Aminiya:
2025-11-06@10:35:48 GMT

NAJERIYA A YAU: Matakan da ciwon suga ke bi kafin illata mai fama da shi

Published: 28th, August 2025 GMT

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Mutane da dama ba sa sanin suna dauke da ciwon suga ballantana su san hanyoyin magance shi kafin ya yi tsanani.

Sau da yawa ciwon sai ya kai wani matakin da zai yi wa mutum illa sannan yake sanin yana dauke da shi.

NAJERIYA A YAU: Ci Gaban Da Harshe Da Al’adun Hausa Suka Samu A Shekaru 10 DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa

Shirin Najeriya  A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan matakan da ciwon suga ke bi kafin ya yi tsanani da kuma hanyoyin magance shi.

Domin sauke shirin, latsa nan

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

An yi musayar yawu tsakanin Barau da Akpabio a majalisa kan barazanar Trump

An yi musayar yawu a zauren Majalisar Dattawa a ranar Talata yayin da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin da Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, kan zargin Shugaban Amurka, Donald Trump, na yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya.

Zaman majalisar ya biyo bayan sanarwar Trump da ke bayyana Najeriya a matsayin “Ƙasa Mai Ƙalubale Na Musamman,” yana zargin Gwamnatin Tarayya da bari a ci gaba da kashe Kiristoci a ƙasar.

DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar Makamai Ba addini ne kaɗai ke haifar da rikici a Nijeriya ba — EU

Batun ya taso ne a ƙarshen zaman majalisar na ranar Talata, lokacin da Akpabio ya shaida wa ’yan majalisar cewa ’yan Najeriya na son jin matsayar Majalisar Dattawa kan lamarin.

Sai dai ya ce ba za a ɗauki matsaya ba har sai Gwamnatin Tarayya ta gabatar da matsayinta a hukumance kan batun.

“Ni waye da zan mayar wa Trump da martani?” in ji Akpabio cikin tambaya, yana mai bayyana cewa Majalisar Dattawa ba za ta tattauna batutuwa ba sai an gabatar da su ta hanyar da ta dace.

Ya ƙara da cewa duk da cewa ’yan Najeriya na son majalisar ta mayar da martani, za su jira bayanai a hukumance kafin su ɗauki mataki.

Sai dai kalamansa sun jawo martani kai tsaye daga mataimakinsa, Sanata Barau Jibrin.

“Kar ka ji tsoro, ni zan yi magana. Ba na tsoron Trump. Zan faɗi ra’ayina,” in ji Barau.

Ya ci gaba da cewa, “Ni ɗan Najeriya ne, ɗan majalisa, kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa na ƙasa mai cikakken ’yanci. Ba na tsoron Trump. Kada ku ji tsoron Trump. Kuna da ’yancin faɗar ra’ayinku a kansa. Mu ƙasa ce mai cikakken ’yanci. Yana yaɗa ƙarya game da ƙasarmu, kuma muna da ’yancin musanta hakan.

“Idan ka ce ba za ka yi magana ba, hakan daidai ne, amma abin da nake ƙoƙarin faɗa shi ne kada ka ji tsoronsa.”

Akpabio ya katseshi yana mai cewa, “Na ce ba na tsoro. Yaya za a ce Shugaban Majalisar Dattawa na ƙasa zai ji tsoron Trump?”

Ya ƙara da cewa, “Ka fahimta, ka faɗi ra’ayinka, amma kada ka bari mutane su danganta maka abin da ba ka faɗa ba. Amma idan kana so na faɗa yanzu, zan faɗa. Amma ka saurara, zan faɗi abin da muka tattauna ne kawai.”

Daga nan sai Akpabio ya juya ga Akawun Majalisar, yana umarnin a goge kalaman Barau daga kundin rubuce-rubucen majalisar, yana mai cewa Barau ya “fita daga layin magana.”

Sai dai Barau bai nuna damuwa ba, ya tashi ya nufi kujerar Akpabio, inda suka yi gajeriyar tattaunawa a sirrance da ta ja hankalin sauran ’yan majalisar, kafin ya koma kujerarsa.

Aminiya ta rawaito cewa kalaman Trump, da Sakataren Yaƙi na Amurka, Pete Hegseth, a shafin a X cewa kasar na “shirin ɗaukar matakin soja,” sun haifar da fushi a fagen siyasa da diflomasiyya.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya musanta zargin Trump, yana mai jaddada cewa Najeriya ƙasa ce mai dimokuraɗiyya da ke ba da ’yancin addini da zaman lafiya tsakanin al’umma.

Haka kuma, ƙasar China ta nuna rashin amincewa da kalaman Trump, tare da bayyana goyon bayanta ga Najeriya, tana mai bayyana ta a matsayin “abokiyar”.

Beijing ta gargaɗi cewa babu wata ƙasa da ya kamata ta yi amfani da batun addini ko ’yancin ɗan adam a matsayin uzuri don tsoma baki cikin harkokin cikin gida na wata ƙasa mai ’yanci.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Cutar Basir
  • Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka
  • An yi musayar yawu tsakanin Barau da Akpabio a majalisa kan barazanar Trump
  • Ba addini ne kaɗai ke haifar da rikici a Nijeriya ba — EU
  • China ta yi martani kan barazanar Trump ta kai hari Najeriya
  • NAJERIYA A YAU: Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Su A Najeriya
  • Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki
  • Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan
  • Komai zai iya faruwa a hare-haren da za mu kai Nijeriya — Trump
  • Najeriya : tun kafin kalamman Trump muka dauki matakai