Aminiya:
2025-06-16@04:05:02 GMT

’Yan bindiga sun sace mutum 22 a ƙauyukan Kaduna

Published: 26th, January 2025 GMT

An sace aƙalla mutum 22 a wasu sabbin hare-hare da ake zargin ’yan bindiga da kaiwa a ƙauyen Kugauta da ke Kusheka da kuma Kitanda da ke Gashere a masarautar Kumana da ke Ƙaramar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna.

Wani mazaunin yankin, Emmanuel Johnson, ya bayyana wa Aminiya cewa hare-haren sun afku ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren Juma’a.

Shin wannan ce kaka mafi muni ga Man-United a Gasar Firimiya? Gobarar tankar mai ta yi ajalin mutum 18 a Enugu

Ya bayyana cewa ’yan bindigar sun farmaki ƙauyen Kitanda ne da farko inda suka yi awon gaba da mutum 12 —galibinsu mata da ƙananan yara — sannan suka kai hari na biyu a ƙauyen Kugauta inda suka sake sace mutum 10.

Johnson, wanda ya nuna takaicinsa kan yadda rashin tsaro ke ƙara ƙamari a yankunansu, ya ce jami’an ’yan sanda uku ne kacal ke kula da ƙauyen da wasu yankunan da ke makwabtaka da su.

“Ana ci gaba da kai mana hare-hare a kai a kai, ana sace mana mutane kusan kullum,” in ji shi.

“’Yan sanda uku ba za su iya kare mu ba. Ya kamata gwamnati ta tabbatar mana cewa mu ma ’yan Nijeriya ne da ke da ’yancin samun kariya”

Ya ƙara da cewa sama da naira miliyan 60 aka biya a matsayin kuɗin fansa a lokuta daban-daban kuma har yanzu akwai wasu da aka sace da ke hannun ’yan bindigar.

Haka kuma, ya ce hare-haren sun sa mutane da dama ƙauracewa gidajensu.

Johnson ya kuma bayyana yadda matsalolin rashin ababen more rayuwa suka ƙara dagula musu rayuwarsu, musamman rashin kyawawan hanyoyi da asibitoci da kuma makarantu.

Ya ce, “Ba ma iya kai kayan gonarmu kasuwa saboda lalacewar hanyoyin.”

Ya yi kira ga gwamnati da ta tura ƙarin jami’an tsaro, ta kuma kafa ofisoshin ‘yan sanda, tare da na sansanan sojoji a muhimman wurare domin daƙile matsalar tsaron da ke ƙara ta’azzara.

Haka kuma, ya buƙaci sojoji da su kai samamen kawar da sansanonin ’yan bindiga a yankin.

“’Yan bindigar nan sun kassara mana tattalin arzikinmh kuma sun jefa mu cikin talauci. Muna kiran Gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa don kawo ƙarshen wannan wahalar da muke ciki,” in ji shi.

Ƙoƙarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya ci tura yayin da bai amsa kiran waya da sakonnin da wakilinmu ya tura masa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Sin Ta Yi Kira Ga Isra’ila Da Ta Dakatar Da Kaddamar Da Hare-hare Kan Iran

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Ta Cilla Makamai Kan HKI Da Rana A Karon Farko A Yau Lahadi
  • Kungiyar Abokan Yarjejeniyar M.D.D Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Da Isra’ila Ke Kai Wa Kan Iran
  • Trump ya dakatar da kamen baƙin haure a wasu wurare na Amurka
  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 100 a Benuwe
  • Wutar lantarki ta kashe mutum 5, ta jikkata 13 a Gombe
  • Wutar Lantarki Mai Ƙarfi Ta Yi Ajalin Mutum Biyar A Gombe
  • Gwamnan Kaduna ya bai wa sabon Sarkin Moro’a sandar mulki
  • Sin Ta Yi Kira Ga Isra’ila Da Ta Dakatar Da Kaddamar Da Hare-hare Kan Iran
  • Mahara sun kashe mutum 26 a sabon hari a Binuwai
  • Yadda mota ta kashe mutum 8 ’yan gida daya bayan dawowa daga yawon Sallah a Kaduna