2025-11-27@23:01:54 GMT
إجمالي نتائج البحث: 203
«zaɓen cike gurbi»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya tabbatar da naɗin Sarkin Yarbawan Funtuwa, Oba Alhaji Murtala Sani Adeleke a matsayin sabon Sarkin Yarbawan Jihohin Arewa 19 har da Abuja. Mataimakin Gwamnan JIhar Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe ne ya tabbatar da naɗin a madadin gwamnan a lokacin da yake karɓar baƙuncin tawagar Sarakunan Yarbawan Arewa da suka miƙa masa takardar amincewarsu ga zaɓen Alhaji Murtala Sani Adeleke a matsayin sabon Sarkin Yarbawan Arewa a fadar gwamnati da ke Katsina. Ta kashe saurayinta saboda ya gaisa da tsohuwar abokiyar karatunsa Abba ya naɗa sabon Sakataren Gwamnatin Kano Gwamnan ya nuna matuƙar farin ciki da jinjina wa yadda aka gudanar da zaɓen shugabannin Majalisar Sarakunan Yarbawan na Arewa lami lafiya. Ya ce,...
Wata Babbar Kotu a Jihar Akwa Ibom, ta yanke wa Farfesa Ignatius Uduk hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan yari kan laifin sauya sakamakon zaɓe. An gurfanar da Farfesan kan tuhume-tuhume uku da suka haɗa da gazawa wajen aiwatar da aikinsa, sauya sakamakon zaɓe, da kuma yin rantsuwar ƙarya a gaban kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe. Ɗan sanda ya harbe kansa har lahira a Nasarawa Tinubu ya ƙara kasafin kuɗin 2025 zuwa N54.2trn Lamarin ya shafi zaɓen ‘yan majalisar jiha da aka gudanar a Essien Udim a shekarar 2019. A ranar Laraba ne, Mai shari’a Bassey Nkanang ya same shi da laifin sauya sakamakon zaɓe da yin rantsuwa bisa ƙarya. Hakan ya sa alƙalin ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekara uku...
Dakarun rundunar Operation Fansar Yamma sun ce sun ƙwato tarin makamai a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda na Jihar Zamfara. Dakarun tare da haɗin gwiwar jami’an tsaron farin kaya (DSS), sun kai samamen ne bayan samun bayanan sirri kan masu safarar makamai daga Jamhuriyar Nijar zuwa Najeriya. Tankar mai ta sake fashewa a Neja Jadawalin Gasar AFCON 2025 da za a fafata a Morocco Wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran rundunar, Laftanar-Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar, ya ce sun ƙaddamar da farmaki ranar 27 ga watan Janairun 2025, abin da ya kai ga ƙwato makaman kan hanyar Namoda zuwa Zurmi. Ya ce waɗanda ake zargin sun tsere zuwa cikin daji tare da barin motarsu bayan artabu da sojoji. Kanal Abubakar ya...
