2025-11-09@20:37:41 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7705
«wa sallar idi»:
Babban jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Yobe, Alhaji Sani Adamu Yarin Fika, ya sauya sheƙa zuwa APC da ke mulki a jihar. Yarin Fika, ya sanar da sauya sheƙarsa a wani biki da aka gudanar a Damaturu, inda ya ce ya yanke shawarar shiga APC ne saboda irin ƙoƙarin da Gwamna Mai Mala Buni ke yi wajen ci gaban jihar. Lakurawa sun kashe jami’in kwastam a Kebbi Gwamna Kebbi ya gargaɗi manoma da makiyaya kan su zauna lafiya ko su fuskanci hukunci Ya ce zai ba da gudunmawa wajen ganin Gwamna Buni ya ci gaba da nasarorin da yake samu a jihar. Tsohon ɗan takarar PDP, ya kuma bayyana cewa, dukkanin magoya bayansa a yankin sun bi sahunsa wajen...
Babban jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Yobe, Alhaji Sani Adamu Yarin Fika, ya sauya sheƙa zuwa APC da ke mulki a jihar. Yarin Fika, ya sanar da sauya sheƙarsa a wani biki da aka gudanar a Damaturu, inda ya ce ya yanke shawarar shiga APC ne saboda irin ƙoƙarin da Gwamna Mai Mala Buni ke yi wajen ci gaban jihar. Lakurawa sun kashe jami’in kwastam a Kebbi Gwamna Kebbi ya gargaɗi manoma da makiyaya kan su zauna lafiya ko su fuskanci hukunci Ya ce zai ba da gudunmawa wajen ganin Gwamna Buni ya ci gaba da nasarorin da yake samu a jihar. Tsohon ɗan takarar PDP, ya kuma bayyana cewa, dukkanin magoya bayansa a yankin sun bi sahunsa wajen...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabar kwamitin wasannin Olympics na duniya (IOC) Kirsty Coventry da kuma shugaban kwamitin na karramawa Thomas Bach a Guangzhou, babban birnin lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin. Xi ya nuna cewa, kasar Sin ta kasance mai himma, mai ba da kariya kuma mai yayata ruhin wasannin Olympics. Ya ce, gasar wasanni ta kasa ita ce babban bikin wasanni mafi girma a kasar Sin. Kuma yankunan Guangdong, Hong Kong da Macao ne suka hada hannu wajen shirya gasar wasannin ta kasa karo na 15. Ana kyautata zaton cewa, wannan gasar wasannin ta kasa ba wai kawai za ta bayyana sabbin nasarorin da kasar Sin ta samu a sabon zamani ba ne, har...
CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji November 9, 2025 Daga Birnin Sin Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15 November 9, 2025 Daga Birnin Sin Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba November 9, 2025
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta yi kira ga hukumar gudanarwar asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni da ta ba da kulawa ta musamman ga yan asalin jihar wajen daukar aiki. Gwamna Umar Namadi ya yi wannan kiran a lokacin da babban likitan asibitin Dr. Salisu Mu’azu Babura da ma’aikatan asibitin suka kai masa ziyarar a gidan gwamnati dake Dutse. Malam Umar Namadi ya bayyana cewar jihar Jigawa tana da kwararru da kuma masana da za su iya cike gibin guraben ayyukan lafiya a asibitin na Rasheed Shekoni. Gwamnan ya kuma bada tabbacin ci gaba da tallafawa asibitin don cimma nasarorin da aka sanya a gaba. Malam Umar Namadi ya kuma bayyana cewar gwamnatin jihar za ta kari...
Gwamna Namadi Ya Bukaci Asibitin Koyarwa Na RSUTH Ya Bada Fifiko Ga ‘Yan Asalin Jihar Yayin Daukar Ma’aikata
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta yi kira ga hukumar gudanarwar asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni da ta ba da kulawa ta musamman ga yan asalin jihar wajen daukar aiki. Gwamna Umar Namadi ya yi wannan kiran a lokacin da babban likitan asibitin Dr. Salisu Mu’azu Babura da ma’aikatan asibitin suka kai masa ziyarar a gidan gwamnati dake Dutse. Malam Umar Namadi ya bayyana cewar jihar Jigawa tana da kwararru da kuma masana da za su iya cike gibin guraben ayyukan lafiya a asibitin na Rasheed Shekoni. Gwamnan ya kuma bada tabbacin ci gaba da tallafawa asibitin don cimma nasarorin da aka sanya a gaba. Malam Umar Namadi ya kuma bayyana cewar gwamnatin jihar za ta kari...
’Yan ta’addan Lakurawa sun kai hari sansanin Hukumar Kwastam da ke Maje, a Ƙaramar Hukumar Bagudo ta Jihar Kebbi, inda suka kashe wani jami’i guda ɗaya. Wani mazaunin yankin ya ce ’yan ta’addan sun zo da yawa, inda suka fara harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa, sannan suka ƙone sansanin jami’an kwastam. Gwamna Kebbi ya gargaɗi manoma da makiyaya kan su zauna lafiya ko su fuskanci hukunci Ya kamata duk ɗan Najeriya ya damu da barazanar Trump– Jigon APC Ya ce, “Lakurawa sun zo da yawa, suna harbe-harbe ta ko ina. Sun ƙone sansanin kwastam tare da kashe wani jami’i.” Mai magana da yawun hukumar Kwastam a Jihar Kebbi, Muhammad Tajudeen, ya tabbatar da faruwar harin. Ya ce jami’an hukumar suna asibiti suna...
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya gargaɗi manoma da makiyaya a Ƙaramar Hukumar Arewa, da su daina faɗa tare da zama lafiya, ko kuma su fuskanci hukunci a kotu. Gwamnan, ya yi wannan gargaɗi ne yayin da ya ziyarci mutanen da suka rasa muhallansu sakamakon rikici, waɗanda yanzu ke zaune a harabar sakatariyar Ƙaramar Hukumar Arewa da ke Kangiwa. Ya kamata duk ɗan Najeriya ya damu da barazanar Trump– Jigon APC Mataimakin Shugaban Majalisar Kebbi ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga “Na zo ne don jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a dalilin wannan rikici, amma dole ne mutane su daina ɗaukar doka a hannunsu,” in ji shi. Gwamnan, ya ce gwamnati ta fara bincike don gano musabbabin rikicin,...
Iran ta bakin ministan harkokin wajen kasar ta bayyana cewa a shirye take ta taimaka wajen warware rikicin da ke tsakanin Pakistan da Afghanistan wanda ya kara ta’azzara kwanan nan bayan fadan kan iyaka mai muni da ya faru. Abass Araghchi ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Pakistan, Mohammad Ishaq Dar, yau Lahadi, inda suka tattauna dangantakar kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a yankin. Mista Araghchi ya bayyana damuwa game da halin da ake ciki a yanzu tsakanin Afghanistan da Pakistan, yana mai jaddada bukatar ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu, tare da taimakon kasashen yankin masu tasiri, don sasanta takaddamar da rage tashin hankali. A watan da ya...
Ministocin tsaro na kasashen Burkina Faso, Nijar, da Mali sun yunkuri anniyar kafa rundunar tsaro ta hadin gwiwa, wacce zata tunkari magance barazanar ta’addanci mai nasaba da kungiyoyin JNIM da ISIS a yankin Sahel. Kasashen sun bayyana hakan ne bayan wani taro da suka gudanar a Niamey karkashin jagorancin shugaban kasar Nijar Abdourahamane Tiani da ministocin tsaron kasashen da ke kungiyar kawacen sahel ta (AES). Ministocin tsaro na Mali, Sadio Camara; Burkina Faso, Célestin Simporé; da Nijar, Salifou Mody, sun sanar da shawararsu ta hanzarta aiwatar da aikin rundunar hadin gwiwa ta AES. Shawarwarin da aka amince da su sun tanadi musayar bayanan sirri, da kuma hadin guiwa ta fanin ayyukan soji. Kasashen na fuskantar barazanar kungiyoyin ta’addanci da suka...
Majalisar Dinkin Duniya, ta yi Allah wadai da mummunan ta’addancin da aka aikata kan fararen hula a yankin El-Fasher na Sudan. Ofishin kare hakkin dan adam na Majalisar Dinkin Duniya da ke Sudan ya yi gargadin cewa El-Fasher ya zama birnin makoki a yayin da ake ci gaba da kai hare-hare masu muni, wanda hakan ya haddasa wahalhalu marasa misaltuwa. A cikin wani bidiyo da aka wallafa a dandalin sada zumunta na X, Li Fung, Wakiliyar Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan, ta ce: “A cikin kwanaki goma da suka gabata, yankin El-Fasher ya kasance wurin da ake samun karuwar hare-haren ta’addanci. A cewarta, “an kashe daruruwan mutane, ciki har da mata, yara, da wadanda suka...
Shugaban reshen Akure na NBA, Mr. Friday Umar, wanda ya yi wannan kira, ya lura cewa “wani lokacin, yanke hukuncin masu karo da juna, suna tasowa ne daga bambance-bambancen ra’ayoyin alkalai” kuma ya amince cewa Majalisar Shari’a ta Ƙasa (NJC) tana ƙoƙarin kawo ƙarshen wannan yanayi. Ya ƙara da gargaɗin cewa, ya kamata a riƙa shigar da ƙara a inda aka yi laifi don kiyaye mutuncin shari’a. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga November 9, 2025 Labarai Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra November 9, 2025 Manyan Labarai Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura November 9,...
Kamfanonin Jiragen Sama Da Dama Na Amurka Sun Dakatar Da Jigilar Matafiya Saboda Rufe Ayyukan Gwamnati
Kafafen watsa labarun Amurka sun ce, kamfanon jiragen sama sun dakatar da zirga-zirga 1330 a jiya Asabar saboda ci gaba da rufe ayyukan gwamnatin tarayyar kasar dalilin rashin cimma matsaya akan kasafin kudi a Majalisun kasar. Masu sanya idanu akan kai da komowar jiragen sama ne su ka dakatar da aiki saboda ba za su karbi albashi ba, idan su ka yi aiki alhali ayyukan gwamnati suna a rufe. Hukumar filayen jiragen sama ta tarayyar Amurka ce ta sanar da cewa masu aikin kula da zirga-zirgar jiragen sama a hasumiyoyin dake cikin filayane jiragen sama 25 sun dakatar da aiki. Daga cikin garuruwan da tsaikon aikin ya shafa da akwai Chicago, Sanfarancisco, New York, New Rock da kuma Atalanta. Tashar...
Wasu Karin kasashe takwas sun yi kira da a kama Fira ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamine Netanyahu saboda laifukan yakin da ya aikata. Kasashen Turkiya, Norway, Italiya, Canada, Slovenia da Lithuania, sun bayyana cewa a shriye suke su kama fira ministan na haramtacciyar Kasar Isra’ila. A kasar Turkiya mai shiga da kara na birnin Istanbul ya fitar da sammacin kamo mutane 37 masu hannu a kisan kiyashin Gaza daga cikinsu da akwai Netanyahu, ministansa na yaki, Kats, da babban hafsan hafsoshin sojan ‘yan sahayoniya Iyal Zamir. A ranar 21 ga watan Nuwamba 2024 ne kotun manyan laifuka ta kasa da kasa ta fitar da sammacin kamo Fira minista Netanyahu da tsohon ministansa na yaki Yoav Gallant saboda amfani da yunwa...
Shirin Majalisar Dinkin Duniya Na Samar Da Abinci ( WFP) ya fitar da gargadi akan cewa, yankin gabashin DRC yana fama da matsananciyar yunwa. Daraktar cibiyar ta WFP a kasar ta DRC Cynthia Jones ce ta yi wannan gargadin yana mai kara da cewa; Da akwai iyalan da suke tsallaken cin abinci, bayan da su ka sayar da kayan gidansu da kuma dabbobin da su ka mallaka.” Hukumar da yake kula da wadatar abinci ( IPC) ta ce da akwai mutanen da adadinsu ya kai miliyan 25 da suke cikin matakin karshe na yunwa, daga cikinsu da akwai wasu miliyan 3 da suke cikin hatsari. Hukumar ta MDD ta kuma ce, a halin yanzu mutane suna ta mutuwa saboda babu...
Mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kebbi, Muhammad Sama’ila Bagudo, ya kuɓuta bayan shafe fiye da mako guda a hannun ’yan bindigar da suka yi garkuwa da shi. Aminiya ta ruwaito cewa an sace mataimakin shugaban majalisar ne a ranar Juma’a 31 ga Oktoba, 2025, jim kaɗan bayan ya kammala sallar la’asar a masallacin garinsu na Bagudo. ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra Gwamna Soludo ya lashe Zaɓen Anambra karo na biyu Sakataren gwamnatin jihar, Yakubu Tafida, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin Asabar. Bayanai sun tabbatar da cewa lamarin na zuwa ne daidai da lokacin da aka gudanar da addu’o’in haɗin kai tsakanin Musulmai da Kiristoci domin neman zaman lafiya...
Babban mai tattara zaɓe da hukumar ta turo, Farfesa Edogah Omoregie, kuma shugaban jami’ar Benin, shi ne ya karanta sakamakon na karshe a hedkwatar zaɓe da ke Awka. Nasarar Soludo ta nuna cewa APGA na ci gaba da daƙile siyasar yankin, tare da samun cikakken goyon bayan jama’ar jihar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga November 9, 2025 Manyan Labarai Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura November 9, 2025 Labarai Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza November 8, 2025
Charles Soludo na jam’iyyar All Progressives Grand Alliance wato APGA, ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Anambra wanda aka yi a jiya Asabar, 8 ga watan Nuwamba. Baturen zaɓen jihar, Farfesa Edoma Omoregie ne ya sanar da sakamakon a cibiyar tattara sakamakon zaɓen da ke babban birnin jihar, Awka a safiyar yau Lahadi. Yaran Bello Turji sun kashe mutum 5, sun sace 9 a Sakkwato ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra Ya ce Soludo ya samu ƙuri’a 422,664, sai kuma Nichola Ukachukwu na jam’iyyar APC mai biye masa da ƙuri’a 99,445. George Moghalu na jam’iyyar Labour ne ya zo na uku da ƙuri’a 10,576, sai Jude Ezenwafor na PDP mai ƙuri’a 1401. Charles Soludo wanda tsohon shugaban babban...
Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani kansila mai suna Nze Ala Kuru Orji yayin da ya fita jefa ƙuri’arsa a rumfar zaɓe da ke ƙauyen Orumba, a yankin ƙaramar hukumar Orumba ta Kudu, lokacin zaɓen gwamnan Jihar Anambra da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata. Rahotanni sun nuna cewa, lamarin ya faru ne da ranar Asabar, a akwatin zaɓe na mazabar Ezukaka 1, da misalin ƙarfe ɗaya na rana. Ban taɓa zargin Shettima da ƙirƙiro Boko Haram ba — Sheriff Yaran Bello Turji sun kashe mutum 5, sun sace 9 a Sakkwato Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa: “Ana tsaka da jefa ƙuri’a sai wasu matasa da ke sanye da abun rufe fuska suka bayyana, suka harbe mutumin...
Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bagher Ghalibaf ya ce faɗaɗa cinikayyar kan iyaka da hadin gwiwar tattalin arziki Tsakanin Iran da Pakistan zai taimaka wajen ƙarfafa tsaro da kuma habaka ci gaban kasashen biyu, yayin da ake kokarin samar da sabbin damammaki don ci moriyar juna a tsakaninsu. Da yake magana bayan dawowarsa daga ziyarar kwanaki uku da ya kai Pakistan ranar Juma’a, ya ce, “Idan aka habaka kasuwannin kan iyaka kuma ciniki da Pakistan ya ci gaba da bunkasa, to za a magance yawancin matsalolin rashin tsaro da kalubalen kan iyaka tsakanin kasashen biyu, domin mayar da yankunan kan iyaka zuwa cibiyoyin manyan ayyukan tattalin arziki zai rage fasa-kwauri da rashin tsaro, haka nan kuma zai share fagen...
‘Yan sandan Tanzania sun kama Amani Gologowa, mataimakin sakatare janar na jam’iyyar adawa ta Chadema a ranar jiya Asabar, bayan zanga-zangar da ta barke bayan zaben makon da ya gabata. Hukumomi sun sanar da sunayen wasu mutane 9 da ake nema ruwa a jallo dangane da abubuwan da suka faru. Jam’iyyar Chadema da wasu mambobi na kungiyoyi masu fafutukar kare hakkin dan adam da dama sun yi ikirarin cewa, jami’an tsaro sun kashe mutane sama da 1,000 yayin da suke tarwatsa zanga-zangar, alkaluman da gwamnati ta yi watsi da su a matsayin marasa tushe, amma kuma gwamnatin ba ta bayar da adadin wadanda suka mutu a hukumance ba. ‘Yan sanda sun sanya Gologowa da wasu mutane tara a cikin jerin...
Tsohon Shugaban Amurka Biden ya yi dirar mikiya kan shugaba Trump cewa; Ba wai kawai yana lalata Fadar White House ba ne har ma da dukkan al’ummar kasar Tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya yi dirar mikiya kan magajinsa Donald Trump, yana mai cewa: Shugaban na yanzu ba wai kawai ya kawo wani abin kunya ga Fadar White House ba ce, har ma ga dimokuradiyyar Amurka. CNN ta ambato Biden yana cewa: A lokacin wani taron Jam’iyyar Democrat a Nebraska a yammacin Juma’a a Omaha: “Biden na cewa, ya san Trump zai kawo wani abin kunya a kasar, amma bai sani ba shin dole ne ya amince cewa akwai wani abin kunya da ya riga ya faru.” Biden yana magana...
Daga cikin ƙorafe-ƙorafen da masu ƙara suka zayyana sun haɗa cewa, ya danganta halittar Annabi SAW da ƙasƙantun halittu (‘Ya’yan Tumkiya, da Karya, da Ƙwarƙwata), sannan kuma ya taɓa alfarmar iyayen Annabi SAW wanda a cewarsu, hakan bai dace ba a alfarmarsa fiyayyen halitta. Gwamnatin Kano, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ba tare da ɓata lokaci ba, ta miƙa koken ga Majalisar Shura ta jihar domin fayyace gaskiyar lamari. Majalisar Shura, ta bakin Sakatarenta, Shehu Wada Sagagi, a wani taron manema labarai da ta gudanar, ta tabbatar da cewa, za ta gudanar da cikakken bincike akan zargin da aka yi wa Malamin (Abubakar Triumph). Sannan kuma, za ta gayyaci masu ƙorafe-ƙorafe da kuma Malamin domin sauraron bayanansu....
Ministan Kasa a Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya, Bello Muhammad Goronyo, ya sake jaddada kudirin Gwamnatin Shugaban Kasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu na tabbatar da kammala aikin gyaran titin Abuja zuwa Kaduna har zuwa Kano, da kuma wasu manyan tituna a Arewacin ƙasar nan. Ministan, Barrister Bello Goronyo (ESQ), ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyara don duba yadda aikin ke gudana, domin tabbatar da cewa ana sa idanu sosai, kuma ‘yan kwangila suna gudanar da aikin cikin inganci da nagarta. Ministan ya fara duba aikin tun daga Tungan Maje, Madalla, Zuma Resort, Sabon Wuse, Jere, Abuja Junction, Gwanin Gora, sannan ya ci gaba zuwa Zaria har zuwa Kano, inda aikin ke ci gaba yadda ya dace. Haka kuma,...
Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdelatty da takwaransa na Rasha Sergey Lavrov sun yi tattaunawa ta wayar tarho game da batun halin da ake ciki a yankin, inda suka mayar da hankali kan batun tsagaita wuta a Gaza da kuma yakin da ake yi a Sudan. A cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Masar ta fitar a ranar Asabar, Abdelatty ya yi nazari kan ci gaba da kokarin da Masar ke yi na karfafa yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da kuma tabbatar da aiwatar da tanade-tanaden da yarjejeniyar ta kunsa. Ya jaddada muhimmancin ci gaba da aiwatar da wannan yarjejeniya zuwa mataki na biyu na shirin tsagaita wuta, wanda zai magance matsalolin siyasa da ayyukan jin kai domin samun...
Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi November 8, 2025 Daga Birnin Sin Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne November 8, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin November 8, 2025
Kazalika, duk dai a jiya Jumma’ar, yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da taron, Chen Binhua, mai magana da yawun Ofishin Harkokin Taiwan na Majalisar Gudanarwar Kasar Sin ya ce taron wanda ya gudana shekaru goma da suka gabata ya karfafa muhimmiyar rawar da Yarjejeniyar 1992 ta taka a matsayin ginshikin siyasa ta bunkasa zaman lumana a dangantakar bangarori biyu na mashigin tekun, kana matukar an ci gaba da amincewa da Yarjejeniyar 1992 kuma aka nuna adawa da batun “‘yancin kai na Taiwan”, to dangantakar bangarorin biyu za ta iya bunkasa cikin lumana kuma za a iya kara inganta muradun ‘yan kasa da ke bangarorin biyu na mashigin tekun. (Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga...
Wasu ’yan bindiga da Bello Turji ke jagoranta sun kai hari ƙauyen Bargaja da ke Ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato da safiyar ranar Asabar. Rahotanni daga yankin sun bayyana cewa ’yan bindigar sun kashe mutum biyar, tare da jikkata wani ɗan sa-kai, sannan suka sace wasu mutum tara waɗanda mafi yawansu mata ne. Ban ɓata zargin Shettima da ƙirƙiro Boko Haram ba — Sheriff Uwargidan Gwamnan Gombe ta nemi a tsawaita hutun haihuwa na mata ma’aikata Kafin faruwar harin, wani mai ɗan gwagwarmaya a yankin mai suna Basharu Altine Guyawa, ya wallafa a kafafen sada zumunta inda ya yi gargaɗin cewa Bello Turji da tawagarsa suna shawagi a yankin Fadanar Tursa da Dorawar Madugu zuwa Dan Huntuwa ta gadar...
BBC Hausa ta yi nazari kan kasashen Afirka da dakarun Amurka suka shiga da sunan dakile wata matsala kamar annoba ko kuma yakar “‘yan ta’adda”. Somalia (1992–1994) Kasar Somalia ta kasance daya daga cikin wuraren da Amurka ta aika da sojojinta a wani mataki mafi girma a farkon shekarun 1990s. A lokacin da kasar ke cikin rikicin yakin basasa da yunwa mai tsanani, Amurka ta tura sojoji don tallafawa da jigilar kayan agaji da tabbatar da zaman lafiya. Wannan ya haifar da sanannen yakin Mogadishu da ake kira “Battle of Mogadishu” a 1993, wanda ya jawo hankalin duniya kan irin kalubalen da ke tattare da tsoma bakin soja a rikicin cikin gida. Amurka ta kaddamar da harehare na jiragen...
Rahotanni sun nuna cewa dan wasan Taekwando na kasar Iran mai suna Abulfazl zandi ya zamo shi ne na daya a duniya a bangaren maza a ma’aunin kilograme 58, bayan yayi nasarar samun lambar yabo ta zinariya a gasar taekwando ta duniya a kasar China, Hukumar kula da wasan taekwando ta duniya ta fitar da sunayen wadanda suka yi fice a duniya a watan nuwamba, inda ta sanya gasar teakwando ta duniya da aka yi a kasar china , yan wasan kasar Iran da dama maza da mata sun samu gagarumin ci gaba a jerin fannonii daban daban na wasanni. Zandi ya zo na daya a duniya da maki 170.80 kuma yana mataki na 4 a bangaren Olympic, A gefe...
Gasar cin kofin Afirka ta 2025 za a fafata tsakanin kasashe 24 da aka raba rukuni shida dauke da hurhudu kowanne. Da zarar an kammala fafatawar cikin rukunin, duk wadda ta yi ta daya da ta biyu za ta kai wasan zagaye na biyu wato na ‘yan 16 da kuma hudun da suka kare a mataki na uku a rukuni da maki mai yawa. Sai dai zagaye na biyu za a buga ne ziri daya kwalle, duk wadda aka doke sai dai ta tattara kayanta zuwa gida. Gabaki dayan gasar wasanni 52 za a buga, 36 a karawar cikin rukuni da takwas a zagaye na biyu da hudu a kwata fainal da biyu a zagayen daf da karshe da neman...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin November 8, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong November 8, 2025 Daga Birnin Sin Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE November 8, 2025
CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin
A bana ne ake cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da Sinawa suka yi da mamayar dakarun kasar Japan da yakin duniya na kin tafarkin murdiya, gami da kawo karshen mulkin mallakar kasar Japan a yankin Taiwan da dawo da shi kasar Sin. Kwanan nan ne CMG wato babban rukunin gidajen radiyo da talabijin na kasar Sin ya wallafa jerin wasu rahotannin talabijin guda biyar dangane da batun dawowar Taiwan kasar Sin. ’Yan jarida ma’aikatan CMG ne suka dauki rahotanni da bidiyo a yankin Taiwan, inda suka yi amfani da kwararan shaidun tarihi, don mayar da martani ga wasu kalaman karya da ke cewa wai “matsayin Taiwan ba shi da tabbas”, tare kuma da bankado markarkashiyar mahukuntan jam’iyyar DPP...
Uwargidan Gwamnan Jihar Gombe, Hajiya Asma’u Muhammadu Inuwa Yahaya, ta jagoranci wani yunƙuri na ganin an tsawaita hutun haihuwa na mata ma’aikata daga watanni uku zuwa shida. Ta jagoranci manyan jami’an lafiya zuwa majalisar dokokin jihar domin neman goyon bayan doka kan wannan shiri. Barau ya nemi Trump ya janye kalamansa, ya nemi afuwar Najeriya Matsalar Tsaro: Mun samu gagarumin ci gaba a shekaru biyu — Tinubu A yayin taron wayar da kai a majalisar, Hajiya Asma’u ta bayyana cewa shayar da jarirai nono har watanni shida yana da matuƙar amfani wajen rage mace-macen jarirai, inganta garkuwar jikinsu, da bunƙasa ƙwaƙwalwarsu. Uwargidan ta roƙi majalisar, ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Abubakar Mohammed Luggerewo, da su samar da doka da za ta...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025 November 7, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku November 7, 2025 Daga Birnin Sin An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka November 7, 2025
Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Rano, A Jihar Kano: Haduwa da kawayen banza da kuma kuntatawa da wasu malaman suke nuna musu, saboda kin amincewa da su na bukatun da suke nema a wajensu. Da yawa iyayen ba sa tsayawa su saurari matsalolin ‘ya’yansu kan abin da ke damunsu a makaranta, da kuma rashin bibiyar karatunsu da abokansu. Iyaye su tabbatar da suna bawa yara kudi da kayan abincin da zai ishesu idan a makarantun kwana suke, sannan su tabbatar da tarbiyyar malaman da za su kai yaran nasu. Sunana Aisha Isah Gama (Mai Waka), Jihar Kano: A gaskiya abin da ke janyo wa baya wuce gurba tattun abokai, har da lefin malamai saboda malami ne za ka ga ya kulla...
Barau Zai Yi Ƙarar Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gawuna/Garo Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi November 8, 2025 Manyan Labarai Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja November 8, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC November 8, 2025
Ya ƙara da cewax gwamnatinsa ta fara gyara daga tushe, inda ilimi ya zama ginshiƙin farko. “Shekaru takwas kafin mu hau mulki, ɗalibanmu ba su samun takardun WAEC, sannan tsawon shekaru biyu suna fama da matsalar NECO. Na biya Naira Biliyan huɗu don magance wannan matsala,” inji shi. Gwamnan ya bayyana irin matsalolin da ya gada, yana mai cewa: “Na samu asusun gwamnati da naira miliyan huɗu kacal. Ma’aikata suna karɓar albashi cikin rashin tabbas, babu ruwa, asibitoci kuwa suna cikin mummunan yanayi.” Lawal ya ce, ya sake fasalin tsarin gwamnati, inda ya rage yawan kwamishinoni da manyan sakatarorin don rage ɓarna da ƙara inganci. “Yanzu muna daga cikin jihohi mafi ci gaba wajen tara haraji, inda kuɗaɗen...
Kotun koli ta tarayyar Najeriya ta tsayar da ranar 20 ga watan nan na Nuwamba domin zama shari’ar shugaban kungiyar ‘yan awaren Biafara Nnamdi Kanu. Zaman shari’ar da za a yi zai mayar da hankali akan tuhumar ayyukan ta’addanci da ake zargin shugaban kungiyar ‘yan awaren Biafara din da aikatawa. An bai wa Kanu kwanaki shida a jere domin ya kare kansa akan zargin ta’addancin, sai dai bai iya yin hakan ba. A jiya Juma’a Kanu ya gabatar da nashi bayanin akan cewa; Ai daina daukar ta’addanci a matsayin laifi a Najeriya, domin an yi wata sabuwar dokar da ta maye gurbin tsohuwar da ake da ita akan hakan. Har ila yau Kanu ya ce babu wata madogara ta doka...
Bisa ga imanin da yake da shi ya bayyana cewa “Ba za ka iya samar da zaman lafiya da bama-bamai ba; sai dai ka gina shi da amana,” ya kaddamar da abin da yanzu ake kira ‘Samfurin Zaman Lafiya na Kaduna’. Tsarin Hadin Gwiwa:r Gwamnatin Kaduna Da ofishin ONSA A tsakiyar wannan sauyi akwai hadin gwiwa mai karfi a tsakanin Ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro (ONSA) da Gwamnatin Jihar Kaduna. Tare suka kafa kwamitin fasaha na hadin gwiwa wanda ya kunshi masu ruwa da tsaki, masana halayyar dan’Adam, da shugabannin kananan hukumomi, wannan tawaga ba ta zo da tankoki ko jiragen yaki ba, ta zo da tausayawa, tattaunawa da bayanai. A babban aikinsu na farko, ’yan...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: A bayyane yake cewa Amurka tana da hannu dumu-dumu wajen wuce gona da iri kan kasar Iran Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ismail Baqa’i ya mayar da martani ga amincewar da shugaban Amurka ya yi na daukar alhakin harin da sojojin Sahayoniyya suka kai wa Iran, yana mai cewa: “Tun daga farko a bayyane yake cewa Amurka tana da hannu a harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai wa al’ummar Iran.” Baqa’i ya rubuta a shafinsa na X-Platform: “Shin kuna tuna cewa Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya sanar a ranar 13 ga watan Yunin shekara ta 2025 cewa: Amurka ba ta da hannu a harin da ‘yan Sahayoniyya suka...
A cewar ‘yansanda, “A ranar 10/10/25, an gayyato wani Mista Oke Emmanuel, dan NYSC kuma abokin dakin wanda ya bace, domin yi masa tambayoyi. Ya tabbatar cewa wanda ake nema ya kasance tare da iyalan George har zuwa 06/10/25. “An samu karin bayani daga George cewa dan NYSC din ya koka da rashin lafiya, aka kai su Asibitin Kaiama Referral Hospital a ranar 04/10/25, kuma aka sallame shi ranar 05/10/25. Sai dai a ranar 06/10/25, dan NYSC din ya bace zuwa wani wurin da ba a sani ba.” ‘Yansanda kuma suna binciken zargin karbar kudin rashawa na Naira 100,000 daga iyayen wanda ya bace, da wasu fursunoni biyu da ke gidan gyaran hali na Igbara, Abeokuta, Jihar Ogun, wadanda suka...
Sanarwar ta ce, “A ranar 2 ga Oktoba, 2025, misalin karfe 08:25 na safe, wani mutumin kirki ya kai rahoton kisan gilla a ofishin D Dibisional Police Headkuarters. “Rahoton ya bayyana cewa wasu mutane biyu sun je gidan wani Ahmad Lawan, namiji, mai shekaru 29, wanda ake kira Soje, mazaunin Sabon Kasuwa, wanda ake zarginsa a matsayin shahararren dan sara-suka.” “Suka kwankwasa kofar gidansa, bayan da ya bude, sai suka soka masa wuka a kirji sannan suka tsere zuwa wani wuri da ba a sani ba.” Wakili ya bayyana cewa jami’an da ke karkashin D’ Dibision, karkashin jagorancin DPO CSP Mubarak Sani Baba, “sun hanzarta zuwa wurin da abin ya faru, suka dauki wanda abin ya shafa zuwa Asibitin Koyarwa...
Tun da farko, Daraktan DSS na Jihar Kaduna, Mr. Hakeem Abiola, an shirya taron ne domin nazarin ƙalubalen aiki da kuma karfafa haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro. Ya bayyana cewa hukumar DSS a ƙarƙashin jagorancin Mr. Oluwatosin Adeola Ajayi tana amfani da dabaru biyu – na ƙarfi da na sulhu – domin tabbatar da zaman lafiya. Ya ƙara da cewa ci gaba da tattaunawa da shugabannin addinai da na al’umma kamar JNI da CAN ya taimaka wajen shawo kan rikice-rikice kafin su zama tashin hankali. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah November 7, 2025 Manyan Labarai Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi...
Daga Usman Muhammad Zaria Gidauniyar Tunawa da Marigayi Sir Ahmadu Bello (ABMF) ta yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa sauƙin kai, tawali’u da jajircewarsa wajen ci gaban Jihar Jigawa. Shugaban Kwamitin Amintattu na Gidauniyar kuma tsohon Gwamnan Jihar Neja, Dr. Mu’azu Babangida Aliyu ne ya yi wannan yabon yayin da ya jagoranci tawaga zuwa gaisuwar ban girma a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse. Ya ce salon jagoranci na Gwamna Namadi na ɗauke da ƙima da marigayi Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, ya shahara da su, musamman tsari, girmama jama’a da shugabanci na gaskiya da rikon amana. Dr. Aliyu ya yi kira ga shugabannin Arewa su rungumi jagoranci da ke maida hankali kan al’umma, tare da fifita ilimi a...
Ya ci gaba da cewa, rungumar wannan tsari; zai kuma taimaka wajen yakar yunwa a kasar nan, inda ya yi nuni da cewa; ana aiwatar da wannan dabarar yakar sauyin yanayi ne ta hanyar yin amfani da dabarun noman gargajiya, wato yin amfani da takin gargajiya da sauyawa daga gonar da aka yi noma zuwa wata gonar daban. Sauran dabarun ya bayyana cewa, sun hada da yin shuka da ingantaccen Irin noma da kuma yin noman rani. Kazalika, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sanya wannan tsari ya zama na kasa baki-daya da za a rika yin amfani da shi. Shi ma a nasa jawabin a wajen taron, Shugaban Jami’ar Farfesa Suleiman Bala-Mohammed ya ce; kasidar da aka...
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya gana da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Juma’a. Sarkin Musulmi, wanda shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ya gana da Shugaban Ƙasa ba tare da ’yan jarida ba. Matsalar Tsaro: Mun samu gagarumin ci gaba a shekaru biyu — Tinubu Kamfanin wutar lantarki na Abuja ya salami ma’aikata 800 Ganawar na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Shugaba Tinubu ya gana da Archbishop Ignatius Kaigama na Katolikan Abuja, a wani yunƙuri na inganta dangantakar addinai da zaman lafiya a Najeriya. Ko da yake ba a bayyana abin da suka tattauna ba, amma ganawar ba za ta rasa nasaba da ƙarfafa...
An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka
A nata tsokacin kuwa, kwamishiniya mai lura da ababen more rayuwa da makamashi a hukumar zartarwar kungiyar AU Lerato Dorothy Mataboge, kara tabbatar da alaka ta yi tsakanin hadin gwiwar Sin da Afirka, da burin da ake da shi na bunkasa masana’antu a sassan nahiyar. Mataboge ta kara da cewa, yunkurin bunkasa samar da masana’antu a Afirka na bukatar karfafawa ta hanyar gina kwarewa, da horar da sana’o’i, da samar da cibiyoyi da albarkatun al’umma, don haka ta yi kira da a hada karfi-da-karfe wajen tsara shirye-shiryen bunkasa sanin makamar aiki a cikin gida, da samar da cibiyoyin horo masu nagarta, don horar da jama’a fasahohin amfani da makamashi marar gurbata yanayi. (Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA ...
Wanda ya jagoranci sallar juma’a a birni Tehran Hujjatul-Islami Wal Muslimin Muhammad Hassa Abu Turabi Fard, ya bayyana cewa; Tsayin dakar da kungiyar Hizbullah ta Lebabon da Ansurllah na kasar Yemn da kuma al’ummar Iran su ka yi wajen fada da masu girman kai na duniya, sakamako ne na koyarwar alkur’ani maigirma, Ahlul Bayt ( a.s) da kuma Ashura da jagorar matan duniya Fatima az-Zahra ( a.s). Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya ambato limamin na birnin Tehran yana kuma cewa; Makarantar gwgawarmaya tana yi wa zuriya bayan zuriya tarbiyya akan riko da gaskiya da kuma kalubalantar masu danniya. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name*...
Tarayyar turai ta bayyana cewa ma’aikatan Agaji ba za su iya isha cikin garin Al-fahar ba,kuma birnin ya zama tamkar makabarta. Tarayyar turai din ta bakin mai Magana da yawunta Eva Herneserova ta kuma ce; Sudan ta zama daya daga cikin kasashen da gudanar da ayyukan agaji ya tsananta a duniya,kuma har yanzu da akwai fararen hula da aka killace su adaidai lokacin da ake ci gaba da kai wa asibitoci hare-hare. Eva Herneserova ta kuma ce; Babu sauki ko kadan a kokarin shiga cikin birnin domin isar da kayan agaji. Ma Magana da yawun kungiyar tarayyar turai din ta kuma yi gagradi akan cewa bai kamata a rika amfani da yunwa da kuma kisan kiyashi a matsayin makamin yaki...
Wani yaro ɗan shekara biyu mai suna Danjuma Salman, ya rasu bayan ya faɗa cikin rijiya a Jihar Kano. Lamarin ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Gwale. Gwamnatin tarayya ki amince damu a matakin ƙasa – Bijilanti Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawa Rahotanni sun nuna cewa yaron ya zame ne sannan ya faɗa cikin rijiyar wadda murfinta ya lalace. Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 10:05 na safe daga wani mai suna Saminu Dayyabu, wanda ya sanar da su cewa wani yaro ya faɗa cikin rijiyar. “A lokacin da jami’anmu suka isa wajen, sun tarar...
Kwamandan Ƙungiyar sa kai ta Vigilante Group of Nigeria (VGN) reshen Jihar Kaduna, Abdulwahab Muhammed ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta amince da Ƙungiyar a matakin ƙasa ta hanyar sanya hannu a kan ƙudurin da aka gabatar. A cewar ƙungiyar bisa la’akari da irin rawar da take takawa wajen daƙile ayyukan miyagu da samar da tsaro a sassan ƙasar nan. An gano gawar wata mai shekara 96 a cikin masai Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawa Ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta sa hannu kan kudurin amincewa da kungiyar domin kasancewa cikin jerin hukumomin tsaro na kasa, la’akari da irin jajircewar da suke nunawa musamman a Jihar Kaduna. Abdulwahab...
3. A Hangen Nesansa wajen jagorancin al’umma, ya mayar da hankali kan masana’antu, sabunta ababen more rayuwa da kuma gina Dan’adam; domin mayar da Jihar Nasarawa matsayin wata babbar cibiyar zuba jari a Nijeriya da horar da aikin injiniya tare da kyautata jin dadin al’ummar jihar; an zabi Injiniya Abdullahi A. Sule a matsayin Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025. Injiniya Abdullahi Sule: Wanda Ya Fi Yin Fice Kan Harkokin Masana’antu A Duk Fadin Arewa 4. Shugabancinsa ya yi matukar kawo sauye-sauye a Jihar Ekiti, musamman ta hanyar gudanar da mulki na adalci, sabunta ayyukan more rayuwa, karfafa matasa da fadada aikin gona; sakamakon tawali’un da yake da shi da horon da ya samu wajen tafiyar harkokin kudi da gina jama’a tare...
Al’ummar Ƙauyen Sarai da ke Ƙaramar hukumar Dawakin Kudu a Jihar Kano sun shiga ruɗani a ranar Alhamis bayan da aka gano gawar wata mata mai shekara 96 a cikin masai. Jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya bayyanawa manema labarai a ranar Juma’a. Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawa Kamfanin wutar lantarki na Abuja ya salami ma’aikata 800 Abdullahi ya ce, sashin bayar da agajin gaggawa na hukumar ya samu kiran gaggawa daga wani mai suna Usman Adamu ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa wata tsohuwa ta faɗa cikin masai a ƙauyen Sarai. “Hukumar kashe gobara ta...
Wata kotu a Ƙasar Jamus ta yanke wa wani ma’aikacin jinya hukuncin ɗaurin rai da rai bayan ta same shi da laifin kashe marasa lafiya 10 da kuma yunƙurin kashe ƙarin wasu 27 ta hanyar yi musu allurar guba. Kotun da ke birnin Aachen a yammacin Jamus, ta tabbatar da cewa mutumin mai shekaru 44 ya aikata laifukan ne tsakanin watan Disamban 2023 zuwa Mayun 2024 a asibitin Wuerselen. Sama da gidaje 8,000 za su samu wutar lantarki daga hasken rana a Gombe Harin bam a masallacin Juma’a ya jikkata sama da mutum 50 a Indonesia Kotun ta bayyana cewa laifin da ya aikata babban laifi ne, wanda zai hana shi samun ’yanci bayan shekaru 15 kamar yadda ake yadda...
“A yayin da ake tarwatsa masu kai harin, DPO na Sassan A da B sun tura ma’aikatansu suka harba hayaki mai sa hawaye, amma wasu motoci cikin motar gwamnan sun lalace,” in ji Abiodun. Ya bayyana cewa mutane uku na farko da ake zargi sune Ali Mohammed da Adamu Hussain, dukkansu daga yankin Nasarafu, Bida, da Isah Umaru na yankin Darachita, Bida. Ya kara da cewa an kama Nagenu, mai shekaru 39, daga yankin Bello Masaba, daga baya dangane da wannan lamari, sannan ya ambaci wasu biyu, Salihu Mohammed da Abdulrahman Baba, yayin tambayoyi. “Dukkan wadanda ake zargi suna karkashin bincike kuma suna taimaka wa ‘yansanda wajen gano wasu. Ana ci gaba da kokarin kama karin mutane da ake zargi,”...
“Wannan mummunan hari ya yi sanadiyyar mutuwar jaruman jami’an tsaro da suka sadaukar da rayukansu wajen kare shi,” in ji sanarwar. Majalisar ta yi ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka mutu, da hukumomin tsaro, da al’ummar jihar Neja, tare da yi wa waɗanda suka ji rauni fatan samun sauƙin cikin gaggawa. A ƙarshe, Majalisar Wakilai ta sake tabbatar da jajircewarta wajen ganin an tabbatar da tsaron jama’a da jami’an gwamnati. Ta yi alƙawarin ci gaba da bai wa ɓangaren zartarwa da hukumomin tsaro goyon bayan doka wajen yaƙi da ta’addanci, da fashi da makami, da sauran nau’o’in laifuka da ke barazana ga zaman lafiyar ƙasar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa...
Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)
Annabi Ibrahim ne ya fara kafa massallaci ya fara tsaida sallah, wadannan salloli na Ikamu da muke yi Annabi Ibrahim ya fara, Annabi Ibrahim ya fara canza a yi layya dabba maimakon dan Adam, saboda darajar da dan Adam yake da ita wajen Allah. Ya kawo tsarin a bar layya da mutane a yi da dabbobi da abubuwa da yawa, sai dai wadannan malamai na wannan lokaci ba su yarda wani ya yi tunanin wani ilmi a waje ba, saboda suna tsoron kar ya yi wani tunani da ya fi nasu, don haka jama’a kar mu ji tsoron wani ilimi, babu wani ilimi da Annabi bai zo da shi ba, amma har yau wanda ba su san ilimin ba suna...
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya kaddamar da aikin samar da wutar lantarki ta hasken rana mai ƙarfin megawat 1 a garin Talasse, karamar hukumar Balanga. Aikin, wanda aka kulla ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara (REA), Bankin Duniya, da kamfanin MIDS Dynamics, na da aniyar samar da wutar lantarki ba tare da yankewa ba ga sama da gidaje 8,000 a Talasse da kauyuka makwabta, idan aka kammala shi cikin watanni huɗu. Harin bam a masallacin Juma’a ya jikkata sama da mutum 50 a Indonesia Kamfanin wutar lantarki na Abuja ya salami ma’aikata 800 A wajen bikin kaddamar da aikin, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana shi a matsayin muhimmin ci gaba a...
’Yan sanda a kasar Indonesia sun ce an garzaya da daruruwan mutane zuwa asibiti bayan wani abu da ake zargin bam ne ya fashe a wani masallacin Juma’a da ke Jakarta babban birnin kasar. Lamarin ya faru ne a lokacin sallar Juma’a a cikin wani ginin makaranta da ke Kelapa Gading, a arewaci Jakarta. Mun fara tattaunawa da Amurka kan barazanar Trump – Gwamnatin Tarayya Kamfanin wutar lantarki na Abuja ya salami ma’aikata 800 Kwamishinan ’yan sandan birnin, Asep Edi Suheri, ya ce har yanzu ana bincike don gano musabbabin fashewar. Shaidun gani da ido sun ce sun ji fashewa biyu masu ƙarfi da misalin ƙarfe 12 na rana a agogon kasar, daidai lokacin da aka fara hudubar sallar Juma’a...
Dangane da fargaba game da karancin abinci na amfanin gona da aka canza jinsinsu (GMOs), farfesan ya ce domin tabbatar da lafiyar abinci da kare lafiyar jama’a, dole ne kowace iri da za ta shigo kasar ta bi matakan doka da ka’idoji da ke tabbatar da cewa tana da aminci. Ya ce, dokokin da ake amfani da su wajen kula da GMOs ma sun fi tsauri fiye da na amfanin gona na gargajiya saboda an kara musu sinadaran halittu (genetic materials). “Kafin a saki kowane irin amfanin gona domin a fara amfani da shi a kasuwanci, dole ne ta bi diddigin binciken halittu da sinadaran gina jiki sosai. Bayanai da ake da su a halin yanzu sun nuna cewa amfanin...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kira da a kafa kwamitin kasa da kasa domin tantance makomar wadanda suka bata a Gaza Shugaban Kwamitin Binciken Mutane da Suka Bace a tawagar Babban Hafsan Rundunar Sojin Iran, Birgediya Janar Seyyed Mohammad Baqirzadeh, ya gabatar da shawarar kafa kwamitin kasa da kasa don neman fiye shahidai 10,000 da suka bace a yankin Gaza. Birgediya Janar Baqirzadeh ya bayyana hakan ne a lokacin wani taro na bangarori uku wanda ya hada da Iran, Iraki, da Kwamitin Kungiyar Red Cross ta Duniya (ICRC), da nufin tantance makomar shahidai da suka bace da kuma mayar da gawarwakinsu ga iyalansu. Ya jaddada muhimmancin rawar da Kungiyar Red Cross take takawa wajen bin wannan batu na jin...
Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’ar amincewa da dage takunkumin da ya sanya wa al-Julani Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’a a ranar Alhamis domin amincewa da daftarin kudirin da zai cire takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba wa Shugaban rikon kwaryar kasar Siriya Abu Muhammad al-Julani da Ministan Harkokin Cikin Gidan kasar Anas Khattab, inda kasashe 14 suka kaɗa ƙuri’a kan amincewar, yayin da kasar China ta kauracewa kada kuri’a. Daftarin kudurin, wanda Amurka ta rubuta kuma ta gabatar, ya yi kira da a dage takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba wa al-Julani da Khattab. A cewar jami’an diflomasiyyar Majalisar Dinkin Duniya, ofishin jakadancin Amurka ya rarraba daftarin kudurin ga mambobi, kuma an...
Sudan na fuskantar matsalar jin kai mafi girma a duniya a daidai lokacin da ake kara samun karuwar fada a Darfur da El Fasher Asusun Kula da kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya yi gargadin cewa: Matsalar karancin abinci mai gina jiki ta kara ta’azzara a Sudan, yana mai tabbatar da cewa matsalar karancin abinci mai gina jiki ta wuce matakin gaggawa a cikin sama da kashi 60 cikin 100 na yankunan. A halin yanzu, shugaban Majalisar Gudanar da Mulki a Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya jaddada kudurin rundunar sojin kasar na tabbatar da tsaron dukkan iyakokin Sudan da kuma murkushe ‘yan tawayen. Wani sabon gargadin Majalisar Dinkin Duniya ya sanya Sudan a kan gaba wajen fuskantar bala’in...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an November 6, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST November 6, 2025 Daga Birnin Sin Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya November 6, 2025
Yau 7 ga watan Nuwamba, Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya Paul Biya murnar yin tazarce a wani sabon wa’adin shugabancin kasar Kamaru. Shugaba Xi ya ce, kasar Sin da Kamaru suna da daddadiyar alaka mai kyau. A cikin ‘yan shekarun nan, amincewar siyasa tsakanin kasashen biyu ta kara zurfafawa, kuma an samu nasarori masu yawa a fannoni daban-daban na hadin gwiwa, tare da mara wa juna goyon baya a kan batutuwan da suka shafi muradunsu da kuma batutuwa masu muhimmanci. A shekara mai zuwa ce za a cika shekaru 55 da kulla alakar diflomasiyya tsakanin kasar Sin da Kamaru, matakin da ya samar musu da sabbin damammaki na ci gaban huldarsu. Xi yana dora muhimmanci sosai kan ci...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tattalin Arziki Ma’aikatan NPA Wasu Ginshikai Ne Na Ciyar Da NPA Gaba —Dantsoho November 7, 2025 Tattalin Arziki Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria October 25, 2025 Tattalin Arziki Gwarzon Kamfanin Samar Da Kaya Na Shekarar 2025, Kamfanin Nestlé Pure Life October 25, 2025
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump November 7, 2025 Manyan Labarai Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari November 7, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A FCT November 6, 2025
Shugaban ya kuma yaba bisa gudunmawar da kwararrun matasa ke samar wa, musamman masu yiwa kasa hidima da ke yin aikin yiwa kasa hidama, a Hukumar ta NPA. Ya danganta su a matsayin matasan gobe da za su samar da sauyi wajen ci gaba da bunkasa fannin tattalin azrki na Teku da kuma ga daukacin tattalin arzikin kasar nan. An kirkiro da wannan ranar ta NMD ce, a shekarar 2014 wadda kuma aka kaddamar da ita a kasar Ingila a shekarar 2016, wadda kuma ake gudnar da bikin zagoywar ranar, a duk ranar 27 na watan Okutobar kowacce shekara. Kazalika, gudanar da bkin wannan ranar, ta yi daidai da cimma muradun karni, na Majalisar Dinkin Duniya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA ...
A ranar Juma’ar da ta gabata ne, Trump ya sake mayar da Nijeriya matsayin kasa mai matukar damuwa, sannan ya yi gargadin cewa; “idan gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bayar da izinin kashe kiristoci, nan take Amurka za ta dakatar da duk wani taimako da take bai wa Nijeriya, sannan kuma mai yiwuwa ta shiga kasar, domin kakkabe ‘yan ta’addan Islama da ke aikata wadannan munanan ayyuka na ta’addanci.” Kazalika, ya kuma umarci Ma’aikatar Yakin Amurka, da ta shirya domin daukar mataki. Pete Hegseth, Sakataren Yakin Amurka, a ranar Asabar ya ce; Ma’aikatar Yaki na shirin daukar mataki. Barazanar Trump dai, ta biyo bayan zargin da wani dan majalisar dokokin Amurka, Ted Cruz, ya yi a shafinsa na D,...
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na shiyyar Abuja (AEDC) ya fara aikin rage ma’aikata kusan 800, a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke ci gaba da fama da hauhawar farashi, tsadar rayuwa, da rashin tabbas wajen samun wutar lantarki. Matakin korar wanda ta fara a ranar Laraba, ya biyo bayan watanni na sake fasalin cikin gida a kamfanin da ke ba da wutar lantarki ga Babban Birnin Tarayya Abuja da jihohin Kogi, Neja da Nasarawa. Mun fara tattaunawa da Amurka kan barazanar Trump – Gwamnatin Tarayya Majalisar Dokokin Amurka na neman a hukunta ’yan kungiyar Miyetti-Allah Majiyoyi da dama da ke da masaniya kan lamarin sun shaida cewa shugabannin kamfanin sun fara ne da shirin korar ma’aikata 1,800, kafin su rage...
Sai dai, bisa batun gasakiya, karya ce tsagwaronta kan batun kisan kiyashin da ake yamadidin cewa, ana yiwa Kiristoci kisan gilla a Nijeriya. Bugu da kari, wannan batun ana wani yunkuri ne na son kawo rudadi a kasar nna, musamman duba da cewa, masu son kawo rudadin, a zahiri, sun jahilci irin yanayin sarkakiyar lamarin tsaro na kasar nan. Wannan Jaridar, ta sha yin tsokaci, kan kalubalen rashin tsaro da ke addabar kasar nan, tare da kuma yawan gabatar da kira ga Gwamnatin kasar da ta tashi tsaye, domin daukar matakan da suka dace, na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya. Batun aikata ta’addanci, yin garkuwa da mutane da kuma aukuwar rikici a tsakanin manoma da makiyaya, matsaloli ne, da...
An rantsar da Paul Biya mai shekaru 93 a matsayin shugaban kasar Kamaru karo na takwas a majalisar dokokin kasar da ke Yaoundé. Ya shafe shekaru 43 yana mulki, kuma yanzu zai fara wani wa’adi na tsawon shekara bakwai. Biya wanda shine shugaban kasa mafi tsufa a duniya, ya sami kashi 54 na kuri’un zabe, yayin da abokin hammayarsa, Issa Tchiroma Bakary ya samu kashi 35%, a cewar sakamakon zaɓen hukumar kasa. Tchiroma Bakary dai ya yi iƙirarin cin nasara a zaben, yana zargin cewa an yi maguɗi,wanda hukumomi suka musanta. Lamarin dai ya janyo zanga-zanga a sassa daban-daban na kasar inda aka yi asarar rayuka da dukiyoyi. Shugaban Kamaru Paul Biya ya yi alkawarin dawo da doka a kasar...
Shugaban kasar Iran Mas’ud pezeshkiyan yace rarrabuwa da sabanin tsakanin musulmi shi ne babban abin da makiya musulunci suke so, kuma yayi gargadin cewa rabe-rabe na cikin gida yana kare manufofin makiya ne da kasashe ma’abota girman kai na duniya. shugaban ya fadawa manya- manyan malaman Ahalus sunna da sauran malaman addini dake Sanandaj a yammacin lardin Kurdistan cewa ta hanyar hadin kai da rikon amana da kuma riko da yan uwantaka na musulunci ne kawai musulmin duniya za su iya tunkarar makircin Amurka da Israila da ma sauran yan sahayuniya. Har ila yau ya kara da cewa wannan rarrabar ce isra’ila da Amurka da sauran yan sahyuniya na duniya suke so, domin su shagaltar da kasashen musulmi su yi...
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na tattaunawa da sauran ƙasashen duniya “ta hanyar difilomasiyya” game da matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta a yanzu. Kalaman shugaban na zuwa ne bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ke barazanar kutsawa Najeriyar domin kai wa ‘yan bindiga hare-hare bayan ya zargin gwamnatin Tinubu da ƙyale su suna “yi wa Kiristoci kisan gilla” Da yake magana yayin zaman majalisar ministocinsa a jiya Alhamis, Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta kawo karshen”ta’addanci”. “Duk da kalubalen irin na siyasa da fargabar da mutanenmu ke ciki, muna ci gaba da tattaunawa da kawayenmu, muna tattaunawa a difilomasiyyance,” “Ina tabbatar muku cewa za mu kawo karshen ta’addanci. Abin da muka saka a...
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya ce Gwamnatin Tarayya ta buɗe kofofin tattaunawa da ƙasashen duniya, ciki har da Amurka, dangane da barazanar kasar ta kaddamar da yaki a Najeriya. Yayin da yake jawabi ga manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa bayan taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta, Ministan ya ce gwamnatinsu ba ta son ƙara yin yamadidi da maganar. An rantsar da shugaban Kamaru Paul Biya karo na 8 Kwalara ta kashe mutum 10 a Ƙaramar Hukumar Adamawa “Babban nauyin da ke kanmu a matsayin gwamnati shi ne tabbatar da cewa gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da ɗaukar mataki a kan duk wata damuwa ta gaskiya da ke da alaƙa da tsaron ’yan...
An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST November 6, 2025 Daga Birnin Sin Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya November 6, 2025 Daga Birnin Sin Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji November 6, 2025
Kungiyar Genoa ta naɗa tsohon ɗan wasan tsakiyar Italiya, Daniele De Rossi, a matsayin sabon kociyarta, domin maye gurbin Patrick Vieira wanda ya bar ƙungiyar a ƙarshen mako. A wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, Genoa ta bayyana cewa tana “maraba da Daniele De Rossi” wanda ya jagoranci atisaye na farko da yammacin wannan ranar. Za a gudanar da taron manema labarai na farko da shi a ranar Juma’a.” Victor Osimhen ne kan gaba a yawan zura ƙwallaye a Champions League Ajax ta kori kocinta John Heitinga De Rossi, wanda ya taka leda na tsawon shekaru 17 a Roma kuma ya lashe Kofin Duniya tare da Italiya a 2006, ya taɓa horas da ƙungiyoyin Spal da Roma. Roma...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya November 6, 2025 Labarai Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu November 6, 2025 Ra'ayi Riga Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari November 6, 2025
Ɗan wasan gaba na Nijeriya, Victor Osimhen, ya sha gaban fitattun ‘yan wasa irin su Erling Haaland, Harry Kane, da Kylian Mbappé a yawan zura ƙwallaye a gasar Champions League ta bana. Osimhen ya cimma wannan nasarar ce bayan ya zura ƙwallaye uku rigis a ragar Ajax a wasan zagaye na huɗu na gasar. Ajax ta kori kocinta John Heitinga Cin zarafin Wakilin NTA ya tada ƙura a Yobe Wannan ya kai adadin ƙwallayensa zuwa shida, yayin da Haaland, Kane da Mbappé ke da ƙwallaye biyar-biyar kowannensu. A watan da ya gabata, Osimhen ya kuma zura ƙwallaye uku a ragar Jamhuriyyar Benin a wasan neman tikitin shiga gasar Kofin Duniya ta 2026, abin da ya ƙara masa farin jini a...
A yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada bukatar gina ingantaccen yankin ciniki cikin ’yanci na tashar ruwa ta Hainan ko FTP a takaice. Shugaba Xi ya bayyana bukatar ne yayin dake sauraron rahoton aiki game gina yankin na FTP a birnin Sanya na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin. A cewarsa, gina yankin FTP na Hainan muhimmiyar manufa ce ta kwamitin kolin JKS, wadda aka tsara domin zurfafa cikakkun sauye-sauye, da bude kofa ga waje a sabon zamani. Shugaban na Sin ya kara jaddada bukatar kyautata nazari, da aiwatar da ka’idojin aiki na cikakken zama karo na hudu na kwamitin kolin JKS na 20, tare da kokarin cimma burikan da aka sanya gaba, dangane da bunkasa yankin...
Wannan matakin ya zo ne a daidai lokacin da Amurka ke ci gaba da nuna damuwa kan abin da ta bayyana a matsayin cin zarafin Kiristoci da sauran tsirarun addinai a Nijeriya. Dan majalisa Smith ya yaba wa shugaban Amurka Donald Trump kan ayyana Nijeriya a matsayin ‘Kasar da ke da damuwa ta musamman’ (CPC), inda ya ambato cewa, akwai rahotanni da ke cewa, ana kai wa Kiristoci hare-hare a sassan jihohin Benuwe da Filato. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama November 6, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro November 6, 2025 Manyan...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Harin Amurka ya bayyana karara kan Venezuela Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa: Barazanar da ake yi wa Venezuela ba ta dace da al’ummar duniya ba, yana mai jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kasance kuma za ta ci gaba da kasancewa cikin hadin kai da gwamnati da al’ummar Caracas. Da yake jawabi a bikin rantsar da ofishin wakilin Ma’aikatar Harkokin Waje a Lardin Hamadan, Araqchi ya bayyana cewa: Wannan ofishin zai taimaka wajen karfafa alakar tattalin arziki, kimiyya, da al’adu ta lardin, da kuma sauƙaƙe hulɗar jakadanci da gudanarwa ga ‘yan ƙasar. Ya lura cewa: Baba’i Ragheb, wani jami’in ma’aikatar da ya ƙware, zai jagoranci sabon...
Shugaban Majalisar Dokokin kasar Iran ya jaddada muhimmancin aiwatar da kuma kammala yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin Iran da Pakistan Shugaban Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Baqir Qalibaf, ya jaddada muhimmancin matakin da ake dauka a yanzu na dangantakar da ke tsakanin Iran da Pakistan a dukkan fannoni na hadin gwiwa. Ya bayyana ziyararsa zuwa Pakistan a matsayin wani bangare na kokarin da ake yi na fadada dangantaka, musamman hadin gwiwar yankin tsakanin kasashen biyu. A cikin wata sanarwa da ya aike wa kamfanin dillacin labaran Iran ‘IRNA’ bayan ya isa birnin Islamabad, fadar mulkin kasar Pakistan, a safiyar Laraba, Qalibaf ya ce: “Iran da Pakistan, a matsayin kasashe makwabta, suna jin dadin hulda daban-daban a fannin tattalin arziki, siyasa, da...
Kwamitin Tsaro Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Amurka ta bukaci duba kudurin da aka gabatar na neman kafa rundunar kasa da kasa a Gaza Rahotannin daga Amurka sun bayyana cewa: Gwamnatin Amurka ta Trump tana neman amfani da rikicin Gaza wajen kwace makaman kungiyar Hamas da take amfani da ramuka wajen yakar ‘yan sahayoniyya, don aiwatar da wani tsari na kwace makamai daga hannun ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa. A ƙarƙashin tutar tsaro da kwanciyar hankali, Amurka, da kuma Isra’ila, suna ƙoƙarin kafa sabon tsari a Gaza wadda ke neman murkushe ‘yan gwagwarmaya, tare da tabbatar da tsarin babakeren ‘yan mamaya karkashin wani tsari mai sauƙi, da zai buɗe sabon babi na iko a kan yankin. A tsakiyar tambayoyi game da...
Muhimmin fadakarwa daga Sayyid Muqtada al-Sadr kwanaki kafin zaɓen kasar Iraki Malamin Tafarkin Shi’a na Iraki Muqtada al-Sadr ya umurci magoya bayansa a ranar Alhamis da su dakatar da duk wani zaman dirshan da zanga-zanga har zuwa lokacin zaben ‘yan majalisa dokokin kasar mai zuwa. A cikin wata sanarwa, ofishin al-Sadr ya ce ya yi nazari kan ayyukan da suka hada da tarurrukan kabilanci da na matasa da ke goyon bayan shawararsa ta kauracewa zaben kuma ya yi tsokaci, “Daga yanzu har zuwa ranar zabe, babu bukatar wani karin zanga-zanga.” Wannan shawarar ta ci gaba da tsarin al-Sadr na nisantar da kansa daga tsarin zaben tun bayan sanarwarsa a watan Yunin shekara ta 2022 na janye kansa gaba daya daga...
An rantsar da Paul Biya a matsayin shugaban ƙasar Kamaru karo na takwas mai shekaru 93 a majalisar dokokin ƙasar da ke Yaoundé. Paul Biya ya shafe shekaru 43 yana mulkin ƙasar, kuma yanzu zai fara wani wa’adi na tsawon shekara bakwai nan gaba. Ƙungiyyar Ƙwallon yashi ta Kada BSC ta fatattaki Kebbi BSC Kwalara ta kashe mutum 10 a Ƙaramar Hukumar Adamawa Biya wanda shine shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya, ya sami kashi 54 na ƙuri’un zaɓe, yayin da abokin takararsa, Issa Tchiroma Bakary ya samu kashi 35%, a cewar sakamakon zaɓen hukumar ƙasa. Tchiroma Bakary dai ya yi iƙirarin cin nasara a zaɓen da aka yi yana kuma zargin cewa an yi maguɗin zabe, wanda hukumomi suka...
Kwamishinan lafiya na Jihar Adamawa, Dokta Felix Tangwami ya bayyana cewa, cutar kwalara a Ƙaramar hukumar Mubi ta yi sanadin mutuwar mutane 10, inda ya buƙaci mazauna yankin da su kula da tsaftar jikinsu. Da yake yi wa Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) bayani a Yola ranar Laraba, Tangwami ya ce marasa lafiyan sun mutu ne a gida maimakon a cibiyoyin lafiya. Majalisar Dokokin Amurka na neman a hukunta ’yan kungiyar Miyetti-Allah An kashe babban limami a Kwara saboda zargin maita Ya ƙara da cewa, gwamnatin jihar tare da haɗin gwiwar hukumar lafiya ta duniya (WHO) sun ɗauki matakin gaggawa don daƙile ɓarkewar cutar. “Tun daga farko, mun ɗauki matakin gaggawa a kan lamarin, kasancewar mu a can, kuma ba...
Wasu fusatattun matasa a ƙauyen Sokupkpan da ke karamar hukumar Edu a jihar Kwara, sun kashe Babban Limamin yankin, Mallam Abdullahi Audu, bisa zargin shi da alhaki kan mutuwar wani matashi, Ibrahim Gana ta hanyar maita. Shaidu sun ce lamarin da ya faru a ranar Laraba ya jefa al’ummar yankin cikin rudani da firgici. Gwamnatin Tarayya ta fara shirin sayar da matatun manta ga ’yan kasuwa Za a gudanar da wasannin ƙwallon yashi a Abuja An ce wannan farmakin ya samo asali ne daga zargin cewa limamin ya yi amfani da maita wajen cutar da mamacin. A cewar majiyoyi, kafin rasuwarsa, Gana ya dade yana fama da wata cuta da ba a bayyana ba, kuma ya sha faɗa cewa Babban...
Dakarun Sojin Amurka sun kammala shirye-shiryen kai hare-hare a Najeriya bayan umarnin da Shugaba Donald Trump, ya bai wa Ma’aikatar Tsaron ƙasar kan ɗaukar mataki game da zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Jaridar The New York Times ta ruwaito cewa rundunar sojin Amurka da ke nahiyar Afirka (AFRICOM), ta gabatar da yadda hare-haren za su kasance. An kama mutum 2 kan sukar shugaban karamar hukuma a Kano Gwamnatin Tarayya ta fara shirin sayar da matatun manta ga ’yan kasuwa Daga cikin shirin akwai kai wa ’yan ta’adda hare-hare da jiragen yaƙi da amfani da jirage marasa matuƙa. Sannan kuma akwai tsarin haɗin gwiwa da sojojin Najeriya ta hanyar musayar bayanan leƙen asiri da tallafin kayan aiki. Sai dai...
Ministan Harkokin Wajen Iran ya yaba da juriyar da kasar ta nuna yayin hare-haren Amurka da Isra’ila, wanda ya tilasta musu rokon a tsagaita wuta ba tare da shiri ba. Da yake jawabi a yammacin ranar Laraba a taron Majalisar Gudanarwa ta Lardin Hamadan, Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa abokan gaba sun gaza a dukkan manufofinsu a lokacin yakin na kwanaki 12. Kalaffafen yakin na kwanaki 12 ya bamu babban darasi inji shi, saboda mun fi karfi da a ranar 13 ga watan Yuni. A karon farko, an yi amfani da makamai masu linzami na Iran a wani rikici na gaske, wanda hakan ya ba da damar gano ƙarfi da rauninsu. A yau, Iran tana...
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi gargadin cewa Moscow za ta dauki “matakan mayar da martani” idan Amurka ta koma gwada makaman nukiliya, a yayin da ake kara samun takun saka tsakanin manyan kasashen biyu masu makamman nukiliya. A yayin wani taro da ya yi da Majalisar Tsaron Rasha a ranar Laraba, Putin ya umarci Ma’aikatar Harkokin Waje, Ma’aikatar Tsaro, hukumomin leken asiri, da su tantance yiwuwar sake fara gwaje-gwajen makamman nukiliya da kuma gabatar da shawarwari don matakan farko. “Dangane da wannan batu, ina umurtar ma’aikatun dasu gabatar da shawarwari kan matakan farko da za su iya mayar da hankali kan shirye-shiryen gwaje-gwajen makaman nukiliya,” in ji Putin. Umarnin da ya bayar ya nuna martani ne ga umarnin da...
Kasahen Iran, Rasha da kuma China sun gana a tsakaninsu a jajibirin taron Kwamitin Gwamnonin Hukumar kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA), Zaman ya hada jakadun kasashen uku a birini Vienna ranar Laraba don daidaita matsayinsu kan manyan batutuwan da suka shafi zaman na gwamnonin IAEA da ke tafe. Michael Ulyanov, jakadan Rasha kuma wakilin dindindin a kungiyoyin kasa da kasa a Vienna, ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa kasashen uku sun yi “wani zagaye na shawarwari ” game da batun nukiliyar Iran. Ya kara da cewa wakilan sun daidaita matsayinsu don su shirya sosai don taron Kwamitin Gwamnonin da ke tafe. A cewar shirin da aka sanar, za a gudanar da zaman kwamitin na gaba daga ranar...
Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da matakin da Gwamnatin Amurka ta dauka na sanya sunan Najeriya cikin jerin “Kasashen Da Ake Tauye ’Yancin Addini” , wato jerin kasashen da ake zargi da take hakkin addini. Ministan Yada Labarai da Al’adu, Mohammed Idris Malagi ne, ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja, inda ya ce matsalar tsaro da ake fuskanta a Najeriya ba ta shafi wani rukuni na addini ko kabila kai-tsaye ba. Gwamnatin Tarayya ta fara shirin sayar da matatun manta ga ’yan kasuwa Hafsan sojin sama ya umarci a yawaita yi wa ’yan ta’adda ruwan bama-bamai Ya ce masu yada bayanan karya ne suka sa ake ganin kamar Najeriya tana nuna bambanci ta fuskar addini. Malagi, ya ce...
Gwamnatin Najeriya ta jaddada matsayinta na yin watsi da ayyata a matsayin kasa mai take hakkokin addinai da Amurka ta yi. Da yake kare tarihin Najeriya, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Ƙasa na Najeriya, Mohammed Idris, ya ce “barazanar Trump na ɗaukar matakin soja ba ta da tushe kuma hakan yana a matsayin kawar da ido ne daga ƙalubalen tsaro masu sarkakiya da Najeriya ke fuskanta,” ya ƙara da cewa “duk wani labari da ke nuna cewa Najeriya ta gaza ɗaukar mataki kan hare-haren da ake kai wa mabiya addini ya dogara ne akan bayanan ƙarya ko maganganu marasa tushe.” A ranar Litinin, Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Olufemi Oluwedi, ya bayyana cewa “Najeriya tana fuskantar ta’addanci, ba kai...
Hafsan Sojin Sama na Najeriya, Air Marshal Sunday Aneke, ya umarci dukkanin kwamandojin rundunar da su ƙara ƙaimi wajen yi wa ’yan ta’adda ɓarin wuta ta sama A yayin wani taron da suka gudanar da Abuja a ranar Laraba, Aneke, ya umarci kwamandojin da su kai hare-hare masu yawa domin kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa. Za a gudanar da wasannin ƙwallon yashi a Abuja An amince da hukuncin yi wa malamai ɗaurin shekara 14 kan lalata da ɗalibai Ya ce, “Dole ne yayin kowane aiki a nuna ƙwarewa da ƙaunar ƙasa.” Mai magana da yawun rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce taron ya mayar da hankali kan duba dabarun aiki da kuma ƙarfafa haɗin kai a tsakanin kwamandoji....
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar basir na daga cikin cututtukan da mutane da dama ke da mabanbantan ra’ayoyi akan ta. A lokuta da dama za ka ji yadda mutane ke fadin dalilai daban daban da ke janyo cutar basir, yayin da wasu ke ganin yawan zama ne ke kawo ta, wasu kuwa gani suke yi zaki da maiko ne ke kawo ta. Wannan shine abun da da yawa daga cikin mutane suka sani kan wannan cuta, sai dai masana kiwon lafiya na da nasu fahimtar daban kan wannan cuta. NAJERIYA A YAU: Rashin aikin yi da hanyoyin magance su a Najeriya DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar Makamai Shirin Najeriya A...
“Wannan babban shiri ne da zai sake fasalin Zamfara, ya tabbatar da ci gaba mai ɗorewa tare da inganta rayuwar al’umma,” inji shi. Ya ƙara da cewa, a mafi yawan ƙananan hukumomin jihar ana gina sabbin hanyoyi na kilomita biyar a cikin birane, baya ga Gusau wadda ake gudanar da manyan ayyuka na musamman. Ya ce hakan zai rage cunkoso, ya haɗa al’umma, ya kuma farfaɗo da kasuwancin ƙauye da birane. A fannin lafiya, gwamnati ta ƙaddamar da gina sabon babban asibiti a Nasarawa Burkullu a ƙaramar hukumar Bukkuyum, tare da sabunta cibiyoyin kiwon lafiya da dama a yankunan karkara, domin sauƙaƙa samun ingantaccen magani. An kuma sanar da ci gaba da gyaran makarantu a dukkan...
Hukumar shirya gasar ƙwallon yashi ta ƙasa ta tabbatar da cewa za a gudanar da wasannin ƙarshe na bana a filin wasa na Jabi Lake Park, da ke babban birnin tarayya Abuja. Kodinetan hukumar a Najeriya, kuma shugaban hukumar a nahiyar Afirka, Mahmud Hadejia, ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake zantawa da Trust Radio a cikin shirin “Bakin Raga” da safiyar yau Laraba. An amince da hukuncin yi wa malamai ɗaurin shekara 14 kan lalata da ɗalibai Yara biyu sun mutu bayan faɗawa rijiya a Kano Shugaban ya bayyana cewa wannan ce gasa ta biyar da za a buga, kuma ta farko da za a fafata a Abuja. A cewarsa, za a fara buga wasannin ƙarshe daga...