2025-09-18@11:42:49 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7259

«Uwaidu»:

    Kwamitin koli na tsaron kasa ya amince da yarjejeniyar da hukumar makamashin nukiliya ta duniya IAEA Kwamitin koli na tsaron kasar Iran ya yi gargadin cewa, idan aka dauki wani mataki na nuna adawa ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran da cibiyoyinta na makamashin nukiliya, ciki har da sake farfado da kudurorin kwamitin sulhu na Majalisar...
    Adadin mutanen da suka yi shahada sakamakon kisan kiyashin da ‘yan sahayoniyya suke yi a Gaza ya doshi 65,000 Adadin mutanen da suka yi shahada sakamakon yakin da yahudawan sahayoniyya suka kakaba wa Falasdinawa a yankin Zirin Gaza ya karu zuwa shahidai 64,871 da kuma jikkatan wasu 164,610 tun daga ranar 7 ga watan Oktoban...
    Gwamnatin Sudan ta ce: Babu batun sasantawa da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces na kasar wadanda take daukansu a matsayin ‘yan tawaye Gwamnatin Sudan ta yi watsi da shawarar sasantawa da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces (RSF) da kasashen kasashe masu shiga Tsakani suka gabatar, tana mai jaddada cewa,...
    A ƙalla fasinjoji 17 ne suka rasa rayukansu bayan wata motar haya ta faɗa cikin wata gada da ta ruguje a kan titin Gwalli da ke ƙaramar hukumar Gummi, jihar Zamfara. A cewar hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) reshen Zamfara, hatsarin ya faru ne a daren Lahadi lokacin da motar ɗauke da kaya da...
    Hukumar jin daɗin jama’a ta Jihar Kwara tare da haɗin gwiwar Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya sun kama wasu mabarata a titunan Ilorin, ciki har da wasu da aka samu da kuɗaɗen ƙasashen waje. Daga cikin waɗanda aka kama akwai wani mabaraci mai suna Musa Mahmud daga Jihar Kano, wanda aka samu da takardar daloli....
    Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Barcelona ta koma matsayi na biyu a kan teburin gasar La Liga ta Sifaniya bayan ta lallasa ƙungiyar Valencia a filin wasa na Johan Cruyff da ke birnin Barcelona. Fermin Lopez, Raphinha da Lewandowski ne suka zura ƙwallaye shida a ragar Valencia a wasan da aka buga da misalin ƙarfe 8...
    Babban attajirin Afirka kuma Shugaban Rukunin Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ɗauki nauyin gina ɗakunan kwanan ɗalibai masu gadaje 250 da Babban Masallacin Juma’a na Ilorin ya tsara a Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara.   An kiyasta aikin zai ci kusan naira biliyan 1.1, kuma an ƙaddamar da shi ne domin samar da hanyar...
    Ma’aikatar tsaron Isra’ila ta ce fiye da sojojin kasar 20,000 ne suka ji rauni tun farkon yakin da aka fara a Gaza a watan Oktoba 2023, inda fiye da rabinsu ke fama da matsalolin lafiyar kwakwalwa, ciki har da ciwon damuwa. A cewar sashen bayar da shawarwari na ma’aikatar, kusan kashi 56 cikin 100 na...
    Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya koka bisa yawan bashin da Najeriya ke ciyowa da kuma yadda gwamnati ke facaka da kuɗaɗen. Sarkin wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ne, ya kuma bayyana cewa cire tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi shi ne mafi alheri, yana  mai cewa da Gwamnatin...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ambaliyar ruwa na cigaba da salwantar da dukiyoyi da rayukan al’ummomi da dama a sassa daban-daban na Najeriya.   Ko a farkon makon nan, hukumomi sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar samun ambaliyar a jihohi akalla 11. Sai dai wasu alummomin tuni suka dauki matakai don rage barnar...
    Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya roƙi Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na KEDCO ya gaggauta dawo masa da wuta bayan rasuwar wasu marasa lafiya da ke samun kulawa ta ceton rayuwada na’ura. Wata sanarwa da kakakin asibitin, Hauwa Inuwa Dutse ta fitar ta nuna takaici bisa rasuwar marasa lafiyan, tana mai cewa mace-macen waɗanda...
    Sarakunan suna bada haɗin kai wajen tafiyar da harkokin gwamnatin ƙasarsu, suna kuma jin basu tare da wata matsala ba tare da matsayinsu. Yawancin Sarakuna da kuma wasu manyan msu Sarautar gargajiya bugu da ƙari suna cikin majlisar dattawa a lokacin. Duk kuma wani lokaci da Sarakunan gargajiya suka fahimci suna fuskantar barazana dangane da...
    A yau Lahadi ne wakilan kasashen Sin da na Amurka, sun isa birnin Madrid na kasar Sifaniya, domin gudanar da tattaunawa game da batutuwan tattalin arziki da cinikayya. Cikin kwanaki masu zuwa, sassan biyu za su zanta game da batutuwan da suka hada da matakin Amurka na kakaba haraji, da karya ka’idar kayyade fitar da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ƙwallon ɗaya tilo da kyaftin din ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars Ahmed Musa ya ciwa ƙungiyar tayi sanadiyar samun nasarar farko da ƙungiyar tayi tun bayan fara wannan kakar wasannin ta bana. Pillars ta doke abokiyar karawarta Enugu Rangers da ci 1-0 a wasan da suka buga a filin wasa na Sani Abacha dake...
    Tun daga ranar 18 ga wata, za a kaddamar da fim mai taken 731 a sassan duniya da dama, fim din da ya bayyana yadda rundunar sojojin kasar Japan da suka kutsa kasar Sin suka gudanar da nazari a kan hada makamai da cututtuka tare da gudanar da gwaje-gwaje a jikin al’ummar kasar Sin, a...
    Mazauna garin Manchok a masarautar Moro’a, da ke Ƙaramar Hukumar Kaura, a Jihar Kaduna, sun roƙi gwamnatin jihar da ta tarayya su kai musu ɗauki bayan ambaliyar ruwa ta lalata gidaje da gonaki a yankin. Ambaliyar ta auku ne sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da aka shafe kwana uku a jere ana yi. Hakan ya...
    Bikin baje kolin hada-hadar ba da hidima na kasa da kasa wato CIFTIS a takaice na shekarar 2025 da aka rufe a yau Lahadi, ya ja hankalin masu saka jari daga tarin kasashen waje. Manyan jami’an kamfanoni na kasashen waje sun bayyana cewa, suna daukar bikin a matsayin wata babban dandamali na more damammaki tare...
    A cikin shekaru uku da kafuwarta, gidauniyar Misilli, ta mayar da yara 150 makarantar boko a Jihar Gombe, ciki har da mata 88 da maza 62, tare da ɗaukar nauyin kuɗaɗen karatunsu. Wannan mataki ya taimaka wajen rage nauyin iyaye marasa hali, inda suka samu ’yancin zaɓar makarantun da ke kusa da su. Ambaliya: NEDC...
    Ya zuwa ranar Alhamis 11 ga watan nan, lokacin da aka kammala taron baje kolin kasa da kasa na hada-hadar zuba jari da cinikayya na kasar Sin karo na 25, an riga an sanya hannu kan yarjejeniyar gudanar da ayyukan zuba jari a sassa daban daban da yawansu ya kai 1,154, tare da tsara shigar...
    Masana’antar Kannywood Na Tsananin Buqatar Addu’a – Hauwa Garba Dole Mu Hada Kai Da ‘Yan Siyasa Don Ciyar Da Masana’antar Kannywood Gaba -Shugaban MOPPAN Ko za ka faɗawa masu karatu ɗan taƙaitaccen tarihinka? Ni haifaffen ɗan Zaria ne, wani gari da ake cewa, Samaru ana yi masa laƙabi da Samarun Zaria. Kuma nan nake a...
    Gwamnatin Tarayya ta sanar cewa Samun Lambar Tantance Haraji (Tax ID) zai zama wajibi ga duk ƴan  Nijeriya da ke hulda da bankuna da sauran ayyukan hada-hadar kudi daga ranar 1 ga Janairu, 2026. Wannan sabon umarni yana cikin Dokar Gudanar da Haraji ta Nijeriya, 2025, wacce shugaban kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kwanan...
    A cewar sanarwar, bisa wannan sanarwar, fadar ta shugaban ƙasa, ta yanke duk wata huɗɗa da Umunubo. Sanawar ta kuma jaadda cewa, ya zama wajbi ɗaukacin masana’antun da ke a ƙasar nan, su nesanta kansu, da yin dukka wata huɗɗa da Umunubo da sunanan gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu. Idan za a iya tunawa, Jaridar...
    An gano gawar Haneefa, yarinya ’yar shekara uku da ruwa ya tafi da ita lokacin da yayarta Fatima, ke goye da ita yayin ambaliyar da ta rutsa da su a Tudun Jukun da ke Zariya, a Jihar Kaduna. An tsinci gawar ne bayan kwanaki shida da aka kwashe ana nemanta, a gangaren ƙasan Kilaco, unguwar...
    Sama da kashi casa’in (90%) na kabilu da mabiya addinai da ke raye cikin Nijeriyar yau, ba su damu da samar da shugabanci nagari cikin Kasar ba a aikace, sai dai kawai a mafarkance. Za a iya gane hakan ne ta hanyar nazartar aiyukansu hada da furuce-furucensu!!!. Da daman mutane ba sa zaɓar wani kansila...
    “Shawarar tsarin shugabancin duniya” ta zama kalmar da aka sha karanta a rahotannin kafofin watsa labaru na duniya cikin kwanakin baya. Shugabannin wasu kasashe da dama suna ganin cewa, wannan shawarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a yayin taron koli na SCO da aka gudanar a kwanan baya a birnin Tianjin, tana...
    An yi wa ’yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Jihar Akwa Ibom ruwan kuɗi, bayan sun yi fice a gasar wasannin motsa jiki ta ƙasa da aka yi wa laƙaba da IBOM 2025, wacce aka kammala a ƙarshen makon nan. Gwamna Umo Eno, ya bai wa gwarazan ’yan wasan da suka lashe kambin Zinare kyautar...
    Misali, ya sauya lokacin da aka tsara yin wasan sada zumunta da ƴan  ƙasa da shekara 20 na ƙungiyar Flamengo a lokacin da Leɓerkusen ta je atisaye a Brazil. An buga wasan kwana biyar kafin ranar da aka tsara tun farko, inda Leɓerkusen ta sha kashi da ci 5-1. Haka nan a kusan wannan lokacin...
    Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC), ta raba wa mutum 2,261 da ambaliyar ruwa ta shafa a Potiskum, Nangere da Jakusko a Jihar Yobe, kayan agaji. An raba kayan ne a unguwanni 21 na Potiskum, ƙauyukan Kolo da Ajim a Nangere, da kuma kauyukan Dachia, Yim, Saminaka, Garin Maji da Amshi a Jakusko. Gwamnati...
    An karrama fitattun fina-finai daban daban a bikin “Golden Panda” da ya gudana jiya Asabar a birnin Chengdu na lardin Sichuan dake kasar Sin. A bana, an gudanar da bikin ne a karo na biyu, wanda kuma gungun sassan bunkasa harkokin adabi da al’adu da gwamnatin lardin Sichuan suka dauki nauyin shirya shi. Bikin na...
    A cikin sanarwarsa, Daso ya ce: “Rundunar Ƴansanda ta Jihar Borno na sanar da jama’a cewa an gano gawar wani mutum da ba a tantance ba a kusa da na’urar sauya wuta (transformer) a Jami’ar Jihar Borno, Maiduguri. “Binciken farko ya nuna cewa marigayin ya mutu ne sakamakon jan wutar lantarki yayin da yake ƙoƙarin...
    Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗi cewa jihohi 11 na iya fuskantar ruwan sama mai yawa wanda ka iya haddasa ambaliya daga ranar Lahadi zuwa Alhamis. A cikin sanarwar da Cibiyar Gargaɗin Ambaliya ta Ƙasa, ƙarƙashin Ma’aikatar Muhalli, ta fitar, jihohin da abin ya shafa sun haɗa da Adamawa, Benuwe, Nasarawa, Taraba da Delta. An yi...
      A cewar kakakin ‘yansandan, jami’an sun tare wata mota kirar Toyota Corolla mai launin toka mai lamba GGE 473 BH bayan direban ya kasa bayar da kwakkwaran bayanin kansa da kuma motar.   Ya bayyana cewa binciken da aka yi wa motar ya kai ga gano wata bindiga da aka kera a cikin gida,...
    Lawal ya ƙara da cewa, ɗaukacin guraren da Jiragen Ruwa ke tsaya, akwai launin da kuma lamba da aka amince,manyan motocin za su rinƙa yin amfani da su, domin yin zirga-zirga  a Tashar ta Apapa. “Misali, a APMT, manyan motocin za su rinƙa yin amfani da lamba  001 mai ɗauke launin ruwan bula, inda kuma...
    An yi wa ’yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Jihar Akwa Ibom ruwan kuɗi, bayan sun yi fice a gasar wasannin motsa jiki ta ƙasa da aka yi wa laƙaba da IBOM 2025, wacce aka kammala a ƙarshen makon nan. Gwamna Umo Eno, ya bai wa gwarazan ’yan wasan da suka lashe kambin Zinare kyautar...
    Hakazalika, sojojin na Brigade 12 tare da hadin gwiwar dakarun hadin gwiwa da ’yan banga a wannan rana, sun ceto fasinjoji 17 da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Lokoja ta jihar Kogi.   Hakazalika, dakarun Sashe ta 1 ‘Operation Whirl Stroke (OPWS)’ sun ceto wani a karamar hukumar Katsina-Ala...
    Rundunar ‘yansandan jihar Adamawa ta ce ta ceto wasu yara biyar da ake zargin sato su aka yi, daga Maiduguri jihar Borno zuwa Adamawa. Kwamandan yankin na Mubi, ACP Marcos Mancha, a ranar 13 ga Satumba, 2025, a yayin da ya samu wasu bayanan sirri, ya jagoranci tawagarsa inda ya samu wasu yara biyar akan...
    Kabiru Abubakar Aliyu, wanda aka fi sani da Nakwango, ɗaya ne daga cikin jiga-jigan da aka kafa masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood da su. A cikin wannan tattaunawar, ya bayyana cewa bai taɓa yin da-na-sanin shigarsa sana’ar ba, sannan ya bayyana dalilin da yanzu ba a cika ganin sa sosai a fina-finai ba, da...
    Kamar yadda Oche, wadda ‘ya’yan ‘yar’uwarta suke zuwa makarantar Reno ta Oluwami da Firmare , da take Abuja inda shekarun baya suke biyan wajen Naira 600,000 ko wane zangon karatu, saboda wasu haraje- harajen da aka haɗa da su ciki. “Maganar gaskiya kowace shekara idan za’a shiga sabon zangon karatu, makarantu su kan ƙara kuɗin...
    Kona mutanen da suka rasa matsugunansu a cikin tantunansu, a cikin dare mai wahala ga zirin Gaza Da sanyin safiyar Lahadi 14 ga watan Satumban shekara ta 2025 jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka ci gaba da kai munanan hare-haren bama-bamai a zirin Gaza, musamman birnin Gaza, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da jikkata...
    Amurka ta bayyana cewa: Harin da Isra’ila ta kai wa Qatar ba ya barazana ga kawancenta haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya fada a ranar Asabar din nan cewa: Harin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a Doha babban birnin kasar Qatar a makon jiya ba zai shafi dangantakar...
    Kungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa (NARD) ta sanar da janye yajin aikin gargaɗi da ta fara bayan kwanaki biyu kacal. Sai dai ƙungiyar ta sake bai wa Gwamnati Tarayya mako biyu ta biya buƙatunta ko ta sake tsunduma yajin aiki. Shugaban ƙungiyar, Dakta Tope Osundara ne ya bayyana haka a ranar Asabar tare da umartar...
    ADC ta ce, “APC tana tsoron ƙaruwar shaharar ADC a faɗin ƙasar nan ne, kuma yana bayyana cewa shi ne kawai hanyar da za su iya bi wajen tarwatsa ƴan adawa a ƙasar nan. “An fara ne a Jihar Edo da gargaɗin shugabannin ADC kan ka da su ziyarci jihar, sannan Kogi ta biyo baya,...
    Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta yi nasarar korar Falasɗinawa sama da mutum 250,000 daga birnin Gaza tun bayan da suka fara zafafa kai hare-hare a yankin. Wannan dai na zuwa ne a yayin da jami’an Falasɗinu suka ce da dama sun gaza ficewa daga kudancin ƙasar saboda cunkoso. Najeriya ta daɗe tana fama da...
    Aƙalla mutane 19 ne suka mutu a yayin da suka ɗauko wata amarya zuwa ɗakin mijinta bayan motarsu ta faɗa a ƙarƙashin gadar Gwalli da ke yankin Fass a Ƙaramar Hukumar Gummi a Jihar Zamfara. Lamarin ya faru ne da yammacin Asabar da misalin ƙarfe 4:45 na yamma, lokacin da motar, da ke ɗauke da...
    Tsohon kwamandan dakarun IRGC na kasar Iran Mosen Razai ya bayyana cewa kasashen yanking abas ta tsakiya su saurari fadowar boma boman HKI a kan kasashensu idan sun ki daukar matakin hada kai da kuma samar da rundunar kawance don fuskantar haramtacciyar kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rezayi yana fadar...
    A birnin Auckland, babban birnin kasar New Zealanda, dubban mutane sun fito tattaki da jerin gwano don goyon bayan al-ummar Falasdinu a gaza kan kissan kiyashin da HKI take wa mutanen gaza kimani shekaru biyu da suka gabata. Tashar talabejin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, a jiya Asabar 13 ga watan Satumba...
    Haka kuma, kamfanonin gwamnatin tarayya da suka durƙushe a jihar sun haɗa da: Nigeria Paper Mill, Jebba; Nigeria Sugar Company, Bacita; da Nigeria Yeast and Alcohol Manufacturing Company, Bacita. Yadda Tinubu Ya Shawo Kan Gwamnonin Arewa Wajen Amincewa Da Kafa Ƴansandan Jihohi Yadda Tinubu Ya Shawo Kan Gwamnonin Arewa Wajen Amincewa Da Kafa Ƴansandan Jihohi...
    A yau Asabar aka kaddamar da tashar watsa labarai ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) ta Sichuan, tare da kaddamar da wasu jerin ayyuka na CMG din a Chengdu babban birnin lardin Sichuan. Daraktan CMG Shen Haixiong ya halarci taron, inda a ciki jawabinsa ya ce kafar CMG za ta...
    Rahotanni sun bayyana cewa kasar masar ta bayyana cewa Isra’ila na shirya makarkashiyar kashe jagororin kungiyar Hamas a kasarta, don haka ta gargadi tel aviv da cewa duk wani hari dai dai yake da shelanta yaki kuma za su daga mata kafa ba, Wata majiyar labarai ta bayyana cewa jami’an kasar masar sun yi kira...