2025-11-08@23:46:03 GMT
إجمالي نتائج البحث: 208
«ya yi sanadiyyar shahadar»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
A rana Juma’a da ta gabata, aka kaddamar da gasar wasannin kankara ta nahiyar Asiya karo na 9, a birnin Harbin na lardin Heilongjiang na kasar Sin. Wannan gasa ta kasance babbar gasar wasannin kankara ta kasa da kasa karo na 2 da Sin ta karbi bakuncinta, biyo bayan gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi da ta gudana a birnin Beijing na Sin, a shekarar 2022. An ce, gasar wasannin kankara ta wannan karo ta samu halartar ‘yan wasa fiye da 1270 da suka zo daga kasashe da yankuna 34 dake nahiyar Asiya, alkaluman da suka kai matsayin koli a tarihi. Inda har wasu kasashen da ba sa samun yanayi mai sanyi da muhalli mai kankara a cikin gida, kamarsu...
Firay Ministan HKI Banyamin Natanyahu ya bawa kasar Saudiya Shawara samarwa Falasdinawa kasa daga cikin hamada mai girma da take da shi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Natanyahu yana fadar haka wa wata tashar talabijin ta HH a safiyar yau Asabar. Amma a maida martani ga Natanyahu, dan majalisar dokokin kasar Burtania a jam’iyyar Larbor Afzal Khan yace, wannan shawarar ta Natanyahu tabbaci ne na laifin fitta mutane daga kasarsu da karfi, don kawai ya na son a kwace zirin gaza daga Falasdinawa. Falasdinawa basa bukatan karin kasa suna son yenci ne a kasarsu. Inji dan majalisar dokoki Kim Johnson na jam’iyyar Lebour.. Kafin haka dai sarki Saman bin Abbdul azizi na kasar Saudiya yace ba...
A yau ne ake sa ran kwamitin kare haƙƙin dan adam na MDD zai yi zaman gaggawa kan yaƙin da ya rincabe a jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo. Ƴan tawayen M23 da Rwanda ke mara wa baya dai sun karɓe iko da birnin GOMA. MDD ta yi ƙiyasin cewa sama da farar hula 2,900 ne aka kashe, yayin da rahotanni ke cewa faɗa na kara yaɗuwa zuwa wasu sassan ƙasar, sannan take hakkin ɗan’adam na ƙara munana. Jakadan Congo a Geneva ya ce gwamnatin ƙasar na buƙatar MDD ta gudanar da cikakken bincike kan hakan. Kungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam sun yi amannar cewa ƴan tawayen M23 da sojojin Rwanda da na Congo duk sun aikata munanan laifuka. Sai dai har yanzu Rwanda...
Sojojin kasar Iran sun nuna karfinsu a yankin Asiya ta kudu tare da itisayen da ta yi ta gudanarwa a cikin yan makonnin da suka gabata. Tare da nuna iya diblomasiyyar kasar tare da sauran kasashen yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rear Admiral Habibollah Sayyari mataimakin shugaban rundunar sojiji na kasar yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa, iya diblomasiyyar kasar Iran a tsakanin kasashen yankin, ya tabbatar da karfin da kasar take da shi a fagen karfin soje. Kuma ta tabbatar da cewa zata iya kula da al-amuran tsarom da kuma tabbata shi a yankin. Sayyari yace an gudanar da atisayen na sojoji kimani rundunonin fiya da 100 inda suka yi musayar tunani...
Jam’iyyar PDP ta yi irin wannan martani. Mataimakin shugaban matasan jam’iyyar PDP na kasa, Timothy Osadolor, ya ce furucin na Buhari ya nuna gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. Haka zalika, shugaban matasan jam’iyyar LP na kasa, Prince Kennedy Ahanotu, ya ce bai yi mamakin jawabin tsohon shugaban kasar ba, domin yana daya daga cikin ‘yan Nijeriyar da suka kasa daukaka kasar. Ahanotu ya kara da cewa, lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su bai wa matasa damar gyara matsalolin da suka faru a baya. Ya ce, “Gaskiya ni ba masoyin Buhari ba ne kuma ban taba tsammanin zai yi abin kirki ba. Don haka ban yi mamakin cewa bai yi komai tsawon shekaru takwas ba. Amma abin da nake...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Shin shure-shure Jam’iyyar PDP take yi da ba ya hana mutuwa, ko kuwa motsi ne na alamun samun lafiya? Wannan ce tambayar da wasu ’yan Najeriya suke yi game da fito-na-fito da shugabannin jam’iyyar suka jima suna yi da juna. Tuni wasu ma suka fara ɗigaayar tambaya a kan makomar jam’iyyar bisa la’akari da tarin rikice-rikicen da suka dabaibaye ta. NAJERIYA A YAU: Ainihin Dalilan Taƙaddama Kan Kafa Kotunan Musulunci A Kudu DAGA LARABA: Dalilan Da Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai nazari don bankado abin da yake faruwa da jam’iyyar yayin da 2027 take kara matsowa. Domin sauke shirin, latsa nan
Jami’an tsaro sun mamaye Sakatariyar Jam’iyyar PDP, bayan rikici ya ɓarke kan shugabancin jam’iyyar. Rikicin ya kunno kai ne tsakanin Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye kan wanda ke da haƙƙin zama Sakataren jam’iyyar na ƙasa. Matashiyar da ta watsa wa mai naƙuda tafasasshen ruwa ta shiga hannu Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS? Rikicin ya fara ne lokacin da duka mutane biyun suka iso taron kwamitin amintattun. A lokacin taron, wani hadimin Anyanwu ya tilasta wa Ude-Okoye fita daga zauren taron, wanda hakan ya janyo gardama tsakanin magoya bayan ɓangarorin biyu. Jami’an tsaro sun shiga tsakani domin kwantar da tarzoma. Matsalar ta samo asali ne bayan Anyanwu ya yi murabus daga kujerarsa don...
Bayan hare haren da mutane suka kai kan ofisoshin jakadancin kasashen Ugandan, Rwandan, Kenyan, Japan, Amurka da kuma Faransa a birnin Kinshasa na kasar Democradiyya Congo masu zamga-zanga sun fara kwasar ganima a manya-manyan shaguwa a birnin. Masu zanga-zangar sun fara tada hankali a kasar ne saboda irin saurin ci gaban da yan tawayen M23 suke mamayar kasar. Kuma suna ganin wadannan kasashe suna da hannu a tallafawa yan tawayen wadanda suke ci gaba da kwace garuruwa daga hannun sojojin Gwamnati. Labarin ya kara da cewa an ga hayaki na tashi a ofishin jakadancin kasar Faransa a Kinshasa, kuma suna yin haka ne don nuna turjiya ga halayen mulkin mallaka na kasar faransa, wacce take daga cikin wadanda suke goyon...
