2025-09-24@17:32:31 GMT
إجمالي نتائج البحث: 9307
«cutar HIV a»:
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yaba da buɗe ofishin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a Majalisar Dattawa, inda ya ce haɗin kai ya yi nasara a kan zalunci. A ranar Talata ne Majalisar ta buɗe ofishinta, bayan rufe shi da aka yi tun daga 6 ga watan Maris, 2025, lokacin da aka dakatar da ita na tsawon watanni shida saboda zargin karya ƙa’idojin majalisar. Darajar Naira ta ƙaru bayan CBN ya rage kuɗin ruwa Mawaki Davido ya ba matarsa kyautar motar miliyan 240 Ko da yake Kotun Tarayya ta yanke hukunci a ranar 4 ga watan Yuli cewa dakatarwar “ta yi tsauri kuma an yi ta ba bisa ƙa’ida ba.” Da yake mayar da martani, Atiku ya ce sake buɗe...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi Allah wadai da hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai a watan Yuni a kan kasar. A lokacin da yake jawabi a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 80 ya shaidawa mahalarta taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York a yau Larabar cewa, hare-haren wani babban rauni ne ga zaman lafiya a yankin. Shugaban ya ce hare-haren, wadanda suka afkawa garuruwa, gidaje, da ababen more rayuwa na Iran, yayin da ake ci gaba da tattaunawar diflomasiyya, “babban cin amanar diflomasiyya da raunana kokarin da ake yi na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ne.” Pezeshkian ya zargi Washington da Tel Aviv da ruguza tattaunawar da gangan da karfin soji. Shugaban na...
Jiya Talata 23 ga wata ne firaministan kasar Sin Li Qiang, ya halarci babban taro kan shawarar samar da ci gaba ga duniya baki daya, tare da gabatar da jawabi a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya dake birnin New York na kasar Amurka. A gun taron da kasar Sin ta dauki nauyin shiryawa, firaminista Li ya ce, shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarar raya duniya baki daya a wajen babban taron MDD a shekara ta 2021, shawarar da ta mayar da hankali kan muradun daukacin bil’adama. Li ya kuma jaddada cewa, Sin za ta kara zama kasar dake nuna goyon-baya, da taimakawa samar da ci gaba na bai daya, da ci gaba da daukar matakan zahiri, da kara daukar nauyin...
“Bayan tattaunawa mai yawa, aka samu damar tara ₦100,000, wanda ya biya a cikin asusun da masu garkuwa da mutanen suka bayar, bayan wata ɗaya, sai aka bukaci ya biya wani Abdulmajid Dan-Azumi karin ₦10,000, ba tare da sun saki yaron ba,” Abiodun ya bayyana. Waliyyin da ya fahimci lamarin ba mai ƙarewa ba ne, sai ya kai rahoto ga ‘yansanda a watan Satumba, inda nan take aka mayar da karar zuwa sashin yaki da garkuwa da mutane na SCID. ‘Yansandan sun bi sawun Abdulmajid Dan-Azumi mai shekaru 32 dan garin Kwana, wanda, daga nan aka yi nasarar kama abokin hulɗarsa, Abdulnafiu Usman wanda suke zaune duk a unguwa ɗaya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
Darajar Naira ta ɗan ƙaru a kasuwanni, bayan Babban Bankin Najeriya (CBN), ya sanar da rage kuɗin ruwa daga kashi 27.5 zuwa kashi 27. Wannan mataki, a cewar masana tattalin arziƙi, na nufin gwamnati na ƙoƙarin rage matsin tattalin arziƙi da farashin kayayyaki ga ’yan ƙasa. ’Yan bindiga sun kashe mai juna biyu, sun sace mutum 8 a Kwara Mawaki Davido ya ba matarsa kyautar motar miliyan 240 A ranar Talata, an sayar da dala ɗaya kan Naira 1,487.36 a hukumance, inda hakan ya nuna samun sauyi idan aka kwatanta da Naira 1,488.60 da aka sayar da ita a baya. Hakazalika, farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ya tashi zuwa dala 67.82 a kan kowace ganga ɗaya, abin da ya...

An Fara Nuna Hotuna Da Shirye-Shiryen Bidiyo Da Matasan Kasa Da Kasa Suka Dauka Don Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafa MDD A Kasar Sin
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
’Yan bindiga sun kai hari wasu ƙauyuka na Patigi a Jihar Kwara, inda suka kashe wata mata mai juna biyu tare da wasu mutane. Haka kuma sun yi garkuwa da mutane takwas tare da jikkata da dama. Mawaki Davido ya ba matarsa kyautar motar miliyan 240 Tarihi da rayuwar Sheikh Abdulaziz Al-Sheikh (1943-2025) Shaidu sun ce maharan sun shiga ƙauyukan ne a babura, inda suka dinga harbi ba ƙaƙƙautawa wanda ya sa mazauna ƙauyukan suka gudu. Ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Motokun, Egboro da Fanagun. Wani mai suna James Ibrahim, ya ce: “Mun farka da safe muka ga mutane suna gudu daga Motokun bayan harin. An harbi wata mace wadda daga bisani ta rasu a asibitin Patigi....
Fitaccen mawakin nan na kudancin Najeriya David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya ba matarsa Chioma kyautar sabuwar motar alfarma kirar Mercedes-Benz G-Wagon ta shekarar 2025. Wannan motar mai tsada, wadda aka kaddamar da ita kwanan nan a kasuwar duniya, tana da farashin sama da $150,000 (kimanin Naira miliyan 240). Yada labaran karya a intanet babban laifi ne a Musulunci – Sheikh Ibrahim Khalil UNGA: Yau Shettima zai gabatar da jawabin Najeriya a MDD Sabuwar motar ta 2025 na dauke da sabon fasali mai ban sha’awa da kuma Zubin da ya sa ta fi tsofaffin nau’ikan da suka gabace ta inganci. A wani bidiyo da Davido ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Laraba, an ga lokacin...
A lokacin hatsarin karfen sauya hanyar ya karye gaba daya, wanda ya haifar da hatsarin. Hukumar ta kuma gano cewa duk da cewa direbobin jirgin ƙwararru ne, ba a ba su sabon horo ba. An kuma gano cewa wasu muhimman kayan aiki kamar na’urar CCTV, na’urar sadarwa da agogo sun samu matsala. NSIB ta shawarci NRC da ta gyara dukkanin kayan da suka lalace, ta sanya sabbin karafan sauya hanya, sannan ta riƙa horar da ma’aikata akai-akai don gujewa irin wannan matsala. A lokacin hatsarin, mutane 21 ne suka ji rauni daga cikin fasinjoji 618 da ke cikin jirgin, amma babu wanda ya rasu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
Kafar watsa laabrun Politico ta fitar da wani rahoto a jiya Talata wanda yake cewa, hukumar bincike ta ‘yan sandan Amurka ta sami bayanan sirri da su ka shafi muhimman matakan siyasa na gwamnatin Amurka da kuma masu alaka da makaman kare dangi. Majiyar ta ambaci cewa binciken da aka yi a ranar 22 ga watan Ogusta da ya shude ya sami bayanan da aka bayyana a matsayin “Na sirri’ matuka”. Kafar watsa labarun ta ” Politico” ta kuma ce bayan binciken ofishin bolton da a ka yi, da aka sami na’urar kwamfuta mai cike da bayanan sirri, an kuma kai wani samamen a gidansa dake Jahar Maryland, said ai kuma babu wani bayanai akan nau’oin abubuwan da aka samu...
Babban magatakardar malajisar koli ta tsaron kasar Iran Dr. Ali Larijani ya bayyana cewa; Batun sake kakabawa Iran takunkumi yana nuni da gajiyawar kasashen turai. Dr. Ali Larijani wanda tashar talabijin din al’mayadin’ta yi hira da shi, ya kara da cewa, matakin da kasashe uku na Faransa, Birtaniya da Jamus, su ka dauka akan batun sake kakabawa Iran takunkumi, yana sake yin nuni ne da tsohuwar gabar da kasashen turai da Amurka suke da ita akan al’ummar Iran. Haka nan kuma ya ce wannan tsohuwar gaba ta yi tasiri mai girma a cikin siyasar mulkin mallaka ta kasashen turai da yadda suke son Dannen sauran kasashe. Dr. Ali Larijani ya kuma ce, wanann irin kiyayya da siyasa tana cin karo...
HKI tana ci gaba da kai wa muhimman cibiyoyi da gidajen Falasdinawa a fadin Gaza. Majiyar Falasdinawa ta ce daga safiyar yau Laraba adadin wadanda su ka yi shahadar sun kai 45 sanadiyyar hare-haren da jiragen yakin ‘yan sahayoniyar su ka kai. Har ila yau an sami wasu Karin shahidan biyar a wuraren karbar agaji dake arewacin Rafaha. A wani labarin mai alaka da hakan shugaban hukumar lafiya ta duniya ( w.h.o) Tedross Adhanom ya ce; Kai hare-haren da ake yi a kusa da asibitin Rantisy, dake Gaza, ya yi sanadiyyar tsayuwar aikin Asibiti, domin rashin tsaro. Har ila yau ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta kara da cewa; Jinkirin shigar da makamashi zuwa yankin yana barazanar tsayar da aikin...
A ranar Talata, 1 ga Rabi’ul Thani 1447H, daidai da 23 ga Satumba 2025, Allah Ya yi wa Babban Mai Bayar da Fatawa na kasar Saudiyya, Sheikh Abdul Aziz Al-Sheikh, rasuwa. An yi jana’izarsa a Masallacin Imam Turki bin Abdullah da ke birnin Riyadh a ranar Talata bayan sallar La’asar, wanda Yarima Mai Jiran Gado, Muhammad bin Salman ya jagoranci manyan malamai da jami’an gwamnati da dubban mutane. Haka kuma, an yi masa Salatul Gaib a Masallacin Ka’aba da ke Makkah da kuma Masallacin Annabi Muhammad (SAW), da kuma sauran daukacin masallatan da ke kasar bisa umarnin masarautar UNGA: Yau Shettima zai gabatar da jawabin Najeriya a MDD Yarima Salman ya jagoranci jana’izar babban mai ba da fatawa na Saudiyya...
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima a ranar Laraba zai gabatar da jawabin Najeriya a taron Babban Zauren Majalisar Dinkin duniya (UNGA) karo na 80 da ke gudana a birnin New York na Amurka. Zai yi jawabin ne a madadin Shugaban Kasa Bola Tinubu tsakanin karfe 3:00 na yamma zuwa 9:00 na dare agogon birnin New York. Mun ci ribar Naira biliyan 601 a watanni shidan farkon 2025 – Bankin GT Dalilin da muke goyon bayan Tinubu kan karɓo bashi — Majalisar Wakilai Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa ana sa ran Najeriya za ta bayyana sabbin kudurorinta na kasa (NDCs) da aka sabunta a karkashin yarjejeniyar Paris yayin wannan jawabi. A baya, Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima,...
Da6n uwansa, Chuks, ya tabbatar da kama shi, amma ya ce Victor ba shi da laifi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kamfanin GTCO, mamallakin bankin GT, ya bayyana samun ribar Naira biliyan 601 a watanni shida na farkon shekarar 2025. Sai dai bankin ya ce duk da haka ribar tasa raguwa ta yi a kan ta Naira tiriliyan daya da ya ci a farkon shekarar da ta gabata. Kotun Indiya ta daure dan Najeriya shekara 10 kan safarar miyagun kwayoyi DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata Wannan na kunshe ne a cikin sakamakon binciken kudi kamfanin ya fitar, wanda ya ƙare ranar 30 ga Yuni, 2025. Bankin ya kuma ce amma ribar kafin a cire haraji ce, idan aka cire kuma za ta koma biliyan 449.01, idan aka kwatanta da biliyan 905.57...
Jagoran juyin juya halin Musulunci a cikin jawabinsa ya bayyana cewa: Dangane da hadin kan al’ummar Iran, batu na farko shi ne cewa a lokacin yakin kwanaki goma sha biyu, hadin kai da hadin kan al’ummar Iran ya sanya makiya kunya. Jagoran ya jaddada cewa tun tsakiyar tsakiyar yakin makiya sun gane cewa ba za su cimma manufa da manufofin da suka cimma ba. A yammacin ranar Talatar da ta gabata a wani jawabi da ya gabatar ga al’ummar Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa;“Na ga ya wajaba a wadannan kwanaki, a ranar shahadar shahidan Sayyid Hassan Nasrallah, a tuna da shi. Sayyed Hassan Nasrallah ya kasance wata babbar kadara ga duniyar Musulunci...
Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron kasa, ya rubuta a daren Talata a wani sako da ya wallafa a dandalin sada zumunta na X:“Da farko dai Amurka ta fice daga JCPOA, sannan Turai ta kasa cika alkawuran da ta dauka, a karshe ma sun kai harin bama-bamai, yanzu haka jam’iyyu suna yin kamar su ne ake bi bashi.” A cewar Pars Today, Larijani ya kara da cewa Iran tana da tsayin daka wajen kare tsaron kasarta, kuma ba za ta bari a sanya wasu sharudda na wulakanci ba, kamar takunkuman da aka dora wa makamai masu linzami. Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya jaddada cewa kafa sharadin takaita iyaka da makamai masu linzami zuwa kasa da kilomita...
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya jaddada cewa: Iran ba za ta taba yin watsi da inganta uranium ba, kuma tattaunawa da Amurka za ta haifar da illa A jawabin da ya yi wa al’ummar Iran ta gidan talabijin a yammacin jiya Talata, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce: Ba za su mika wuya ga matsin lamba kan wani lamari na su ba. A cikin jawabinsa ta gidan talabijin ga al’ummar Iran a daren jiya, Jagoran ya taya al’ummar Iran murnar shigowar watan Mehr (23 ga watan Satumba, bisa kalandar Iran), da watan komawa makarantu da jami’o’i da ilmantarwa, da kuma shirin kaddamar da miliyoyin matasa a fadin kasar wajen samun ilimi da mulki. Wannan...
Rundunar sojojin ta ce waɗannan hare-hare sun nuna ƙudirin gwamnati wajen yaƙi da rashin tsaro a faɗin ƙasar nan. Ta kuma tabbatar wa ‘yan ƙasa cewa za ta ci gaba da ƙoƙari domin kare al’umma daga ‘yan ta’adda da sauran masu laifi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shawarwari biyu na Turai da na Rasha suna gaban Iran, kuma za ta amince da duk wata mafita ta gaskiya da ke kiyaye muradunta Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani, ya bayyana ikirarin cewa; Iran ba ta amincewa da tattaunawa, a matsayin “karya” ne, yana mai tunatar da cewa, Iran na cikin wani yanayi na tattaunawa ta fuskanci farmakin soji na wuce gona da iri. Larijani ya ce: Iran za ta amince da duk wata shawara mai ma’ana da adalci da za ta kiyaye muradunta, yana mai bayyana cewa, “Iran tana nazarin shawarwarin Turai da na Rasha da suka gabatar mata.” Larijani ya tabbatar da cewa: Iran ta amince da duk shawarwarin biyu a kan wasu sharudda,...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya tattauna da fira ministan Norway game da alakar kasashen biyu da ci gaban kasa da kasa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi wanda ke ziyara a birnin New York domin halartar taron shekara shekara na Majalisar Dinkin Duniya ya gana da fira ministan kasar Norway Jonas Gahr Støre. A yayin ganawar da aka yi a ranar Talata, bangarorin biyu sun tattauna kan dangantakar da ke tsakanin kasashen Iran da Norway, tare da yin musayar ra’ayi kan ci gaban yankin da kasa da kasa. Taron dai ya yi tsokaci kan matsalar jin kai da Falasdinawa ke fuskanta daga sojojin mamayar Isra’ila sakamakon kisan kiyashin da ake ci gaba da yi a zirin Gaza da kuma...
Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ya sanar da cewa: Masu binciken hukumarsa suna kan hanyarsu ta zuwa Iran Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya bayyana cewa: Masu sa ido na hukumar IAEA na kan hanyarsu ta zuwa Iran. Rafael Grossi ya bayyana cewa: Masu sa ido na hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA na kan hanyarsu ta zuwa Iran, amma shigarsu ta dogara ne da manufofin siyasar Iran. Ya ce: “Damar da suke da shi tana da kunci sosai, don haka tawagar hukumar IAEA tana da ‘yan sa’o’i kadan ko ‘yan kwanaki don sanin ko yarjejeniya da bangarorin biyu suka rattaba hannu a kai za...
Kasashen Burkina Faso, Nijar, da Mali sun fice daga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya Kasashen Burkina Faso, Mali, da Nijar sun sanar a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar na ficewa daga yarjejeniyar Rome ta kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC. Sanarwar wadda wakilin gwamnati kuma ministan sadarwa na Burkina Faso, Benguendé Gilbert Ouédraogo ya karanta, ta ce: Gwamnatocin Burkina Faso, Jamhuriyar Mali, da Jamhuriyar Nijar, wadanda suka kafa kungiyar hadin kan kasashen Sahel, sun sanar da ra’ayin jama’a na wannan kungiyar da al’ummar duniya kan matakin da suka dauka na ficewa daga yarjejeniyar Rome ta kotun hukunta manyan laifuka ta duniya nan take. A baya, kasashen uku sun bayyana kotun da aka ambata a matsayin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk da amfanin kifi ga lafiyar jikin mutum da kuma samar da kudin shiga masana sun ce ba a amfani da shi yadda ya kamata a Najeriya. Baya ga bai wa jiki lafiya, kifi ka iya samar da kudaden shiga ga daidaikun ’yan Najeriya da ma kasar gaba daya. NAJERIYA A YAU: Abin Da Doka Ya Ce Kan Kisan Jami’an ‘Yan Sanda DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa ’yan Najeriya basa samun cin kifi kamar yadda ya kamata. Domin sauke shirin, latsa nan
A yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci hada karfi da karfe wajen gina yankin Xinjiang ya zama mafi kyau a cikin tsarin zamanantar da kasar Sin. Ya bukaci hakan ne yayin da ya gana da wakilai daga dukkan kabilu da sauran fannonin rayuwar al’umma a yankin Xinjiang mai cin gashin kansa na arewa maso yammacin kasar Sin. Xi, wanda shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin koli na soja, ya isa birnin Urumqi, babban birnin yankin Xinjiang da safiyar yau, domin halartar bukukuwan cika shekaru 70 da kafuwar yankin. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
Rundunar ’yan sanda a Jihar Kano ta sanar da cafke wani mutum da ke yi mata sojan-gona yana yaudarar jama’a domin karɓar musu kuɗi. An cafke wanda ake zargin ne a ranar Lahadi, 21 ga Satumbar 2025 a yankin Kofar Dawanau, sanye da kayan ’yan sanda, wanda bayanai suka ce ya daɗe yana aika-aikar. An yi wa sojoji ɗaurin rai da rai kan sayar wa ’yan ta’adda makamai a Borno Sanata Natasha ta koma Majalisar Dattawa Sanawar da rundunar ta fitar ta bayyana cewe an kama shi ne bayan da jama’a suka shigar da ƙorafe-ƙorafe da dama game da ayyukan wasu da ke yin kutse da shigar ’yan sanda domin damfarar jama’a. Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa,...
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya isa birnin New York na Amurka da yammacin jiya Litinin, don halartar babban taron mahawara na MDD karo na 80. Yayin da yake birnin na New York, Li zai halarci wasu jerin ayyuka da Sin ta tsara, ciki har da taron manyan jami’ai game da shawarar tsarin shugabancin duniya, kana zai gana da babban magatakardar MDD Antonio Guterres da shugabannin kasashe masu ruwa da tsaki. Yayin tarukan cudanyar mabanbantan sassa, da na bangaren Sin da daidaikun kasashen, Li zai yi karin haske dangane da mahangar kasar Sin game da yanayin da ake ciki a harkokin kasa da kasa a halin yanzu, da manyan batutuwa da ayyukan MDD. Zai kuma fayyace manufofin kasar Sin na...
Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa tuni gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ɗauki manyan matakai na gyara tattalin arziki, ciki har da cire tallafin man fetur, haɗa farashin musayar kuɗi, da kuma sabunta tsarin haraji da kwastam. Ya ƙara da cewa waɗannan sauye-sauye sun fara samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari, inda ya nuna cewa manyan kamfanonin tantance darajar kuɗi irin su Fitch da Moody’s sun ɗaga matsayin Najeriya saboda ingantattun manufofi da ƙaruwar ajiyar kuɗi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Guguwar Amincewa Da Kasar Falasdinu Ta Nuna Yadda Amurka Da Isra’ila Suka Zama Saniyar Waren Da Ba A Taba Gani Ba
Ya zuwa ranar 23 ga watan Satumba agogon Beijing, kasashe 152 cikin 193 na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da Falasdinu a matsayin kasa. A cikin kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD, Amurka ce kadai ba ta amince da kafuwar kasar Falasdinu ba. Wannan guguwar ta amincewa da kafuwar kasar Falasdinu ta sanya Amurka da Isra’ila sun zama saniyar ware a fannin diflomasiyya game da batun rikicin Falasdinu da Isra’ila. Wata kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a da CGTN ta gudanar a duniya ta nuna cewa kashi 78.2 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa, babbar hanyar warware matsalar Falasdinu ita ce aiwatar da shawarar “kafa kasashe biyu”, wadda kuma ita ce ginshikin samar da...
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, ta koma ofishinta da ke harabar majalisar bayan ƙarewar wa’adin dakatarwar watanni shida da aka yi mata. A wani bidiyon komawarta ofis da ya karaɗe shafukan sada zumunta, ’yar majalisar ta zargi Shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Godswill Akpabio da ɗaukarta a matsayin baiwarsa. Yarima Salman ya jagoranci jana’izar babban mai ba da fatawa na Saudiyya Kotu ta hana NUPENG rufe Matatar Ɗangote A cewarta, kamar yadda Akpabio ke matsayin sanata haka ita ma sanata ce. Sanata Natasha ta ce duk da cewa an dakatar da ita ba bisa ƙa’ida ba, ta riƙa sauke nauyin al’ummar mazaɓarta na Kogi ta Tsakiya, saboda a cewarta ba ta son al’ummarta su ji...
Hassan Jibril wanda ke zaune a yankin Pata da ke fama da ambaliyar ruwa a duk shekara, ya ce a yanzu haka suna cikin fargaba, duk da cewa a ko wace shekara sun saba yin gudun hijira tun bayan afkuwar ambaliyar ruwa ta 2012 da ta mamaye wasu al’ummomi a wasu kananan hukumomin jihar. Ƙananan hukumomin dake cikin fargaba sun haɗa da Kogi, Ajaokuta, Ofu, Ibaji, Adavi, Bassa da Omala. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yarima mai jiran gado na Masarautar Saudiyya, Sheikh Muhammad bin Salman, ya jagoranci sallar jana’izar fitaccen malamin addini, Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Muhammad Al-Sheikh. Shafin Inside Haramain ya ruwaito cewa an gudanar da jana’izar ce a Masallacin Imam Turki bin Abdullah da ke birnin Riyadh. CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin 100 Kotu ta hana NUPENG rufe Matatar Ɗangote Aminiya ta ruwaito cewa za a yi masa Salatul Ga’ib a Masallacin Harami na Makkah da kuma Masallacin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da ke Madina. A wannan Talatar Allah Ya yi wa Babban Mai Ba da Fatawar na Saudiyya rasuwa yana da shekara 82. Fadar Masarautar ƙasar da kuma Shugaban Majalisar Malaman Masallata Haraman Makkah da...
Yawan tashoshin fasahar sadarwa ta 5G a kasar Sin ya kai kusan miliyan 4.65 a karshen watan Agusta, kamar yadda alkaluman mahukunta suka nuna a yau Talata. A cewar ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin, adadin ya kai kashi 36.3 na adadin tashoshin sadarwar wayar hannu a fadin kasar baki daya. A halin yanzu, ana samun karuwar masu wayar salula a kasar Sin da ke rungumar amfani da fasahohin sadarwa na 5G. Alkaluman da aka fitar zuwa karshen watan Agusta sun nuna cewa, yawan masu amfani da wayar salula na manyan kamfanonin sadarwa uku da kuma kamfanin China Broadnet ya kai kimanin biliyan 1.82. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
A cewar kakakin rundunar ‘yansandan Kano, binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa, Shitu ba jami’in ‘yansanda ba ne kuma ba konstabulari na musamman ba ne. Ya kara da cewa, za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu, yayin da ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin sanin girman munanan ayyukansa da kuma duk wani mai hannu a ciki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas (NUPENG) ta tabbatar da cewa ta samu takardun kotu da ke hana mambobinta sayar da tikiti ko duk wani yunƙuri da zai kawo tsaikon al’amura a Matatar Ɗangote. Shugaban NUPENG, Williams Akporeha, ya bayyana haka yayin taron manema labarai a Abuja ranar Talata, wanda aka gudanar tare da haɗin gwiwar Kungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur da Gas (PENGASSAN). An ƙone al’aurar ’yar shekara 5 saboda fitsarin kwance a Bauchi CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin 100 Akporeha ya ce kungiyar tana mutunta doka, kuma za ta bari shari’a ta yi aikinta har sai an kammala duk wani sha’ani a kotu. “Kamar yadda kowa ya sani, Ɗangote ya kai mu kotu, kuma...
Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae, zai gabatar da jawabi ga mutanen kasar Iran nan gaba kadan, saboda shigowar makin tsaro mai tsarki, inda ake saran zai tabo al-amura da suka shafi tsaron kasar da kuma siyasar kasa da kasa. Makon tsaro dai shi ne makon da aka fara yakin tsaron kasar mai tsari wanda ya zama masomin yakin tsaron na shekaru 8 tare da gwamnatin Ba’ath ta kasar Iran karkashin shugabancin Saddam Hussain a lokacin An fara yakin ne a ranar daya ga watan Mehr shekara 1359 wato a shekara 1980 har zuwa shekara 1988. Har’ila yau ana saran zai yi Magana kan sabbin al-amura da suke tasowa a cikin gida. Share...
A yau talata da yamma ce aka yi jana’izar shahidan Bintijbail na kudancin kasar Lebanon, wanda HKI ta kaisu ga shahada a lokacinda ta cilla makamai masu linzami kan motar da take dauke da su a ranar Lahadin da ta gabata. Tashar talabijin ta Al-Manar ta kungiyar Hizbullah ta bayyana cewa, shahidan mutane 5 biyar ne wadanda suka hada da kananan yara 3 da mahaifinsu da kuma sannan mahaifiyarsu ta ji Rauni mai tsanani, da kuma yar’uwassu wacce itama ta ji Rauni. Almanar ta nakalto cewa shahadar da kuma kissan kiyashin bai karawa mutanen garin ba sai karfin giwa na riko da kasarsu da kuma gwagwarmayansu. Ministan kiwon lafiya Rakan Nasiruddeen tare da rakiyar minister watsa labarai Paul mahaifiyar yaran...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa dandalin jawabi a MDD wata dama ce ta kasashen duniya su bayyana ra’ayinsu kuma Iran zata bayyana ra’ayinta a gobe Laraba 23 ga watan Satumba na wannan shekara ta 2025. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka jim kadan fafin ya shiga jirgi zuwa birnin NewYork a safiyar yau talata. Ya ce duniya a halin yanzu tana fuskantar danniya da babakere na wasu tsirarun kasashe a duniya. Sannan gaskiya mai dacin da ke faruwa a halin yanzu shi yadda yara da jarirai da suke mutuwa a gaza, a kisan kiyashin da HKI take aiwatarwa a Gaza kimani shekaru 2 da suka gabata. Sannan yayi allawadai da...
Daya daga cikin shuwagabannin kungiyar yan ta’adda ta Deash kuma kungiya mafi kiyayya ga Amurka a fadin ta a yau ya kama hanya zuwa NewYork don gabatar da jawabin a babban zauren MDD a karon farko. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, tun lokacinda tawagar Amurka ta ziyarci kasar Siriya bayan kifar da gwamnatin shugaba Bashar Al-Asad a shekarar da da ta gabata, shugaban tawagar Barbara Leaf mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amurka na lokacin, bayan ganawa da Abu Muhammad Julani, ta bada sanarwan gwamnatin Amurka ta dauke ladar kudede miliyon $10,000 wanda ta saka don a kawo mata kan Abu Muhammad Al-julani shugaban kungiyar Al-ka’isa bayan hare-haren 11 ga watan satumban shekara ta 2001. Ya kuma...
Tom Barrack, jakadan Amurka a turkiya sannan manzonta na musamman a Siriya da Lebanon ya amince da cewa gwamnatin Trump tana son ta hada mutanen kasar Lebanon da sojojin kasar yaki. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Tom Barrack yana fadar haka a wata hirar da yayi da yan jaridu a birnin Abudhabi a yau Talata, ya kara da cewa ya takurawa gwamnatin kasar Lebanon ta kwance damarar kungiyar Hizbullah. Jakadan ya kara da cewa Hizbullah makiyarmu ce makiyar HKI kuma tana da karfi, amma ba zamu taba bamawa sojojin Lebanon makamai ba, saboda zasu yaki HKI da su. Amma zami iya basu kananan makamai don su yi mutanen kasar wanda kuma suna kungiyar Hizbullah. Share...
Ana zargin wata matar aure, Rabi Nuhu da ke garin Magama Gumau a ƙaramar hukumar Toro ta Jihar Bauchi, da cin zarafin wata yarinya ’yar shekara biyar ta hanyar ƙone mata al’aura, saboda zargin tana yawan yin fitsarin kwance. Wakilinmu ya gano cewa yarinyar marainiya ce wadda mahaifiyarta ta rasu kusan shekara ɗaya da ta gabata, inda take zaune tare da mahaifinta, Mohammed Umar, da matarsa. CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin 100 Mahara sun kashe ɗan sanda sun ɗauke bindigarsa a Taraba Wani mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama a garin, Kabiru Abdulkadir, ya bayyana cewa sai bayan kwana biyar da ƙonewar ta faru ne al’amarin ya bayyana. “Don guje wa matsala, mahaifin yarinyar ya sayi wata...
Ana zargin wata matar aure, Rabi Nuhu da ke garin Magama Gumau a ƙaramar hukumar Toro ta Jihar Bauchi, da cin zarafin wata yarinya ’yar shekara biyar ta hanyar ƙone mata al’aura, saboda zargin tana yawan yin fitsarin kwance. Wakilinmu ya gano cewa yarinyar marainiya ce wadda mahaifiyarta ta rasu kusan shekara ɗaya da ta gabata, inda take zaune tare da mahaifinta, Mohammed Umar, da matarsa. CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin 100 Mahara sun kashe ɗan sanda sun ɗauke bindigarsa a Taraba Wani mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama a garin, Kabiru Abdulkadir, ya bayyana cewa sai bayan kwana biyar da ƙonewar ta faru ne al’amarin ya bayyana. “Don guje wa matsala, mahaifin yarinyar ya sayi wata...

Xi Jinping Zai Halarci Bikin Murnar Cika Shekaru 70 Da Kafuwar Yankin Xinjiang Na Uygur Mai Cin Gashin Kansa
A ranar Alhamis 25 ga watan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci wani babban taro a birnin Urumqi, babban birnin yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa, domin murnar cika shekaru 70 da kafuwar yankin. An shirya fara bikin da shugaba Xi zai halarta da karfe 10:30 na safiyar Alhamis, kuma babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) da dandalin shafin intanet na kamfanin dillancin labarai na kasar Sin (Xinhuanet) za su watsa shi kai-tsaye. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
Kwamitin da ke kula da tsare-tsare da manufofin kuɗi na Babban Bankin Najeriya (CBN) ya zaftare maki 60 daga nauyin kuɗin ruwa da ke kan masu karɓar basussuka. Wannan dai shi ne karo na farko cikin shekaru biyar da aka samu babban bankin ya yi rangwamin kuɗin ruwa a ƙasar. CBN ɗin ya ce kwamitin a wannan Talatar ya rage yawan kuɗin ruwan daga kashi 27.5 da yake karɓa a baya zuwa kashi 27 a yanzu. Mahara sun kashe ɗan sanda sun ɗauke bindigarsa a Taraba An yi garkuwa da ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato Gwamnan Babban Bankin, Olayemi Cardoso, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai bayan kammala taron kwamitin karo na 302 da ya gudana a Abuja....
Haka kuma sun tabbatar da cewa manoma da suka koma gonakinsu kwanan nan sun samu kariya. Babu wanda aka sace ko ɗaya, yayin da jama’ar yankin ke ci gaba da zama lafiya. A ranar 19 ga watan Satumba, Birigediya Janar Ugochukwu Unachukwu, wanda shi ne muƙaddashin kwamandan rundunar sojojin 7 Division, ya kai ziyara Banki don yaba wa sojoji kan jarumtar da suka nuna. Ya ce ‘yan ta’addan sun yi mummunan rashi kuma ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar sojojin Nijeriya za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi. Sai dai rundunar ta tabbatar da cewa wani soja ya rasa ransa yayin kare mutanen, yayin da wasu suka ji rauni. Sojojin sun ce wannan shaida ce ta jajircewar rundunar...
An kashe wani ɗan sanda mai muƙamin Sajan a wani hari da ’yan bindiga suka kai wani shingen bincike, inda suka ɗauke bindigarsa bayan sun halaka shi a Jihar Taraba. Wata majiyar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na dare a garin Tella, cikin Ƙaramar Hukumar Gassol, lokacin da ’yan bindigar suka yi wa shingen binciken ƙwanton ɓauna. An ce maharan sun harbi ɗan sandan ne a kansa, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa nan take, lamarin da ya sa sauran abokan aikinsa da ke wurin suka tsere. Bayan sun yi kisan, ’yan bindigar sun ɗauke bindigar marigayin sannan suka tsere daga wurin. Kakakin rundunar ’yan sandan Taraba, ASP Leshen James, bai ɗaga wayar kiran da...
Yanzu da aka buɗe ofishinta kafin komawar zaman majalisar, hankali ya karkata kan zaman majalisar na watan Oktoba, don ganin ko za a gabatar da kuɗirin dawowarta, da kuma ko za a tilasta mata ta nemi afuwa kafin ta dawo ta zauna a kujerarta a cikin zauren majalisar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato, mai wakiltar Mazaɓar Pankshin ta Kudu, Laven Denty Jacob. A yammacin ranar Litinin aka yi garkuwa da shia gidansa da ke Anguwan Kagji, a Unguwar Dong, a Ƙaramar hukumar Jos ta Arewa. Wani na kusa da shi ya tabbatar wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:30. A cewar mai taimaka wa ɗan majalisar, wasu mutane uku ne, da suka rufe fuskokinsu suka kai hari a ƙofar gidansa, a lokacin da suke jiran jami’an tsaronsa su buɗe kofar. Ya bayyana cewa maharan sun ɗauke ɗan majalisar da ƙarfi daga cikin motarsa zuwa wani wuri, da ba a sani ba. Ya ce masu garkuwar sun...
Allah Ya yi wa Babban Mai Ba da Fatawa na kasar Saudiyya, Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Mohammed Al Al-Sheikh, rasuwa. Hukumomin ƙasar Saudiyya sun sanar da cewa Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Mohammed Al Al-Sheikh ya rasu yana da shekara 82 a duniya. Fadar Masarautar ƙasar da kuma Shugaban Majalisar Malaman Masallata Haraman Makkah da Madina, Sheikh Abdul Rahman Sudais, sun gabatar da ta’aziyyar iyalai da ɗaliban mashahurin malamin. Za a gudanar da Sallar Jana’izarsa a Masallacin Imam Turki bin Abdullah da ke birnin Riyadh bayan Sallar La’asar. Kazalika za a yi masa Salatul Ga’iba a Masallacin Harami na Makkah da kuma Masallacin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da ke Madina.
Sojojin HKI sun amabci cewa sojoji biyu sun halaka a wani kwanton bauna da mayaka a Gaza su ka yi, daga ciki har da kwamandan rundunar “Folcan”. Kakakin sojan HKI ya bayyana cewa wanda aka kashe din shi ne Manjo Shahir Natna’il, sai kuma Midgal Haimik a wani fada da aka yi a arewacin Gaza. Wasu kafafen watsa labarun HKI sun ambata cewa mayakan kungiyar gwagwarmaya ta Hamas sun yi wa sojoji kwanton bauna a wasu wurare biyu mabanbanta. A bisa kididdigar sojojin HKI adadin wadanda aka kashe zuwa yanzu a yakin Gaza, sun kai 911. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website...
Shugaban kasar Afirka Ta kudu Cyril Ramaphosa da ya gabatar da jawabi a taron babban zauren MDD ya jaddada matsayar kasarsa na son ganin an bai wa al’ummar Falasdinu kasarsu akan iyakar 1967. Da yake Magana akan abinda yake faruwa yanzu a Gaza, shugaban kasar ta Afirka Ta Kudu ta caccaki HKI akan yadda take azabatar da al’ummar Falasdinu a dunkule. Haka nan kuma ya yi kira da a kawar da dukkanin abubuwan da suke kawo cikas wajen kafawa Falasdinawan kasar tasu. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks...
A yau Talata ne dai kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato, ta bude wani zama na musamman a birnin Brussels domin tattauna zargin da ta yi wa kasar Rasha da keta hurumin sararin samaniyar kasar Istonia. Taron na kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato, yana a karkashin aiki da doka ta 4 ne na tsarin aikin kungiyar wacce ta yi kira da a rika yin tarukan gaggawa domin yin shawara a duk lokacin da wata memba ta fuskanci barazana. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Estonia ce dai ta bayyana cewa jiragen yakin Rasha, samfurin Meg-31 guda 3 su ka keta hurumin sararin samaniyarta a ranar juma’ar da ta gabata, sun kuma dauki tsawon mintuna 12 suna karakaina a samaniya. Ma’aikatar harkokin wajen kasar...
‘Yan bindiga sun sace ɗan majalisar dokokin Jihar Filato, mai wakiltar Pankshin Kudu, Laven Denty, a gidansa da ke unguwar Dong na ƙaramar hukumar Jos ta Arewa. A makon da ya gabata ma, Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito yadda ‘yan bindiga suka kutsa cikin unguwar Dong, inda suka yi garkuwa da wani mai yi wa ƙasa hidima (NYSC), da kuma ɗalibin Jami’ar Jos. Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Ɓullar Cutar Mpox A Jihar Yadda Aka Bai Wa Ousmane Dembélé Kyautar Ballon d’Or Ta 2025 Masu garkuwar da mutanen sun shiga gidan iyalan Solomon Dansura, da misalin ƙarfe 10 na dare inda suka tafi da baƙinsa guda biyu a lokacin. Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto babu wani martani daga hukumomin jihar ko kuma...
Ya ce Kano na cikin hatsari saboda cunkoson jama’a da kuma zirga-zirgar mutane daga wurare daban-daban. KNCDC ta gudanar da cikakken bincike a Ungogo, inda aka duba unguwar da marar lafiyan yake da kuma asibitocin da ya ziyarta. Duk wanda aka bincika yana cikin ƙoshin lafiya kuma babu wanda ya kamu da cutar. Farfesa Abbas ya jaddada muhimmancin wayar da kan jama’a don hana yaɗuwar cututtuka. Ya nemi kafafen watsa labarai su ci gaba da yaɗa bayanan lafiya ga al’umma. Ya kuma buƙaci jama’a su kasance masu lura, inda ya tabbatar da cewa Kano tana da tsarin sa ido da shiri don shawo kan kowace irin cuta nan gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi wa tsohon Ministan Shari’a kuma Antoni-Janar na Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami, tambayoyi a kan harin da aka kai wa ayarin motocinsa a Jihar Kebbi. An gudanar da tambayoyin ne a ofishin hukumar na Birnin Kebbi a ranar Litinin, inda Malami ya bayyana cewa an yi masa tambayoyin cikin ƙwarewa da mutuntawa. A ranar 1 ga Satumba, 2025 ne aka kai wa ayarin motocin da ke rakiyar Malami hari a Birnin Kebbi, bayan ya dawo daga gaisuwar ta’aziyya ga iyalan marigayi Babban Limamin Masallacin Dakta Bello Haliru Jumu’a. Shaidu sun bayyana cewa an lalata motocin rakiyarsa kusan guda 10, sannan da dama daga cikin magoya bayansa sun jikkata. Burkina Faso, Mali da Nijar...
Ya ce Kano na cikin hatsari saboda cunkoson jama’a da kuma zirga-zirgar mutane daga wurare daban-daban. KNCDC ta gudanar da cikakken bincike a Ungogo, inda aka duba unguwar da marar lafiyan yake da kuma asibitocin da ya ziyarta. Duk wanda aka bincika yana cikin ƙoshin lafiya kuma babu wanda ya kamu da cutar. Farfesa Abbas ya jaddada muhimmancin wayar da kan jama’a don hana yaɗuwar cututtuka. Ya nemi kafafen watsa labarai su ci gaba da yaɗa bayanan lafiya ga al’umma. Ya kuma buƙaci jama’a su kasance masu lura, inda ya tabbatar da cewa Kano tana da tsarin sa ido da shiri don shawo kan kowace irin cuta nan gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
Majalisar Dokoki ta Kasa ta ɗage ranar dawowarta daga hutu zuwa 7 ga watan Oktoba, 2025. Karin bayani na tafe..
An bayyana dan wasan a matsayin wanda ya lashe kyautar ne a bikin da aka gudanar ranar Litinin 22 ga watan Satumban 2025 a dakin taro na Theatre du Chatelet da ke birnin Paris a kasar Faransa. Ballon d’Or kyauta ce da akan bai wa dan wasan da ya nuna gwaninta a kowace shekara, inda akan yi la’akari da gudunmawar da dan wasan ya bayar ga kungiya da kuma kasarsa. Tun farko an fitar da jerin ‘ƴan wasa 30 cikin wadanda ake sa ran za su lashe kyautar. Dembele ya taka rawar gani wajen taimakon kungiyar PSG ta lashe gasar Ligue 1 da da kuma samun nasarar lashe gasar Champions Leage na farko a tarihinta, sannan ta kai wasan karshe...
Ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar da sojoji ke mulki sun sanar cewa sun fice daga Kotun Duniya ta Hukunta Manyan Laifuka (ICC). A sanarwar da suka fitar ranar Litinin sun bayyana ICC a matsayin “kayan aikin mulkin mallaka na zamani.” Ƙasashen ukun, waɗanda aka yi juyin mulki a cikinsu tsakanin shekarun 2020 zuwa 2023, sun kafa ƙawance mai suna Kungiyar Kasashen Sahel (AES) domin haɗa kai da nisantar da kansu daga ƙasashen Yamma, musamman tsohuwar mai mulkinsu, Faransa. A cikin sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar, ƙasashen sun ce kotun da ke birnin Hague “kayan aikin danniya ce a hannun masu mulkin mallaka.” ’Yan sanda sun kama mutum 4 kan kai wa Lakurawa babura a Kebbi Faransa ta...
Mohammad Hindi mataimakin sakatare janar din kungiyar gwagwarmaya ta jihadil Islami ya bayyana cewa an karbi bukatar dakatar da bude wuta a gaza, amma kasar Amurka da kasashen turai basa son a dakatar da bude wuta har sai an kawar da dukkan kungiyoyin gwagwarmaya baki daya ba wai a yankin falasdinu ba kawai. Haka zali ya kara da cewa HKI ta kai hari kan wajen da wakilan kungiyar hamas suke a birnin doha na kasar Qatar don tattaunawa kan batun dakatar da bude wuta. Isra’ila ta sanar a hukumance cewa prime minister Natanyaho ya sanar da shugaban Amurka Donald trump jim kadan kafin kai harin cewa isra’ila za ta kai wa Qatar hari, Harin ya jawo nuna damuwa sosai kan...
Masana da shugabanni da suka halarci taron, ciki har da Farfesa Isah Ali Pantami, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da sauran fitattun malamai, sun yaba da wannan ƙudiri na gwamnatin Katsina. Rahotanni sun nuna cewa sama da yara 300,000 ne ba sa zuwa makaranta a Katsina, ciki har da dubban almajirai da ‘yan mata. Wannan ne ya sa gwamnati ta ɗauki wannan mataki domin inganta ilimi da kuma bai wa matasa damar samun kyakkyawar makoma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An ba shi kyautar ne a daren ranar Litinin a Theatre du Chatelet da ke birnin Paris, inda ya doke matashin Barcelona, Lamine Yamal, wanda ya lashe kyautar matashin ɗan wasa mafi ƙwazo. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Ƙididdiga a Najeriya, NBS ta ce arzikin cikin gida da kasar ke samu ya karu da kashi 4.23 cikin 100 a rubu’i na biyu na shekarar 2025 da muke ciki. Sabbin alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa an samu karin kashi 3.48 idan aka kwatanta da irin wannan lokacin a 2024, lamarin da hukumar ta ce alamu ne na ingantar tattalin arzikin kasar. Hukumar ta NBS ta ce fannin aikin gona ne kan gaba wajen samar da karuwar arzikin kasar, wannan ya karu zuwa kashi 2.82 sabanin kashi 2.60 a 2024. Sauran fannonin da hukumar ta ce an samu ci gaba sun hada da fannin masana’antu da, da fan fetur da kuma fannin ma’adinai. NBS ta ce...
Rahotanni sun bayyana cewa kimanin kaso 8% na mambobin majalisar dinkin diniya ne suka sanar da amincewarsu da kasar falasdinu, a daidai lokacin da Isra’ila take ci gaba da kisan kare dangi a Gaza kuma take kara fadada mamaye yankuna a gabar yammacin kogin jodan. Kasaashen faransa, luxambourg , malta da manako ne suka sanar da amincewa da yankin falasdinu a matsayin kasar a wajen taron babban zauren majalisar dinkin duniya, prime ministan kasar kanada marka caney ya fadi cewa amincewar tana da muhimmanci sosai, kana yayi gargadin cewa an shafe batun yancin cin gashin kai ga yankin falasdinu. Sai dai duk da amincewa da yankin na falasdinu a matsayin kasa, amma ta’addancin da Isra’ila ke yi a yankin gaza...

He Lifeng: Ya Kamata Sin Da Amurka Su Karfafa Dangantakar Tattalin Arziki Da Cinikayya Mai Dorewa Cikin Lumana
Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng ya gana da tawagar ‘yan majalisar wakilan Amurka karkashin jagorancin Adam Smith a yinin yau Litinin 22 ga wata a birnin Beijing. He Lifeng ya ce, a ranar 19 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaba Donald Trump sun yi wata tattaunawa ta wayar tarho, kuma sun cimma muhimmiyar matsaya, tare da samar da jagoranci bisa manyan tsare-tsare don tabbatar da daidaiton dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka a mataki na gaba. Kasashen Sin da Amurka na da sararin yin hadin gwiwa da kuma samun moriyar juna. Ana sa ran Amurka za ta sa kaimi wajen yin magana da kasar Sin bisa ka’idojin mutunta juna, da zaman lafiya da samun nasara...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau 22 ga wannan wata cewa, a yayin da ake raya duniya bisa tsarin bai daya, musayar kwararru a tsakanin kasa da kasa ta sa kaimi ga raya fasahohi da tattalin arzikin kasashen duniya. Kasar Sin tana maraba da kwararru daga bangarori da sana’o’i daban daban na kasa da kasa su zo kasar ta Sin su gudanar da harkokinsu don sa kaimi ga raya zamantakewar al’ummar dan Adam da kuma samun ci gaban sha’aninsu baki daya. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ayyana gobe Talata, a matsayin ranar ɗaya ga watan Rabi’ul Thani, 1447 bayan hijira, wanda ya kawo ƙarshen watan Rabi’ul Awwal, 1447, daidai da ranar 23 ga Satumba, 2025. Sanarwar ta fito ne a wata takarda da Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid, wanda shi ne shugaban kwamitin da ke bai wa Majalisar Sarkin Musulmi shawara kan al’amuran addini, ya sanya wa hannu ya kuma raba wa manema labarai. A sanarwar, Sarkin Musulmi bai fayyace wuraren da aka ga sabon watan ba, sai dai ya bayyana cewa ya gamsu da sahihan rahotannin da aka gabatar, lamarin da ya sa ya ayyana ganin watan a hukumance. Ya yi addu’ar Allah Ya kawo zaman lafiya da...
29. Florian Wirtz (Liverpool) 28. Virgil van Dijk (Liverpool) 27. Declan Rice (Arsenal) 26. Erling Haaland (Man City) 25. Denzel Dumfries (Inter Milan) 24. Fabian Ruiz (PSG) 23. Jude Bellingham (Real Madrid) 22. Alexis Mac Allister (Liverpool) 21. Serhou Guirassy (Borussia Dortmund) 20. Lautaro Martinez (Inter Milan) 19. Joao Neves (PSG) 18. Scott McTominay (Napoli) 17. Robert Lewandowski (Fc Barcelona) 16. Vinicius Jr (Real Madrid) 15. Viktor Gyokeres (Arsenal) 14. Desire Doue (PSG) 13. Harry Kane (Bayern Munchen) 12. Kvicha Kvaratskhelia (PSG) 11. Pedri Gonzalez (Fc Barcelona) 10. Nuno Mendes (PSG) 9. Gigio Donnarumma (Man City) 8. Cole...
Ɗan wasan gaban PSG da Faransa, Ousmane Dembélé ya lashe kyautar Ballon d’Or ta bana. Balon d’or dai ita ce lambar yabo mafi girma a duniyar ƙwallon kafa wacce ake bai wa gwarzon ɗan wasa na shekara.

Nau’o’in Jirage Uku Sun Kammala Sauka Da Tashin Farko Bisa Taimakon Majaujawar Maganadisu A Jirgin Dako Na Fujian Na Kasar Sin
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Faransa ta bi sahun Birtaniya, Australia da Canada da sauran ƙasashen duniya sama da 140 da suka amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai ’yanci. Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ne ya tabbatar da amincewar gwamnatinsa na kafa ƙasar Falasdinu a hukumance. Tattalin arzikin Najeriya ya ƙara haɓaka — NBS NEF za ta ƙaddamar da taron zuba jari don bunƙasa Arewa Macron ya bayar da tabbacin ne a yayin da yake jawabi a babban taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York. Mista Macron ya ce lokaci ya yi da ya kamata a kawo ƙarshen yaƙin Gaza tare da sakin sauran Isra’ilawa 48 da Hamas ke garkuwa da su. Ya ce lokaci kaɗan ne ya rage wa duniya ta iya wanzar...
Hukumar Ƙididdigar a Najeriya, NBS ta ce arzikin cikin gida da ƙasar ke samu ya ƙaru da kashi 4.23 cikin 100 a rubu’i na biyu na shekarar 2025 da muke ciki. Sabbin alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa an samu ƙarin kashi 3.48, idan aka kwatanta da daidai wannan lokacin a 2024, lamarin da hukumar ta ce alamu ne na bunƙasar tattalin arzikin ƙasar. An gudanar da bikin ɗaga tutar Falasɗinu a Birtaniya CAC ta soma yi wa kamfanoni rijista da fasahar AI NBS ta ce fannin aikin gona ne kan gaba wajen samar da ƙaruwar arzikin ƙasar, wanda ya ƙaru zuwa kashi 2.82 saɓanin kashi 2.60 a 2024. Sauran fannonin da hukumar ta ce an samu ci...
Sanarwar ta ƙara da cewa, Gwamna Lawal ya jaddada cewa tsarin dimokuraɗiyyar Kanada, ƙarfafan tattalin arziƙi, hakar ma’adinai ta hanyar da ta dace, da kuma harkokin kasuwanci masu zaman kansu masu kirkire-kirkire sun sanya ta zama abokiyar haɗin guiwar da ta ta dace ga Afrika. Ya ce, “Idan Afrika za ta cika burinta gaba ɗaya, dole ne mu gane cewa ci gaba ba wai kawai batun manufofin ƙasa bane; yana kuma buƙatar aikace-aikacen matakan jihohi da ƙananan hukumomi. “Yayin da Gwamnatocin Tarayya ke ba da jagorar manufofi, a matakin Jihohi, larduna, da Ƙananan Hukumomi ake fassara alƙawuran kasuwanci, zuba jari da ci gaba zuwa ainihin gaskiya. “Matakan jihohi sune inda manoma ke noma abincin da ke ciyar...
Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta ce a karon farko za ta shirya taron zuba jari da samar da masana’antu na Arewacin Najeriya, wanda aka shirya gudanarwa a ranakun 29 da 30 ga watan Satumba a Abuja. Taron wanda aka shirya tare da hadin gwiwar jihohin arewa 19 da kuma kamfanin raya yankin – NNDC, na da nufin mayar da yankin a matsayin wata cibiya ta samun bunkasar tattalin arziki da habaka masana’antu. An gudanar da bikin ɗaga tutar Falasɗinu a Birtaniya CAC ta soma yi wa kamfanoni rijista da fasahar AI Da yake magana a taron manema labarai da aka gudanar ranar Litinin a Abuja, kakakin kungiyar, Farfesa Abubakar Jika Jiddere, ya bayyana taron a matsayin “kira domin zaburar da...
Dangane da halin da ake ciki game da rikicin Falasdinu da Isra’ila, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau Litinin 22 ga wata cewa, karfin soja ba zai iya samar da zaman lafiya ba, kuma tashin hankali ba zai iya samar da tsaro ba. Kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da kasashen duniya wajen ci gaba da jajircewa a kan tsagaita bude wuta da kawo karshen yakin da ake yi a zirin Gaza, da kuma matukar nuna goyon baya ga tabbatar da adalci ga al’ummar Falasdinawa wajen maido da hakkinsu na kasa, da kuma kara azamar warware matsalar Falasdinu tun da wuri ta hanyar samar da cikakkiyar mafita, mai adalci...
Tawagar jami’an diflomasiyyan Falasɗinu ta gudanar da bikin ɗaga tutar ƙasar a Litinin ɗin nan a birnin Landan kamar yadda kafar labarai ta DW ta ruwaito. Bikin ɗaga tutar na zuwa ne kwana guda bayan da Birtaniya ta amince da Falasɗinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta. CAC ta soma yi wa kamfanoni rijista da fasahar AI Dalilin da muke goyon bayan Tinubu kan karɓo bashi — Majalisar Wakilai Shugaban tawagar jami’an diflomasiyyan Falasdinawa a Burtaniya Husam Zomlot, ya daga wani allo mai ɗauke da rubutun ‘Ofishin jakadancin Falasɗinu’ sannan kuma ya ce nan ba da jimawa ba za a buɗe ofishin a hukumance bayan kammala wasu sharudda dangane da dokoki da kuma tsarin gudanarwa. Mista Zomlot ya yi...
A halin yanzu, shugaba Bola Tinubu yana ganawa da gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara a fadar shugaban kasa dake Abuja a yammacin yau Litinin. Ganawar na zuwa ne kwanaki kadan bayan Fubara ya koma ofis a ranar 19 ga watan Satumba bayan da Shugaba Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da aka kafa a jihar Ribas tun farko. Tinubu ya bayyana matakin ne domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali bayan shafe watanni ana rikicin siyasa da ke barazana ga harkokin mulki da tsaro a jihar mai arzikin man fetur. Cikakken bayanai na nan tafe… Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da amincewar da kasashen Birtaniya, Australia, da Canada suka yi wa kasar Falasdinu, tana mai bayyana hakan a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da hakkin al’ummar Palasdinu na kasarsu. A cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Lahadi, kungiyar ta yi kira ga kasashen duniya da MDD da su mayar da Isra’ila saniyar ware tare da dakatar da duk wani nau’i na hadin gwiwa da ita. Hamas ta yaba da wannan amincewa da ita a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da ikirarin da al’ummar Falastinu ke yi na neman kare filayensu da wuraren ibadarsu masu tsarki, tare da fatan samun kasa mai cin gashin kanta wacce take da Quds a...
Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, ta bayyana cewa “Kisan kare dangi da ake ci gaba da yi a zirin Gaza ya zama babban gwaji ga Majalisar Dinkin Duniya. Idan muna son kungiya mai inganci kuma mai amfani, dole ne mambobinta su dauki matakin gaggawa tare da tsayin daka wajen dakatar da wannan zalunci da hukunta masu laifi.” Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya ce zasu hadu a birnin New York domin halartar taron shekara-shekara na Majalisar Dinkin Duniya. Wannan zaman dai na gudana ne a daidai lokacin da MDD ke bikin cika shekaru 80 da kafuwa, a daidai lokacin da muhimman ka’idojinta da manufofinta ke fuskantar barazanar da ba a taba ganin irinta ba da...
A Italiya dubun dubatan mutane ne suka fito kan tituna domin yin Allah wadai da yakin kisan kiyashi da Isra’ila ke yi a Gaza. Wannan gangami ya zo ne a ranar da wasu kasashe da dama ke shirin amincewa da Falasdinu a matsayin kasa a Majalisar Dinkin Duniya, bayan Birtaniya, Australia da Canada a ranar Lahadi. Duk da cewa Italiya ba ta da niyyar daukar irin wannan matakin a yanzu, A birnin Rome, fiye da mutane 20,000, ne suka taru dauke da tutocin Falasdinu domin nuna goyan bayansu. An gudanar da zanga-zangar a wasu garuruwa da dama a fadin kasar, ciki har da Milan inda mutane 50,000 suka shiga zanga zangar in ji masu wadanda suka shirya ta. Saidai Kamfanin...
Iran ta yi Allah wadai da harin da aka kai kan wani masallaci a Sudan tare da yin kira da a kawo karshen hare-haren da ake kai wa fararen hula cikin gaggawa. Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi Allah-wadai da harin na baya-bayan nan da aka kai da jirage marasa matuka a wani masallaci a birnin Al-Fashir na kasar Sudan, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da jikkata wasu da dama da ba su ji ba ba su gani ba. A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, ma’aikatar harkokin wajen Iran ta kira harin a matsayin ” keta dokokin jin kai na kasa da kasa.” Ta kuma jaddada bukatar gaggauta dakatar da kai hare-hare kan...
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau Litinin 22 ga wata cewa, nan ba da jimawa ba kasar Sin za ta gudanar da taron mata na duniya a birnin Beijing a daidai lokacin da ake cika shekaru 30 da gudanar da babban taron mata na duniya a shekarar 1995. Ya ce, kasar ta Sin tana son yin aiki kafada da kafada da dukkan kasashen duniya don kara hanzarta aiwatar da sabon tsarin ciyar da mata gaba a dukkan fannoni, da kuma rubuta wani sabon babi na raya al’amuran mata a duniya. Guo ya ce, ta fuskar abin da aka sa gaba a duniya, akwai sauran shekaru biyar kafin a cimma muradun samar...
Majalisar Wakilai ta bayyana cewa ta amince da duk wasu tsare-tsare da dabarun karɓo rancen kuɗaɗe na Shugaba Bola Tinubu, bisa la’akari da ƙoƙarin da yake yi na farfaɗo da tattalin arziki da kuma rage talauci a ƙasar nan. Shugaban Majalisar, Abbas Tajudeen ne ya bayyana hakan a yayin da yake jawabi ranar Litinin, a taron shekara-shekara karo na takwas kan bitar kasafin kuɗaɗe na majalisun dokokin nahiyyar Afirka (African Network of Parliamentary Budget Offices) da ke gudana a Abuja. Sarkin Ruman Katsina ya rasu Jariri ya mutu a bayan uwarsa yayin tsere wa ’yan bindiga a Neja Abbas ya ƙaryata raɗe-raɗin cewa majalisar ta ƙi amincewa da tsare-tsaren karɓo rance na shugaban ƙasar, inda ya ce zantuka ne marasa...
Hukumar da ke kula da yi wa Kamfanoni Rajista ta Najeriya (CAC) ta ƙaddamar da sabon shafin intanet mai amfani da fasahar ƙirƙirarriyar basira wato AI domin sauƙaƙa rajistar harkokin kasuwanci da kamfanoni a Najeriya. Shugaban Hukumar, Hussaini Ishaq Magaji (SAN), ne ya bayyana a yayin taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya a Kano ranar Litinin. Dalilin da muke goyon bayan tsare-tsaren Tinubu na karɓo bashi — Majalisar Wakilai Sarkin Ruman Katsina ya rasu Ya kuma ce hukumar ta kawo sabbin sauye-sauye da za su inganta ayyukanta da kuma sauƙaƙa wa ’yan kasuwa yin rajista da ita. Magaji ya ce, “Ko ina kake, daga dakinka, ba tare da ka san kowa a CAC ba, kuma ba tare...
Yayin da “bikin girbi na manoman kasar Sin” na takwas ke karatowa, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, shugaban kasar, kuma shugaban kwamitin kolin soja Xi Jinping, a madadin kwamitin kolin JKS, ya mika gaisuwar bikin, da fatan alheri ga manoma da ma’aikatan dake gudanar da ayyukan da suka shafi harkokin noma, da kauyuka da kuma manoma a fadin kasar. Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a bana, mun shawo kan illar bala’o’i kamar fari, da ambaliyar ruwa, da samun daidaiton noman hatsin rani, da karuwar noman shinkafa mai nuna da wuri, ana kuma sa ran samun karin girbin hatsi. Xi Jinping, ya jaddada cewa, zamanantarwa irin ta kasar Sin ba za a iya...
Majalisar Wakilai ta bayyana cewa ta amince da duk wasu tsare-tsare da dabarun karɓo rancen kuɗaɗe na Shugaba Bola Tinubu, bisa la’akari da ƙoƙarin da yake na farfaɗo da tattalin arziki da kuma rage talauci a ƙasar nan. Shugaban Majalisar, Abbas Tajudeen ne ya bayyana hakan a yayin da yake jawabi ranar Litinin, a taron shekara-shekara karo na takwas kan bitar kasafin kuɗaɗe na majalisun dokokin nahiyyar Afirka (African Network of Parliamentary Budget Offices) da ke gudana a Abuja. Sarkin Ruman Katsina ya rasu Jariri ya mutu a bayan uwarsa yayin tsere wa ’yan bindiga a Neja Abbas ya ƙaryata raɗe-raɗin cewa majalisar ta ƙi amincewa da tsare-tsaren karɓo rance na shugaban ƙasar, inda ya ce zantuka ne marasa tushe...
Na hudu, an yi ta samu ci gaban sayayya sakamakon masu yawon bude ido daga ketare. Bisa ga manufar rage haraji lokacin barin kasa da kasar Sin ke gudanarwa, an shirya shirin “Sayayya a Sin” yadda ya kamata, wanda hakan ya canza fa’idar yawan baki daga ketare da suke yawon shakatawa a kasar zuwa habaka kudin da ake kashewa. (Bilkisu Xin) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A yau Litinin Allah Ya yi wa Sarkin Ruman Katsina kuma Hakimin Batsari, Alhaji Tukur Ma’azu, rasuwa. Marigayin, wanda ya shafe shekaru 74 a duniya, ya daɗe yana fama da jinya gabanin rasuwarsa. Hisbah ta kama masu safarar mata zuwa Saudiyya a Kano Jariri ya mutu a bayan uwarsa yayin tsere wa ’yan bindiga a Neja Alhaji Tukur wanda ya shafe shekaru 43 yana riƙe da sarautar Hakimin Batsari, ya rasu ya bar mata biyu, ’ya’ya da kuma jikoki. Za a gudanar da jana’izarsa da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin yau a gidansa da ke cikin garin Batsari, kamar yadda sanarwa daga iyalansa ta tabbatar.
Mutune 70 da aka yi garkuwa da su sun samu ƴanci a Jihar Katsina, bayan yarjejeniyar sulhu da aka ƙulla da fitaccen shugaban ƴan bindiga, Isiya Kwashen Garwa. A wani faifan bidiyo da ya bayyana, Garwa ya saki mutane 40 a ƙaramar hukumar Faskari, kwanaki biyu bayan ya fara sakin wasu 30, wanda hakan ya kai adadin zuwa 70 gaba ɗaya. Rahotanni daga mazauna yankin sun ce sakin na baya-bayan nan ya biyo bayan tattaunawa tsakanin shugabannin al’umma da sansanin Garwa, a wani mataki da ake ganin zai rage tashin hankali da hare-hare a yankin. Duk da haka, Garwa ya nuna rashin jin daɗi kan abin da ya kira sumamen Sojoji a unguwar Ruwan Godiya a lokacin Sallar Juma’a, inda...
Wani jariri ya rasu a bayan mahaifiyarsa a yayin da take guje wa harin ’yan bindiga a kauyen Allawa da ke Karamar Hukumar Shiroro a Jihar Neja. Sarkin yankin Bassa, Bagudu Amos, ne ya bayyana hakan a lokacin taron tattaunawa da mata kan zaman lafiya da kare su daga cin zarafi, mai taken: “Ƙarfafa kariya daga cin zarafin jima’i da na jinsi a Jihar Neja.” Kungiyar Tunani Initiative, tare da goyon bayan Dorothy Njemanze Foundation da Ford Foundation, ce ta shirya taron domin ƙarfafa mata wajen yaki da cin zarafi da ke ƙara ta’azzara a sakamakon rashin tsaro. Bagudu Amos ya bayyana cewa mahaifiyar ta yi tafiya mai nisa a kafa da jaririn a bayanta domin tserewa daga harin ’yan...
Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba sun sace Hakimin Birbyang, Alhaji Zubairu Garba, tare da wasu mata biyu a daren Lahadi a ƙaramar hukumar Kanam ta Jihar Filato. Rahotanni sun ce ƴan bindigar sun shigo ƙauyen ne da tsakar dare, suna harbi a iska kafin daga bisani su yi awon gaba da mutanen. Matar hakimin, wadda aka yi garkuwa da ita a farkon harin, ta samu damar tserewa daga hannun masu garkuwa. Wannan lamari na baya-bayan nan ya biyo bayan sace-shi-da-kashe wa da aka yi wa Dagacin Shuwaka a yankin Kyaram, wanda shi ma ke cikin ƙaramar hukumar Kanam, mako guda kacal da ya gabata. Hakan ya ƙara tayar da hankali a tsakanin al’ummar yankin...
A kasar Guinea an fara kidaya kuri’un da aka kada na zaben kasa da ake hasashen cewa shugaban mulkin soja zai sami nasara. Kada kur’iar ta raba gardama akan sabon tsarin Mulki zai sama wani gagarumin mataki na fitar da kasar daga mulkin soja zuwa na farar hula. Shugaba Janar Mamadi Doumbouya wanda ya yi juyin Mulki zai iya samun damar ci gaba da zama akan Kargar Mulki. Jam’iyyun hamayyar siyasa a kasar Guinea sun yi kira da a kauracewa kada kuri’ar raba gardamar. Da akwai mutane miliyan 6.7 da su ka cancanci kada kuri’a a fadin kasar. A bisa dokar zaben kasar, idan kaso 50% su ka kada kuri’a, to za a amince da sakamakon abinda su ka zaba....
Ana ci gaba da takaddama a duniyar kwallon kafa kan wa ya fi cancanta da lashe kyautar Ballon d’Or a matsayin gwarzon dan wasan duniya na bana. A ranar Litinin din na za a bayar da Kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2025 a birnin Paris na kasar Fasansa, ga wanda alakalai suka zaba a matsayin Gwarzon Dan Wasan Kwallon Kafa na Duniya. Ballon d’Or ce kyauta mafi girma ta shekara-shekara ga ’yan wasan kwalllon kafa saboda bajintar da ya nuna ga ƙungiyarsa da ƙasarsa. Gasar ta bana ta kasance mafi zafi duba da yadda alkaluma ke nuna irin zakakurancin kowanne daga manyan ’yan wasan da ake hasashen za su iya lashe kambin. An rufe sansanin NYSC da kasuwanni saboda rashin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ana ci gaba da takaddama a duniyar kwallon kafa kan wa ya fi cancanta da lashe kyautar Ballon d’Or a matsayin gwarzon dan wasan duniya na bana. A ranar Litinin din na za a bayar da Kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2025 a birnin Paris na kasar Fasansa, ga wanda alakalai suka zaba a matsayin Gwarzon Dan Wasan Kwallon Kafa na Duniya. Ballon d’Or ce kyauta mafi girma ta shekara-shekara ga ’yan wasan kwalllon kafa saboda bajintar da ya nuna ga ƙungiyarsa da ƙasarsa. Gasar ta bana ta kasance mafi zafi duba da yadda alkaluma ke nuna irin zakakurancin kowanne daga manyan ’yan wasan da ake hasashen za su iya lashe kambin. An rufe sansanin NYSC da kasuwanni saboda rashin...
Kwamandan sojan Iran Amir Hatami wanda ya gana da kwamandan dakarun kare juyin musulunci Janar Muhammad Pakpour saboda tunawa da makon hadin kai, ya kara da cewa; Bayan cin nasarar juyin musulunci a Iran, Iran da al’ummarta sun fara aiki tukuru domin kare cikakken ‘yancin Iran.” Har ila yau, Amir Hatami ya yi ishara da hadin gwiwa a tsakanin sojojin da dakarun kare juyin juya halin yana a matsayin ginshikin tsaron kasar Iran, kuma wata kofa ta kai wa mataki na koli na tsaro. A gefe daya dakarun kare juyin musulunci ( irgc) sun jaddada matsayarsu ta ci gaba da zama cikin Shirin fuskantar abokan gaba. A cikin wata sanarwa da suka fitar a farkon makon tsaro mai alfarma, na...
Shugaban kasar Korea Ta Arewa Kim jung Un ne ya sanar da cewa kasarsa ta kera wani sabon makami na sirri, kuma ta samu ci gaba sosai a fagen nazari da binciken kayan tsaro. Shugaban kasar ta Korea Ta Arewa Kim Jun Ung wanda ya yi Magana da kamfanin dillancin labarun kasar ya kara da cewa; Sabbin makaman da su ka kera za su taimaka matuka wajen karfafa sojojin kasar.” Haka nan kuma ya ce, kasar Korea ta Arewa ta kuma karfafa sojojinta na ruwa ta hanyar kara samar da jiragen ruwa na yaki masu ninkaya a karkashin ruwa.” Kamfanin dillancin labarun Korea Ta Arewa ya sanar da cewa, a ranar Juma’ar da ta gabata ne shugaban kasar Kim Jun...