2025-05-11@17:44:09 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3186

«Gwamnan Jihar»:

    Sabon shugaban darikar ‘yan katolika na duniya Fafaroma Leo na 14 ya ce yana matukar bakin ciki da abin da ke faruwa a zirin Gaza, inda ya bukaci a tsagaita wuta nan da nan, a ba da agajin jin kai ga fararen hula da suka gaji, kuma a sako duk wadanda aka yi garkuwa da su.” Fafaroman ya kuma yi kira ga “manyan kasashen duniya” da su dakatar da yaki, ya kuma yi kira da a samar da zaman lafiya “adalci” mai “dorewa” a Ukraine a wani jawabi da ya gabatar yau Lahadi a sallarsa ta farko bayan zama fafaroma. Shugaban ‘yan katolika na duniya ya kuma yi maraba da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma tsakanin Indiya da...
    “Babu shakka cewa INEC na fuskantar matsin lamba mai tsanani, daga mambobin APC da sauran abokan huldarsu wadanda ke tsoron TNN, domin sun shirya yin magudi a zaben 2027 wajen samun nasararsu. “Amma muna kira ga INEC da ka da ta bayar da kai bori ya hau a matsayinta na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa tare da kare mutuncnta ta hanyar kin yin abin da ya saba wa doka.  “Muna tunatar da hukumar INEC cewa ‘yan Nijeriya suna sa ido sosai kan yadda za ta magance wannan batun na TNN, kuma duk abin da za ta yi zai tantance ko ‘yan Nijeriya za su iya dogaro da ita don shirya sahihin zabbe mai cike da adalci a 2027,”...
    Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana fatan ganin kasashen India da Pakistan sun kai zuciya nesa, tare da warware sabani ta hanyar shawarwari da tattaunawa, kana su gujewa sake rura wutar tashin hankali. Wang ya bayyana hakan ne a jiya Asabar, yayin tattaunawa ta wayar tarho da mashawarcin gwamnatin India ta fuskar tsaro Ajit Doval, inda ya ce Sin na goyon baya, da fatan sassan biyu za su kai ga cimma cikakken yanayi mai dorewa na dakatar da bude wuta ta hanyar tattaunawa, wanda hakan muhimmiyar moriya ce ta kasashen biyu, kuma zai cika burin sassan kasa da kasa. Ya ce Sin ta yi tir da harin ta’addanci da ya auku a yankin Pahalgam, tana kuma adawa...
    Wata muhawara ta kunno kai a Jihar Kano da ma wajenta bayan gwamnatin jihar ta ba da umarni a cire naira miliyan 670 daga asusun ƙananan hukumomin jihar domin saye da kuma gyaran motocin Mai Martaba Sarkin Kano, Muhanmmadu Sanusi II. Gwamnatin jihar ta bayyana cewa za a kashe naira miliyan 50 daga cikin kudin wajen gyaran wasu motoci biyu na sarkin, ragowar kuma za a sayo wasu sababbin motoci huɗu. Shekara 10: Me ya sa Kofin Zakarun Turai ya gagari Barcelona? Za a kwaso ’yan Nijeriya 15,000 da ke gudun hijira a ƙetare Ɓullar takardar da ke ɗauke da umarnin ta haifar da ce-ceku-ce, amma gwamnatin jihar ta hannun Kwamishinan Watsa Labarai, Ibrahim Waiya, ta kare matakin da cewa...
    Kazalika, sanarwar ta sanar da cewa, ana bukatar kwamtin ya sanya ido wajen ganin an gabatar da kasidu da alkalan da za su yi hunci kan bayanan da za a tattauna a wajen taron da baje kolin kanana da matsakaitan sana’oi da za a yi a wajen taron tare da kuma mika kyaututtuka ga ‘yan kasuwar kasar da suka dace, a wajen taron. Acewar sanarwar, Mataimakin Shugaban Ma’aikata da ke a ofishin Mataimakin Shugaban kasa Sanata Ibrahim Hassan Hadejia ne, zai shugabaci kwamtin. Sauran ‘ya’yan kwamtin sun hada da, Ministar Ma’aikatar Kasuwanci da zuba hannun jari Dakta Jumoke Oduwole; Ministan sadarwa da kere-kere da kuma tattalin arziki na fasahar zamani Dakta Bosun Tijani; Ministar yawon bude ido da kirkiren tattalin...
    Wasa na uku da kungiyoyin suka hadu a bana shi ne wasan karshe na kofin Copa Del Rey inda nan na Barcelona ta sake samun nasarar doke Madrid da ci 3-2, a wannan karon kocin Madrid Carlo Ancelotti na fatan ganin kungiyarsa ta samu nasara akan Barcelona duba da cewar wannan ka iya zama wasan karshe da ita a matsayinsa na kocin Real Madrid. Manyan yan wasan da bazasu buga wannan wasa sakamakon raunin da suka samu sun hada da Joules Kounde da Pablo Torre a bangaren Barcelona, sai kuma Antonio Rudiger, Eduordo Camavinga da Ferlnad Mendy a bangaren Real Madrid. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
    A Talatar makon jiya ce Inter Milan ta ƙara lalata wa Barcelona mafarkinta na ɗaukar Kofin Zakarun Turai a shekaran nan, bayan an yi kare-jini-biri-jini tsakanin kungiyoyin guda biyu a wasan kusa da na karshe. An tashi wasan ne da ci 4-3 a San Siro gidan Inter Milan bayan sun yi 3-3 a gidan Barcelona. Lautaro Martinez da Hakan Calhanoglu ne suka fara zura wa Inter ƙwallo a ragar Barcelona. Za a kwaso ’yan Nijeriya 15,000 da ke gudun hijira a ƙetare Matakan da gwamnonin Arewa suke so a ɗauka kan matsalar tsaron yankin Davide Frattesi ne ya ci ƙwallon da ta bai wa Inter nasara a cikin ƙarin lokaci, bayan ƙwallon ne kuma aka kaure da ruwan sama. Barça,...
    Falasdinawa mazauna yankunan Khan-Yunus dake kudancin zirin Gaza suna fama da matsananciyar yunuwa, a lokaci daya suna fuskantar hare-hare masu tsanani daga sojojin HKI. Mata mazauna yankin sun fi fuskantar matsaloli saboda kananan yaran da suke tare da su, alhali kuma an rushe gidajensu. A tsawon yakin kisan kiyashin da HKI take yi, matan da su ka yi shahada sun kai 12,000 da 400. Bugu da kari wasu matan da sun kai 14 sun bace ba a gano su ba, sai kuma wasu matan masu ciki da sun kai 60,000 da suke fuskantar hatsari mai tsanani saboda rashin kula da su, da kuma rusa asibitoti da sojojin HKI su ka yi. A cikin wani tanti a Khan-Yunus da akwai wata...
     Ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakistan ta jadada cewa ko kadan sojojin kasar ba su keta tsagaita wutar yaki da Indiya ba.  A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen ta Pakistan ta fitar ta ce; kasar tana ci gaba da aiki da tsagaita wutar yaki wacce aka sanar da ita, kuma sojojin kasar sun kai zuciya nesa, duk da cewa Indiya ce ta keta wutar yakin. Saanrwar da Pakistan ta biyo bayan zargin da Indiya ta yi wa kasar ne cewa tana keta yarjejeniyar wutar yaki bayan an cimma yarjejeniya a kan hakan. Jami’i a ma’aikatar harkokin wajen Indiya Bigram Maisari ne ya bayyana hakan a wani taron manema labaru da ya gabatar a yau, sannan ya kara da cea;...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta iran, Dr. Isma’ila Baka’i ya bayyana cewa; Tsagaita wutar yakin da aka yi a tsakanin Indiya da Pakistan abin yin maraba da shi ne, sannan kuma ya kara da cewa; Ya zama wajibi kasashen biyu su yi amfani da wannan dama domin rage tashin hankali a yankin da kuma tabbatar da zaman lafiya. Baka’i ya yaba da hikimar shugabannin kasashen biyu da su ka dakatar da yaki, yana kuma nuna fatansa na ganin kasashen biyu sun mayar da alakarsu kamar yadda take a baya a cikin gaggawa. A jiya Asabar ne dai ministocin harkokin wajen kasashen biyu su ka sanar da tsagaita wutar yaki,bayan kwanaki da su ka dauka suna musayar wuta a...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta cafke wani mutum mai suna Samson Oghenebreme a unguwar Odomola ɗauke da kawunan mutane. Sanarwar da kakakin ’yan sandan Legas, Benjamin Hundeyin ya fitar, ta ce an kai kawunan da aka gano asibiti a Epe, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin. Indiya da Pakistan sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta Matsalar Tsaro: Zulum ya haramta sayar da man fetur a Bama An kama matashin ne ɗan shekara 25 bayan da jami’an bijilanti da ke sintiri a yankin suka sanar da jami’an tsaro cewa ba su yadda da take-takensa ba. Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa ’yan sandan sun yi zargin cewa matashin yana kai kawunan Jihar Edo wajen wani boka —...
    Gwamnatin Nijeriya ta ce tattaunawa ta yi nisa domin kwaso ’yan ƙasar guda 15,000 da suke gudun hijira a ƙasashen Kamaru da Nijar da Chadi da wasu ƙasashen cikin mutunci. Kwamishinan hukumar kula da ’yan gudun hijira ta Nijeriya, Alhaji Tijjani Ahmed ne ya bayyana haka a zantawarsa da manema labarai a Abuja. Matakan da gwamnonin Arewa suke so a ɗauka kan matsalar tsaron yankin An kama matashi da kawunan mutanen a Legas Ya ce akwai aƙalla ’yan Nijeriya miliyan shida da ke zaman gudun hijira a cikin ƙasar, sannan akwai wasu dubbai da suke zaune a wasu ƙasashen na duniya. “Akwai ’yan Nijeriya 15,000 da suke so su dawo da kansu; haka kuma muna da ’yan ƙasashen waje aƙalla...
      Sai dai a cikin takardar murabus din, Edema ya bayyana rashin tsarin jam’iyyar a matsayin dalilin da ya sa ya fice daga jam’iyyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sai kaga mutum daga ya samu wata yar dama to do yake ace ya samu wata hanyar wulakanta wannan wanda yayi masa rana kokuma ya wuce shi a matsayi ko wani abin Duniya ba tareda la’akari da cewar wannna wanda ya koya maka to ya fika sanin komai a wannan harkar musamman ma a nan masana’antar Kannywood. Don haka kamata ya yi ce mutane sun fahimci cewar babu ta yadda za a yi ka ci gaba matukar ka na da wata niyyar cin amanar wanda ya taimake ka ka kai wani matsayi na rayuwa, ni yanzu a matsayina na Ayatullahi Tage na yi biyayya ga maigidana Alhaji Tage wanda ya nuna mani hanya, ya rike ni kamar dan da ya...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana fuska biyu na kasashen yamma, dangane da shirin magakamashin nukliya na kasarsa, da kuma yadda basa magana kan makaman nukliya wanda HKI take da su. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Asabar, a birnin Doha na kasar Qatar a inda yake halattan taron JMI da kasashen larabawa a jiya Asabar. Ministan ya kara da cewa, wannan rashin adalci ne a fili sannan nuna fuska biyu, Iran wacce babu tabbas kan shirinta na makamashin nukliya na soje ne, an cika duniya da cewa tana son ta mallaki makaman nukliya amma ga HKI wacce aka tabbatar da cewa tana da makaman na nukliya, babu...
    Jakadan JMI a MDD ya musanta zargin kamfanin dillancin labaran reuters dangane da rotohonsa na cewa JMI tana aika makamai masu linzami zuwa kasar Rasah don taimakawa kasar Rasha yakin da take fafatwa da kasar Ukraine fiye da shekaru 3 da suka gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ofishin jakadancin JMI dake birnin NewYork ya kara da cewa, abin mamaki da kamfanin dilancin laraban reuters, shi ne ba wannan ne karo na farko yake yada labaran karya a duniya wanda wai yake samu daga wasu wadanda basa son a bayyana sunansu. Kafin haka dai JMI ta sha nanata cewa bata bayan wani bangare daga cikin bangarori biyu da suke fafatawa a kasar Ukraine. Don haka bata...
    Shugaban kasar Rasha Vladimir Puttin Ya gana da tokwaransa na kasar Masar Abdul alfattah Asisi bayan halattar bikin cika shekaru 80 da nasarar da kasar Rasah ta samu kan sojojin Nazi a yakin duniya na biyu wanda aka gudanar a birnin Mosco. Shafin yanar gizo na labarai ya bayyana cewa harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen biyu tana bunkasa inda a shekarar da ta gabata ya kai dalar Amurka biliyon $9. Har’ila yau kowa ya san yadda kasar Masar ta zama sansanin sojojin kasar Rasha a lokacin yakin duniya na biyu. Da kuma yadda kasar ta taimakawa kasar Rasha a yakin da ta fafata da sojojin Nazi na kasar Jamus. Har’ila yau shugaban kasar  Rasha Vladimir Putin ya godewa shugaban kasar...
    Amma sha’awar taka leda a Real tare da babban abokinsa kuma abokin wasansa na Ingila Jude Bellingham ya sa shi canza ra’ayi, yunkurin da Alexander-Arnold ya yi zuwa Real Madrid ya raba kan magoya bayan Liverpool, inda wasu ke ganin ya kamata ya zauna ya zama gwarzon kulob daya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnoni da kuma Sarakunan gargajiya na Arewacin Nijeriya sun gudanar da taro a Kaduna, domin tattaunawa kan matsalolin rashin tsaro da suka addabi yankin. Taron wanda ya gudana ne a gidan gwamnatin jihar ta Kaduna, inda suka tattauna kan matsalar talauci da yaran da ba su zuwa makaranta da kuma sauran al’amura da suke damun yankin. An kama matashi da kawunan mutanen a Legas Indiya da Pakistan sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta Gwamnonin jihohin Katsina da Zamfara da Kebbi da Gombe da Neja da Filato da Yobe da Jigawa da Kogi da Adamawa da kuma Zamfara na cikin waɗanda suka halarci taron. A ɓangaren sarakunan gargajiya kuma akwai mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III da Sarkin Zazzau, Ahmed...
    A jawabinsa a wajen tarbar Jirgin Ruwan na na yankin Asia Jim Stewart, ya bayyana jin dadinsa ga Hukumar ta NPA, bisa goyon bayan da ta bayar wajen samar da kyakyawan yanayi a babban wajen da Jiragen Runwan na Tashar Onne suke tsayawa. “Muna da kyakaywar dangantakar gudanar da ayyuka da Manajan Tashar ta Onne Mista Abdulrahmon Hussain da kuma sauran ‘yan tawagar Hukumar ta NPA, “Inji Stewart. Ya ci gaba da cewa, a karkashin shugabancin shugaban Hukumar ta NPA Dakta Abubakar Dantsoho, wanda kuma kashin bayan duk wata nasara da muka zamu. “Sake farfado da babban wajen tsayawar Jiragen Ruwan a Tashar Onne, hakan ya kara mana kwarin Guiwa”. A cewar Stewart. Kazalika, Stewart ya yi kira ga Gwamnatin...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta cafke wani mutum mai suna Samson Oghenebreme a unguwar Odomola ɗauke da kawunan mutane. Sanarwar da kakakin ’yan sandan Legas, Benjamin Hundeyin ya fitar, ta ce an kai kawunan da aka gano asibiti a Epe, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin. Indiya da Pakistan sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta Matsalar Tsaro: Zulum ya haramta sayar da man fetur a Bama An kama matashin ne ɗan shekara 25 bayan da jami’an bijilanti da ke sintiri a yankin suka sanar da jami’an tsaro cewa ba su yadda da take-takensa ba. Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa ’yan sandan sun yi zargin cewa matashin yana kai kawunan Jihar Edo wajen wani boka —...
    Sarkin Katsina Muhammadu Dikko Allah ya yi ma shi rasuwa,a shekarar 1944 da ba’a dade da shigarta ba,bayan ya sanu damuwa daga rashin lafiya, wannan shi yasa aka fara fafutukar neman wanda zai gaje shi.Ta bnagare daya akwai gidan Sarautar Dallazawa  a karkashin jagorancin Yarima, wanda shi dan Sarkin Katsina Abubakar ne wanda yake ganin Sarautar Katsina wata dama ce ta shi,sai ta daya bangaren kuma akwai ‘ya’yan marigayi Sarkin Katsina Muhammadu Dikko,wadanda su ma suna da matukar karfi,wadanda daga cikinsu ma da akwai wata ‘yar jayayya kan wanda zai gaji mahaifin nasu. Watan Maris 1944,sai masu zaben Sarki suka zabi  karami daga cikin ‘ya’yan Dikko da ake kira da suna Usman Nagogo,wanda shi ne Turawan mulkin mallaka na Ingila...
    Ya kara da cewa bukatar kasa da kasa game da karfin ma’adinai na Kaduna yana karuwa, tare da masu saka hannun jari da yawa wadanda suke bincike kan yadda za su yi amfani da wadannan albarkatun da ba a taba amfani da su ba. “Baya ga wannan, muna da ma’adanan karfe. Kamfanin ‘African Mines’ ya riga ya zo Kaduna don hakar wannan albarkatun, wanda ya nuna a fili cewa Kaduna tana da ma’adanan karfe da za a iya gudanar da kasuwancinsu,” in ji shi. Bello ya jaddada cewa tsarin kamfanin yana nuna jajircewa don kokarin killace iyakokin ma’adinai da kuma habaka su. Ya ce tun lokacin da aka kafa kamfanin, hukumar gudanarwaar kamfanin ta ba da fifiko ga ayyukan da...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Dole ne duniya ta dauki matakin kalubalantar laifukan ‘yan sahayoniyya da magoya bayansu kan zaluncin Gaza Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, yayin da yake karbar bakwancin dimbin ma’aikata a yau Asabar, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan “Makon ayyuyka da Ma’aikata” ya bayyana cewa: A yau duniya ta shaida yadda ake daukar manufofin son zuciya kan wasu kasashe. Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa daga cikin wadannan manufofi na son zuciya da ake aiwatarwa a yau akwai kokarin mantar da al’umma batun da suka shafi Falasdinawa, yana mai cewa: Kada al’ummar musulmi su kuskura wannan kyale hakan ya faru, domin ko dan...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Amfanin da fira ministan gwamnatin mamaya ya yi da ƙungiyar ta’addanci babbar alama ce ta cikakkiyar yanke ƙauna Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Matakin da fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya dauka na yi amfani da wata karkatacciyar kungiyar ta’addanci ta “MKO” wato kungiyar Munafukai wajen yada labaran karya game da shirin makamashin nukiliyar Iran, don tsoratar da al’ummar duniya kan Iran, wata babbar alama ce ta yanke kauna. A sakon da ya wallafa shafinsa na X ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Yayin da ake ci gaba da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, ana...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran yayi Allah wadai da harin da aka kai kan ginin ofishin jakadancin kasarsa da ke Stockholm na kasar sweden Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya yi Allah wadai da harin da aka kai ofishin jakadancin Iran da ke Stockholm tare da yin kira ga gwamnatin Sweden da ta dauki mataki mai tsanani kan wadanda suka kai harin. A yayin wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi da ministar harkokin wajen Sweden Maria Malmer Stenergård, bangarorin biyu sun tattauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu da kuma na ofishin jakadancin. A yayin tattaunawar, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi Allah wadai da harin da aka kai ofishin...
    Shugaban kasar Amurka ya sanar da cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Indiya da Pakistan Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa: Indiya da Pakistan sun cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta nan take, wanda Amurka ta shiga tsakani wajen kulla ta. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana farin cikinsa da wannan ci gaba, da aka samu, inda ya yaba da amfani da hankali da basirar da kasashen biyu suka nuna wajen daukar wannan mataki. Ya kuma jaddada cewa, dogon tattaunawar da aka yi tsakanin bangarorin biyu ya haifar da wannan yarjejeniya, wanda ke nuna muradin bangarorin biyu na samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Wannan sanarwar...
    Wani babban hafsan sojin Yemen ya bayyana dabarun Yemen da suka tilastawa Amurka dakatar da kai hare-hare kan kasar Yemen Kwararren kan harkar sojin kasar Yemen kuma kwararre kan harkar yaki Birgediya Janar Aziz Rashid ya jaddada bunkasar karfin sojan kasar Yemen, yana mai nuni da dalilan da suka sanya aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Yemen. A wata hira ta musamman da ya yi da tashar talabijin ta Al-Alam, kwararren sojan kasar Yemen kuma kwararre kan harkar dabarun yaki birgediya Janar Aziz Rashid ya tabbatar da cewa: Kasar Yemen ta samu wani matsayi mai inganci a arangamar da take yi da haramtacciyar kasar Isra’ila, inda ta yi nasarar sauya ma’aunin karfin iko da kuma karuwar matakan soji...
    Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum ya haramta sayar da man fetur a Ƙaramar Hukumar Bama ta jihar, ciki har da garin Banki. Gwamnan ya ce haramcin ya zo ne bayan tattaunawa da hukumomin tsaro a jihar, kuma an yi haka ne domin shawo kan matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta. Gidauniya ta yi wa masu cutar gwaiwa dubu 12 tiyata kyauta a Katsina Za a faɗaɗa Gasar Kofin Duniya ta Mata zuwa ƙasashe 48 — FIFA Wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yaɗa labarai Dauda Iliya ya fitar, ya ce matakin wani ɓangare ne na tsare-tsaren da gwamnatin jihar ke yi na daƙile ayyukan ’yan ta-da ƙayar baya. “Na bayar da umarnin haramta sayar da da man...
    Gidauniyar attajirin ɗan kasuwar nan na Jihar Katsina, Alhaji Dahiru Mangal, ta yi wa masu fama da cutar gwaiwa da taruwar ruwa a wasu sassan jiki fiye da 12,300 tiyata kyauta. Da yake yi wa wakilin bayani, Malam Husaaini Kabir, mamba a kwamitin amintattu na gidauniyar ne ya tabbatar da hakan a Katsina, a lokacin ƙaddamar da aikin kashi na biyu. Za a faɗaɗa Gasar Kofin Duniya ta Mata zuwa ƙasashe 48 — FIFA Sauya sheƙa bayan cin moriyar jam’iyya butulci ne — Kwankwaso Kabir ya bayyana cewa gidauniyar tana gudanar da aikin tiyatar da bayar da magani kyauta a duk bayan watanni uku tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 2013. Ya ƙara da cewa, “majinyata masu rauni...
    Hukumar Ƙwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta ce za ta faɗaɗa Gasar Kofin Duniya ta Mata daga tawagogi 32 zuwa 48. FIFA ta ce sabon tsarin zai fara aiki ne daga gasar 2031, wadda Amurka ce kawai ke neman ɗaukar nauyinta. Sauya sheƙa bayan cin moriyar jam’iyya butulci ne — Kwankwaso HOTUNA: An ƙaddamar da tashin sahun farko na maniyyatan Nijeriya zuwa Saudiyya Tuni dai FIFA ta faɗaɗa gasar cin Kofin Duniya ta Maza da za a yi nan gaba, zuwa wannan adadi. FIFA ta ce ta ɗauki matakin ne saboda yadda gasar ke ci gaba da samun karɓuwa da farin jini tsakanin masoya ƙwallon ƙafa a duniya. Masu suka sun zargi hukumar da fifita kuɗin da za ta samau...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei  ya fada a yau Asabar cewa: Ma’aikata ne jari mafi muhimmanci na samun zaman lafiya a cikin al’umma da kuma cimma manufar sunan da aka bai wa wannan shekarar na : “Zuba Hannun Jari Domin Yin Kere-Kere.” Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gana da ma’aikata da su ka fito daga sassan Iran, ya yi ishara da sake bude kamfanoni da dama a zamanin shugabancin Shahid Ra’isi, alhali gabaninsa an rufe su,tare da bayyana hakan da cewa daya ne daga cikin ayyukan da Shahidin ya aiwatar. Jagoran juyin musuluncin na Iran ya kuma bayyana ma’aikatar da cewa, su nekashin bayan kowace al’umma, yana kuma mai yin addu’ar Allah ya ba su...
    Fira ministan kasar Pakistan Shahbaz Sharif ya kira yi Majalisar kasa wacce take kula da makaman Nukiliyar kasar  da su yi taro. Wannan matakin da ake yi wa Kallon mai hatsari yana faruwa ne a daidai lokacin da kasar ta Pakistan take yaki da Indiya. Ita  dai Majalisar  kasar Pakistan dake kula da makaman Nukiliya da kuma manufofin kasa na koli, ta kunshi manyan kwamandojin soja, da fararen hula, aikinta kuma  shi ne kula da manyan batutuwa da su ka shafi kasa daga ciki har da siyasar makaman Nukiliya da kuma makamai masu linzami.An kafa wannan majalisar ne dai a 2000. Tashar talabijin din “Sama News” ta bayar da labarin dake cewa; Mahalarta taron za su yi bitar halin da...
    Na yi wannan wannan ziyara ne saboda shaukin da nike da shi a kan abin da ya shafi kishin kasata Nijeriya, da kuma neman hadin kan kasashen Afirika ta yamma mu zama tsintsiya madaurinki daya,da son zaman lafiya da ci gaban Dimokaradiyya. Kazalika, na yi wannan rangadi ne domin murnar cikar kungiyar ECOWAS shekara 50 da kafuwa. Kasan an kafa kungiyar ne ranar 28 ga watan Mayu,1975 bana kungiyar za ta cika shekaru 50. To kasancewa shekaru 50 sun wuce wasa na ga cewa, kungiyar ta cancanci a yaba mata, kuma a kara matakaimi da azama. Kuma za ka yarda da ni idan na ce ma cikin wadannan shekaru 50, Kungiyar ta taka muhimmiyyar rawa ta a zo a gani...
    A sanarwar da mataimaki na musamman ga ministan kan harkar yaɗa labarai, Malam Rabi’u Ibrahim ya fitar, ya bayyana cewa a jawabin sa na buɗe taron, ministan ya nuna jin daɗin sa kan yadda haɗin kai ke ƙaruwa a tsakanin manyan masu ruwa da tsaki a fannin yaɗa labarai a cikin gwamnatin.   Ya ce haɗin kan da daidaiton manufa sun ƙara inganta isar da saƙo da kuma fahimtar manufofin gwamnatin Tinubu.   Ministan ya yaba da yadda Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai take aiki tare da shugabannin hukumomin yaɗa labarai da kuma mataimakan shugaban ƙasa a ɓangaren watsa labarai da dabarun sadarwa.   Ya ce wannan haɗin gwiwa ya taimaka wajen tabbatar da cewa saƙonnin gwamnati suna...
    Duba da yadda yanayin muhalli yake, zai  ba da dama wajen rage fuskantar sauyin yanayi tare da inganta kiwon lafiyarsu, abincinsu da kuma ingancin ruwan shansu. 2- Fashin Baki Kan Abin Da Zai Iya Afkuwa A Wajen Kiwon Su: Ga wanda zai fara wannan kiwo, ana so ya zabi wajen da ya dace da kuma tsarin da zai yi, don guje wa abin da zai iya afkuwa a bangaren sauyin yanayi mai tsanani. 3- Raba Kafa A Yayin Kiwon: Masu iya magana na cewa, ‘Ba a zuba kwai a cikin kwando daya’, wato ma’ana, ana so ka raba kafa ta hanyar yin wata dabara a kan kayanka, don kaucewa yin asara. Kazalika, raba kafa na taimakawa wajen kara bunkasa kiwo...
    Bugu da kari, wasu kwararru a fannin aikin noma, su ma tuni suka gargadi manoman kan kaucewa yin shuka da wuri, inda suka shawarce su da su tabbatar da sun kiyaye da hasashen na hukumar ta NiMet, domin kaucewa tabka asara da kuma yin da-na-sani. Lokacin Da Ya Fi Dacewa Manona Su Yi Shuka: Wata kungiya mai bayar da agajin gaggawa, (Christian Aids) tare da hadaka da wasu abokan hudda, sun samar da wata taswira da ke kunshe da lokacin da ya fi dacewa manoman da ke jihohin kasar 36 ciki har da babban birnin tarayayyar Abuja, su yi shuka. Taswirar wadda ta kasance mai saukin amfanai, sun tsara matakan da suka kamata manoman su bi, na kiyaye lokacin yin...
    BBC ta rawaito cewa, babban abin da ke damun kamfanin na Meta shi ne, yadda al’amarin ya shafi Hukumar Kare Bayanan Sirri ta Nijeriya (NDPC), wanda kamfanin ke zargin karya dokokin kare bayanan sirrin kasar. Baya ga tarar Hukumar FCCPC, hukumar ta NDPC ta ci tarar kamfanin Meta dala miliyan 37.8, bisa zargin satar bayanan sirri, yayin da hukumar kula da tallace-tallace (ARCON) ta fitar da wani hukuncin daban na dala miliyan 37.5, kan abin da ta kira da cewa, tallan da ba a ba da damar aiwatar da shi ba.    Daga cikin ka’idojin da ake da su, akwai bukatar kamfanin na Meta ya samu izini kafin tura bayanan ‘yan Nijeriya zuwa kasashen waje, yanayin da kamfanin ke ganin “ba...
    Dubban daruruwan mutane a kasar Yemen sun fito kan tituna suna bayyana jin dadinsu da samun nasara a kan kasar Amurka a yakin da suka dau makokinni suka fafatawa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa an daw makonni jiragen yakin Amurka suna kai hare-hare kan wurare daban daban a kasar Yemen da sunan tilastawa kasar dakatar da kaiwa jiragen ruwan Amurka da kuma na HKI wucewa da tekun Red sea don tallafawa mutanen Gaza, wadanda HKI take masu kissan kare dangi da kuma hana shigar abinda zuwa cikin gaza don kashesu da yunwa. A ranar Laraban da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fito ya fadawa duniya kan cewa, ya cimma yarjeniya da...
    Hukumomi a Jami’ar Colombia dake birnin NewYork na kasar Amurka sun bada sanarwan cewa, sun dakatar da karatun daliban jami’ar fiye da 65 saboda shiga cikin zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a kusa da babban dakin ajiyar littafai ko karatu a Jami’ar a ranar Laraban da ta gabata. Tashar talabijin ta Press tv a nan Tehran ta nakalto kakakin Jami’ar a jiya Jumma’a na cewa a ranar Laraba yansandan NewYork sun kama talibai kimani 80 inda suke tsare da su, a halin yanzu suke kuma ci gaba da gudanar da bincike a kansu. Amma duk da haka an dakatar da karatun wasu daga cikinsu zuwa wani lokaci nan gaba. Labarin ya kara da cewa akwai wasu karin mutane 33 wadanda Jami’ar...
    Kamfanin man fetur da gas na kasar Iran zai fara aikin nema da hakar man fetur a tekun Caspian da ke arewacin kasar, wanda mataki ne na ci gaba ga kamfanin musamman a halin da ake ciki. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto jami’an kamfanin na cewa tuni sun kai kayakin aiki zuwa wuraren da suke zata akwai danyen man fetur a cikin tekun, sannan a shirye suke su fara aiki don hakar man daga yanzun. Ba wannan ne karon farko wanda gwamnatin kasar Iran take hakar danyen man fetur a cikin tekun Caspian ba, saboda a shekara ta 1997 ne ta dakatar da hakar mai daga gabar tekun, sannan ta dakatar da hakar man a tsakiyar...
    Janar Hussain Salami babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran ya kaddamar da sabon sansanin jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa na karkashin kasa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Janar Salami yana cewa, wadannan jiragen yakin da ake sarrafasu daga nesa, suna iya daukar hotunan jiragen yakin Amurka wadanda suka kasance sansanin jiragen saman yaki na kasar wadanda suke cikin tekuna, don amfani da hotunan saboda kai wa sansanin hare hare. Salami yace gabatar da wannan sansanin gargadi ne ga mjakiya, sannan duk wata kasa a yankin wacce ta bar Amurka ta yi amfani da dandanin sojojinta da ke kasar don kaiwa kasar Iran hare0hare kasar ma ta zama filin daga....
    Bugu da kari, Sanarwar ta ce Sin da Rasha na goyon bayan kasancewar MDD jigo na shugabancin batutuwan da suka shafi kirkirarriyar basira ko AI, da jaddada muhimmancin martaba ikon mulkin kai na kasashe daban daban, da nacewa bin dokokin kasashe mabanbanta, da martaba ka’idojin MDD yayin gudanar da hakan. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An ƙaddamar da tashin sahun farko na maniyyatan Nijeriya zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da Aikin Hajjin 2025. Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ne ya ƙaddamar da tashin maniyattan a filin jirgin Sam Mbakwe da ke birnin Owerri na Jihar Imo. ’Yan kungiyar asiri sun kashe masu shirin tafiya NYSC a Bayelsa JAMB ta saki sakamakon jarrabawar 2025 Sahun farko na maniyyata 315 waɗanda suka kama hanyar ƙasa mai tsarki sun fito ne daga jihohin Imo da Abia da Bayelsa inda jirgin Air Peace ne ya kwashe su. Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma da Shugaban Hukumar Alhazan Nijeriya, Farfesa Abdullahi Usman da Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’adu Abubakar III da sauran manyan jami’an gwamnatin Nijeriya ne suka tarbi Kashim Shettima...
    A wani lokaci a gobe Asabar ne ake sa ran ministan harkokin wajen Iran zai fara wata ziyara a kasashen Saudiyya da kuma Qatar. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa, ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi zai ziyarci Saudiyya da Qatar a, bayan rahotannin da ke cewa akwai yiwuwar yin wata sabuwar tattaunawa tsakanin Tehran da Washington. M. Baghai ya bayyana cewa ziyarce ziyarce da Araghchi zai yi na daga cikin manufofin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na ci gaba da karfafa alakarta da makwabtanta. “Ministan harkokin wajen kasar ta Iran, zai fara tafiya birnin Riyadh don ganawa da manyan jami’an Saudiyya, sannan kuma zai tafi Doha don halartar taron tattaunawa tsakanin Iran da kasashen Larabawa.” Bayanin hakan ya...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce za a gudanar da zagaye na hudu na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka ranar Lahadi. Araghchi ya bayyana a yau Juma’a cewa Oman ce, zata kasance mai shiga tsakani, kuma ita ce ke tantance lokaci da wurin da za a yi tattaunawar. Ya kara da cewa bisa ga dukkan alamu kasar Oman ta tattauna da bangaren waccen bangaren. Babban mai shiga tsakani na Iran ya jaddada cewa tattaunawar Tehran da Washington tana ci gaba. Iran da AMurka dai sun yi jerin tattaunawa har guda uku a Oman, sannan a Italiya sai kuma a Oman. Dukkan bangarorin dai sun bayyana tattaunar da mai kyakyawan fata.
    Wannan mataki ya haifar da gagarumar muhawara a duniya. Yayin da manufar ke da nufin farfado da Hollywood da karfafa shirya fina-finai na cikin gida. Amma mu tambayi kanmu, shin da gaske wannan ita ce hakikanin manufar? Amma bari mu yi la’akari da wannan hasashen mu gani, ko shi ne ya fusata Amurka ta maka harajin kashi 100 bisa 100 kan fina-finai da ake shigar da su daga kasashen waje ko kuma wadanda aka shirya a ketare? Akwai wani kirkirerren fim mai suna ‘Ne Zha 2’ da masana’antar shirya fina-finai ta kasar Sin ta shirya a baya-bayan nan. Kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayar da rahoton cewa, wannan fim ya zama na farko da ya samar da dala biliyan...
    An kama mutane 78 tare da kwace tulin miyagun kwayoyi da makamai da kayan sata a wani samame da ’yan sanda suka kai kwanan nan domin ayyukan laifi a Jihar Kano. A yayin samamen, an kama gawurtaccen dillalin miyagun kwayoyi, Sulaiman Danwawu, da wasu haramtattun kwayoyi bayan an taba kama shi a shekarar 2022. Daga cikin sauran wadanda aka kama har da wani da ake zargin dan fashi da makami ne da bindigogi biyu da harsasai. Kwamishinan ’yan sanda, Ibrahim Adamu Bakori, ya sanar a taron ’yan jarida da ya gudana a hedikwatar rudunar da ke Bompai a ranar Juma’a cewa aikin kamen ya yi daidai da umarnin Shugaban ’Yan Sanda na Kasa kan a aiwatar da ingantattun matakai domin...
    Gwamnatin Nijeriya ta sanar da dakatar da tsarin bai wa ɗalibai tallafi domin samun damar zuwa ƙetare ƙarin ilimi. Ministan Ilimi, Tunji Alausa, shi ne ya sanar da wannan mataki, da ke nufin cewa za a kawo ƙarshen wannan tsari da aka share tsawon shekaru ana aiwatarwa. Yadda yara 5 suka mutu a cikin motar da aka yi watsi da ita Yadda rashin wutar lantarki ke ajalin rayuka a manyan asibitoci Mista Alausa ya bayyana cewa wannan matakai ya samu ne sakamako nazari da aka yi wajen sanya ƙaƙƙarfan jari a manyan makarantun ƙasar. Ministan ya ce daga yanzu babu batun bai wa ’yan ƙasar kuɗaɗen ƙaro ilimi daga ƙetare, saboda yanayi da ake ciki da ma kyawun tsari da...
    Wasu kananan yara biyar sun mutu a cikin wata mota da aka yi watsi da ita a harabar wani gida a yankin Agyaragu da ke Karamar Hukumar Obi da ke Jihar Nasarawa. Yaran sun rasu ne a sakamakon daukewar nunfashinsu a cikin motar, lamarin da ya jefa mazauna yakin yankin, wadanda yawancinsu manoman ne, daga kabilu daban-daban, cikin alhini. An gano gawarwakinsu ne da misalin karfe 1 na rana a cikin motar bayan mutanen yankin sun shafe tsawon lokaci ana neman su. Misis Ifeoma Nnaji, wacce ta rasa ’ya’yanta biyu, Nmesoma da Chidima, ta bayyana yadda aka gano gawarwakin ta ce, “Mun duba ko’ina… Daga karshe, wani ya ba da shawarar mu duba motar da aka yi watsi da ita,...
    Kotun tarayya da ke Abuja ta ɗage ƙarar tuhumar tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello kan zargin badaƙalar kuɗi da hukumar EFCC ta gabatar zuwa ranakun 26, 27 ga Yuni da 4, 5 ga Yuli don yanke hukunci kan buƙatar masu gabatar da ƙara ta “yi wa shaidar tambayoyi” da kuma ci gaba da shari’ar. Alkali Emeka Nwite ya ɗage shari’ar bayan ya saurari hujjojin daga ɓangaren masu gabatar da ƙara da na masu kare Yahaya Bello. An Karrama Shugaban Qausain TV, Kanar Sani Bello Da Lambar Yabo Da Ɗumi-ɗumi: Sanata Lawal Yahaya Gumau Ya Rasu Yana Da Shekara 57 Wani shaidar hukumar EFCC, Nicholas Ojehomon, wanda ya faɗi a kotun cewa ba a tura kuɗin karatar ƴaƴan gidan Yahaya...
    Alkaluman hukumar kwastam ta kasar Sin sun nuna cewa a watan Afirilun bana, hada-hadar cinikayyar shige da ficen hajoji ta amfani da kudin kasar yuan ta karu da kaso 5.6 bisa dari. Alkaluman da hukumar ta fitar a Juma’ar nan sun nuna cewa, adadin hajojin da kasar Sin ta fitar ya karu da kaso 9.3 bisa dari a shekara zuwa yuan tiriliyan 2.27, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 314, yayin da adadin hajojin da kasar ta shigo da su daga waje ya karu da kaso 0.8 bisa dari a shekara zuwa kimanin yuan tiriliyan 1.57. Cikin watanni 4 na farkon shekarar bana, jimillar hajojin da Sin ta shigo da su, da wadanda ta fitar ketare a hada-hadar kudin kasar yuan sun...
    Ƙungiyar Allied Group of Nasarawa Professionals (AGNP), wadda ta ƙunshi ’yan kasuwa da masu sana’o’in hannu, ta goyi bayan tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Mohammed Adamu, wanda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a 2027. A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ofishinta da ke Keffi, AGNP ta ce matakin da Adamu ya ɗauka na tsayawa takara ya sanya al’ummar jihar cikin farin ciki. ’Yan sanda sun kama harsasai 500 a Filato Jami’an tsaro na ba da gudunmawar aikata miyagun laifuka a Nijeriya — Zulum “Wannan lokaci ne na kyawawan fata ga jiharmu,” in ji ƙungiyar. Ƙungiyar ta yi alƙawarin tattara ƙuri’u aƙalla miliyan daya domin mara wa Adamu baya a zaɓen. AGNP ta yaba...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Masana harkokin masana tsaro sun nuna rashin amincewarsu da iƙirarin sojojin Najeriya cewa baƙi daga ƙasashen waje ne ke kai yawancin hare-haren da ake kaiwa al’ummomin ƙasar, musamman a jihohin Filato da Benue. Wannan ƙalubalen ya fito ne bayan wata sanarwa da Hedikwatar Tsaro ta yi a ranar Alhamis, cewa yawancin hare-haren da ake kai wa manoma da kashe-kashe a sassan kasar, makiyaya ne ’yan kasashen waje suka fi aikatawa. Daraktan Ayyukan Yada Labarai na Tsaro, Manjo-Janar Markus Kangye, ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da hare-haren a kan manoman. Wani kwararre a kan sha’anin tsaro, Jackson Lekan, ya ce  bayanan Manjo-Janar Kanye ya nuna laifi da kuma gazawar hukumomin da ke da alhakin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bukukuwan cika shekaru 80 da cimma nasara a yakin kishin kasa na tsohuwar Tarayyar Soviet. An gudanar da faretin soja na ranar samun nasara, wanda ke ayyana cika shekaru 80 da samun nasara a yakin kishin kasa na Tarayyar Soviet ne a birnin Moscow. Shugabanni daga kasashe da hukumomin duniya sama da 20 ne aka gayyata domin halartar bukukuwan. (Fa’iza Mustapha)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A wani bangare na manufofinsu na kara yawan masu kada kuri’a, Alhaji Gamawa ya bayyana cewa, kungiyar mai zaman kanta za ta taimaka wa ‘yan kasa wajen karbar katin zabe, “Lokacin da INEC ta bude dandalin rajistar katin zabe, za mu taimaka musu wajen karbar katin zabe domin su bada gudunmawa a zabe da kuma amfani da ’yancinsu. Gamawa ya kuma yi magana kan muhimmancin samun katin shaidar zama dan kasa, inda ya ce, yayin da tsaro ya yi karanci, abu ne mai sauki a laka wa dan Nijeriyar ba shi da katin dan kasa sharrin zama bako ko dan mamaya ko kuma sanya shi cikin masu garkuwa da mutane. “Rashin katin shaidar zama dan kasa babbar matsala ce ga...
    Masana harkokin masana tsaro sun nuna rashin amincewarsu da iƙirarin sojojin Najeriya cewa baƙi daga ƙasashen waje ne ke kai yawancin hare-haren da ake kaiwa al’ummomin ƙasar, musamman a jihohin Filato da Benue. Wannan ƙalubalen ya fito ne bayan wata sanarwa da Hedikwatar Tsaro ta yi a ranar Alhamis, cewa yawancin hare-haren da ake kai wa manoma da kashe-kashe a sassan kasar, makiyaya ne ’yan kasashen waje suka fi aikatawa. Daraktan Ayyukan Yada Labarai na Tsaro, Manjo-Janar Markus Kangye, ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da hare-haren a kan manoman. An kashe mutane da yawa tare da raba wasu dubbai da gidajensu a jihohin Filato da Benue a sakamakon hare-hare da makiyaya ɗauke da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hukumomi a jihar Yobe sun ɗora alhakin ƙazancewar matsalar tamowa a kan rikicin Boko Haram da rashin shayar da jarirai nonon uwa yadda ya kamata da kuma gurɓacewar harkar kiwon lafiya, da sauran su. Bayanin hakan na zuwa ne bayan Babban Jami’i mai Kula da Ayyukan Jinƙai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Mista Mohamed Malick Fall, ya sanar cewa yara miliyan daya a jihohin Borno da Adamawa da Yobe suna fuskantar barazanar rasa rayukansu sakamakon cutar tamowa a bana. An kuma ruwaito shi yana cewa wannan adadi ya ruɓanya na yaran da suka fuskanci barzanar a bara. NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ’Ya’yansu DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan...
    Minista Tuggar ya bayyana cewa, kasar Cuba ta taka mihimmiyar rawa wajen samar da ‘yancin kai ga wasu kasashen Afrika a lokacin da ake gwagwarmaryar kwato ‘yanci daga ‘yan mulkin mallaka a shekkarun 60s, 70s, 80s da 90s. “Cuba da Nijeriya sun yi aiki tare wajen yaki da ‘yan mulkin mallaka a kasashen Angola, Namibia, Afrika ta Kudu da Zimbabwe” in ji shi, ya kara da cewa, wannan sabon yarjejeniyar za ta karfafa hadin kai a bangarorin kimiyya da fasaha, bincike da kuma samar da ci gaba mai dorewa. A nasa tsokacin, Ministan harkokin waje na Cuba, ya ce, dangantakar da ke tsakanin Cuba da Afrika mai karfi ne, ya kuma gode wa Nijeriya a kan goyon bayan da ta...
    Kwamandan dakarun kare juyin musulunci na Iran Janar Husaini Salami ya bayyana cewa; Dangane da Shirin Nukiliyar Iran, muna bai wa diplomasiyya fifiko, amma kuma a lokaci daya muna cikin Shirin fuskantar kowane irin yaki duk yadda ya zo. Janar Salami wanda ya gabatar da jawabi a wurin karrama shahidan yi wa kasa hidima, a hubbaren Imam Ridha ( a.s) ya kuma kara da cewa;  Ya kamata Amurkawa su kwana da sanin cewa, idan su ka yi mana barazana, to a shirye muke domin fuskantar kowane irin yaki, a duk yadda ya zo. Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musuluncin na Iran ya kuma zargi Amrukawa da cewa su, ba masu cika alkawali ba ne, saboda yadda su ka yi...
    Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-husy ya bayyana cewa kisan kiyashin  da HKI take yi wa Falasdinawa a tsawon  watanni 19 a jere, shi ne laifi mani muni  akan bil’adama da ya faru a cikin karni daya. Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kuma ce, abinda ya kara munin wannan laifin shi ne yadda yake faruwa a tsakiyar duniyar musulunci,kuma dukkanin duniya tana Kallon abinda yake faruwa. Shugaban na kungiyar Ansarullah ya kuma ce, a baya, ba a Kallon laifuka irin wadannan kai tsaye ta talbijin amma a yanzu ana Kallon ta akwatin talabijin. Shugaban kungiyar ta “Ansarullah” ya kuma yi gargadin cewa da akwai sakamakon da zai biyo bayan wadannan manyan laifuka,yana mai kara da cewa. Alummar musulmi,...
    Shugabannin kasashen Rasha da China Sun yi alkawalin fuskantar siyasar Amurka akansu,a yayin wani taro da su ka yi a birnin Moscow a daidai lokacin bikin tunawa da zagayowar cikar shekaru 80 da samun galaba akan ‘yan Nazi na kasar Jamus. Shugaba Vladmir Putin na Rasha da takwaransa na China Xi Jing Ping sun yi tattaunawa ta fiye da sa’oi 3, sun rattaba hannu akan yarjeniyoyi a tsakaninsu da su ka kunshi kara yawan hannunu jarin da su ka zuba a cikin kasashen junansu, haka nan kuma yin aiki a tsakaninsu domin tabbatar da zaman lafiya a duniya sannan kuma da zurfafa girman alaka a tsakaninsu. Bayanin bayan taron kasashen biyu ya kunshi nuna damuwa akan yadda Amurka take kara...
    Hukumar kare hakokin masu sayayya ta ta kasa tare da haka da Hukumar Kare Data ta kasa NDPC ne, suka gudanar da binciken na watanni 38.   A cikin binciken na su, sun bayyana yadda ake take saba ka’ida tare da take dokar kasa da kuma take hakkin ‘yan Adama na kasa da kasa.   Wannan Jaridar na da ra’ayin cewa, ‘yayan Kotun uku da Mai Shari’a Alkalan Kotun Thomas Okosun da ya yanke wannan hukunci, sun canci yabo kan tsaywar da suka yi kai da Fata na yanke wannan hukuncin, duk da matsin lambar da suka fuskanta, inda suka tabbatar da ikon da Hukumomin FCCPC da NDPC suke da shi.   Kazalika, abinda ya kara nuna mahimmancin hukuncin Kotun,...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Alhamis cewa, a yayin da ake fuskantar sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a duniya, kasashen Sin da Rasha sun ci gaba da zurfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa, da hadin kai bisa manyan tsare-tsare, da kiyaye daidaito da hadin gwiwa a harkokin kasa da kasa, da sanya kwanciyar hankali da kyakkyawan kuzari a duniyar mai fuskantar sauyi da tashe-tashen hankula. Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yayin ziyarar da ya kai kasar ta Rasha. Yana mai cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha ta samu ci gaba mai dorewa, cikin koshin lafiya kuma a babban mataki, sakamakon...
    Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni a ranar Alhamis ya ziyarci sojojin Hedikwatar Task Force Brigade ta 27 Buni Gari, domin jajantawa waɗanda aka kashe kan harin da ’yan tada ƙayar baya suka kai.  A cikin jawabinsa Gwamna Buni ya bayyana cewa, abin takaici ne ga sake ɓarkewar tashe-tashen hankula da kuma hare-haren da ake kaiwa jami’an tsaro. ’Yan sanda sun ƙaddamar da ƙwararrun Jami’an tsaro saboda makarantu a Bauchi An gurfanar da mutum 10 kan yi wa nakasasshiya fyaɗe a Kaduna Gwamnan ya jajanta wa sojoji da iyalan ma’aikatan da suka mutu, yana mai cewa, “Jami’an ba su mutu a banza ba, sun mutu suna ƙoƙarin kare ƙasarsu sosai”. Ya bayar da tallafin Naira miliyan 2m ga kowane iyalan...
    A yau Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Rasha Vladimir Putin suka rattaba hannu kan wata sanarwa ta hadin gwiwa game da kara zurfafa hadin gwiwar abokantaka bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni tsakanin Sin da Rasha a sabon zamani. (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Babban Sufeto Janar na ’yan sandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun ya ƙaddamar da Ƙwararrun Jami’an tsaro da za su kare makarantu a Bauchi, Egbetokun ya ƙaddamar da tawagar ne a ranar Alhamis a Bauchi. A wajen ƙaddamar da taron masu ruwa da tsaki na ‘Saɓe Schools’ a ɗakin taro na otal ɗin Hazibal.  Ya ce, ta hanyar haɗa kai da masu ruwa da tsaki ne jami’an tsaro za su iya kaiwa ga samar da ingantaccen tsaro a makarantu ga yaran Najeriya. An gurfanar da mutum 10 kan yi wa nakasasshiya fyaɗe a Kaduna An zaɓi Robert Prevost sabon fafaroma Egbetokun wanda ya samu wakilcin AIG Abubakar Sadiƙ Aliyu, ya shawarci Kwamishinan ’yan sandan jihar da ya yi amfani da ƙwarewarsa...
    Wata kotun majistare da ke titin Ibrahim Taiwo a Kaduna ta gurfanar da wasu mutane 10 da suka haɗa da kaka, bisa laifin yi wa wata yarinya ’yar shekara 16 fyaɗe a ƙauyen Likoro da ke ƙaramar hukumar Kudan ta jihar. An ruwaito cewa wanda ake zargi mutum na 11 na hannu a lokacin da shari’ar ta taso, ranar Alhamis. An zaɓi Robert Prevost sabon fafaroma Ficewar ’Yan Majalisa 3 a PDP: Raɗɗa ya halarci zauren Majalisar Wakilai Waɗanda ake zargin, a cewar rahoton farko da aka samu, sun ce wacce aka yi wa fyaɗen an yi ta aikat fyaɗen a lokuta daban-daban ta hanyar yaudara da kuma lallashinta ta zuwa wurarensu daban-daban inda suke da masaniya game da ita....
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa akwai bukatar kasashen Indiya da Pakisatan su daure su daina musayar wuta a tsakaninsu saboda tabbatar da zaman lafiya a yankin Asiya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a safiyar yau Alhamis bayan isarsa birnin News Delhi. A jiya larabace sojojin kasar Indiya suka cilla makamai masu linzami kan kasar Pakisatan da kuma yankin Kashamir da ke karkashinn ikon Pakisatn. Inda mutane 31n sauka rasa rayukansu a yayinda wasu 46 suka suka ji Rauni. Shehbaz Sharif firai ministan kasarPakisatan ya bayyana cewa kasar Pakisatan zata rama, kuma ya sha alwashin maida martani kan duk wani jinin mutanen Pakisatan da sojojin Indiya suka zubar....
    Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kasim, ya bayyana cewa mutanen kasar Lebanon zasu ci gaba da gwagwarmaya da HKI wacce ta ke mamaye da wasu kasashen larabawan yankin har zuwa nasara. Tashar talabijibn ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sheik Kasim yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar ta kafar bidiyo a taron da aka fara gudanarwa a yau a makarantar Darushafia dake birnin Qom. Taron na Qom yana Magana dangane da “Makarantun Hauza a Qum, Juyin juya halin musulunci a Iran da kuma Gwagwarmaya’. Sheik Kasim ya kara da cewa mutanen kasar Lebanon sun fara gwagwarmaya ne bayan gwamnatin HKI ta mamaye kasarsu, sannan bayan sun sami jagoranci da tunanin Imam Khumaini (q)...
    Wasu yan jaridu masu bincike a kasar Amurka sun gano sunan sojan HKI wanda ya bindige yar rahoton tashar Aljazeera ta kasar Qatar a shekara ta 2022 a lokacinda take Shirin bada rahoton hare-harenn da sojojin yahudawan suke kaiwa kan wata unguwa ta Falasdinawa a birnin Jenin na yankin yamma da Kogin Jordan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wadanda suka shirya film na tattara bayanai yadda aka kashe Shirin Abu Akela wato ‘ Zeteo’ dake da cibiya a birnin Washington na kasar Amurka na cewa sunan sojan HKI ta ya kashe Shirin shi ne Alon Skajio, wanda shima daga baya an kashe shi a birnin na Jenin daga bayan a wani farmakin da sojojin yahudawan suka...
    Tsohon ministan kudin kasar Amurka John Connally ya ce, dala kudi ne na Amurka, amma matsala ce ga sauran kasashen duniya. Yanzu haka tsarin kudin na haifar da karin radadi ga kasashe daban daban, sakamakon matakan kasar Amurka na kashin kai, lamarin da ya sanya dimbin kasashe neman kauracewa tsarin dalar Amurka. Misali, a rubu’in farkon bana, darajar cinikin da kasar Sin ta yi tare da kasashen Malaysia da Cambodia da kudin RMB, ta karu da kaso 27%, da 24%, bisa makamancin lokacin bara. Kana a nata bangare, kasar Najeriya za ta kulla yarjejeniyar musayar kudin Naira zuwa kudin Sin RMB kai tsaye, tare da kasar Sin, bisa wani labarin da jaridar Vanguard ta kasar Najeriya ta gabatar. Kudi wani...
    A yau ne aka bude kasuwar baje koli na kayakin da suka shafi man fetur da gasa wadanda aka kera a JMI karo na 29  a yau a nan birnin Tehran. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kasuwar zata ci ne daga yau 8-11 ga wannan watan na mayu da muke ciki. Labarinn ya kara da cewa kamfanoni fiye da 2000 daga ciki da kuma wasu kasashen duniya  14 ne suka halarta ta. Baje kolin yana nuna matsayin JMI a fagen makamashi a duniya.
    Fadar Vatican ta sanar da Robert Prevost a matsayin sabon fafaroma, wanda zai maye gurbin Fafaroma Francis. Sabon fafaroman wanda shi ne na farko daga ƙasar Amurka kuma wanda zai jagoranci cocin na Katolika na duniya. Ficewar ’Yan Majalisa 3 a PDP: Raɗɗa ya halarci zauren Majalisar Wakilai An kama mutum 6 da ake zargi kan garkuwa da mutane Robert Prevost zai yi amfani da sunan Leo a muƙamin – wanda shi ne fafaroma na 14 da ya yi amfani da sunan (Pope Leo XIV). Sabon Fafaroman mai shekara 69 ya shafe shekaru yana ayyukan addini a ƙasar Peru.
    Yau Alhamis, kakakin ofishin jakadancin Sin dake Amurka ya amsa tambayoyi game da taron koli na tattaunawa kan batun ciniki da tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka.   A cewar kakakin, bangaren Amurka ta aikewa kasar Sin sakwanni da dama ta hanyoyi daban-daban don bayyana fatanta na tattaunawa da Sin kan batun harajin kwastam da sauransu. Kuma Sin ta yanke shawarar amincewa da shawarwarin ne bayan ta nazarci sakwannin da Amurka ta aika mata, kuma bisa rokon bangaren Amurka ne za a gudanar da shawarwarin. Ya ce Sin na nacewa ga matsayin kin yarda da matakin Amurka na yi gaban kanta wajen kakkabawa sauran sassan duniya harajin kwastam, kuma za ta ci gaba da kiyaye muradunta mai dacewa da kiyaye...
    Da safiyar Alhamis ɗin nan ne Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa ya halarci zauren Majalissar Wakillai ta ƙasa domin sheda ficewar Ƴan Majalissa uku na Jihar Katsina daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC Ƴan majalissar sun haɗa da Ɗan majalisa mai wakiltar (Mashi/Dutse) Hon. Salisu Yusuf Majigiri, da na (Bakori/Ɗanja) Hon. Abdullahi Balarabe Dabai, sai na (Batsari/Safana/Ɗanmusa) Hon. Iliyasu Abubakar. An kama mutum 6 da ake zargi kan garkuwa da mutane A yi amfani da fasahar zamani don yaƙar ta’addanci — Ganduje Gwamnan Raɗɗa ya taya ’yan majalissar murnar dawowa cikin Jama’iyyar APC, wanda dawowar su jam’iyyar ya nuna irin haɗin kai da jam’iyyar take da shi a Jihar Katsina.
    Hukumar jindadin Alhazai ta jihar jigawa ta gudanar da taro da shugabanin shiyya shiyya da kuma jami’an alhazai na kananan Hukumomi Jihar 27 a shelkwatar hukumar dake Dutse gabannin fara jigailar maniyatan aikin hajjin bana. A lokacin da yake jawabi, Darakta Janar na Hukumar Alhaji Ahmed Umar labbo ya ce taron yana da muhimmanci kasancewar aiki yayi nisa na fara jigilar maniyata zuwa kasa mai tsarki. Yana mai cewar, hukumar ta kammala duk wani shiri ga maniyyata domin fara jigilar su zuwa kasa mai tsarki. Alhaji Ahmed Umar Labbo ya kara da cewar, a lokacin taron da suka gudanar da jami’an sun rabawa shugabanin shiyya-shiyya da jami’an su dukkanin kayayyakin maniyyata da dukkan sauran muhimman abubuwa daya dace. Game da...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Akwa Ibom ta ce, ta kama wasu mutum shida da ake zargi da yin garkuwa da wasu mutane a jihar kwanan nan. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan, DSP Timfon John ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya sanarwa manema labarai a ranar Alhamis a garin Uyo, inda ya ce an kama su ne biyo bayan sahihan bayanai game da shirin yin garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Eket. A yi amfani da fasahar zamani don yaƙar ta’addanci — Ganduje Sojoji sun kama mutum 4 kan zargin ta’addanci a Taraba John wanda ya bayyana cewa mace ɗaya tilo a cikin waɗanda ake zargin ba ’yar Najeriya ba ce, ya bayyana cewa an...
    Tawagar jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta haɗa da sakataren gwamnatin jihar, da masu ba da shawara na musamman guda biyu, da babban sakataren ZITDA, tare da Siobhan Wilson, shugaban Oracle na Ingila da kuma babban mataimakin shugaban EMEA.   Sanarwar ta ƙara da cewa: “Gwamnatin jihar Zamfara ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya mai muhimmanci tare da Oracle don bunƙasa fasahar dijital a faɗin jihar, wanda aka samu ta hanyar Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Zamfara (ZITDA), haɗin gwiwar za ta yi amfani da ƙwarewa da ayyukan koyo na makarantar Oracle da jami’ar Oracle a ƙoƙarinsu na kawo sauyi. “Haɗin gwiwar yana nuna sadaukar da kai ga ilimi da saka hannun jari a makomar matasan Zamfara,...
    Dakarun Birget na 6 na Sojin Najeriya da ke Jalingo Jihar Taraba sun cafke wasu mutane huɗu da ake zargin cewa ’yan ta’adda ne. Kama waɗanda ake zargin ya biyo bayan wani samame da sojojin  suka gudanar a ranar 7 ga Mayu, 2025 a Ƙaramar Hukumar Arɗo-Kola da ke jihar. Kakakin Rundunar, Kyaftin Oni Olubodunde, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a garin Jalingo. Ya bayyana cewa rundunar ta sami kiran gaggawa dangane da shigowar wasu mutane ɗauke da makamai a yankin. ’Yan sanda sun kama harsasai 500 a Filato Jami’an tsaro na ba da gudunmawar aikata miyagun laifuka a Nijeriya — Zulum Kyaftin Oni ya ƙara da cewa dakarun sun yi gaggawar...
    Amurka ta matsa wa gwamnatocin wasu ƙasashe da Shugaba Donald Trump ya ƙaƙaba musu haraji su  amince da kamfanin intanet na Starlink mallakin Elon Musk a ƙasashensu. Elon Musk shi ne mai kuɗin duniya kuma babban makusanci ne ga Shugaba Donald Trump. Jaridar Washington Post ce ta ruwaito hakan a ranar Laraba, tana mai ambaton sakonnin waya na Ma’aikatar Harkokin Waje. Sakonnin sun nuna yadda ofishin Jakadancin Amurka da ma’aikatar suka matsa wa ƙasashe don su kawar da duk wata cikas ga kamfanonin tauraron dan Adam, yana mai ambaton kamfanin Starlink da sunanta, kamar yadda jaridar Post ta ruwaito. Takardun ba su nuna cewa gwamnatin Trump ta buƙaci a ba da fifiko ga Starlink a musayar rage haraji ba, kamar...
    Shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga taron musayar al’adu da cudanyar al’umma da aka shirya domin murnar cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiya da jama’ar kasar Sin suka yi a kan zaluncin Japan da kuma kazamin yakin ceton kasa na tsohuwar tarayyar Soviet. A cikin sakon nasa, Xi ya yi nuni da cewa, shekaru 80 da suka gabata, al’ummomin kasar Sin da na kasar Rasha sun bayar da gudummawa mai tarihi da ba za a taba mantawa da ita ba wajen samun nasarar yaki da zaluncin danniya a duniya, tare da kulla kakkarfar alaka da ba za a iya kassarawa ba ta hanyar sadaukar da jini, wadda ta kafa tubulin raya dangantakar...
    ’Yan sanda sun gano harsasai guda 500 a wata maɓoyar masu aikata laifuka da ke kusa da hanyar Bauchi a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato. Kwamishinan ’yan sandan jihar, Emmanuel Adesina, ya ce an gano harsasan ne ta hanyar rahotannin sirri, inda ya bayyana hakan a matsayin babbar nasara a yaƙi da aikata laifuka a jihar. Kwamishinan ya ci gaba da bayanin cewa an gano harsasan ne bayan wani kisan kai da ya faru a yankin, inda aka kashe wani da ba a gane ko wanene ba. “Bayan samun rahoton faruwar lamarin, nan take muka fara gudanar da bincike domin gano yanayin da ya kai ga mutuwar wanda aka kashe. An kwantar da kishiyoyi a asibiti bayan...
    An kwantar da wasu matan aure kishiyoyin juna a asibiti bayan da suka sha maganin kara sha’awa domin burge mijinsu bayan ya auro mata ta uku. Kishiyoyin biyu da ke yankin Dakwa a Abuja sun sha maganin gargajiyan, wanda aka fi sani da kayan mata ne, kwana uku bayan amaryar da mijinsu ya auro ta tare. Da take tabbatar da faruwar lamarin, mijin nasu ya ce bayan kai su asibiti ne aka yi musu gwaji aka gano cewa wasu gaɓoɓinsu sun samu matsala, wanda ake zargin maganin da suka sha ne ya haddasa. Ya ce, “ina gidan amarya aka kira ni cewa matana ba su da lafiya, inda na je na samu suna birgima cewa cikinsu na ciwo. Sai na...
    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi tsokaci kan jita-jitar cewa: Shugaban kasar Iran zai gana da shugaban kasar Amurka Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya yi watsi da jita-jitar da ake yadawa game da batun cewa shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian zai yi wata ganawa da shugaban Amurka Donald Trump a mako mai zuwa, da rashin gamsuwar bangaren Amurka da Iran da shiga tsakanin masarautar Oman, da kuma cewa Iran ta gabatar da shawarar gudanar da shawarwari kai tsaye da Amurka, da sauran da’awar karya a matsayin batutuwa na jita-jita maras asali da tushe. Dangane da wata tambaya game da jerin jita-jita da ake yadawa a kafafen yada labarai game da matsayin tattaunawar da ake yi tsakanin Iran...
    Kakakin gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa: Duk wanda ya canza sunan Tekun Fasha, tabbas ya jahilci tarihin dubban shekaru na Iran Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatimah Mohajerani ta yi tsokaci kan rahotannin da suke cewa: Shugaban Amurka Donald Trump na yunkurin sauya sunan yankin tekun Fasha. Ta jaddada cewa “wadanda ke neman canza sunan Tekun Fasha ba su fahimci tarihin dubban shekaru na Iran ba.” Malama Mohajerani ta rubuta a dandalin na X cewa: Tekun Fasha bai takaita da kasancewa sunan yanki kadai ba, a’a ya zama wani muhimmin bangare na tarihin al’ummar Iran. Ta kara da cewa: “Wadanda ke neman canza sunan ‘Tekun Fasha’ ba su fahimci tarihin Iran na dubban shekaru ba. Wannan yunkuri na...
    Kasar Yemen ta jaddada cewa: Ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kai munanan hare-hare kan Amurka idan ta dawo da kai hari a kan kasarta Sojojin Yemen sun sanar da aiwatar da hare-haren soji guda uku kan tashar jiragen sama na Ramon, wani muhimmin wuri ne na makiya yahudawan sahayoniyya, da a wurin akwai jirgin ruwan Amurka Truman mai dauke da dauke da jiragen saman yakin Amurka da kuma wasu kayayyakin yakinta. Majiyar sojojin Yemen ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, sojojin samanta sun gudanar da ayyukan soji guda biyu, na farko a kan filin jirgin saman “Ramon” na haramtacciyar kasar Isra’ila da ke yankin Umm al-Rashrash a kudancin kasar Falasdinu da aka...
    Falasdinawa da dama ne suka yi shahada tare da jikkata sakamakon hare-haren bama-bamai da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gidan abinci da wata shahararriyar kasuwa a Gaza Akalla Falasdinawa 20 ne aka kashe tare da raunata wasu da dama a jiya Laraba a wani sabon kisan kiyashi da jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a wani gidan cin abinci na kasar Thailand da wata shahararriyar kasuwa a yammacin birnin Gaza. Sannan suka ci gaba da kai wasu hare-haren wuce gona da iri kan yankunan zirin Gaza a rana ta 213 a jere. Majiyoyi watsa labarai a Gaza sun rawaito cewa: Jiragen saman yakin mamayar Isra’ila sun kai wani hari kai tsaye kan gidan cin abinci...
    Fira ministan kasar Siriya ya bayyana cewa: Kasar Siriya zata gudanar da tattaunawa ba na kai tsaye ba da haramtacciyar kasar Isra’ila! Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Siriya Abu Mohammed al-Julani ya sanar a jiya Laraba cewa: Kasar Siriya zata gudanar da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba da gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ta hanyar masu shiga tsakani domin kwantar da hankulan al’amura da kuma hana bullar rashin kwanciyar hankali a yankin. Al-Julani ya yi nuni da cewa: “Shisshigin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi ba bisa ka’ida ba ne, kuma sun bayyana cewa: Siriya ta amince da yarjejeniyar kawo karshen rikici ta shekara ta 1974,” yana mai cewa “Tsarin mulkin kasar Siriya zai tantance ‘yancin...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk wanda ya shekara arba’in zuwa sama ya san irin tarbiyyar da ya samu daga wurin iyayensa a da, da irin mu’amalar da ke tsakaninsa da iyaye da kuma irin shaƙuwar da ke tsakanin ’ya’ya da iyaye. A yanzu kuwa, abubuwa sun canza daga yadda aka san su, inda abubuwa suka rincaɓe suka yi wa iyaye yawa. Ɗaya daga cikin manyan sauyin da aka samu shi ne aikin gwamnati ko aikin wata da iyaye mata suke yi a wannan zamani wanda a wasu lokuta ke barazana ga irin kulawar da ’ya’ya suke samu. NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ‘Yan Gwagwarmaya Ke Shiga Tasku A Najeriya? DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa...
    “Duk da cewa, ba zan iya yin cikakken bayani dangane da sabbin dabarun da muka dauka ba. Amma mutanen Yobe su kwantar da hankalinsu kuma abubuwa za su inganta.”   Har ila yau, ya yi karin haske dangane da wasu muhimman matakan da za a dauka don magance rashin tsaro a jihar, ciki har da tura karin sojoji tare da kayan aikin tsaro. A nasa bangaren, Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yaba wa COAS kan daukar matakan gaggawa wajen mayar da martani kan hare-haren kwanan nan, sannan ya yi wa sojojin da suka rasu addu’a.   Ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin farar hula da sojoji, inda ya bukaci karfafa hadin gwiwa wajen bayar da bayanan sirri...
    Burin Arsenal na lashe gasar UEFA a karon farko a tarihinta ba zai cika a wannan shekarar ba, sakamakon rashin nasarar da ta yi a hannun PSG a wasan zagayen na kusa da na karshe, Arsenal ta buga wasan karshe a UEFA sau daya a shekarar 2006 tsakaninta da Barcelona. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A jiya ne jakadan Sin a Najeriya Yu Dunhai ya gana da ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tuggar. Jakada Yu ya bayyana cewa, ganawar da ta gudana tsakanin ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da mista Tuggar a kasar Brazil a baya-bayan nan, ta aike da sako mai karfi cewa, Sin da Najeriya na tsayawa tsayin daka kan bin ra’ayin bangarori daban-daban, da tabbatar da adalci da daidaici. A nasa bangare, minista Tuggar, ya yi kyakkyawan nazari kan yadda huldar dake tsakanin kasashen biyu ke gudana, ya kuma jaddada cewa, Najeriya na fatan karfafa hadin gwiwa da kasar Sin a fannonin cinikayya, zuba jari, da hada-hadar kudi da dai sauransu, da zurfafa tuntubar juna da hadin gwiwa a harkokin...
    Bayanai na baya-bayan nan da hukumar kula da harkokin musayar kudaden waje ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, ya zuwa karshen watan Afrilu, asusun ajiyar kudaden waje na kasar Sin ya kai dalar Amurka biliyan 3281.7, wanda ya karu da dalar Amurka biliyan 41 ko kashi 1.27 bisa dari daga karshen watan Mayu. Kazalika, ma’aunin asusun ajiyar kudaden waje na kasar Sin ya kasance cikin daidaito da sama da dalar Amurka tiriliyan 3.2 na tsawon watanni 17 a jere.   Wani jami’in hukumar musayar kudaden waje ta kasar Sin ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana cikin kyakkyawan yanayi, tare da nuna juriya da karfi a ci gaban tattalin arziki, wanda hakan zai taimaka wajen tabbatar da...
    A cewar sa, wannan bita tana da nufin tantance yadda aka samu cigaba a aiki, da kuma tabbatar da cewa hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar suna tafiya daidai da abin da aka ɗora masu a matsayin nauyi.   Ya ce: “Muna nan ne don sauraron shugabannin hukumomi domin mu ga yadda suka aiwatar da muhimman abubuwan da muka rattaba hannu a kai. Idan akwai ƙalubale, za mu tattauna su. Idan akwai cikas, za mu duba abin da za mu iya yi domin shawo kansu.”   Ministan ya bayyana wannan taro a matsayin hanyar tantance kai kafin a kai tsakiyar wa’adin gwamnatin yanzu.   Ya ce: “Ku tuna cewa wannan gwamnati ta fara aiki kusan shekaru biyu da suka gabata. Cikin...