.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Yabawa Gwamna Namadi Bisa Ayyukan Hanyoyi A Fadin Jihar

Daga Usman Mohammed Zaria

Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Injiniya (Dr.) Muhammad Uba, ya yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, bisa amincewa da sabbin ayyukan gina hanyoyi a fadin jihar, ciki har da na Birnin Kudu.

Ya ce wannan mataki na cikin ajandar gwamnati 12, musamman wajen inganta ci gaban ababen more rayuwa.

A cewarsa, Birnin Kudu za ta amfana da gina hanyoyi masu tsawon kilomita 113, wanda ya hada da hanyoyin kauyuka da wadanda ke hada al’umma da sauran sassan jihar.

Dr. Uba ya bayyana aikin a matsayin babban ci gaba wajen saukaka zirga-zirga, inganta harkokin tattalin arziki da samun sauki ga muhimman ayyuka ga jama’a.

Ya bayyana tabbacin cewa za a dade ana cin moriyar aikin hanyoyin,  tare da hanzar ayyukan ci gaba da bunkasar karamar hukumar.

Shugaban ya yi addu’ar dorewar zaman lafiya da cigaba a Birnin Kudu tare da yin alkawarin ci gaba da hada kai da gwamnatin jiha domin tabbatar da cewa jama’a suna amfana da fa’idodin dimokuraɗiyya.

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Yabawa Gwamna Namadi Bisa Ayyukan Hanyoyi A Fadin Jihar
  • Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi
  • Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar