2025-09-17@23:39:50 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1786
«da ƙungiyar»:
Gwamnatin Jigawa ta amince da sabon tsarin ka’idojin aiki domin aiwatar da shirin kula da lafiyar mata masu juna biyu, da jarirai da ƙananan yara kyauta a cibiyoyin lafiya na jihar. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya bayyana haka bayan zaman majalisar zartarwa da aka gudanar a gidan gwamnati Dutse. Ya ce ka’idojin za su taimaka wajen inganta nagartar hidima, fayyace karewar ma’aikata, da kuma tabbatar da gaskiya, da bin doka da tsari a asibitoci. Kwamishinan ya ƙara da cewa matakin ya dace da manufar gwamnatin jihar na rage mace-macen mata da yara da kuma tabbatar da samun ingantacciyar kulawa ga kowa. Ya ce za a fara aiwatar da tsarin nan take, tare da horas da shugabannin asibitoci...

Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Baje Kolin Sin Da ASEAN Ya Fadada Matsayar Bai Daya Ta Cudanyar Sassa Daban Daban
A yau Laraba ne aka bude bikin baje koli karo na 22, na Sin da kasashe membobin kungiyar ASEAN ko (CAEXPO), da kuma taron dandalin kasuwanci da juba jari na Sin da ASEAN ko CABIS, a birnin Nanning na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kai dake kudancin kasar Sin. A shekarun baya bayan nan, Sin da kungiyar ASEAN, sun ci gaba da cimma manyan nasarori tare a fannin bunkasa dunkulewar tattalin arzikin shiyyarsu, da fadada damar bai daya ta cudanyar mabambantan sassa, a gabar da ake fuskantar yanayin tangal-tangal a duniya. Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, ta shaida yadda kaso 92.8 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi suka amince...
Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta sanar da samun nasarar cafke Ifeanyi Eze Okorienta, wanda aka fi sani da “Gentle de Yahoo”, ɗaya daga cikin manyan kwamandojin ƙungiyar IPOB, a wani samame da ta kai a yankin kudu maso gabashin ƙasar. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito wata majiya daga hedikwatar rundunar sojin tana cewa an cafke Gentle de Yahoo ne yayin farmakin da sojojin suka kai a ranar Lahadi kan sansanonin ’yan ƙungiyar a cikin wani dajin da ke ƙaramar hukumar Okigwe a Jihar Imo. An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas Majiyar ta ce a yayin cafke jagoran na IPOB, an kuma ƙwato...
Saboda wannan baiwa daga Allah, iyalai da ‘yan uwan mai akuyar suka sanar da shirye-shiryen gudanar da bikin murnar haihuwar ‘ya’yan akuyar a ranar Lahadi mai zuwa a Garun Dakasoye, karamar hukumar Garun Malam ta Jihar Kano, inda za a yi musu suna da kuma karatun Alkur’ani mai girma. A nasa bangaren, mahaifin budurwar, Malam Aliyu dake Garin Dakasoye, ya tabbatar da cewa za su gudanar da bikin domin nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa wannan ni’ima da ya ba su. Ya kara da cewa: “Mun gode wa Allah bisa wannan arziki, kuma muna sa ran gudanar da bikin tare da sanya musu suna domin nuna godiya ga Allah mai daukaka.” Daga kanmu, magana ta ƙare....

Iran Ta Yi Nasarar Gwajin Tauraron Dan’adam ” Nahid 2″ Da Zai Samar Wa Yankunan Karkara Hanyar Sadarwa Ta “Internet”
Ministan sadarwa na Iran Sitar Hashimi ya bayyana cewa, an sami nasara a gwajin da aka yi na sabon tauraron dan’adam, mai suna “Nahid 2” wnada aikinsa shi ne samar da hanyoyin sanarwa na internet masu nagarta. Ministan sadarwar ya kuma ce dukkanin bangarorin tauraron dan’adam din sun yi aiki yadda ake so a yayin gwajin da hakan yake a matsayin wani ci gaba a fagen sadarwa a Iran. Har ila yau ministan Sadarwar Sitar Hashimi ya kuma ce; A tsakanin kauyuka 10,000 da ba su da hanyoyin sadarwa, yanzu an rage su da 2000, kuma ana ci gaba da aiki tukuru domin isa ga kauyunan da suke nesa,masu wahalar zuwa. Ministan sadarwar na Iran ya kuma kara da cewa;...
Hukumar tarayyar turai ta gabatar da shawara ga kasashe mambobi da su jingine aiki da yarjejeniyar da aka kulla ta kasuwanci da HKI saboda yakin Gaza. A yau Laraba ne dai hukumar tarayyar turai din ta bijiro da wannan shawarar ga kasashen mambobi,sai dai kuma babu cikakken goyon baya daga mafi yawancin kasashen kungiyar da zai sa a yi aiki da shi. Ita kuwa jami’ar harkokin wajen ta tarayyar turai din Kaya Kalas ta gabatar da shawarar a kakaba takunkumi akan wasu ministoci biyu na HKI da kuma ‘yan share wuri zauna da suke amfani da akrfi akan Falasdinawa. Da akwai kungiyoyin kare hakkin bil’adama guda 84 da suke yin kira a yanke duk wata alaka ta kasuwanci da zuba...
Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kano, Alhaji Salim Hashim Idris Gwangwazo, ya kaddamar da shirin kula da ido kyauta domin tallafawa jama’a da ke fama da ‘Glaucoma’ da ke lalata rijiyoyin ido, da ‘Cataract’ wato yanar ido da sauran cututtukan ido. An gudanar da shirin ne a Asibitin Kwalli tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar, ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, da Hukumar Lafiyar Farko ta Jiha, da ƙaramar hukumar da masu bada tallafi daga kasashen waje. Shirin ya haɗa da gwaje-gwajen lafiyar ido, da bayar da magunguna da kuma rarraba tabarau kyauta, musamman ga marasa ƙarfi a cikin al’umma. Shugaban ƙaramar hukumar, ta bakin Kwamishinan Lafiya Alhaji Mustapha Darma, ya bukaci jama’a da su ci gaba da tallafawa gwamnati wajen samar...
Ya ce ya sayi layin wayar ne daga hannun wani Audu, ɗan kungiyar Vikings wanda ya tsere yanzu. A wani lamari kuma, ‘yansanda sun kama wasu mutum huɗu da suka shiga gonar wani mutum a Lapai Gwari, inda suka saci kifi da darajar kuɗinsu ta kai Naira 750,000. Babban wanda ake zargi, Hussaini Garba, ya amsa laifi tare da bayyana Ahmed Yusuf, Ibrahim Musa da Abdulazeez Bawa a matsayin mutanen da suke sayen kifin idan ya sato. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin kasar Iran ta bayyana wasu abubuwan da bata amince da su ba, a jawabin bayan taro na musamman na kungiyar kasashen musulmi ta (OIC) wanda aka gudanar a birnin Doha na kasar Qatar a ranar litinin 15 gawatan Satumba da mukeciki. Sannan ta kara tabbatar da goyon bayanta ga gwagwarmayan da Falasdinawa suke yi da HKI don kwatar kasarsu da ta mamaye. A cikin wani bayanin da ma’aikatar harokokin wajen kasar Iran ta fitar a yau Laraba, Jumhuriyar Musulunci ta Iran, tana kara jaddada goyon bayanta ga al-ummar Falasdina, kuma tana kara jaddada tir da allawai da kissan kiyashin da HKI take yi a Gaza da kuma sauran yankunan falasdinawa da ta mamaye. Kuma tana godewa mutanen kasar Iran...
Hukumar NDLEA ta bayyana cewa wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ce a filin jirgin sama na Kano ta boye jakunkunan ƙwayoyi a cikin kayan matafiyan. An kama shugaban ƙungiyar, Ali Abubakar Mohammed (wanda aka fi sani da Bello Karama), tare da wasu abokan aikinsa. Hukumar ta ce mutanen ukun ba su da laifi kuma an zalunce su ne kawai. An saki su ne bayan bincike da kuma ƙoƙarin diflomasiyya na tsawon makonni. Lamarin ya tayar da hankali kan tsaro a filayen jirgin sama a Nijeriya da yadda masu aikata laifuka ke amfani da fasinjoji marasa laifi. Hukumar ta ce za a ɗauki ƙarin matakai don hana faruwar irin wannan lamari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Ondo ta tabbatar da kama wata mata mai suna Iluyemi Bosede bisa zargin kashe yayarta, Tewogboye Omowumi, a Akure, babban birnin jihar. A cewar sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, Olayinka Ayanlade, ya fitar a ranar Talata, ya ce lamarin ya faru ne a ranar shida ga Satumba, 2025, bayan wata sa’insa da ta kaure tsakanin matar da marigayiyar kan Naira 800. Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya Jami’in ya bayyana cewa Bosede ta ture ’yar uwarta har ta faɗi ƙasa, lamarin da ya haifar da mutuwarta. Ya ce, “Binciken farko ya...
Hukumar NDLEA ta bayyana cewa wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ce a filin jirgin sama na Kano ta boye jakunkunan ƙwayoyi a cikin kayan matafiyan. An kama shugaban ƙungiyar, Ali Abubakar Mohammed (wanda aka fi sani da Bello Karama), tare da wasu abokan aikinsa. Hukumar ta ce mutanen ukun ba su da laifi kuma an zalunce su ne kawai. An saki su ne bayan bincike da kuma ƙoƙarin diflomasiyya na tsawon makonni. Lamarin ya tayar da hankali kan tsaro a filayen jirgin sama a Nijeriya da yadda masu aikata laifuka ke amfani da fasinjoji marasa laifi. Hukumar ta ce za a ɗauki ƙarin matakai don hana faruwar irin wannan lamari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
Mohammad Islami shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya na Iran ta fadi a bayan taron da hukumar ta IAEA dake gudanarwa a Vienna yanzu haka cewa yana neman hukumar ta IAEA ta goyi bayan kudurin da ta fitar kuma ta yi Tir da harin wuce gona iri da hki ta kai kan tashoshin nukiliyarta. Wakilai guda 180 a hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ne suka hallara abirnin viyana daga ranar 15-19 domin gudanar da taron kasa da kasa karo na 69 da hukumar ta duniya ke shiriya a hedkwatarta dake Vienna na kasar Austeria Yace mun bayyana cewa alummar Iran basu da rauni wajen fuskantar duk wata barazana, kuma basu da niyyar mika wuya, ,ya kara da cewa...
Al’ummar garin Dukku a Ƙaramar Hukumar Dukku ta Jihar Gombe sun koka kan mummunan halin hanyar da ta haɗa su da babban birnin jihar, tare da kira ga gwamnati da ta gaggauta gyaran ta. A cewar direbobi, tafiyar Dukku zuwa Gombe wadda a da take ɗaukar mintuna 50 kacal, yanzu ta koma fiye da awa biyu saboda lalacewar hanyar, abin da ke jawo gajiya da takaici ga fasinjoji da masu tuƙi. An fara gina hanyar Gombe-Dukku-Darazo ne tun a shekarun 1980, aka gyara ta a farkon shekarun 2000. Sai dai daga baya aka yi sakaci da ita duk da kasancewarta hanyar da matafiya daga jihohin Adamawa, Taraba, Jigawa, Kano, Bauchi da wasu ke bi. “Gyaran motoci na cinye mana kuɗi”...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Saudiyya na iya taka muhimmiyar rawa wajen hadin kan kasashen musulmi Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Gwamnatin sahayoniyya ba za ta kuskura ta kai hari ko kai wa wata kasa ta Musulunci hari ba matukar kasashen musulmi suka hade kansu; kuma Saudiyya za ta iya taka muhimmiyar rawa a tafarkin hadin kan kasashen musulmi. A yayin ganawarsa da yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman a gefen taron Doha, Pezeshkian ya bayyana jin dadinsa da yadda dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ke kara bunkasa, yana mai cewa: Zurfafa da karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Iran da Saudiyya zai kare muradun kasashen biyu, da kuma muradun al’ummomin kasashen biyu,...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Ta’addancin yahudawan sahayoniyya kan Qatar zalunci ne ga diflomasiyya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Harin wuce gona da iri kan kasar Qatar, wani hari ne da kungiyar yahudawan sahayoniyya ta shirya kai wa, da nufin dakile yunkurin diflomasiyya na kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza. Shugaba Pezeshkian ya bayyana hakan ne a jiya Litinin a yayin taron gaggawa na shugabannin kasashen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa dangane da harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan Qatar. Shugaban ya kara da cewa, wannan cin zarafi na diflomasiyya ya wuce matsayin laifi kawai; ya zama sanarwar aikin rashin kunya da ya...
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta ce: Laifin da Isra’ila ta yi na kashe ‘yan jaridun Yemen babban ta’addanci ne Kungiyar kare hakkin bil’ adama ta Human Rights Watch ta tabbatar da cewa: Harin da yahudawan sahayoniyya suka kai a ranar 26 ga watan Satumba kan ‘yan jaridun kasar Yemen, wanda ya yi sanadiyar mutuwar ‘yan jarida sama da 30, laifi ne da ba za a iya kubutar da girman laifin kan wanda ya aikata ba. A cikin rahoton baya-bayan nan, kungiyar ta fitar ta bayyana cewa, ta tattara bayanan harin da makiya yahudawan sahayoniyya suka kaddamar a ranar 10 ga watan Satumba kan hedkwatar kafafen yada labarai a kasar Yemen, kuma ta yi la’akari da wannan...

Kungiyar Kare Hakkokin Bil’Adama Ta Siriya Ta Bankado Karin Fararen Hula Da Aka Kashe A Rikicin Suweida
Kungiyar Kare Hakkokin Dan Adam ta Siriya ta bayyana sabbin mutanen da suka mutu sakamakon harin Suweida Kungiyar kare hakkin dan adam ta Siriya (SOHR) ta bayyana wasu sabbin fararen hula tara da aka ci zarafinsu a lokacin abubuwan da suka faru a Suweida a watan Yulin da ya gabata. Hukumar da ke sa ido kan lamarin ta bayyana cewa, wadanda aka kashen da suka hada da mata biyu, an kashe su ne a filin wasa a lokacin da wasu ma’aikatun tsaro da na cikin gida na gwamnatin rikon kwarya suke lardin na Suweida, tare da halartar mayakan ‘yan kabilar Larabawan Bedouin. Hukumar da ke sa ido kan lamarin ta ce adadin mutanen da suka mutu a watan Yulin da...
Duk da cewar an yi yarjejeniya tsakanin ɓangarorin biyu, rikici ya sake ɓarkewa bayan NUPENG ta ce Dangote bai cika alƙawari ba. Amma matatar ta musanta zargin, inda ta bayyana cewa ma’aikatanta na da damar shiga ƙungiya idan sun so, amma ba dole ba ne. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Aƙalla masallata 40 ’yan bindiga suka sace a wani masallaci da ke Gidan Turbe a Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara da safiyar wannan Litinin. Majiyoyi sun ce an yi awon gaba da masallatan ne zuwa dazukan Gohori da ke yankin Tsafe. Hauhawar farashi ya ragu a watan Agusta — NBS NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas Wannan harin dai kai tsaye masu ruwa da tsaki na kallonsa a matsayin kawo ƙarshen yarjejeniyar sulhu tsakanin ’yan bindigar da mahukuntan jihohin Zamfara da Katsina. A baya-bayan nan ne jihohin Katsina da Zamfara suka ƙulla yarjejeniyar sulhu tsakaninsu da ’yan bindigar da suka addabi al’ummar jihohin arewa maso yammacin Najeriyar. Yarjejeniyar sulhu da aka cimma...
Yarjejeniyar, a cewar daukacin mahalarta taron, ta nuna wani gagarumin mataki na kawo karshen tashe-tashen hankula, garkuwa da mutane da satar shanu a Arewa maso Yamma, da kuma yankin Arewa. Yarjejeniyar wacce Mai Maradin Katsina da Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi, da shugaban karamar hukumar, Babangida Abdullahi Kurfi suka shirya, ta gudana ne a dajin Wurma, inda ake fama da rashin tsaro. Manyan jagororin ‘yan bindigan da suka hada da Alhaji Usman Kachalla Ruga da Sani Muhindinge da Yahaya Sani (Hayyu) da kuma Alhaji Shu’aibu duk sun yi alkawarin tsagaita wuta. Daga baya suka sako mutanen da suka kama kuma suka bar manoma su koma gonakansu ba tare da wata barazana ba. Sai dai kasa...
Yarjejeniyar, a cewar daukacin mahalarta taron, ta nuna wani gagarumin mataki na kawo karshen tashe-tashen hankula, garkuwa da mutane da satar shanu a Arewa maso Yamma, da kuma yankin Arewa. Yarjejeniyar wacce Mai Maradin Katsina da Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi, da shugaban karamar hukumar, Babangida Abdullahi Kurfi suka shirya, ta gudana ne a dajin Wurma, inda ake fama da rashin tsaro. Manyan jagororin ‘yan bindigan da suka hada da Alhaji Usman Kachalla Ruga da Sani Muhindinge da Yahaya Sani (Hayyu) da kuma Alhaji Shu’aibu duk sun yi alkawarin tsagaita wuta. Daga baya suka sako mutanen da suka kama kuma suka bar manoma su koma gonakansu ba tare da wata barazana ba. Sai dai kasa...
Haka kuma, wannan na faruwa ne makonni biyu bayan yin garkuwa da Pastor Friday Adehi na Christian Evangelical Fellowship of Nigeria (CEFN) tare da wani abokin cocinsa bayan kammala wa’azi. Wannan ya kara nuna yadda matsalar garkuwa ke ta’azzara a yankin Kogi East. A gefe guda, kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), reshen Idah, ta bukaci gwamnati a matakai daban-daban da ta dauki matakan gaggawa don kawo karshen satar mutane a jihar. Shugaban kungiyar, Barr. James Michael, ya ce yawaitar garkuwa a kan titunan yankin ya jefa rayukan jama’a cikin hatsari, don haka gwamnati ya kamata ta dauki tsauraran matakai domin kare lafiyar al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
Kwamitin koli na tsaron kasa ya amince da yarjejeniyar da hukumar makamashin nukiliya ta duniya IAEA Kwamitin koli na tsaron kasar Iran ya yi gargadin cewa, idan aka dauki wani mataki na nuna adawa ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran da cibiyoyinta na makamashin nukiliya, ciki har da sake farfado da kudurorin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da suka kare, za a dakatar da aiwatar da tsare-tsare da yarjejeniyoyin da aka kulla da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA. Sakatariyar kwamitin tsaron kasar Iran ta fitar da wata sanarwa a jiya Lahadi, bayan yarjejeniyar da aka rattabawa hannu tsakanin Seyyed Abbas Araqchi da Rafael Grossi. An yi wannan bayani ne dangane da tsare-tsare da ministan harkokin wajen kasar...
Gwamnatin Sudan ta ce: Babu batun sasantawa da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces na kasar wadanda take daukansu a matsayin ‘yan tawaye Gwamnatin Sudan ta yi watsi da shawarar sasantawa da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces (RSF) da kasashen kasashe masu shiga Tsakani suka gabatar, tana mai jaddada cewa, tana mutunta duk wani kokari da zai taimaka wajen kawo karshen yakin kasar, matukar dai ya mutunta diyaucin kasar da halaltattun hukumomin kasar. Sa’o’i kadan bayan kaddamar da shirin na bangarori hudu masu shiga tsakani wanda ya hada da Masar, Amurka, Saudiyya, da Hadaddiyar Daular Larabawa, na kiran zaman lafiya a Sudan da kawo karshen yakin, dakarun kai daukin gaggawa sun kai hari kan tashar...
Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Barcelona ta koma matsayi na biyu a kan teburin gasar La Liga ta Sifaniya bayan ta lallasa ƙungiyar Valencia a filin wasa na Johan Cruyff da ke birnin Barcelona. Fermin Lopez, Raphinha da Lewandowski ne suka zura ƙwallaye shida a ragar Valencia a wasan da aka buga da misalin ƙarfe 8 na dare agogon Nijeriya. Da wannan nasara, Ƙungiyar da Hansi Flick ke jagoranta ta tara maki 10 a cikin wasanni huɗu da ta buga a gasar. Kano Pillars Ta Samu Nasarar Farko A Gasar Firimiyar Nijeriya Ta Bana Rashford Na Dab Da Komawa Barcelona A Matsayin Aro An yi tsammanin Barcelona za ta fara buga wasan gidanta a sabon filin Spotify Camp Nou da aka...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ambaliyar ruwa na cigaba da salwantar da dukiyoyi da rayukan al’ummomi da dama a sassa daban-daban na Najeriya. Ko a farkon makon nan, hukumomi sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar samun ambaliyar a jihohi akalla 11. Sai dai wasu alummomin tuni suka dauki matakai don rage barnar da ambaliyar ka iya yi musu. NAJERIYA A YAU: Masu Nau’in Jinin AS Sun Fi Masu Nau’in AA Lafiya DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Uku A kan wadannan matakai shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari. Domin sauke shirin, latsa nan
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ƙwallon ɗaya tilo da kyaftin din ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars Ahmed Musa ya ciwa ƙungiyar tayi sanadiyar samun nasarar farko da ƙungiyar tayi tun bayan fara wannan kakar wasannin ta bana. Pillars ta doke abokiyar karawarta Enugu Rangers da ci 1-0 a wasan da suka buga a filin wasa na Sani Abacha dake birnin Kano inda ɗaruruwan magoya bayan ƙungiyoyin biyu suka shaidi wasan. Kano Pillars Ta Ƙulla Yarjejeniya Da Gidan Rediyon RFI Hausa Zan Yi Ƙoƙarin Dawo Da Martabar Kano Pillars A Idon Duniya — Ahmed Musa Kafin yanzu ƙungiyar, mallakar gwamnatin jihar Kano ta yi rashin nasara biyu sannan ta buga canjaras ɗaya a wasanni uku da ta buga a wannan kakar, wannan nasarar da Sai...
A cikin shekaru uku da kafuwarta, gidauniyar Misilli, ta mayar da yara 150 makarantar boko a Jihar Gombe, ciki har da mata 88 da maza 62, tare da ɗaukar nauyin kuɗaɗen karatunsu. Wannan mataki ya taimaka wajen rage nauyin iyaye marasa hali, inda suka samu ’yancin zaɓar makarantun da ke kusa da su. Ambaliya: NEDC ta raba wa mutum 2,200 kayan agaji a Yobe An yi wa zakarun wasan motsa jiki ruwan kuɗi a Akwa Ibom Shirin AGILE ya tallafa wa gidauniyar da litattafai domin ƙarfafa wannan yunƙuri, lamarin da shugabar shirin a Gombe, Dokta Amina Haruna Abdul, ta yaba da shi tare da alƙawarin yin haɗin gwiwa. Ita ma, Dokta Hauwa Yahaya Umar daga SUBEB, ta ce irin wannan...
Ya zuwa ranar Alhamis 11 ga watan nan, lokacin da aka kammala taron baje kolin kasa da kasa na hada-hadar zuba jari da cinikayya na kasar Sin karo na 25, an riga an sanya hannu kan yarjejeniyar gudanar da ayyukan zuba jari a sassa daban daban da yawansu ya kai 1,154, tare da tsara shigar da jarin da ya kai kudin Sin yuan biliyan 644. Yayin taron, tarin kusoshin manyan kamfanonin kasa da kasa sun shaida cewa, har kullum kasar Sin ta zamo wuri da aka fi aminta da shi ta fuskar zuba jari da samar da ci gaba tsakanin sassan duniya. Game da hakan, shugaban kungiyar bunkasa cinikayya ta Amurka dake kudancin kasar Sin Harley Seyedin, ya ce wani...
An gano gawar Haneefa, yarinya ’yar shekara uku da ruwa ya tafi da ita lokacin da yayarta Fatima, ke goye da ita yayin ambaliyar da ta rutsa da su a Tudun Jukun da ke Zariya, a Jihar Kaduna. An tsinci gawar ne bayan kwanaki shida da aka kwashe ana nemanta, a gangaren ƙasan Kilaco, unguwar Gyallesu, da misalin ƙarfe 11 na safiyar ranar Lahadi. Ambaliya: NEDC ta raba wa mutum 2,200 kayan agaji a Yobe Likitoci sun janye yajin aikin da suka fara bayan kwana biyu Babban jami’in ƙungiyar Red Cross a Zariya, Abdulmumin Adamu ne, ya tabbatar da gano gawar, inda ya ce hakan ya kawo ƙarshen binciken neman mutanen da ruwa ya tafi da su. A ranar 8...
Liɓerpool ce mai riƙe da kofin kuma na 20 jimilla da ta lashe a kakar da ta wuce, iri ɗaya da yawan wanda Manchester United take da shi a tarihin gasar premier ta ƙasar Ingila. Ga jerin ƙungiyoyin da suka ci ribar kasuwancin sayen ƴan ƙwallo da waɗanda suka yi hasara a cikin ƙungiyoyin da suke buga gasar Premier League ta bana. Ƙungiyoyin da suka ci riba; LIVERPOOL Ƙungiyar ce kan gaba a yawan kashe kuɗi wajen sayen ƴan ƙwallo a bana, wadda karo biyu ta ɗauki ƴan wasa a matakin mafi tsada a kakar nan. Ta fara da sayen matashin ɗan wasa Florian Wirtz kan fam miliyan 115, sannan ta ɗauki Aleɗander Isak kan fam miliyan 125 ranar da...
Misali, ya sauya lokacin da aka tsara yin wasan sada zumunta da ƴan ƙasa da shekara 20 na ƙungiyar Flamengo a lokacin da Leɓerkusen ta je atisaye a Brazil. An buga wasan kwana biyar kafin ranar da aka tsara tun farko, inda Leɓerkusen ta sha kashi da ci 5-1. Haka nan a kusan wannan lokacin ne Ten Hag ya yanke hukunci kan batun tafiyar Granit Ɗhaka, inda ya ce ya kamata ya tsaye saboda Leɓerkusen ta rasa manyan ƴan wasa da yawa. Sai dai tuni ƙungiyar ta sanar cewa Ɗhaka zai iya tafiya idan aka samu tayi mai kyau. Daga baya ya tafi Sunderland. Haka nan kuma Ten Hag ya soki ƴan wasansa tare da cewa ba su da kuzarin...
Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC), ta raba wa mutum 2,261 da ambaliyar ruwa ta shafa a Potiskum, Nangere da Jakusko a Jihar Yobe, kayan agaji. An raba kayan ne a unguwanni 21 na Potiskum, ƙauyukan Kolo da Ajim a Nangere, da kuma kauyukan Dachia, Yim, Saminaka, Garin Maji da Amshi a Jakusko. Gwamnati ta gargaɗi jihohi 11 kan yiwuwar afkuwar ambaliya a wannan makon Ban taɓa nadamar shiga Kannywood ba — Kabiru Nakwango Kayan da aka bayar sun haɗa da shinkafa, taliya, man girki, da kuma tufafi, kayan mata da shadda. Sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA), Dokta Mohammed Goje, ya ce Gwamna Mai Mala Buni ya ba da umarnin gaggauta tallafa wa al’ummar...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah-wadai da sanarwar ta G7, tana mai cewa ba ta da tushe balle makama Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi Allah-wadai da zarge-zargen da mambobin kungiyar G7 da kawayenta suka yi dangane da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, tana mai kallon hakan ba gaskiya ba ne. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fitar ta bayyana zargin da ke kunshe a cikin sanarwar hadin gwiwa na kasashen G7 da kawayenta dangane da Jamhuriyar Musulunci ta Iran da cewa ba gaskiya ba ne. Sanarwar ta kara da cewa: Yin zargin karya kan wadanda ke da alhakin kare tsaron kasar Iran wani lamari ne karara na murguda gaskiya da kuma...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana dalilin da ya sa tawagarta ba ta halarci kada kuri’a kan batun Falasdinu ba Ofishin Jakadancin Iran ya jaddada cewa, duk wata hanyar warware matsalar Falastinu a zahiri dole ne ta dogara kan amincewa da hakkin al’ummar Falastinu na dogaro da kai da kuma watsi da duk wani batun tilasta musu yin gudun hijira. Ta kuma jaddada cewa, za a iya samun dawwamammen zaman lafiya ne ta hanyar kawo karshen mamaya da kuma samun cikakken ‘yancin kai gami da samun ‘yancin kai na kasar Falasdinu, tare da la’akari da ainihin nufin ‘yan asalinta-Musulmi, Yahudawa, da Kirista—ta hanyar kuri’ar raba gardama mai ‘yanci, kamar yadda aka gabatar a cikin takardar yarjejeniya mail amba S/2019/862. A...
Kungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa (NARD) ta sanar da janye yajin aikin gargaɗi da ta fara bayan kwanaki biyu kacal. Sai dai ƙungiyar ta sake bai wa Gwamnati Tarayya mako biyu ta biya buƙatunta ko ta sake tsunduma yajin aiki. Shugaban ƙungiyar, Dakta Tope Osundara ne ya bayyana haka a ranar Asabar tare da umartar ɗaukacin mambobinsu da su koma aiki a yau Lahadi. Osundara, ya ce gwamnati ta biya musu wasu daga cikin buƙatunsu, tare kuma da alƙawarin duba sauran batutuwan da suke yajin aiki akan su. Tun a daren Juma’a ne likitocin masu neman ƙwarewa suka tsunduma yajin aikin na gargaɗi, bayan ƙarewar wa’adin da ƙungiyar ta ba Gwamnatin Tarayya kan batutuwan da suka shafi albashi, alawus, da...
Aƙalla mutane 19 ne suka mutu a yayin da suka ɗauko wata amarya zuwa ɗakin mijinta bayan motarsu ta faɗa a ƙarƙashin gadar Gwalli da ke yankin Fass a Ƙaramar Hukumar Gummi a Jihar Zamfara. Lamarin ya faru ne da yammacin Asabar da misalin ƙarfe 4:45 na yamma, lokacin da motar, da ke ɗauke da maza da mata da yara ta faɗo daga saman karyayyiyar gadar, ta nutse a cikin ruwa. Wani ɗan uwan amaryar, Babangida Halifa Ibrahim Fass, wanda ya rasa ’yan uwa a cikin hatsarin, ya ce hatsarin ya faru ne a lokacin da ake kai ’yar uwarsa amarya gidan mijinta da ke Jega a Jihar Kebbi. Ya ce, “Motar ta faɗo ne daga kan gada ta nutse...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa alakar iran da Tunusiya wani babban misali ne na irin yadda kasar iran ke son su fadada dangantaka da sauran kasashen musulmi bisa girmamawa da mutunta juna. Haka zalika Araqchi ya jinjinawa kasar Tunusiya game da irin matakin da ta dauka musamman a lokacin harin wuce gona da iri da hki takai a kasar iran a watan yuni, yace wannan goyon bayan ya nuna irin zurfin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Kuma ya bayyana cewa iran a shirye take ta yi aiki da kasar tunusiya a bangarorin daban-daban wajen musayar kwararewar da suke da shi a bangaren kimiya da fasaha da dai sauransu. Ana ta bangaren kasar Tunusiya tace tana...
Mariya Sanusi Dantata, mahaifiyar attajirin Afirka Aliko Dangote, tare da fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Khalil, sun halarci gasar karatun Alƙur’ani da Maryam Shettima ta shirya a Jihar Kano. An yi gasar laƙabi da #ReciteWithShetty, inda taken shi ne “Alƙur’ani: Jagora Wajen Tsaftace Kafofin Sada Zumunta”. ’Yan bindiga sun buɗe wa ’yan zaman makoki wuta a Anambra An kama buhun tabar wiwi 150 bayan hatsarin mota a Kano Manufar gasar ita ce bunƙasa tarbiyya da inganta amfani da kafafen sada zumunta. A yayin karrama waɗanda suka shiga gasar, Shetty, ta bayyana cewa dubban yara daga sassa daban-daban na Najeriya ne suka shiga gasar ta hanyar kafafen sada zumunta. “Na yi mamakin yawan mahalarta. Hakan ya nuna akwai haziƙan matasa...
Dokar Tsabtace Amfani da Wuta ta Ƙasa. Dokar Gyara Yanayi ta Ƙasa. Hanzarta Ba da gargaɗi. Wayar da kan jama’a kan haɗarin ambaliyar ruwa. Tilasta dokokin muhalli. Horarwa da sabunta ƙwarewar jami’ai ƙwararru. Shigar da kayan aiki na zamani, da sauransu. Har ila yau, ya bayyana cewa za a iya sarrafa ambaliyar ruwa ta hanyoyi kamar: Taruwar ruwan sama (rain harɓest) kamar yadda ake yi a China. Gyara da gina ƙarin madatsun ruwa (dams). Kafa hanyoyin ruwa. Kafa ƙarin ɗakunan gwaje-gwaje kan ambaliyar ruwa. Haramta amfani da roba ɗaya-ɗaya (single plastic use). Kulawa akai-akai da tsarin magudanan ruwa a faɗin ƙasa. Gudanar da ruwa (water management) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
Jami’in kungiyar Hamas yayi tsokaci kan yunkurin kashe tawagar kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas a Doha Jami’in kungiyar gwagwagrmayar Musulunci ta Hamas, Osama Hamdan ya ce: Yunkurin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi na kashe tawagar da ke tattaunawa a birnin Doha na kasar Qatar wani hari ne kai tsaye kan shirin shugaban Amurka Donald Trump na neman tsagaita wuta. Ya kara da cewa a wata hira da aka yi da shi a gidan telebijin, “yunkurin kashe tawagar Hamas hari ne kai tsaye kan shirin shugaba Trump, idan har Isra’ilawa sun amince da Shirin na Trump, to su saurari martanin Hamas, maimakon mayar da martani ta hanyar jefa bam a birnin Doha da wurin taron jami’an kungiyar.” Hamdan ya yi...
Sojojin Yemen sun sanar da kai hare-hare kan wasu muhimman wurare a yankuna daban-daban na haramtacciyar kasar Isra’ila Dakarun Yemen sun sanar a yau cewa: Sun kai farmaki kan wasu wurare masu muhimmanci a yankin Jaffa da aka mamaye. Wannan farmakin na goyon bayan al’ummar Falastinu da ake zalunta ne, da kuma mayar da martani kan laifukan kisan kiyashi da kakaba yunwa da makiya yahudawan sahayoniyya suka aikata a kan ‘yan uwa a zirin Gaza, da kuma wani mataki na mayar da martani ga hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila ke kaiwa kasar Yemen. Rundunar sojin kasar ta Yemen ta kuma jaddada cewa; Rundunar sojin kasar ta kuma kai harin ne ta hanyar amfani da makamai masu...
Tabbatar da dakatar da amfani da HCFC-141b a tsarin sandwich panel, spray, da block a ayyukan cikin gida na Vitapur. Daraktan Zartarwa na Vitapurs Ltd, Mista Taiwo Adeniyi, a jawabin maraba da ya yi, ya bayyana cewa cibiyar za ta ƙara ƙwarewa wajen gwaje-gwaje, bincike, da horo tare da amfani da sinadarai masu ƙarancin GWP, ƙara ƙarfin haɗa kayan ODS-free don samfuran rigid PU, da faɗaɗa ayyukan ɗakin gwaje-gwaje wajen nazarin kayan aiki da samfuran ƙarshe, da kuma tasirin tattalin arziki da muhalli. Ya ƙara da cewa Optimized System House zai inganta samar da ayyukan yi da canja fasaha, rage buƙatar kuɗaɗen waje ta hanyar rage dogaro da shigo da kaya, tallafa wa tafiyar masana’antu ta Nijeriya ta hanyar rassan...
“Haka zalika, shi ma matuƙin babur ɗin; ruwan ya yi awon gaba da shi,” a cewar tasa. Ganau ɗin ya ci gaba da cewa, wani ƙwararre a fannin iya ruwa; nan da nan ya garzayo tare da yin sufa a cikin ruwa, domin ƙoƙarin ceto su, amma tuni ruwan ya riga ya yi awon gaba da su. Limamin da ya jagoranci sallar jana’izar gawar da aka samu a kwarin Dangoma, Mallam Musa Umar Al mishawi ya bayyana cewa; marigayin ya samu rauni a goshinsa. “Marigayin, mazaunin Unguwar Gidan Dangoma ne da ke tudun jukun ta garin Zaria, sannan kuma an yi jana’izarsa kamar yadda a safiyar yau kamar yadda addinin musulunci ya tanada,” in ji shi. Kazalika, har zuwa lokacin...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhakan, sharbin bayan labarammu a yau zasu yi magana dangane da ‘yiyuwar gwamnatin kasar Qatar ta nemi maye gurbim Amurka a bangaren tsaron kasarta, bayan cin amanan da Amurka ta yi a ranar talatan da ta gabata. Kamfanin dillancin labaran Parstoday, ta nakalto wani shafin labarai na yanar gizo a Amurka ‘Axios’. A ranar Alhamis da ta gabata ce, shafin yanar gizo na Acios na labarai ya nakalto Firay ministan kasar Qatar tana fadawa fadar white House kan cewa, bayan saba alkawalin da Washington ta yi, dangane da hare-haren da HKI ta kaiwa birnin Doha, Qatar zata sake duba yarjeniyar tsaron da ke tsakaninta da Amurka ta kuma nemi sabon abokin aiki a wannan...
Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta kama jabun magungunan zazzaɓin cizon sauro (maleriya) da darajarsu ta kai sama da Naira biliyan ₦1.2bn a Legas. Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a a shafinta na sada zumunta X, inda ta ce jami’anta sun kai samame a wani ɗakin ajiyar kaya da ke yankin Ilasa-Oshodi, inda aka gano katan 277 na jabun magungunan maleriya nau’in Malamal Forte. Harkar tsaro a gabashin Sakkwato na ƙara taɓarɓarewa — Sanata Lamiɗo ’Yan bindiga sun harbi fasinjoji 2, sun sace makiyaya a Neja NAFDAC ta ƙara da cewa, “Ta kama katan 277 na jabun magungunan zazzaɓin cizon sauro na Malamal Forte...
An kammala taron baje kolin zuba jari na duniya na Sin karo na 25 (CIFIT) a jiya Alhamis 11 a birnin Xiamen. A yayin taro na wannan karo, an kulla yarjejeniyoyin ayyukan zuba jari guda 1,154, inda jimillar kudin dake kunshe a ciki ta kai kudin Sin Yuan biliyan 644 (kwatankwacin sama da dala biliyan 90.5 ). An kuma fitar da rahotanni masu inganci guda 21. Taron mai taken “Hadin kai da Sin don zuba jari ta yadda za a samu bunkasa nan gaba,” ya gudana ne a fadin filin baje koli da ya kai murabba’in kilomita 12. An gudanar da ayyukan habaka zuba jari sama da dari, kuma tawagogin kasashe da yankuna fiye da 120 sun halarta, tare da...
Wani dalili da ba zato ba tsammani ya janyo gazawar kashe manyan shugabannin Hamas a Doha Kafofin yada labarai sun bayyana wani dalili na bazata a ranar Laraba da ya biyo bayan gazawar da Isra’ila ta yi na kashe manyan shugabannin Hamas a Doha babban birnin Qatar. Kamfanin dillancin labaran RT ya nakalto tashar talabijin ta Channel 12 cewa, kwana guda bayan kaddamar da shirin kawar da ofishin siyasa na kungiyar Hamas a birnin Doha, rahotanni na nuni da cewa harin bai yi nasara ba, sakamakon matakin da shugabannin Hamas suka dauka na yin sallar azahar tare da ficewa daga dakin tattaunawar. Wani abin ban mamaki shi ne, shugabannin Hamas sun bar wayoyinsu a cikin dakin tattaunawar, lamarin da ya...
A yayin da suka yi alƙawarin yin adawa da aiwatar da harajin, ƙungiyar ta ƙara da cewa: “Yajin aiki na kan tebur idan gwamnati ta yi ƙoƙarin watsi da wannan gargaɗi ta ci gaba da aiwatar da waɗannan manufofi. Don haka, TUC ta umarci dukkan kwamitocin jihohi, rassan ƙungiya, da tsarin ta a faɗin ƙasa da su kasance cikin shiri, sanya ido, kuma su jira ƙarin sanarwa wanda zai iya kai wa ga ɗaukar mataki mai ƙarfi idan gwamnati ta ƙi sauraron muradin jama’a.” Ƙungiyar ta kuma kira ga abokan hulɗarta – ƙungiyoyin farar hula, ƙungiyoyin ƙwararru, ɗalibai, ƙungiyoyin kasuwa, shugabannin addini da duk ƴan Nijeriya masu kishin ƙasa – da su tsaya tare da ita a wannan gwagwarmaya. “Tare,...
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya yi wata tattaunawa ta wayar tarho a daren jiya Alhamis da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi, inda suka mai da hankali kan shirin nukiliyar Iran da batutuwan da suka shafin yankin. tattaunawar na zuwa ne bayan da Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA suka cimma matsaya ta hadin gwiwa a nan gaba. Tehran ta dage kan kare hakkinta a karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT), yayin da ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta dauki wani mataki mai karfi kan ayyukan sojan Isra’ila a yankin. Manyan kasashen yammacin duniya sun yi barazanar maido da takunkuman kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da aka dage a...
An samu ambaliyar ruwa a tituna da dama na tsakiyar Babban Birnin Tarayya Abuja sakamakon mamakon ruwan saman da aka tafka da safiyar Alhamis. Yankunan da ambaliya ta fi shafa sun hada da Asokoro, Guzape, Jabi, Kado da kuma Wuse. Wasu direbobi da suka zanta da Aminiya sun ce sun sha wahala wajen samun hanyar wucewa a unguwannin Asokoro da Guzape yayin ruwan saman. Jonathan ya tattauna da Peter Obi kan tsayawa takara a 2027 Likitoci sun yi barazanar sake tsunduma yajin aiki A wani bidiyo da wani mai suna Prince Adebisi Adetunji ya wallafa a shafinsa na Facebook, an ga yadda ruwan ya mamaye titin Asokoro, inda direbobi da mazauna yankin suka yi ta kokarin yadda za su tsallake...
Ministan harkokin wajen Tunisiya Mohamed Ali Nafti ya ce kasarsa da Iran sun amince da karfafa hadin gwiwa tare da shirya taron komitin hadin gwiwa, yayin da yake maraba da sabuwar yarjejeniyar da Tehran ta kulla da hukumar IAEA. A cikin rubuce-rubuce uku na X a jiya Alhamis, ministan harkokin wajen Tunisia ya bayyana cewa, an cimma yarjejeniyar fadada huldar dake tsakanin kasashen Tunusiya da Iran a yayin ganawarsa da takwaransa na Iran Abbas Araghchi a birnin Tunis. Nafti ya ce, “Ina mai farin cikin maraba da takwarana Araghchi, ministan harkokin wajen Iran, a ziyarar aiki da ya kai kasar Tunisiya, mun gudanar da tattaunawa mai zurfi don tantancewa da kuma inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, domin samun...
“Gwamnatin Jihar Kaduna ta shirya tsaf domin ɗaukar matakin gaggawa kan kowanne yanayi da ka iya tasowa sakamakon wannan hasashen yanayi. An umurci KADSEMA da ta yi aiki tare da dukkan hukumomi masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cikakken shiri. Ana roƙon jama’a da su bi dukkan umarnin kariya, su share magudanan ruwa, kuma su guji wuraren da ambaliya ke yawan faruwa a wannan lokaci,” in ji Maiyaki. Hakazalika, sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KADSEMA), Dakta Usman Hayatu Mazadu, ya jaddada muhimmancin kasancewa cikin shiri da kuma bin matakan kariya da ke cikin sanarwar. “Hasashen yanayi ya nuna cewa za a samu guguwar iska da ruwan sama mai yawa musamman a ranakun Laraba...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hukumar makamashin nukliya ta Duniya IAEA ta amince da sabuwar yarjeniya tsakaninta da Iran ta yadda ma’amala tsakanin bangarorin biyu zata kasance. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Laraba a birnin Tunis babban birnin kasar Tunisia. A lokacinda yake jawabin hadin guiwa ta tokwaransa na kasar ta Tunisia. Kafin haka dai Aragchi ya yada zango a birnin Alkahira na kasar Masar inda ya gana da Rafael Grossi shugaban hukumar IAEA, suka kuma rattaba hannu kan sabuwar yarjeniya da hukumar, ta yadda hulda tsakaninsu zata kasance bayan hare-haren da HKI da Amurka suka kai wa cibiyoyin sarrafa makamashin nukliya na kasar ta...
Rukunin farko na ’yan Najeriya da aka tsara korar su daga Amurka a karkashin Shugaba Donald Trump sun bar kasar. Shugaban Ghana, John Dramani Mahama, ne ya bayyana hakan ga ’yan jarida a daren Laraba. “Rukunin mutane 14 da aka kora daga Amurka, ciki har da ’yan Najeriya da wani dan kasar Gambiya, sun iso Ghana, kuma gwamnati ta taimaka wajen mayar da su kasashensu,” in ji Mahama a wani taron manema labarai. Budurwa ta mutu a ɗakin saurayin da ke shirin auren ta a Abuja Mota ɗauke da tabar wiwi ta yi hatsari a Kano, ta faɗa hannun jami’an NDLEA Ya ce Ghana ta riga ta shirya jigilar ’yan Najeriya zuwa kasarsu ta mota, yayin da ake ci gaba...
DSS ta ce, shugabannin sun samu horo na musamman a kan amfani da makamai, dabarun yaƙi da kuma ƙera bama-bamai a ƙasashen Mali da Libya. Ta ce Mamuda ya samu horo na musamman daga malamai masu tsattsauran ra’ayi a tsakanin 2013 da 2015. Hakazalika, suna da hannu a sace manyan mutane, ciki har da sace wani Injiniya ɗan ƙasar Faransa, Francis Collomp a 2013 da kuma sace Alhaji Musa Umar Uba, Magajin Garin Daura a 2019. Ana kuma zarginsu da fashi da makami da kuma shirin kai hari wajen wani haƙar uranium a Nijar, wanda shirin nasu bai yi nasara ba. Mai Bai wa Shawara kan Sha’anin Tsaro, Nuhu Ribadu ne, ya tabbatar da kama su yayin wani samamen haɗin...
Jakadan kasar Iran a Rasha ya bayyana cewa daya daga cikin muhimman alamura da ake gab da cimma yarjejeniya akansa tsakaninsu da kasar Rasha a bangaren makamashi shi ne batun kai iskar gas Iran, wanda tuni aka wuce matakin share fage ana gab da kammalawa Kazim Jalali ya fadi a gefen bikin baje kulin kayayyakin rubobi da aka gudanar cewa” tattaunawar baya bayan nan da aka yi tsakanin Iran da Rasha a kasar chine ya nuna cewa an cimma matsaya tsakanin kasashen biyu, musamman game da kwangoglin da suka shafi tattalin arziki . Jalali ya kara da cewa daga cikin muhimman batutuwa dake tsakanin kasashen biyu shi ne batun isar da gas ga kasar Iran a matsayin wani bangare na...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, sabuwar yarjejeniyar da Iran ta kulla da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, kan batun dawo da hadin gwiwa, za ta ci gaba da wanzuwa matukar dai ba a dauki wani mataki kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba, ciki har da yunkurin mayar da takunkumin da MDD ta kakaba mata. A ranar 29 ga watan Agusta ne, kasashen Faransa, Jamus, da Biritaniya (E3) suka yunkura ganin an sake dawo da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya da manyan takunkumin banki da na ruwa a kan Iran. Iran ta yi Allah-wadai da wannan matakin, inda ta ce kasashen uku sun bi sahun Amurka, wadda ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar Iran a...
Stéphane Dujarric, kakakin babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana a jiya Laraba cewa, MDD ta yi maraba da yarjejeniyar da Iran ta kulla da hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA, kan “tsarin da zai ba da damar komawa bincike a Iran”. A yayin taron manema labarai a wannan rana, Dujarric ya ce wannan yarjejeniya wani mataki ne mai kyau da Iran da IAEA suka dauka don komawa cikakkiyar hadin gwiwa. Majalisar tana kuma fatan za a gaggauta aiwatar da yarjejeniyar. Dujarric ya kuma jaddada muhimmancin cikakkiyar hadin gwiwar Iran da IAEA. Yana mai cewa, hakan yana da muhimmanci wajen kafa wani tsari na dogon lokaci, wanda zai “tabbatar da shirin nukiliyar Iran gaba daya don zaman lafiya”. A ranar Larabar, yayin ziyararsa a Alkahira, babban birnin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), ta tsare tsohon Shugaban Hukumar Man Fetur ta Ƙasa (NNPC), Mele Kyari kan zargin karkatar da kuɗaɗen gyaran matatun man Najeriya. Kyari na cikin jerin waɗanda ta hukumar ta sanya ido a kansu, kuma ta isa ofishin EFCC da misalin ƙarfe 2:30 na ranar Laraba. Macron ya karɓi baƙuncin Tinubu a Fadar Elysee Masu zanga-zanga sun ƙone matar tsohon Firaministan Nepal Majiyoyi, sun bayyana cewar ya isa ne don bayar da bayanai kan batutuwan kuɗi da aka ware don gyaran matatun man fetur a Najeriya lokacin da yake shugabantar NNPC. Wani majiya ta shaida wa Aminiya cewa: “Eh, yana ofishinmu. Za a kai shi ɗaki inda masu bincike na...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Jami’ar MAAUN Da Kwalejin Seneca ta Canada Sun Yi Haɗin Gwiwa Domin Samar Da Damarmaki Ga Ɗalibai A Duniya
A yayin taron rattaba hannun, Farfesa Gwarzo ya bayyana manufar wannan yarjejeniya, inda ya ce hadin gwiwar za ta bai wa dalibai da ma’aikata damar cin moriyar albarkatu da kwarewa daga kasashen waje. “Wannan hadin gwiwar alama ce ta jajircewarmu wajen hada jami’o’inmu da manyan cibiyoyi na duniya domin bunkasa kirkire-kirkire da bincike a rukunin jami’o’inmu na MAAUN,” in ji shi. A karkashin wannan yarjejeniyar, cibiyoyin biyu za su rika raba kwarewar su tare da tallafa wa juna don cimma manufofi na bai daya. Muhimman bangarorin hadin gwiwar sun hada da samar da koyarwar harshen Turanci ta yanar gizo ga daliban MAAUN, samar da hanyoyi don ci gaba da karatu a Seneca, da bayar da shawarwari kan harkokin...
Jiragen yakin HKI sun kai sabbin hare-hare kan kasar Yemen a yau Laraba, inji tashar talabijin ta Al-Masirah na gwamnatin kasar. Labarin ya kara da cewa yahudawan sun kai hare-haren ne a tsakanin wasu duwatsu a cikin kasar, da kuma kan cibiyar kungiyar Ansarullah da ke tsakiyar birnin San’a babban birnin kasar, da kuma ma’aikatar tsaron kasar. Wadanda suka ganewa idanunsu sun bayyanawa kamfanin dillancin labaran reuters kan cewa yahudawan sun kai hare-haren kan wani barikin soja ne a yau Laraba. Kafin haka dai sojojin Yemen sun kai kaiwa HKI hare-hare a gewayen birnin Qudus da kuma tashar jiragen saman da Ramona da ke kudancin kasar kusa da birnin Ummu Rashrash ko Ilaat kamar yadda yahudawan suke kiransa. Gwamnatin kasar...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa takaitacce hadin kai ta bawa hukumar IAEA a yarjeniyar da ta cimma da Gorris a birnin Alkahira. Ya nuna irin hakurin da JMI ta nuna bayan hare-haren da aka kai mata kan cibiyoyin Nukliyar kasar . Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana fadar haka a yau a shafinsa na X kan cewa, Iran ta amince da takaitaccen aiki da hukumar IAEA ne saboda dole ne ya zamanto ana kula da ayyukan nukliyar kasar ko da takaitacce ne. Sannan ya ce kasar tana son ci gaba da raya yarjeniyar JCPOA na shekara ta 2015. Ya ce, Iran ta amince da wannan takaitaccen yarjeniya ne bayan ta...
Yayin da aka gano gawar Surajo a ranar Litinin, an gano gawar Fatima washegari, Talata. Sai dai har yanzu ba a gano gawar kanwar Fatima ‘yar shekara uku, Haneefa ba. A lokacin da lamarin ya faru, Fatima tana goye da kanwarta Haneefa mai shekaru uku a duniya. Su biyun suna dawowa ne daga gidan kakarsu da ke Magume zuwa gidan su da ke Tudun Jukun. Malamin Islamiyyar su Fatima, mai suna Malam Daddy ne ya yi musu rakiyar hanya acikin kekensa mai taya Uku (Keke-napep). Shaidun gani da ido sun ce, abin takaicin ya afku ne a mahadar da ke kusa da Cocin Nasara Baptist da ke kan hanyar Gaskiya babban layi a Tudun Jukun. ...
Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta samu nasarar warware tankiyar da ke tsakanin Matatar Dangote da Ƙungiyar Ma’aikatan Dakon Man Fetur da Gas ta Najeriya (NUPENG). Wannan na zuwa ne bayan wani zama da aka gudanar a babban ofishin DSS da ke Abuja, inda rahotanni ke cewa shugabannin NUPENG sun umurci mambobinsu da su dakatar da yajin aikin da aka fara a faɗin ƙasar. ’Yan bindiga sanye da hijabi sun sace mutane 11 a Zamfara An cafke mace mai safarar wiwi da ’yan fashi 4 a Gombe Aminiya ta ruwaito cewa, Ministan Kuɗi, Wale Edun; Ministan Kwadago da Ayyuka, Mohammed Maigari Dingyadi; da Ƙaramin Ministan Ƙwadago, Nkeiruka Onyejeocha, duk sun halarci zaman. Haka zalika, tawagar Kamfanin Dangote ƙarƙashin jagorancin...
Jiragen yakin HKI sun kai hare-hare kan cibiyar gudanarwa na kungiyar Hamas dake birnin Doha na kasar Qatar dazo da rana. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto tashar talabijan ta 13 ta HKI na bada labarin cewa jiragen yahudawan sun kai hare-haren ne a dai-dai lokacinda shuwagabannin kungiyar Hamas suke taro don tattauna sabon shawarar da shugaban kasar Amurka Donal Trump ga bagatar don tsagaita wuta tsakanin HKI da kungiyar a Gaza. Labarin ya kara da cewa shugaban kungiyar Khalil Al-Hayya, da Zaher Jabiran shugaban reshen kungiyar yankin yamma da kogin Jordan, da kuma Khalid Mash’al duk suna cikin taron. HKI ta kira hare-haren, da sunan hare-haren kissan shuwagabannin Hamas. Amma gwamnatin kasar Qatar ta yi allawadai...
Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya TUC ta yi barazanar shiga yajin aiki dangane da matakin da Gwamnatin Tarayya ta ce za ta ɗauka na ƙara harajin kaso 5 cikin 100 a farashin duk litar man fetur. A yayin da ƙungiyar ta yi watsi da matakin, ta kuma kwatanta aiwatar da hakan a matsayin ganganci da mugunta ga tattalin arzikin ƙasar. Dalilin da muka yi watsi da buƙatar dawowar Sanata Natasha — Majalisar Dattawa NAJERIYA A YAU: Tasirin Takaddamar NUPENG Da Dangote A Kan Tattalin Arzikin Najeriya A bayan nan ne dai Gwamnatin Tarayyar ta sanar da ɗaukar wannan mataki da zai fara aiki a farkon watan Janairun 2026, domin samun kuɗaɗen shiga da za a yi amfani da su wajen gina...
Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa Iran ba ta neman fada da wata kasa ta musulmi ba, kuma tana ci gaba da jajircewa wajen ingantawa da kuma wanzar da hadin kai a tsakanin kasashen musulmi. Da yake jawabi a taron kasa da kasa na hadin kan musulmi karo na 39 a birnin Tehran, Mr. Pezeshkian ya bayyana cewa babu wani mahaluki da zai iya cin galaba a kan musulmi idan har suka ci gaba da kasancewa tare da tabbatar da adalci a cikin al’ummominsu. Ya kara da cewa, idan musulmi kan su ya hade waje guda, ba tare da wani rikici ba, sahyoniyawan ba za su taba aikata irin wadannan laifuka a Gaza da kasashen yankin ba....
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya zanta ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Masar Abdulatty donga ne da shirin nukliyar kasar Iran da kuma al-amuran gabasa da tsakiya musamman Gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a halin yanzu dai kasar Masar ta zama mai shiga tsakanin Iran da kasashen yamma dangane da shirin Iran na makamashin nuliya. Haka ma dangane da yaki a Gaza, kasar tana taka rawa don ganin an kawo karshen yakin da kuma shigo da abinci cikin cikin Gaza. Kasashen Iran da Masar dai suna kai kawo tsakanin kasashen musulmi da kuma kasashen larabawa don don dakatar da wannan kissan kiyashin da ke faruwa a Gaza. A cikin yan...

Gwamnatin Tarayya, NUPENG Da Ɗangote Sun Fara Tattaunawa Don Kawo Ƙarshen Yajin Aikin Ma’aikatan Mai
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da jami’an Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), wakilan kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, shuwagabannin kamfanin ‘MRS Holdings Limited’ da kuma kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa (TUC). Da yake bayyana bude taron, Minista Dingyadi ya jaddada aniyar gwamnati na sulhu a tsakanin kungiyar da masu gudanar da masana’antu. Ya bayyana bangaren mai da iskar gas a matsayin jigon tattalin arzikin Nijeriya, yana mai gargadin cewa tsawaita yajin aikin zai haifar da mummunan sakamako ga kasar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
Shugaban kasar China Xi Jinping ya bayyana cewa kungiyar BRICS zata ci gaba da ayyukanta duk tare da matsalolin da take fuskanta. Tashar talabijin ta Al-mayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto shugaban yana fadar haka a taron kungiyar ta BRICS ta hotunan yanar gizo da aka gudanar a yau litinin. Ya kuma kara jaddada cewa kungiyar da sannu zata wuce wadan nan matsalolin da suke gabatan a halin yanzu, sannan ta ci gaba girma da daukaka. Yace a cikin wuta ne ake gane zinari na gaskiya, don haka matsalolin da suke gabar kungiyar BRICS ne zasu fayyace irin karfin da kungiyar take da shi na fuskantar matsaloli, sannan ta ci gaba girma har zuwa lokacinda zata cimma manufar kafata. Shugaban...
Yarima Harry wanda ya koma rayuwa a Jihar California ta Amurka, ya ziyarci kabarin mahaifiyarsa, Sarauniya Elizabeth II, a fadar Windsor da ke yammacin birnin Landan a ranar Litinin. Shekaru uku ke nan daidai da rasuwar Sarauniya Elizabeth II wadda ta riga mu gidan gaskiya a ranar 8 ga Satumba, 2022, kuma aka binne ta a cikin cocin St. George’s Chapel da ke fadar Windsor. An fara samun masu zawarcin kujerar Firaministan Japan Matatar Dangote ta musanta dakatar da aiki Mai magana da yawunsa ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa Harry ya kai ziyara shi kaɗai domin girmama mahaifiyarsa. A halin yanzu dai abin tambayar shi ne ko Yarima Harry zai gana da mahaifinsa, Sarki Charles III,...
Sayyid Abbas Araqci ministan harkokin wajen kasar iran a wani sakon mayar da martani da ya aike da shi game da shirun da kasashen turai suka yi kan fadada shirin nukiliyar HKI ya jaddada cewa yin shiru da baki da suka yi ya nuna cewa yanzu basu da wata dama ko kwarin guiwar yin Magana kan hana yaduwar makamin nukiliya kan kowacce kasa . Rahotan ya bayyana cewa Araqchi ya bayyana a shafinsa na x cewa batun samuwa ko fadada shirin makamin nukiliya ba shi ne a gabansu ba, lamarin shi ne waye ya bada dama a samu ci gaban ilimi ko da ma na shirin nukiliya na zaman lafiya ne, Ya jaddada cewa saboda haka wannan ba’a bin mamaki...
Abdullahi ya tabbatar da cewa rundunar Sojin Nijeriya za ta ci gaba da aiyukanta don kawar da ƴan bindiga da sauran barazanar tsaro a jihar Kogi da kewaye. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta ce ta samu nasarar ceto wasu mata biyu da wata jaririya da ambaliyar ruwa ta rutsa da su a Jihar Kaduna. Shugabar hukumar, Hajiya Zubaida Umar ce, ta bayyana hakan a shafinta na Facebook. Harin Boko Haram: Zulum ya kai ziyarar jaje garin Darajamal Tsadar Rayuwa: NLC ta buƙaci gwamnati ta sake duba albashin ma’aikata Ta ce ambaliyar ta auku ne sakamakon ruwan sama mai yawa da aka yi a ranar Juma’a. Ta ce sama da gidaje 160 da magidanta 500 ne ambaliyar ta shafa a unguwanni irin su Kabala Doki, Bachama, Kigo, Ramat, da Unguwar Dosa/Nasarawa/Mali. Rahoton ya nuna cewa ruwan kogin Kaduna ne ya yi sama, ya shiga unguwanni,...
Ministan harkokin wajen kasar Iran abbas Aragchi ya yi kira ga kasashen turai 3 EU a takaice su dawo kan hanyar diblomasiyya don warware rikicin shirin Nukliyar kasar Iran wanda ya zo cikin yarjeniyar JCPOA na shekara ta 2015. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Argchi yana fadar haka a yau Lahadi a cikin wani rubutun da yayi a cikin Jaridar Guadian na kasar Burtania. Ministan ya kammala da cewa idan sun ki dawowa kasashen turai ne za’a ware nan gaba, don ba zasu taba cimma manufofinsu a kan Iran tare da sake maida takunkuman MDD kan kasar Iran ba. Tsarin Snpback dai wani tsari ne wanda zai bawa kasashe 6 wanda suke cikin yarjeniyar JCPOA danar...
Wasu cibiyoyin bincike na Pew Research da CIA World Factbook sun tabbatar da cewa Najeriya ce ƙasa ta biyar mafi yawan Musulmai a duniya, inda ƙasar ke da Musulmai kimanin mutane miliyan 124. Ƙididdigar ta waɗannan cibiyoyi ta nuna Musulunci na ci gaba da zama addini na biyu mafi girma a duniya, wanda yawan mabiyansa suka kai kusan mutane biliyan 2.45 zuwa shekarar 2023. Firaministan Japan Shigeru Ishiba ya yi murabus DSS ta bai wa shafin X wa’adin goge saƙon Sowore da ke ƙaryata Tinubu Ƙasar Indonesia ce ke kan gaba da Musulmai miliyan 242, sai kuma Pakistan mai miliyan 235. Sai kuma ƙasar India da miliyan 213 sa’annan kuma Bangladesh da miliyan 150. Daga nan kuma sai Najeriya wacce...
Ƙungiyar Al’ummar Musulmi ta Kudancin Kaduna mai suna ‘Concerned Muslim Ummah’ ta zargi wasu manyan mutane a yankin da haifar da rarrabuwar kawuna da kuma juya tarihi domin cimma manufofin siyasa. A taron manema labarai da ta gudanar a Kaduna, ƙungiyar ta yi watsi da iƙirarin cewa Kudancin Kaduna na da Kiristoci ne kaɗai. Ta jaddada cewa Musulunci ya daɗe da wanzuwa a yankin tun ƙarnoni da suka gabata, inda ta ce Musulmi sun kai kusan kashi 40 cikin ɗari na al’ummar yankin. Ƙungiyar ta ce tashe-tashen hankula kamar na Zangon Kataf a 1992 da rikicin bayan zaben 2011 sun tabbatar da cewa rikice-rikicen yankin ba wai na yanzu ba ne. Bikin naɗin Sarkin Ibadan yan hana Musulmi Sallar Juma’a...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran tana ci gaba da musayar saƙon da Amurka ta hanyar masu shiga Tsakani Ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Araqchi ya sanar da cewa: Ana ci gaba da musayar sakwanni da Amurka ta hanyar masu shiga tsakani, yana mai jaddada cewa, Iran za ta kasance a shirye don yin shawarwari a lokacin da Amurka ta nuna aniyar ta na shiga tattaunawa bisa mutunta juna, matukar dai an mutunta hakki da muradun al’ummar Iran. A yayin da yake jawabi a zaman taron kasa kan samun damar zuba jari a yankunan ‘yanci da cinikayya a kasar Iran a ranar Asabar, Araqchi ya ce: Yankin Shenzhen na kasar China ya kasance wani karamin kauye...
Shugaban kasar Tunisiya ya bayyana cewa: Afirka na bukatar sabuwar hanya don tunkarar son ran ‘yan mulkin mallaka Shugaban kasar Tunusiya Qa’is Saeed ya bayyana a ranar Alhamis cewa: Tunisiya tana alfahari da hadin kan kasashen Afirka, kuma ta tsaya tsayin daka kan burin kafa kungiyar tarayyar Afirka mai inganci, duk kuwa da kalubalen da nahiyar ke fuskanta, kamar tashe-tashen hankula, fadace-fadace, laifuffukan safarar bil adama, da rashin samar da muhimman abubuwan rayuwa. A jawabin da ya gabatar a wajen bude taron baje kolin kasuwanci a kasar Aljeriya karo na 4, Saeed ya ce: “Nahiyar Afirka na da dimbin arziki, amma a lokaci guda tana fuskantar talauci da ke sanya matasanta shiga cikin hanyoyin safarar mutane.” Ya ci gaba da...
Shugaban yace jihar Kaduna itace akan gaba daga cikin jihohi 36 da Birnin tarayya Abuja wajen tara kudin fatun layya Wanda ta tara Naira miliyan 23 sai jihar Kebbi wacce tazo ta biyu da Naira milliyan 21 sai kuma jihar Sakkwato wacce tazo ta uku. Yace kudadan da aka tara za’ayi amfani dasu wajen ci gaba da aiwatar da Ayyukan Jami’ar musulunci mallakin kungiyar dake Hadejia a jihar Jigawa wacce ake kan ginawa. Yace irin Wannan sadaka da alumma suke bayarwa zasu tabbatar da cewa anyi amfani da su yadda ya kamata musamman ginin Jami’ar mallakar kungiyar da wasu bangarori domin ciyar da addinin musulunci gaba. Da yake bayani akan taron da kungiyar ta gudanar a jihar...
A jiya Jumma’a 5 ga wannan wata, babban taron MDD karo na 79 ya jefa kuri’a tare da zartas da kudurin hadin gwiwar dake tsakanin MDD da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO da kasar Sin da dukkan kasashe membobin kungiyar SCO kimanin 40 suka gabatar tare. Kudurin ya amince da muhimmiyar rawar da kungiyar SCO ta taka wajen sa kaimi ga samun zaman lafiya da bunkasa da yin imani da juna da kuma hadin gwiwa a yankin, kana ya yaba wa kungiyar SCO bisa kokarin nuna goyon baya ga ayyukan MDD, da kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da tsarin MDD. Mukaddashin shugaban tawagar dindindin ta Sin dake MDD Geng Shuang ya bayyana yayin da yake bayani game...
A wani mataki na tallafawa kasuwanci tsakanin kasashen Afrika an kaddamar da wat kungiyar mai manufartallafawa kasuwanci tsakanin kasashen Afirka tare da saukaka ayyukan raya kasa da sarrafa albarkatun cikin gida. Bankin shigo da kayayyaki na Afirka ne ya kaddamar da kungiyar Don tallafawa kasuwanci, fitar da kayayyaki, da sarrafa albarkatun kasa a Afirka, wanda aka sanar da kirkiro da shi a yayin bikin ranar Afirka. Shugaban bankin Afrexim Bank Oramah Benedict ne ya sanar da hakan a hukumance a birnin Algiers, a yayin bikin ranar ‘yan kasashen Afirka. An gudanar da bikin ne a gefen ranar al’ummar kasashen Afirka, wanda firaministan rikon kwarya na kasar Aljeriya Sifi Ghrib ya jagoranta, tare da halartar jami’ai daga Afirka da dama. Ayman...
Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da aniyarta ta magance matsalolin ambaliya da zaizayar ƙasa ta hanyar aiwatar da muhimman ayyukan gine-gine da aka tsara domin samar da mafita ga matsalolin muhalli a faɗin jihar. Kwamishinan yaɗa labarai da sadarwa na jihar, Kingsley Femi Fanwo, ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna Usman Ododo ta ƙuduri aniyar inganta rayuwar al’umma ta hanyar gina muhimman abubuwan more rayuwa da za su tabbatar da tsaro, da ɗorewa da ingantacciyar rayuwa. Hakimin Da Aka Sace A Jihar Kogi Ya Shaki Iskar ‘Yanci Sojoji Sun Ceto Shugaban Fulani, Mutane 5 Daga Hannun Ƴan Bindiga A Kogi Ya bayyana cewa sabbin magudanan ruwa da aka kammala a wurare irin su Etahi, da Omigbo da Olubojo a ƙaramar hukumar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Khalil al -Hayya shugaban kungiyar Hamas a yankin gaza dake falasdinu tare da yawa daga cikin mambobin kungiyar Hamas da jagororinta na siyasa sun gana da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi a birnin Doha na kasar Qatar, inda suka tattauna game da yakin kwanaki 12, da hakan ke nuna irin goyon baya da iran take bawa yan gwagwarmayar falasdinu ,wanda ya sanya wasu kasashen turai suka amince da falasdinu a matsayin kasa Amurka da HKI suna shirin ganin sun kwashe mutanen Gaza sai dai Arqchi ya aike da sako mai karfi zuwa ga Amurka da HKI a taron da suka yi da jami’an kungiyar hamas a gaza, na irin shirin da iran take da shi na ci gaba...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kasashe takwas, ciki har da Pakistan, Morocco, Syriya, Libya, Jordan, Lebanon da kuma Masar, sun himmatu wajen bayar da fifikon kula da cutar kansa ta yara, ta hanyar kula da ka’idojin kasa, ta hanyar yin gwajin cutar da a kan lokaci, samar da ingantattun magunguna da kuma samar da kudade don bai wa iyali kariya. Kwanan nan, Maroko ta karbi bakuncin taron bita na farko, kan kula da lafiyar yara, yayin da Lebenon kuma ta kafa kwamitin kula da cutar kansar yara, wanda ya shafi wadanda suka tsira da rayukansu, ma’aikatan jinya, sauran ma’aikata da kuma wakilan Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Ghana ta sanar cewa ofishin jakadancinta dake birnin Tehran zai koma aiki a rana 16 ga watan satumnbar da muke ciki bayan rufeshi da aka yi na wucin gadi, Sake bude ofishin jakadancin Ghana a birnin Tehran zai kara bude hanyoyi kyautata dangantakar Ilimi, kasuwanci, da musayar ala’adu da kuma yin aiki tare , adaidai lokacin da kawancen kasashen duniya ke canza sheka, wannan mataki ya nuna aniyar Ghana na karkatar da alakarta ta kasashen duniya. An rufe ofishin jakadancin Ghana ne a ranar 16 ga watan yuni bayan yaki da ya barke tsakanin Iran da Isra’ila domin kare lafiyar ma’aikatanta a wannan lokacin . Wannan matakin da kasar Ghana ta dauka na sake bude ofishin...
Yakin ya farkar da Sin da duniya baki daya, wanda ya zama tushen kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a shekarar 1949, daga bisani kuma ya dora kasar bisa tafarkin zamani. Ga duniya, mulkin mallaka ya fara wargajewa. Kasashe da dama sannu a hankali suka fahimci cewa, in sun jajirce, za su samu ‘yancin kai. Tasirin yaki da zalunci da danniya da Jama’ar Sinawa suka yi, ya sa kasar ta kudiri aniyar yaki da zalunci da danniya a duniya ta rungumi manufar tabbatar da zaman lafiya, inda ta nuna wa duniya cewa, lokacin wariya da danniya, tsarin rayuwar dabbobi (na sama ya buge na kasa), ba zai dore ba amma samar da dawwamammen zaman lafiya da tsaro, na sama ya yi...
Gwamnatin Jihar Yobe ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni, ta amince za ta biya dukkanin kuɗaɗen jinyar fitaccen jarumin Kannywood, Malam Nata’ala, wanda ke fama da ciwon daji. Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Muhammad Lawan Gana ne, ya bayyana haka lokacin da ya kai masa ziyara a gidansa da ke Potiskum. Gwamnatin Sakkwato ta ba jami’an tsaro tallafin motoci 14 da babura 150 ’Yan sandan Kaduna sun gayyaci El-Rufa’i kan zargin yunkurin tayar da zaune tsaye Ya ce gwamnatin za ta haɗa kai da asibitin da yake jinya domin tabbatar da ya samu kulawa ta musamman. Kwamishinan ya ƙara da cewa wannan alheri na nuna yadda Gwamna Buni ke tausaya wa jama’arsa tare da taimaka wa masu buƙatar kulawar gaggawa....
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Amir Saeed Iravani jakadan kasar Iran a MDD ya bukaci kasashen duniya su yi allawadai da hare-haren da aka kaiwa cibiyoyin makamashin nukliya ta kasar Iran, a kuma gurfanar wadanda suka yi hakan gaban kuliya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Iravani yana fadar haka a yau Jumma’a a MDD, yace abinda ya faru a yakin kwanaki 12 ya tana hankalin kasashen duniya tare da sanya ayar tambaya kan yadda shirin makamashin Nukliya na zaman lafiya a duniya na wata kasa. Har’ila yau wannan ya sanya shakka a kan zaman lafiya a duniyar da take ciki da makaman nukl;iya. Har’ila yau da makomar yarjeniyoyi kan makaman kare dangi. Wadanda suka hada da NPT da sauransu. Hare-haren da...
Watanni biyu da rabi da yakin da Amurka da HKI suka dorawa kasar Iran tare da fadin Donal Trump kan cewa sojojinsa sun lalata cibiyoyin makamashin nukliya na kasar Iran, amma har yanzun ba’a san halinda cibiyoyin nukliyar kasar suke ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa hukumar IAEA tana iya kokarinta don sanin halin da cibiyoyin nukliyar kasar Iran suke don bawa Amurka da HKI damar sanin yadda zasu kaiwa Iran hare-hare a yakin da za’a fafata da su nan gaba. Gwamnatin JMI tana zargin hukumar IAEA da kasancewa yar leken asiri Amurka da HKI a cibiyoyin Nukliyar kasar Iran, don basu damar `lalatasu a yaki na gaba. Bayan yakin kwanaki 12 a cikin watan...
Watanni biyu da rabi da yakin da Amurka da HKI suka dorawa kasar Iran tare da fadin Donal Trump kan cewa sojojinsa sun lalata cibiyoyin makamashin nukliya na kasar Iran, amma har yanzun ba’a san halinda cibiyoyin nukliyar kasar suke ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa hukumar IAEA tana iya kokarinta don sanin halin da cibiyoyin nukliyar kasar Iran suke don bawa Amurka da HKI damar sanin yadda zasu kaiwa Iran hare-hare a yakin da za’a fafata da su nan gaba. Gwamnatin JMI tana zargin hukumar IAEA da kasancewa yar leken asiri Amurka da HKI a cibiyoyin Nukliyar kasar Iran, don basu damar `lalatasu a yaki na gaba. Bayan yakin kwanaki 12 a cikin watan...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp