Adadin waɗanda suka mutu a harin Filato ya kai 52
Published: 4th, April 2025 GMT
Adadin waɗanda suka mutu sakamakon hare-haren baya-bayan nan a ƙaramar hukumar Bokkos da ke Jihar Filato ya kai 52 kamar yadda hukumomin yankin suka bayyana.
Hakan ya biyo bayan sake gano wasu gawarwaki 40 ne a ranar Laraba da Alhamis da daddare yayin da masu aikin ceto suka ci gaba da kutsawa cikin dazuka don nemo waɗanda suka ɓata.
Shugaban Ƙungiyar al’adu ta Bokkos Cultural Development Council (BCDC) Vanguard, Farmasum Fuddang, ya shaidawa tashar Talabijin Channels cewa an yi jana’izar mutane 31 a ranar Alhamis tare da wasu yara biyar da suka ƙone ƙurmus a ƙauyen Hurti. An kashe wasu 11 a ƙauyen Ruwi, huɗu a ƙauyen Manguna tare da kashe mutum ɗaya a ƙauyen Daffo.
A cewar Ƙungiyar al’adu ta Vanguard, mazauna garin na jiran sakamako daga ci gaba da bincike da ceto mutanen da suka ɓata a ƙauyukan Hurti da Mbar.
Gwamnatin Jihar Filato ta yi Allah-wadai da hare-haren tare da yin kira da a kwantar da hankula saboda a halin yanzu ana ci gaba da ɗaukar matakan tsaro a yankunan da lamarin ya shafa.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a, kwamishiniyar yaɗa labarai da sadarwa ta jihar, Joyce Ramnap ta bayyana damuwarta game da sabbin hare-haren.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Sarkin Musulmi Ya Ayyana Ranar Talata 1 Ga Watan Zulki’ida
“Saboda haka, Litinin 28 ga Afrilu, 2025, za ta kasance 30 ga Shawwal 1446AH, yayin da ranar Talata 29 ga Afrilu, 2025 za ta zama farkon watan Zulki’ida 1446AH.”
Sanarwar ta ci gaba da cewa, Sarkin Musulmi na mika sakon fatan alheri ga al’ummar Musulmi, ya kuma bukace su da su ci gaba da yi wa kasa addu’ar zaman lafiya, hadin kai, da ci gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp