Gwamnatin Neja Ta Haramta Karbar Haraji A Hannun Masu Kananan Sana’o’i
Published: 26th, February 2025 GMT
Gwamnatin jihar Neja ta haramta wa masu tattara kudaden shiga a fadin kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar karbar haraji daga hannun ‘yan talla da masu kananan sana’o’i.
Gwamnan jihar Mohammed Umar Bago ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnati Minna, babban birnin jihar.
Mohammed Umar Bago wanda ya yi Allah-wadai da yadda ake karbar kudade ba bisa ka’ida ba a hannun kananan ‘yan kasuwa, ya umurci shugabannin kananan hukumomi da kansiloli da su kara sa ido tare da tabbatar da ganin an kawo karshen irin wadannan ayyuka nan take.
Ya tunatar da su cewa gwamnatin jihar Neja tana da tsarin bai daya da ya hana karbar haraji dafa masu kananan sana’o’i domin basu damar dogaro da kai.
“Mun yanke shawarar cewa daga yanzu, babu wwanimai karamar sana’a da za a sake karbar haraji a hannunsa a wannan jihar.”
“’Yan talla da kananan ‘yan kasuwa ba sa biyan haraji a Jihar Neja, kuma duk wanda aka samu yana karbar haraji daga wurinsu zai dandana kudarsa,” inji Gwamnan.
Daga Aliyu Lawal
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: KASUWANCI karbar haraji
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 45 A Jihar Neja
Rundunar sojin ba ta fitar da sanarwa ba game da wannan hari na baya-bayan nan, amma hukumar DSS ta tabbatar da faruwar lamarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp