yan tsagin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike ne. Mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba ne, ya sanar da dakatarwar bayan wani taro da...
    Rikici a babbar jam’iyyar adawa ta PDP, na ƙara ƙamari, bayan da jam’iyyar ta dakatar da sakatarenta na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, da wasu da ake ganin ’yan tsagin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike ne. Mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba ne, ya sanar da dakatarwar bayan wani taro da...
      Ban da haka, shugaban na Sin ya ce, kasarsa na son yin kokari tare da bangarori daban daban, wajen aiwatar da ra’ayin raya kasa na kirkiro sabbin fasahohi, da tabbatar da daidaito, da kare muhalli, da bude kofa, gami da haifar da alfanu ga kowa, ta yadda za a kafa wata al’ummar bai daya...
    Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya soki Shugaban Amurka, Donald Trump, bisa kiran Najeriya “ƙasa mai matsala ta musamman” kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Sani, ya ce kalaman Trump sun samo asali ne daga bayanan da ba su da tushe, da wasu mutane suka ba shi domin su tayar da...
    Daga Abdullahi Shettima Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya wakilci Nijeriya a taron ƙoli na biranen Asiya da ya gudana a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda ya gabatar da kudirorin sauyin ci gaban Kaduna. Taron ya samu halartar manyan baki daga ƙasashe sama da 150, ciki har da gwamnoni, shugabannin birane da jagororin...
    A wani bidiyo daban da PUNCH Metro ta gani a Facebook, wanda Mc Pee ya wallafa, wani mutum da ake zargin dalibi ne na jami’ar ya bayyana abin da ya faru. A cewarsa, marigayin ya roki a bar shi ya rayu kafin daga bisani wanda ake zargin ya kashe shi. Ya ce: “Nanpon ya riga...
    Daga Usman Muhammad Zaria   Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar. Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne...
    Jami’an diflomasiyya a Tanzania sun ce akwai kwararan hujjoji da ke tabbatar da an kashe akalla mutum 500 a cikin kwana biyu da barkewar zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zaben da aka gudanar a ranar Laraba. Sai dai a wani bangaren kuma, alkalumman Yan’adawa sun zarta haka. Wakiliyar BBC ta ce ministan harakokin wajen Tanzania...
    Daga Usman Muhammad Zaria   Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar. Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne...
    Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’ar nuna goyan baya ga wani kudiri da ya jaddada cewa shirin da Morocco ta gabatar kan Yammacin Sahara shi ne mafita ‘’mafi dacewa” ga yankin da ake takaddama a kai.   Kudirin ya nuna goyan bayan kasashe mambobin kwammitin ga shirin na Morocco, tare da bayyana cewa...
    Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani kan jawabin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi inda yake zargin kashe kiristoci a Najeriyar. A martanin da ta mayar, ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, ta ce lamarin ba haka ba ne. Sanarwar da kakakin ma’aikatar Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya sanya wa hannu, ta ce, “duk da cewa Najeriya...
    Tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isa, ta ƙaryata labarin da wata jaridar intanet ta yaɗa cewa wai tana son ta auri shahararren dan TikTok, Ashiru Mai Wushirya, wanda ya yi tashe a kafafen sada zumunta a ’yan kwanakin nan. A wani saƙo da ta wallafa, Mansurah ta ce labarin ƙarya ne kuma ya jefa ta da...
    Harkokin siyasa na Kudancin Kaduna ya dauki wani salo yayin da dan majalisar da ke wakiltar mazabar Jema’a/Sanga a majalisar tarayya, Hon. Dan Amos, ya sanar da komawarsa jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar PDP,  yana mai cewa ya dauki wannan mataki ne domin ya hada kai da gwamnatocin jiha da na tarayya don cigaban...
    Sanata Sunday Marshall Katung, wanda ke wakiltar mazabar Kaduna ta Kudu a majalisar dattawa, ya sanar da hukuncin da ya yanke na komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yana mai cewa wannan mataki ne da ya dace domin inganta aikin wakilci da kuma tabbatar da ƙarin haɗin kai ga al’ummar mazabarsa. A cikin wata sanarwa...
    Shugaba Samia Suluhu Hassan ta kasar Tanzania ta sake lashe zaɓen shugaban ƙasar mai cike da ruɗani. Hukumomin zaɓen ƙasar sun sanar da cewa Shugaba Samia Suluhu ta lashe zaɓen ne da kashi 97 na kuri’un da aka jefa. Hukamar zaɓen ƙasar ta bayyana cewa mutum 31,913,866 ne suka kaɗa kuri’a a zaɓen, wanda ya...