Jirgin Saman Da Kasar Sin Ta Kera Mai Amfani Da Lantarki Ya Yi Tashin Farko Cikin Nasara
Published: 21st, February 2025 GMT
A yau Jumma’a ne jirgin saman da kasar Sin ta kera samfurin AS700D mai amfani da makamashin lantarki ya kammala tashinsa na farko cikin nasara, wanda ya nuna sabon ci gaban da kasar ta samu a sashen samar da kayayyakin sufurin jiragen sama masu amfani da makamashi mai tsafta a fannin tattalin arzikin jirage masu tashi kasa-kasa daga doron kasa, kamar yadda kamfanin sarrafa jiragen sama na kasar Sin (AVIC) wanda ya kera jirgin ya sanar.
Kamfanin AVIC ya bayyana cewa, wannan muhimmin ci gaba ya tabbatar da girman iya kere-kere da ka’idoji na kasar Sin bisa kera jirgin na AS700D da kanta ba tare da sa hannun kowa ba, tare da samar da tanadin da ake bukata na fasaha don bunkasa kera jirage masu amfani da makamashin lantarki da za su biyo baya.
Jirgin na AS700D ya gudanar da tashin na farko ne da safiyar yau Juma’a a Jingmen na lardin Hubei da ke tsakiyar kasar Sin.
Bayanai sun nuna jirgin ya tashi sannu a hankali a tsaye sannan ya yi sauri ya nausa zuwa tsayin mita 50. Bayan ya yi shawagi a takaice, sai ya sauka a tsaye kana daga bisani ya tsaya sannu a hankali. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
এছাড়াও পড়ুন:
Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Bayan an mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, kasashen duniya sun soma zura ido kan kasar Sin. Ana sa ran cewa, taron APEC da za a gudanar a Shenzhen, zai kara habaka hadin gwiwa, da samun ci gaba, da wadata tare a shiyyar, kana zai shaida yadda kasar Sin ke kara samar da sabbin damammaki ga yankin Asiya da Pasifik, bisa ga sabbin nasarorin da take samu ta hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin. (Mai fassara Bilkisu Xin)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA