Matashiyar da ta watsa wa mai naƙuda tafasasshen ruwa ta shiga hannu
Published: 29th, January 2025 GMT
Wata matashiya mai shekaru 20 ta shiga hannun ‘yan sanda bisa zarginta da ƙona matar ɗan uwanta da ke naƙuda da tafasasshen ruwan zafi.
A tattaunawarta da Aminiya, matashiyar ta ce ɓacin rai ne ya kai ta ga ƙone matar lokacin da musu ya kaure a tsakaninsu.
Jirgin Max Air ɗauke da fasinjoji 59 ya tsallake rijiya da baya a Kano Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS?Lamarin ya faru ne a ranar Laraba a garin Dubeli da ke ƙaramar hukumar Yola ta Arewa da ke Jihar Adamawa.
Mijin matar da aka ƙona ya ce yana shago ne inda yake sana’a aka kira shi a waya cewa an watsa wa matarsa ruwan zafi lokacin da take naƙuda.
Kazalika ya nuna takaicinsa na sanin ‘yar uwarsa ce ta aikata ta’asar, kuma jim kaɗan bayan hakan ne matar tasa ta haihu.
A nasa ɓangaren, Kakakin rundunar ‘Yan Sandan Jihar Nguroje ya tabbatar da kama matashiyar da ake zargin, ya kuma ce za su ci gaba da bincike kafin miƙa ta kotu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Matashiya Ruwan zafi
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 45 A Jihar Neja
Rundunar sojin ba ta fitar da sanarwa ba game da wannan hari na baya-bayan nan, amma hukumar DSS ta tabbatar da faruwar lamarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp