Tun lokacin da Donald Trump ya hau mukaminsa na shugaban kasar Amurka a watan Janairu na bana, sau da dama gwamnatinsa ta dauki matakan kakaba harajin kwastan kan abokan cinikinta. A ganinsa, matakan za su tilasta kamfanoni da su maido da tsarin samar da kayayyaki zuwa Amurka, matakin da zai gaggauta bunkasuwar masana’antun kasar.

Ko abin ya tafi kamar yadda Trump ya yi tsamani?

Alal hakika, manufofi marasa dorewa da gwamnatin Trump ta dauka na illata amanar Amurka, har ma hakan ya yi ta dakushe kwarin gwiwar masu zuba jari na ketare da na kamfanonin cikin gidan kasar. Babban mizanin wasu muhimman hannayen jarin Amurka ya yi matukar raguwa kwanan baya, abin da ya shaida damuwar masu zuba jari a duniya kan rikicin ciniki da tafiyar hawainiya a bangaren bunkasuwar tattalin arziki. Ban da haka kuma, kamfanonin kasar Amurka da kamfanoni masu jarin waje dake kasar za su iya fuskantar hauhawar kudaden kashewa, da katsewar tsarin samar da kayayyaki da dai sauran kalubaloli. A idanun masu zuba jari, Amurka ba ta zama wuri mai inganci na zuba jari a halin yanzu. Ke nan yaya za a kai ga kare masana’antun cikin gidan kasar?

Mun Yi Watsi Da Ayyana Dokar Ta-Ɓaci Da Tinubu Ya Yi A Ribas – Shugabannin Adawa Cikar NUJ Shekaru 70: ‘Yan Jarida Abokan Hulɗa Ne Wajen Aza Kyakkyawar Makoma – Gwamnan Gombe

Baya ga haka, yanzu al’ummar kasar Amurka na fuskantar hauhawar farashin kayayyaki, har ma bisa nazarin da jami’ar Yale ta yi, an ce ko wane iyalin Amurkawa zai biya karin kudi da yawansa ya kai dala 1600 zuwa 2000 a ko wace shekara, sakamakon karin harajin kwastan da gwamnatin kasar ke bugawa a kan kayayyakin da ake shigar da su daga Mexico, da Canada da Sin.

Kamfanonin dake Amurka da al’ummar kasar, su ne suka fi yin asara karkashin manufar da Trump ya dauka, amma abun tambayar shi ne me ya sa ya yi haka? Kuma wa zai ci gajiyar hakan? (Mai zane da rubutu: MINA)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Amurka Dangane Da Batun Ukraine

Kasar Sin ta sake neman Amurka, da ta daina zarginta, da dora mata laifi, ya kamata kasar Amurka ta taka rawa wajen tsagaita bude wuta, da kara azama ga gudanar da shawarwarin shimfida zaman lafiya. Jami’in ya ce, ana bukatar hadin kai wajen warware rikicin Ukraine, a maimakon rarrabuwar kawuna da yin fito-na-fito. (Tasallah Yuan)

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasar Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Amurka Dangane Da Batun Ukraine
  • Afirka ta Kudu na shirin daukar matakan kauce wa tasirin harajin Amurka
  • Amurka Ta Kakabawa Jami’an Gwamnatin Falasdinawa Takunkuman Hana Shiga Amurka
  • Amurka: “Afirka Ba Ta Cikin Jerin Fannoni Da Muka Ba Da Fifiko A Kai”
  • Tinubu Ya Tsawaita Wa’adin Shugaban Kwastan Da Shekara Ɗaya
  • Kamfanin NNPCL ya sake haka sabbin rijiyoyin man fetur 4 a Kolmani
  • Za a kammala shimfiɗa layin dogo daga Kaduna zuwa Kano a 2026 — Gwamnatin Tarayya
  • Amurka Ta Ce HKI Ba Zata Fice Daga Kasar Lebanon Ba Sai An Kwance Damarar Hizbullah
  • An Kaddamar da Makon MNCH na 2025, Ya Rarraba Fakitin Bayarwa 6,000, Kayan C/S 500
  • Gwamnatin Tinubu ta mayar da Arewa saniyar ware – ACF