2025-10-13@20:22:52 GMT
إجمالي نتائج البحث: 116

«hauhawar farashin»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Yayin da watan Ramadan ya shiga kwana na 6, masu lura da al’amura da dama na kokawa kan tsadar kayan marmari a Kano, wanda suke ganin wani muhimmin bangare ne na karin kumallo da ake yi a sahur da kuma lokacin buda baki.   Malam Bello Ibrahim da Abdulmajeed Baba, masu amfani da ’ya’yan itatuwa musamman a lokacin azumin Ramadan, a wata tattaunawa da suka yi da gidan rediyon Najeriya, sun bayyana rashin jin dadinsu da tashin gwauron zabi.     ‘Ya’yan itatuwa na da matukar muhimmanci ga lafiyar mu a lokacin azumi, amma farashin na kara zama wanda ba zai iya jurewa ba,” in ji su.   Malam Ado Shehu, jami’in hulda da jama’a na kasuwar ‘ya’yan itacen Naibawa,...
    “A kan batun kafafen yada labarai, muna son mu yi taka-tsan-tsan don kada mu wuce gona da iri. Al’amari ne da ke cikin Majalisar Dattawa, kuma yin hakan ta hanyar kafafen yada labarai na iya daukar mana hankali. Zauren kwamitin zai iya ɗaukar mutane da yawa, kwamitin yana da mambobi kusan 23 ko 24. Muna son mu mai da hankali kan lamarin da ke gabanmu, kada wani lamari ya dauke mana hankali.”   Ya ba da tabbacin cewa za a yi wa Sanata Akpoti-Uduaghan adalci, inda ya ce: “Mai girma Sanata Natasha na da gata kamar kowane Sanata, kuma za a kare gatanta. Za ta samu adalci a wannan al’amari matukar ina wannan mukami. Kawata ce, kuma ba wanda zai...
    Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Nasarawa da Toto daga Jihar Nasarawa, Honorabul Abdulmumin Ari ya ba da cekin Naira miliyan 45 don biyan kuɗin jarabawar WAEC ga daliban sakandare a mazaɓarsa. Da yake jawabi a wajen taron a garin Keffi, Abdulmumin Ari ya bayyana cewa kimanin shekara biyar ke nan yake aikin agaza wa daliban mazaɓar a duka matakai don cika alkawura da ya yi a baya. Ya ce ya yanke shawarar yin haka ne don tallafa wa iyayen ɗalibai marasa galihu don ba su damar cimma burinsu na samar wa ’ya’yansu ilimin zamani dana addini. Ya ce kawo yanzu ya kashe sama da Naira miliyan 500 a cikin shekara biyar da duka gabata a kan irin wannan aiki....
    ‘Yan majalisar dokokin kasar Iran sun kada kuri’ar tsige ministan harkokin tattalin arziki da kudi Abdonnasser Hemmati daga mukaminsa saboda matsalolin tattalin arziki da kuma faduwar darajar kudin kasar. Hemmati ya rasa kuri’ar amincewa a zaman majalisar na wannan Lahadi inda ‘yan majalisa 182 daga cikin 273 suka kada kuri’ar tsige shi. ‘Yan majalisa tamanin da tara ne suka bukaci ya ci gaba da zama a kan mukaminsa. A yayin Zaman ministan da kansa da shugaban kasar Masoud Pezeshkian sun halarci wurin, yayin da kuma ‘yan majalisar kan batun kudurin, amma dai kudirin ya wuce bayan samun rinjayen amincewa da shi. Shugaba Pezeshkian ya kare Hemmati, tsohon gwamnan babban bankin kasar Iran, ya kuma ce kasar na cikin yakin tattalin...
      Barazanar Ata Kan Ficewa Daga APC A cikin bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta, Minista Yusuf Ata ya yi magana da magoya bayansa, yana mai cewa idan ba a sauya shugabancin APC a Kano ba, to zai fice daga jam’iyyar. “Muna faɗa wa kowa, idan aka mayar da irinsu, duk irinmu fita za mu yi,” in ji Ata. Ya ƙara da cewa, “Idan suka dawo da shi, za mu fice, kuma na rantse da Allah jam’iyyar za ta sake faɗuwa a zabe.” Wannan rikici na ƙara nuna rabuwar kai a cikin APC a Kano, wanda ka iya shafar ƙarfi da tasirin jam’iyyar a jihar nan gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
    Manufar ita ce a kawo karshen wannan tashin hankalin ta hanyar adalci, mai dorewa, wace dukkanin bangarorin da abin ya shafa za su aminta da ita” in ji Rubio ga menema labarai, duk da cewa babu jami’an Yukiren ko na Turai a wurin tattaunawar. A wani labarin kuma, shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya shaida wa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio cewa kasarsa ba za ta amince da korar Falasdinawa daga Gaza ba. Mohammed bin Zayed Al Nahyan na mayar da martani ne ga shirin Shugaba Trump na Amurka na karbe ikon Zirin bayan sauya wa al’ummar Gaza matsuguni. Shugaban na Hadaddiyar Daular Larabawa ya ce sake ginin Gaza abu ne da ya kamata a hada shi da shirin da...
    Hamshakan attajirai da ’yan siyasa sun bayar da gudunmawar sama da Naira biliyan 16 a bikin kaddamar da littafin tarihin tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida. Taron ƙaddamar da littafin, mai suna ‘A Journey in Service’, wanda aka gudanar a Abuja ya tara manyan baƙi daga ciki da wajen Najeriya. Mahalarta taron da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis sun bayar da gudunmawar ne domin ginin dakin karatun da tsohon shugaban ƙasan ke shirin ginawa. Attajiri mafi yawan arziki a Afirka kuma Shugaban Rukunin Kamfanonin Ɗangote, Alhaji Alikon Ɗangote ya ba da gudunmawar Naira biliyan takwas, Naira biliyan biyu a duk shekara, na tsawon shekara huɗu. Ya kuma yi alƙawarin karin biliyan biyu a duk shekara...
    “A watannin da suka gabata, masu ruwa da tsaki a cikin dillalan sun nuna damuwa game da hauhawar farashin kayayyakin abinci. Yanzu da farashin ya ragu, kamar garin da ya fadi daga naira 81,000 a kowace buhu zuwa kasa da naira 60,000, da taliya wanda ya fadi daga naira 20,000 zuwa naira 15,000. “Adalci ne a bar masu amfani da kayayaki su amfana da wannan rage farashin abincin da aka samu,” in ji Kyari. An dai bayar da rahoton cewa, hauhawar farashin kayan abinci ya ragu zuwa kashi 24.48 da kuma kashi 26.08 a watan Janairun 2025, inda ya ragu daga kashi 34.8 bisa dari da kuma kashi 39.84 a watan da ya gabata, sakamakon sake fasalin farashin kayan masarufi...
    Taron dai na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da majalisar dattawan kasar a ranar Laraba ta gayyaci shugabannin hukumar leken asiri don gudanar da bincike kan zargin da dan majalisar dokokin Amurka, Perry Scott ya yi na cewa, hukumar bayar da tallafi ta kasa da kasa ta Amurka, USAID na tallafa wa kungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram.   Da yake jawabi a zaman taron na ranar Laraba, Akpabio ya ce Nijeriya ba za ta bar Hukumar USAID ta ci gaba da aiki a Nijeriya ba idan aka same ta da laifin daukar nauyin ta’addanci.   Ya ci gaba da cewa, yana da muhimmanci Nijeriya ta tabbatar da gaskiyar wannan zargi.
    Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta ce alƙaluman hauhawar farashi sun koma kashi 24.48 daga 34.8 cikin 100 a watan Janairun da ya gabata. Wannan ne karon farko da hukumar ta NBS ta fitar da rahoton bisa sabon tsarin tattara alƙaluma da ta fara amfani da shi, abin da ke nufin da wuya a iya gane haƙiƙanin raguwa ko hauhawa a yanzu. Hajji 2025: Kamfanin Saudiyya zai maka Najeriya a Kotun Duniya Dattijon Neja Delta Edwin Clark ya rasu Alƙaluman sun nuna cewa hauhawar farashin kayan abinci ta kai 26.08 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. Da yake yi wa manema labarai jawabi shugaban hukumar, Prince Adeyemi Adeniran, ya faɗa ranar Talata cewa sun sauya tsarin ne saboda...
    Jaridar Daily Telegraph ta watsa labarin cewa: Shugabannin Iran sun bukaci Jagoran juyin juya halin Musulunci Sayyid Khamenei da ya janye fatawarsa kan haramcin mallakar makamin nukiliya Jaridar Daily Telegraph ta kasar Birtaniya ta watsa rahoton cewa: Shugabannin sojojin Iran sun bukaci Jagoran juyin juya halin Musulunci Sayyid Ali Khamenei ya yi watsi da haramcin mallakar makaman nukiliya da ya fitar da fatawa kanta a farkon takaddamar Shirin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Jaridar ta ruwaito a cikin wani rahoton da wakilinta na musamman Akhtar Muhammad Makoy ya fitar cewa: Manyan jagororin sojojin Iran sun ce dole ne Jagoran juyin juya halin Musulunci ya soke fatawar da ta haramta kera makaman nukiliya matukar gwamnatin Iran na son ci gaba...
    Gwamnan ya bayyana haka a yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai yankin na Rimin Zakara a yammacin ranar Alhamis 06, ga watan Febarairun 2025.   A yayin ziyarar l, gwamnan ya yi alkawarin gina wa jama’ar yankin na Rimin Zakara katafaren Masallacin Juma’a a matsayin sadaka jariya ga wadanda suka rasu a dambarwar filayan yankin da Jami’ar Bayero. Gwamnan ya yi kuma alkawarin samar da Asibitin sha-ka-tafi da samar musu da hanya da kai hasken wutar lantarki da rijiyoyin burtsatsai da bai wa iyalan mamatan jari da daukar dawainiyar karatun yaransu gwargwadon iko da kuma daukar nauyin jinyar wadanda suka ji rauni a yankin a yayin rusau da aka yi a makon da ya gabata.
    Babban jami’in jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Cai Qi, ya yi kira a ranar Laraba, da a ci gaba da yin kokari wajen kawar da ayyukan da ba su da ma’ana, da rage nauyin da ke wuyan jami’an kananan matakai, don tabbatar kyakkyawan salon aiki tsakanin ’yan jam’iyya da jami’ai wajen cimma burin da aka sa a gaba a cikin shirin shekaru biyar-biyar karo na 14 wato daga shekarar 2021 zuwa ta 2025. Cai, wanda kuma mamban zaunannen kwamitin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin JKS ne, kuma mamba a sakatariyar kwamitin kolin JKS, ya bayyana hakan ne a wani taro na matakin koli game da wannan batu. Taron ya bayyana cewa, ya kamata a mayar da hankali wajen...
    A hannu guda kuma, Gwamnan ya yi kira ga sojoji da sauran bangarorin jami’an tsaro da su kara kaimi wajen fadada yin sintiri a yankunan da ke kan iyakokin jihar, domin dakile shigowar yan ta’adda cikin jihar. A nashi bangaren, Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, ya sake baiwa Gwamnan tabbacin cewa sojoji za su ci gaba da jajircewa wajen kawo karshen matsalar yan ta’adda tare da ta yan bindiga a Nijeriya baki daya. “Babbab burinmu shi ne mu wayi gari mu ga wannan matsala ta zo karshe cikin gaggawa, kuma ina mai jaddada kira ga shugabannin siyasa da yan Nijeriya, su ci gaba da bayar da gudummawa wajen ganin mun cimma wannan buri.” In ji COAS. Hakazalika kuma, ya bayar da...
    Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a gaggauta kwashe yara 2,500 da suka jikkata a yakin da Isra’ila ta kwashe watanni 15 tana yi a Gaza domin samun kulawar gaggawa. Rokon nasa ya biyo bayan ganawar da ya yi da likitocin Amurka ne wadanda suka yi gargadin cewa yaran na fuskantar barazanar mutuwa a makonni masu zuwa. Likitocin hudu, wadanda suka yi aikin sa kai a Gaza sun bayyana mummunan halin da yanayin  kiwon lafiyar yankin ke ciki, wanda yakin ya yi wa illa. Guterres ya ce ya ji dadin matuka  bayan tattaunawarsa da likitocin Amurka ranar Alhamis.  Ya kuma”Dole ne a kwashe yara 2,500 ba tare da bata lokaci ba, tare da ba...
    Ya kuma yi gargadi cewa rashin ɗaukar matakai na gyara tattalin arziƙi zai ci gaba da haifar da asara mai yawa, inda tallafin man fetur da na musayar kuɗaɗe ke laƙume kashi biyar cikin ɗari na GDP na ƙasar. Wannan, in ji shi, babban ƙalubale ne ga cigaban tattalin arziƙin Nijeriya.