2025-09-17@21:54:44 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7236

«kasashe masu tasowa»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wani sabon salo da wannan zamani ya zo da shi shi ne auren gwaji, inda mata kan yi shiga gidan miji da niyyar fita bayan wani lokaci.   Sai dai manazarta suna cewa hakan ka iya haddasa matsalolin musamman idan mazajen auren ba su san da wannan shirin ba. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Da Mutane Zasu Bi Wajen Neman Diyya DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu mata suke yin auren gwaji. Domin sauke shirin, latsa nan
    Tun kafin zaɓen 2023 PDP ke fama da rikici, matsalar da ake ganin ta taimaka wajen hana jam’iyyar samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa ta dala biliyan 2.5 da gwamnatin kasar Habasha, domin gina daya daga cikin manyan masana’antun  takin zamani a duniya a garin Gode. An rattaba hannu kan yarjejeniyar tsakanin rukunin Dangote da kamfanin zuba jari na Habasha (EIH), wanda zai baiwa rukunin Dangote damar rike hannun jarin kashi 60 cikin dari, yayin da EIH zai rike kashi 40 cikin dari. Ana has ashen cewa idan an kammala aikin,  zai kasance cikin  manyan masana’antun samar da takin zamani guda biyar na duniya, wanda zai rika samar da takin zamani ton miliyan uku a kowace shekara. A cewar EIH, za a kammala aikin a cikin...
    Rundunar sojin Yaman ta sanar da cewa ta kaddamar ad wasu manyan hare-hare a kan wasu mihimamn wurare na tsaro da tattalin arzikin Haramtacciyar Kasar Isra’ila. Tun a ranar Litinin da ta gabata ta sanar da cewa za ta aiwatar da ayyukan soji biyar masu girma a kan wasu muhimman wurare da suka hada da hedikwatar tsaro,  tashar wutar lantarki ta Hadera, filin sauka da tashin jiragen sama na Lod da ke Jaffa ko Tel Aviv, da kuma tashar jiragen ruwa ta Ashdod, da kuma tashr jiragen ruwa ta MSC ABY da ke arewacin tekun Bahar Maliya. An gudanar da ayyukan ta hanyar amfani da jirage marasa matuka da dama da kuma makamai masu linzami. Kakakin Rundunar Sojojin Yaman Birgediya...
    Hukumar kwallon kafa ta Masar ta yi watsi da shawarar buga wasan sada zumunci da Zambia saboda masu horar da ‘yan wasan Zambia sun hada da ‘yan Isra’ila, kamar yadda kafafen yada labaran Masar suka rawaito a wannan Laraba. Wannan rashin amincewar ba a kai ga kai ga babban kocinta Avram Grant ba, wanda a baya ya taba horar da Ghana, ko mataimakinsa Eyal Lachman, sai dai a fagen siyasar da suke wakilta. Rahotanni sun bayyana cewa, an shirya wasan ne domin hutun kasa da kasa na watan Nuwamba, wanda zai gudana bayan kammala wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin  Afirka, kuma wasan share fage ne gabanin gasar cin kofin nahiyar Afirka, da za a yi a Morocco daga...
    Alal hakika, akidar mulkin danniya akida ce wadda take tarnaki ga ci gaba da wayewa ta bil Adam, kuma yaduwar wannan akida barazana ce ga daukacin bil Adam. Don haka yaki da wannan akida ta bazu kamar wutar daji tsakanin sama da kasashe 80 daga nahiyoyin Asia, Turai, Afirka da Oceania. An kuwa tafka asarar rayukan da za su kai sama da miliyan 100, wadanda daga cikinsu sojoji da fararen hula miliyan 35 ne Sin ta yi asara. Kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen yaki da wannan mummunar akida ta mulkin danniya, yayin da ta shiga cikin sahun sojojin sauran kasashe a yakin duniya na biyu. Kafada da kafada suka yi gumurzu wajen murkushe maharan kasashen Japan, Jamus da...
      Kun tuna jita-jitar ake yaɗawa game wai arzikin sa ya kai Naira Tiriliyan 9? Kuma Mutane da yawa sun gaskata.   A matsayin sa na gwamnan jihar Zamfara, ina da abubuwa da yawa da zan iya cewa game da Dauda Lawal, musamman da yake ina cikin makusantan sa, mai yin aiki kafaɗa da kafaɗa da shi a matsayin kakakin sa sama da shekaru biyu.   A shekarun baya na yi rubuce-rubuce da dama a kan Dauda Lawal, ma’aikacin banki kuma mai taimakon al’umma.   Amma, yayin da ya cika shekara 60 a yau, zan so in fitar da wasu ’yan muhimman abubuwa da Dauda Lawal ya yi a matsayin gwamna, wanda ke mayar da Jihar Zamfara daga kufai da...
    Babban sakataren MDD António Guterres, wanda ya halarci taron kolin kungiyar hadin gwiwar Shanghai wato SCO da aka gudanar a birnin Tianjin dake kasar Sin, ya bayyana cewa, Sin ta taka rawar gani sosai wajen cimma nasarar yakin duniya na biyu. Kuma gudummawar da Sin ta bayar ita ce mabudin nasarar da kawancen kasashen duniya suka samu a yakin duniya na biyu.   Bugu da kari, Guterres ya jaddada ta hanyar nuna batutuwan tarihi cewa, babbar mamayar da Japan ta yi wa Sin ita ce farkon yakin duniya na biyu na gaskiya. Guterres ya yi imanin cewa, tsayin daka da kasar Sin ta yi wajen yin tir da hare-haren Japan, ya taka muhimmiyar rawa a tsawon shekaru da dama, tare...
    A ranar Litinin 8 ga Satumba, 2025 ne gwamnatin jihar Kano za ta kaddamar da sabuwar majalisar Shurah, karkashin jagorancin gwamna Abba Kabiru Yusuf. Za a gudanar da bikin kaddamarwar ne a gidan gwamnati dake Kano. Hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar a 2 ga Satumba, 2025. Xi: Alakar Sin Da Rasha Ta Zama Misali Na Kyakkyawar Dangantakar Manyan Kasashe Sabuwar Ajandar Kasar Sin Ta Inganta Magance Gibin Kudi A Duniya Kafa majalisar Shurah na zuwa ne domin karfafa gudanar da mulki cikin hadin kai, da bayyana gaskiya wajen yanke shawara. Ana sa ran majalisar za ta kasance kamar wata kungiya mai ba da...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta cafke wani ɗan bindiga da ake zargin ɗan ƙungiyar Lukurawa ne tare da shanu goma da ya sato, a wani samame da aka kai kasuwar shanu ta Bachaka. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Nafi’u Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata. Gwamnatin Kano za ta sake yi wa zawarawa da ’yan mata auren gata Zabarmawa Sun Bayyana Dalilin Bai wa Gwamnan Kebbi Sarautar Garkuwa A cewarsa, “bayan samun sahihan bayanan sirri, an kama wani Salihu Umar, mai shekaru 42, ɗan asalin Dogon Dutse a Jamhuriyar Nijar, wanda ya shiga kasuwar shanu ta Bachaka da shanu 10 da ya sace wa wani Usman...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da ajandar mulkin duniya a taron “SCO+” na birnin Tianjin a jiya Litinin. Wannan ajanda, ta nuna hanyar da za a bi, tare da ba da jagoranci ga aiwatar da ayyukan gina tsarin mulkin duniya mai adalci da dacewa, a karkashin yanayin duniya mai fuskantar manyan sauye-sauye, da kuma jagorancin cike gibin kudi na samar da ci gaba da bunkasa. Sabuwar ajandar mulkin duniya da Xi Jinping ya gabatar, ta yi magana kai tsaye kan wasu muhimman abubuwa guda uku a tsarin jagorancin duniya, wato rashin daidaiton iko, da rarrabuwar ra’ayoyi, da kuma rashin daukar matakai. Ajandar, wadda ta fitar da wasu ka’idoji guda biyar, wato tabbatar da daidaiton ikon mulkin kasa, da...
    Gwamnatin Kano ta sanar da cewa tana shirye-shiryen gudanar da auren zawarawa da ’yan mata, wanda ya zarce na baya da ta yi. Babban Kwamanda Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne bayyana hakan a yayin ziyarar gaisuwa da ya kai wa Fadar Sarkin Rano a ranar Litinin. Zabarmawa Sun Bayyana Dalilin Bai wa Gwamnan Kebbi Sarautar Garkuwa Cibiyar Ayyukan Daular Usmaniyya za ta karrama Sarkin Zazzau Sheikh Daurawa ya ce a wannan karon angwaye da amaren za su mori gwaggwaban tanadi na musamman daga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf. Ana iya tuna cewa, a watan Oktoban 2023 ne Gwamnatin Kano ta ɗaura auren mata 1,800 da angwayensu 1,800 wanda ta ɗauki watanni tana shiryawa. Tun bayan hawansa mulki...
    Gwamnatin Kano ta sanar da cewa tana shirye-shiryen gudanar wa auren zawarawa da ’yan mata, wanda ya zarce na baya da ta yi. Babban Kwamanda Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne bayyana hakan a yayin ziyarar gaisuwa da ya kai wa Fadar Sarkin Rano a ranar Litinin. Zabarmawa Sun Bayyana Dalilin Bai wa Gwamnan Kebbi Sarautar Garkuwa Cibiyar Ayyukan Daular Usmaniyya za ta karrama Sarkin Zazzau Sheikh Daurawa ya ce a wannan karon angwaye da amaren za su mori gwaggwaban tanadi na musamman daga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf. Ana iya tuna cewa, a watan Oktoban 2023 ne Gwamnatin Kano ta ɗaura auren mata 1,800 da angwayensu 1,800 wanda ta ɗauki watanni tana shiryawa. Tun bayan hawansa mulki...
    Kwace makaman kungiyar Hizbullah… Fadan ne da ba zai yi nasara, inda daga karshe zai zame siyasa bayan gazawar nuna karfi Ana ci gaba da tabka muhawara kan batun neman kwance damarar kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah a kasar Labanon, a daidai lokacin da ‘yan sahayoniya da Amurka ke kokarin cimma wannan buri a siyasance bayan gazawarsu ta hanyar nuna karfin soji. Shugaban kasar Labanon Joseph Aoun ya yi imanin cewa; Kwance damarar kungiyar Hizbullahi ya dogara ne da samar da sharuddan da suka dace. A nasa bangaren, shugaban majalisar dokokin kasar Nabih Berri ya yi watsi da duk wata barazana, yana mai kallon makaman ‘yan gwagwarmayar Hizbullahi a matsayin abin daukaka da alfahari. A halin da ake ciki kuma,...
    Majiyar ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da cewa: Falasdinawa 76 ne suka yi shahada yayin da wasu 281 na daban suka jikkata a Gaza cikin sa’o’i 24 Ma’aikatar lafiya a zirin Gaza ta sanar da cewa, adadin mutanen da suka yi shahada sakamakon yakin kisan kiyashi da sojojin mamayar Isra’ila suke ci gaba da yi tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023 ya karu zuwa shahidai 63,633, tare da jikkatan wasu 160,914. Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu a Gaza ta bayyana a cikin rahotonta na kididdiga na yau da kullun cewa: Falasdinawa 76 ne suka yi shahada yayin da wasu 281 suka jikkata a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, a cewar alkalumman baya-bayan nan da ma’aikatar ta...
    Kungiyar Zabarmawa ta Najeriya ta karrama Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, da sarautar Garkuwan Zabarmawa, saboda gudummawar da ya bayar wajen ci gaban al’umma da tallafa wa ƙungiya. Da yake bayyana dalilin bai wa gwamnan sarautar a madadin shugaban ƙungiyar na ƙasa, Sarkin Zabarmawa, Alhaji Bello Zabarmawa, ya ce: “An ba da wannan sarauta ne domin nuna gamsuwa da irin ci gaban da Gwamna Idris ya kawo wa talakawa. Cibiyar Ayyukan Daular Usmaniyya za ta karrama Sarkin Zazzau Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da sabon manhajin karatun firamare da sakandire “Mun tuntubi mutane da yawa kafin a zaɓe shi, kuma kowa ya tabbatar cewa shi ya cancanta.” A nasa jawabin, Sarkin Zabarmawa na Jihar Kebbi, wanda kuma shi ne tsohon...
    Cibiyar Ayyukan Daular Usmaniyya da ke Sakkwato ta bayyana aniyar karrama Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli CFR, da lambar yabo ta musamman saboda rawar da ta ce yana takawa wajen ƙarfafa haɗin kai da raya zumunci tsakanin ’ya’yan Daular Usmaniyya. A cikin sanarwar da cibiyar ta fitar mai ɗauke da sa hannun shugabanta kuma Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ta ce za a karrama Sarkin tare da wasu fitattun ’yan Najeriya guda shida a babban taron shekara-shekara da cibiyar ke shiryawa. Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da sabon manhajin karatun firamare da sakandire Manchester City ta ɗauki golan PSG, Gianluigi Donnarumma Taron zai gudana ne a ranar Alhamis, 11 ga watan Satumba, 2025, a Cibiyar Karatun Alƙur’ani...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da sabon manhajin karatu na makarantun firamare zuwa sakandire wanda zai fara aiki a sabon zangon karatu na bana da za a soma a watan Satumbar nan. Wannan na zuwa ne bayan kammala nazari mai zurfi kan manhajoji karatu a fannin ilimi a matakin farko da na manyan makarantun sakandire da kuma fannin fasaha. Manchester City ta ɗauki golan PSG, Gianluigi Donnarumma Ndume ya koka kan sabbin hare-haren Boko Haram a Borno Gwamnatin ta ce ta ɗauki wannan matakin ne da nufin rage nauyin karatu kan ɗaliban da kuma inganta tsarin koyarwa a faɗin ƙasar. Ƙaramar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Sa’id Ahmad, ce ta bayyana hakan a madadin Ministan Ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa a ƙarshen...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City ta ɗauki mai tsaron ragar PSG, Gianluigi Donnarumma ɗan asalin ƙasar Italiya. Donnarumma wanda tsohon mai tsaron ragar AC Milan ne ya sanya hannu kan kwantiragin shekara biyar a Etihad, inda zai zai ci gaba da tsare ragar ƙungiyar zuwa kakar 2030. Ndume ya koka kan sabbin hare-haren Boko Haram a Borno Kemi Badenoch ta shiga tsaka mai wuya kan karatun likitanci Golan zai riƙa amfani da riga mai lamba 99 domin ranar haihuwarsa ta 1999, kamar yadda ƙungiyar ta sanar. A jawabin da ya yi dangane da komawa ƙungiyar, Donnarumma ya ce yana cike da farin ciki da jin daɗi. “Na koma ƙungiya da ke cike da zaratan ’yan wasa, sannan kuma ƙungiya...
    Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi na Najeriya (ALGON), ta yi kira ga Ƙungiyar ’Yan Jarida Masu Rubuta Labaran Wasanni (SWAN) da ta ƙara mayar da hankali wajen yada labarai kan wasannin gargajiya, irin su langa da kokawa. Shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe wanda shi ne shugaban ALGON reshen Gombe, Barista Sani Ahmad Haruna, ya bayyana haka ne a lokacin da shugabannin SWAN na jihar suka kai masa ziyarar ban girma, inda suka nemi goyon bayansa kan babban taron bita da ƙungiyar ke shirin gudanarwa. A cewarsa, ƙara bayar da muhimmanci ga wasannin gargajiya zai taimaka wajen jan hankalin matasa zuwa harkokin ci-gaban rayuwa, tare da rage yawan fadawa cikin laifuka da shan miyagun ƙwayoyi. Ya kuma shawarci SWAN da ta ƙulla alaƙa...
    Hukumar bada agaji ta MDD mai kula da Falasdinawa UNRWA ta bayyana cewa yara fiye da 660,000 a gaza aka haramtawa karatu a wannan shekarar saboda yakin da HKI ta dorawa yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto , Philippe Lazzarini shugaban hukumar UNRWA yana fadar haka a wani sakon da ya tura a shafinsa na X a ranar Litinin. Ya kuma kara da cewa, ba yadda wadannan yara zasu je makaranta saboda yakin, babu makarantun da zasu shiga don HKI ta rusa mafi yawan makarantu a gaza, sannan ta kashe da dama daga cikin malaman makarantun a yankin. Lazzarini ya yake nanata bukatar a tsagaita budewa juna wuta saboda yara a gaza su sami damar zuwa...
    Ta ce cikin ƙasa da shekara biyu, Kaduna ta fito daga durƙushewar tsari zuwa zama jihar da ake ganin tsari. Haka kuma, gwamnatin ta yi zargin cewa El-Rufai ya ƙara ƙoƙarin tayar da rikici bayan abokan siyarsarsa sun sha kaye a zaɓen cike gurbi na ranar 16 ga watan Agusta. Ta ce sakamakon ya nuna rashin amincewa da salon mulkin El-Rufai na “rabuwar kai da wariya” tare da amincewa da salon mulkin Gwamna Uba Sani. An yi ƙoƙarin jin ta bakin El-Rufai kan waɗannan zarge-zarge, amma ba a iya samun shi ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
    Al’ummar kurame sun koka bisa matsalolin da suke fuskanta a fannin kiwon lafiya, sakamakon rashin masu yi musu fassara a asibitoci a Jihar Yobe. Malam Kolo Abba, Shugaban Ƙungiyar Kurame a Ƙaramar Hukumar Damaturu, ya ce kurame majinyatan sukan koƙarta wajen fahimtar ƙa’idojin likitoci da na kiwon lafiya, amma duk da hakan suna cikin haɗari. Abba ya yi wannan kira ne ta bakin wani mai fassara a taron masu ruwa da tsaki kan shirye-shiryen tattaunawa kan kasafin kuɗin shekarar 2026 da aka shirya don inganta aiki. Ya ce rashin masu fassara a asibitoci alama ce ta rashin kula da kurame a jihar, don haka akwai buƙatar ɗaukar matakan gaggawa don tabbatar da samun damar gudanar da ayyukan yau da kullum...
    ’Yar Najeriya kuma Shugabar Jam’iyyar Conservative a Birtaniya, Kemi Badenoch, ta shiga tsaka mai wuya kan iƙirarinta na cewa Jami’ar Stanford ta ba ta gurbin karatun horon shiga likitanci bisa rangwamen kuɗi tun tana ’yar shekara 16. An fara sanya alamar tambaya a kan iƙirarinta ne bayan da wani tsohon jami’in kula da ɗaukar ɗalibai a jami’ar mai suna Jon Reider, ya musanta iƙirarin na Kemi Badenoch, wadda ta yi kaurin suna wajen sukar ƙasarta ta haihuwa. Kemi Badenoch ta yi iƙirari cewa ta samu gurbin ƙaramin tallafin kuɗi daga Jami’ar Stanford, amma rashin kuɗin iyayenta ya hana ta amfani da damar. Sai dai Jon Reider, wanda a lokacin yake kula da ɗalibai daga ƙasashen waje da tallafin karatu a Stanford,...
    An gudanar da janazar manyan jami’an gwamnatin kasar Yemen 9 da suka yi shahada a wani harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kaddamar a kansu,a  lokacin da suke gudanar da wani zama na gwamnati, domin bin kadun ayyukan ma’aikatun da suke jagoranta. Dubban daruruwan mutane ne dai suka halarci janazar wadda ta gudana a birnin San’a fadar mulkin kasar ta Yemen a jiya, inda aka gabatar da jawabai daban-daban, da ke kara tabbatar da aniyar al’ummar kasar Yemen wajen ci gaba da bin tafarkin wadanda suka yi shahada, domin mara baya ga al’ummar Gaza mara kariya. A nasa bangaren Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyed Abdul Malik al-Houthi ya yi kakkausar suka kan wannan hari na wuce gona da...
    shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana cewa, Aikewa da sojojin ruwan Amurka a yankin Caribbean itace barazana mafi girma ga al’ummomin yankin a cikin wannan karni. Da yake magana a wani taron manema labarai, Maduro ya ce an jibge jiragen ruwan sojan Amurka guda 8 dauke da makamai masu linzami 1,200 da kuma na nukiliya a gabar tekun Venezuela. Inda Ya kira wannan matakin da cewa shi ne mafi muni da Amurka ta dauka a tsawon shkaru a yankin Caribbean. Maduro ya zargi Washington da aiwatar da manufar matsin lamba ta soja a kan Caracas, wanda ya tilasta wa Venezuela ayyana cikakken shirin tsaron kasa. “Venezuela kasa ce mai zaman lafiya, amma al’ummarta mayaka ne kuma ba za su...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce shi da takwarorinsa na Rasha da China sun aike da wasika ga Majalisar Dinkin Duniya, inda suka yi watsi da matakin da Birtaniya da Faransa da Jamus suka dauka a baya-bayan nan na yunkurin maido da takunkumin kasa da kasa kan Iran a matsayin mataki marar ma’ana. Abbas Araghchi ya bayyana hakan ne a cikin wani sakon da ya wallafa a jiya a Shafin X, kwanaki hudu bayan da kasashen Turai wadanda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar nukiliya ta 2015 suka sanar da kwamitin sulhu na MDD cewa, sun yi amfani da tsarin dawo da dukkanin  takunkumin MDD a kan Iran. Ya ce, a cikin wasikar hadin gwiwa da suka aike wa...
    Ya ce wannan dabara, wadda ta yi kama da tsarin ‘community policing’, ta tabbatar da inganci wajen rage laifuka a jihar. A cikin watan Agusta kaɗai, ’yansanda sun ƙwato fakiti 485 na ganyen tabar wiwi, kwalaye 211 na wasu kayan maye, kwalabe 257 na maganin kashe ɓeraye, da kuma ƙwayoyi 21 na Exol. Sauran kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da wayoyi 59, POS guda uku, katin cirar kuɗi na banki 17, na’urar MP3 guda uku, tare da bindigogi, harsasai da sauran makamai masu hatsari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
    Tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami ya tsallake rijiya da baya a garin Birnin Kebbi yayin da wasu matasa suka kai wa tawagarsa hari. Abubakar Malami da tawagarsa, wasu ’yan bangar siyasa sun tare su, a unguwar GRA, inda suka yi amfani da sanduna da addun da sanduna suka farfasa motocin Malami tare da jikkata mutanensa, Kodayake babu asarar rai. Bayan dawowar tsohon ministan a zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari,  gida ya yi zargin siyasa ce ta a da aka kai masa harin, yana mai jaddada cewa, harkar siyasarsa babu gudu babu ja da baya. “Shari’a ta tanadi ka kare kai, in aka kawo maka hari amma kai kar ka kai wa kowa hari, maganar siyasa ba gudu ba ja...
    A yau Litinin shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya iso birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin domin halartar bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin mamayar dakarun Japan, da yakin kin tafarkin murdiyya na duniya. Shugaba Mnangagwa ya sha ziyartar kasar Sin, inda a shekarar da ta gabata ma ya zo birnin Beijing domin halartar taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC tare da gudanar da ziyarar aiki a kasar. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jami’an Hukumar Sibil Difens (NSCDC) sun cafke wani mutum mai shekaru 48, Ibrahim Haruna, tare da ɗansa mai shekaru 15, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 13 fyaɗe a unguwar Jekadafari da ke Jihar Gombe. Wakilinmu ya ruwaito cewa an gabatar da waɗanda ake zargin ne a hedikwatar hukumar a ranar Litinin. An kama ɗan shekara 60 kan yi wa mai shekara 24 fyaɗe Simon Ekpa: An ɗaure ɗan Nijeriya kan laifin ta’addanci a Finland Mai magana da yawun hukumar a jihar, SC Buhari Sa’ad, ya ce bisa binciken da suka gudanar, uban da ɗan sun aikata laifin ne a lokuta daban-daban. A cewarsa, Ibrahim Haruna wanda tela ne ya yi aika-aika ne a shagonsa na ɗinki, yayin...
    Ya bayyana cewa, matan sun fito ne daga jihohin Kano, Katsina, Borno, Jigawa, da Zamfara, inda aka yi musu alkawuran samun ingantattun ayyukan yi a kasar ta Saudiyya.   An kama daya daga cikin wadanda ake zargi da safarar matan mai suna Mohammed Saleh mai shekaru 45 da haihuwa.   Babale ya ce, ana ci gaba da kokarin damke wasu da ake zargi da hannu wajen safarar mutanen. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran da gaske take yi wajen kare muradunta daga bukatun Turai Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi hira da kamfanin dillancin labaran kasar China Xinhua, inda ya tattauna kan taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO), da yarjejeniyar dogon lokaci da kasar China, da kuma batun makamashin nukiliya na kasar Iran. Baqa’i ya bayyana cewa: Yarjejeniyar shekaru 25 tsakanin Iran da China ta fara aiki kuma tana ci gaba. Ya kuma kara da cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tana da kyau kuma tana ci gaba, yana mai jaddada cewa: Iran na daukar muhimmanci sosai kan dangantakarta da China, kuma ziyarar shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian za...
    Adadin wadanda suka mutu a girgizar kasar Afghanistan ya haura 800, yayin da ake sa tsammanin karuwar wadanda suka jikkata Hukumomin kasar Afganistan sun sanar da cewa: Adadin mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasar da ta afku a gabashin Afghanistan ya haura 800, yayin da sama da 1,500 suka jikkata, adadin da ake sa ran zai karu. Da sanyin safiyar yau Litinin ne, kamfanin dillancin labarai na RTA ya ruwaito hukumomin lafiya na kasar na cewa, suna ci gaba da kokarin gano hakikanin adadin wadanda suka mutu, yayin da suke ci gaba da kokarin isa wasu yankunan da lamarin ya shafa. Ma’aikatar lafiya ta kasar ta sanar da cewa, Girgizar kasar ta lalata kauyuka uku a gundumar Konar gaba...
    Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, wanda ya shigo kasar Sin don halartar taron koli na kungiyar hadin-kai ta Shanghai wato SCO na bana, ya zanta da dan jaridan babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a birnin Tianjin, inda ya ce, Xi Jinping shugaban kasa ne mai sanin ya kamata wajen tsara manyan tsare-tsare. Guterres ya ce, akwai misalai da dama da suke iya tabbatar da haka. Alal misali, shugaba Xi ya taba sanar da burin gina na’urorin samar da wutar lantarki bisa makamashin da ake iya sabuntawa, wadanda karfinsu ya zarce kilowatt biliyan 1.2 zuwa shekarar 2030 a kasar Sin, wanda aka riga aka cimma shi. Kazalika, ya yi alkawarin cimma nasarar kaiwa...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta kama wani dattijo mai shekaru 60, Ajayi Femi, bisa zargin yi wa wata budurwa mai shekaru 24 fyaɗe. Mai magana da yawun rundunar, CSP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Lahadi. An kashe mutum 5 an sace limamai da hakimi a Sakkwato Simon Ekpa: An ɗaure ɗan Nijeriya kan laifin ta’addanci a Finland Ya bayyana cewa an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu ta hannun sashen da ke bincike cin zarafin mata na rundunar da ke Ikeja. A cewar Hundeyin, lamarin ya faru ne a ranar 22 ga watan Agusta, 2025, inda ƙanwar wacce abin ya faru da ita ta kai rahoto ofishin ‘yan sanda na Meiran, daga nan...
    A cewar sa, yankin Arewa-maso-yamma ya samu kaso mafi girma na ayyuka da ya kai naira tiriliyan 5.97, Kudu-maso-kudu ya samu naira tiriliyan 2.41, Arewa-ta-tsakiya naira tiriliyan 1.13, Kudu-maso-gabas naira biliyan 407, Arewa-maso-gabas naira biliyan 400, yayin da Kudu-maso-yamma (ban da Legas) ya samu naira biliyan 604.   Idris ya ce dukkan waɗannan yankuna suna amfana da manyan hanyoyi, layukan dogo da kuma hukumomin raya yankuna.   Ministan ya ce daga cikin muhimman ayyukan da ake aiwatarwa akwai Titin Bakin Teku na Legas zuwa Kalaba, da Babban Titin Sakkwato zuwa Badagiri, da gyaran layin dogo daga Fatakwal zuwa Maiduguri, da kuma Hanyar Gadar Neja ta 2.   Haka kuma, gwamnati ta samar da fiye da naira biliyan 250 don ayyukan...
    Wata kotu a ƙasar Finland ta yanke wa ɗan Najeriya mai rajin ɓallewar ƙasar Biyafara, Simon Ekpa, hukuncin ɗaurin shekara shida a gidan yari bisa laifukan da suka shafi ta’addanci, zamba da karya doka. Kotun ta tabbatar da cewa Ekpa ya aikata laifuka da suka haɗa da ƙoƙarin hargitsa jama’a da nufin ta’addanci da kuma shiga cikin ayyukan ƙungiyoyin masu ɗaukar makami. An kashe mutum 5 an sace limamai da hakimi a Sakkwato Gwamnan Neja ya rushe kwamishinoninsa Haka kuma, kotun ta ce an same shi da laifin zamba ta haraji da keta wasu dokokin Finland. A cewar kotun, daga watan Agusta 2021 zuwa Nuwamba 2024, Ekpa ya yi amfani da kafafen sada zumunta wajen yaɗa shirye-shiryen neman ɓallewar Biyafara...
    Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana ƙwarin gwuiwar cewa Shugaba Bola Tinubu zai sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027, inda ya ce ya shirya yin “alwashi” akan wannan nasara. Wike ya yi wannan bayani ne a yayin wata tattaunawa da manema labarai a Abuja, yana mai ƙaryata hasashen tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, wanda ya ce Tinubu ba zai yi nasara ba a zaɓen mai zuwa. Wike ya ce, “Ina da tabbacin Shugaba Bola Tinubu zai yi nasara a zaben 2027. Na ji wani yana cewa zai zo na uku, ban san irin lissafin da ya yi ba. Idan zai zo na uku, to waye zai zama na farko da na biyu?” Wike...
    Gwamna Mohammed Umaru Bago na Jihar Neja ya rushe majalisar kwamishinoninsa. Sakataren Yaɗa Labarai na gwamnan, Bologi Ibrahim, ya ce gwamnan ya sanar da rushe majalisar kwamishinoninsa ne a yayin taron Majalisar Zartarwa ta jihar a safiyar Litinin ɗin nan. Ya kuma yaba musu bisa gudunmawar da suka bayar wajen kawo ci-gaba mai ma’ana a jihar tare da yi musu fatan alheri. Sai dai kuma gwamnan ya sake nada sakataren gwamnatin da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati da mataimakinsa a da wasu jami’ai a kan muƙamansu
    Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan harkokin Tsaro, Nuhu Ribaɗu, ya musanta zargin da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi cewa Gwamnatin Shugaba Tinubu tana biyan kuɗaɗen fansa ga ’yan bindiga don sako waɗanda suka sace. El-Rufai ya yi wannan zargi ne a wani shirin talabijin na Channels, inda ya ce matsalar tsaro a Arewacin Najeriya ta ƙara ƙamari, duk da cewa gwamnati ta yi ƙoƙarin rage yadda ake rahoto a kafafen watsa labarai. “Har yanzu ina kan bakata cewa waɗannan ’yan bindiga a halaka su baki ɗaya, ba a rika lallashi ko yin sulhu da masu ta’addanci ba. Wannan bai taba aiki a ko’ina ba,” in ji shi a yayin tattaunawar. Martanin ONSA A martanin da aka fitar da...
    Gwamnan Neja, Mohammed Umaru Bago, ya sallami dukkan mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar. Gwamnan ya bayyana labari sallamar ta su ne a taron majalisar da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Minna, babban birnin jihar, da safiyar yau Litinin 1 ga Satumbar 2025 Girgizar Ƙasa Ta Kashe Sama da Mutune 600 A Afghanistan Daje Na Jam’iyyar APC Ya Lashe Zaɓen Majalisar Dokokin Jihar Neja Ya gode wa mambobin majalisar bisa gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban jihar, tare da yi musu fatan alheri a duk inda makomar aiki ta kai su. Sai dai, gwamnan ya bayyana cewa ya bar Sakataren Gwamnatin Jihar, da Shugaban Ma’aikatansa da kuma Mataimakinsa da wasu manyan jami’an ofishinsa a muƙamansu. Daga kanmu,...
    ’Yan gudun hijira daga sama da kauyukka 10 a Ƙaramar Hukumar Shagari ta Jihar Sakkwato sun rufe hanyar Shagari zuwa Sakkwato domin nuna fushinsu ga gwamnati kan azabar da suke sha hannun ’yan bindiga a yankinsu. Mata da mazan sun buƙaci daukin gwamnati kan abin da ke addabar su, sun rufe babbar hanyar da ta hada jihohin Sakkwato da Kebbi da Neja. A yayin zanga-zangar a ranar Lahadi, wani daga ƙauyen Rinaye ya shaida wa Aminiya cewa, “Rashin kulawar da gwamnati ta nuna mana ya sa muka rufe hanyar mota don janyo hankalinta da jami’an tsaro gare mu a ɗauki matakin korar mana ’yan bindigar su bar yankinmu. “Yau (Lahadi) sun jera kwana uku kullum sai sun zo sun sace...
    Ana jin tsaron daruruwan mutane ne suka rasa ransa sanadiyyar girgizan kasa mai karfin ma’aunin richter 6 da ta fadawa yankin tsaunuka na kasar Afganistan dake kan iyaka da kasar Pakisatan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran rauters na cewa an jirage masu saukar ungulu suna sauke wadanda suka ji rauni, sannan wasu suna taimaka masu suna daukansu zuwa cikin motocin daukar marasa lafiya. Majiyar kasar ta bayyana cewa da misalign tsakiyar dare ne girgizan kasar ta auku, sannan cibiyar kula da gargizan kasa ta kasar Jamus ta bayyana cewa karfin girgizan kasar ya kasar karfin ma’aunin richter 6.2. Dangane da wannan labarin kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar...
    A safiyar yau litininn ce aka fara jan’izar shugaban gwamnatin kasar Lemen Ahmad Ghalib Arrahwi da ministocinsa da suka yi shahada a hareharen da HKI ta kai kansu a lokacinda suke taro a birnin San’a babban birnin kasar. Tashar talabijin ta al-amayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa an gudanar da taron janaizar ne a ‘dandalin 70 dake tsakiyar birnin San’a babban birnin kasar.   Labarin ya bayyana cewa da farko an kai gawakin jam’an gwamnatin ne zuwa masallacin Jama’a, kuma sun hada da Firay ministan kasar Ahmad Ghalin da ministan watsa labarai Hashin sharafuddeen, ministan sharia, Mai sharia Mujahid Ahmad Abdullahi, ministan tattalin arziki da masana’antu Mu’in Almuhakiri ministan wutan lantarki da ruwa Ali saif Hassan Assami’ii, ministan noma...
    Hukumomin Afghanistan sun bayyana cewa adadin waɗanda suka mutu a girgizar ƙasa da ta afku a gabashin ƙasar ya haura mutane 610, yayin da aka samu ƙarin mutane 12 da suka mutu a Nangarhar, abin da ya kai jimillar mutuwar zuwa 622. Ma’aikatar cikin gida ta ƙasar ta ce sama da mutum 1,500 ne suka jikkata a lamarin. Rahotanni sun nuna cewa asibitoci da dama, musamman na lardin Asadabad, sun cika da marasa lafiya. Shugaban asibitin, Dr Muladad, ya bayyana cewa suna karɓar marasa lafiya daga girgizar ƙasar “a duk bayan minti biyar,” kuma mutane 188 cikin sa’o’i kaɗan aka kawo asibitin, ciki har da mata da yara. Ya Zama Wajibi Amurka Ta Sauke Nauyin Dake Wuyan Ta Game Da...
    Kungiyar Liverpool ta cimma yarjejeniya da Newcastle domin ɗaukar ɗan wasan gaba na ƙasar Sweden, Alexander Isak, akan zunzurutun kuɗi fam miliyan 125, wanda zai sanya shi zama ɗan wasa mafi tsada a tarihin gasar Firimiyar Ingila. Rahotanni sun bayyana cewa Isak zai yi gwajin lafiya yau Litinin tare da zakarun Firimiya, kafin a kammala sanarwar a hukumance da misalin ƙarfe 7 na yamma. Al Hilal Za Ta Biya Yuro Miliyan 53 Don Ɗaukar Nunez Daga Liverpool Liverpool Za Ta Kece Raini Da Bournemouth, Arsena Za Ta Bakunci Man Utd A Wasan Mako Na Firimiya Ta Baɗi A farkon tattaunawar, Newcastle ta dage cewa sai Liverpool ta biya fam miliyan 130 kafin ta sayar da ɗan wasan, amma daga bisani...
    Yanzu an fi wata biyu da Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da taraktoci 2,000 da sauran kayan aikin gona domin haɓaka harkar noma, amma manoma sun ce har yanzu ba a raba musu su ba, abin da ke iya jawo asarar daminar bana. Ganin cewa a halin daminar tana gab da ƙarewa, manoma suna ganin lokaci ya riga ya ƙure. Ƙungiyoyin manoma sun soki jinkirin, suna gargaɗin cewa ana iya fuskantar ƙarancin abinci idan ba a hanzarta ba. Da yake ƙorafi kan lamarin, Shugaban Ƙungiyar Manoma ta Najeriya (AFAN), Injiniya Kabiru Ibrahim ya ce, “Ina rokon gwamnati ta hanzarta. Wannan shekarar ce ta gwaji wajen tabbatar da tsaron abinci.” Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Ƙungiyar Gwamnonin jihohin Arewa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yadda Gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara, da magoya bayansa suka kaurace wa zaben kananan hukumomin jihar, da yadda APC ta lashe kujeru 20 a cikin 23 sun haifar da muhawara a tsakanin ’yan Najeriya.   Shin wannan sakamako alama ce ta yarjejeniyar sulhu da aka cimma a tsakanin Gwamna Fubara da Minsitan Abuja Nyesom Wike a Fadar SHugaban Kasa? NAJERIYA A YAU: “Abin Da Ya Sa Muka Dawo Daga Rakiyar Kirifto” DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Amsar wannan tambaya shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci za iyi yunkurin bicikowa. Domin sauke shirin, latsa nan
    Aƙalla mutum 610 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu sama da 1,300 suka jikkata sakamakon girgizar ƙasa mai ƙarfi da ta afku a ƙasar Afghanistan. Rahotanni daga hukumomi da kafafen watsa labarai na duniya sun ce ibtila’in ya auku ne a yankin gabashin ƙasar Afghanistan, kusa da iyakarta da Pakistan. Rahoton Hukumar Binciken Ƙasa ta Amurka (USGS) ya bayyana cewa ƙarfin girgizar ƙasar ta kai matakin 6.0, kuma cibiyar ta kasance a wani yanki mai tazarar kilomita 27 daga birnin Jalalabad, inda ake da yawan jama’a kimanin 300,000. An gano cewa girgizar ta afku a zurfin kilomita takwas kacal daga saman ƙasa, wanda hakan kan ƙara tsananta illarta. Rushe Kasuwar Alaba Rago: Ya kamata shugabannin Arewa su sa baki...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ƙungiyar Arewa ta ’Yan Jarida (ABMPF) ta roƙi Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya dakatar da rushe Kasuwar Alaba Rago da Gwamnatin Jihar Legas ta fara, tana mai cewa matakin ya jawo asarar biliyoyin naira tare da barin dubban ’yan kasuwa cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi. Shugaban Ƙungiyar, Alhaji Abdullahi Yelwa, ya ce rusau ɗin ya haddasa wa ’yan kasuwar asarar kimanin Naira biliyan 20, tare da ruguza shaguna da wuraren ibada fiye da 40, abin da ya ce “bai dace ba kuma yana iya jawo rikicin ƙabilanci.” Kungiyar ta roƙi gwamnonin Arewa, ’yan majalisa da sarakuna na gargajiya su shiga wajen tabbatar da kare haƙƙin ’yan Arewa da suke zaune a Legas. Haka kuma ta yi kira ga Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya...
    Ya kuma tuna da tsohon abokin ajinsu wanda ya kasance tsohon Sufeton ƴansanda, marigayi Solomon Arase, wanda ya rasu a ranar Lahadi a Abuja bayan gajeriyar rashin lafiya. El-Rufai ya bayyana shi a matsayin mutum nagari, yana mai cewa tsarin ƴansanda na yanzu ya sha bamban da lokacin da Arase ya jagoranta. Daga ƙarshe, ya ce zai sake rubuta ƙorafi ga IGP da kuma hukumar kula da ƴansanda (PSC), yana mai gargadi cewa idan jami’an tsaro suka zama kariya ga masu tada fitina, to hakan zai kai ƙasa ga rugujewa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
    Ƙungiyar Musulunci ta Nasrul-Lahi-L-Fatih (NASFAT) ta yi kira ga malamai da mabiya addinin Islama a duniya da su guji yin kalaman ɓatanci ga sahabban Annabi Muhammad (SAW), tana mai cewa yin hakan zunubi ne mai girma kuma ya saɓa wa koyarwar addini. Ƙungiyar ta yi kiran ne bayan rahotannin da ke nuna cewa wasu malamai a Jihar Kwara da wasu sassan Yammacin Najeriya sun shiga ce-ce-ku-ce saboda irin waɗannan kalamai a jan sahabban Annabi (RA). NASFAT ta ce addinin Musulunci ya umarci a yi biyayya ga Allah da Manzonsa (SAW) tare da girmamawa da ƙaunar sahabbai baki ɗaya. Sanarwar da kakakin NASFAT, Alhaji Shamsideen Owolabi Oseni, ya fitar ta ce,“Sahabbai ne suka fara yaɗa addinin Musulunci, suka kare shi, suka...
    Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyed Abdul Malik al-Houthi ya yi kakkausar suka kan harin wuce gona da iri da Isra’ila ta kai a birnin San’a wanda ya kai ga shahadar firaministan kasar Yemen da wasu jami’an farar hula da dama. A cikin wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin na jinjinawa shahidai, al-Houthi ya bayyana cewa, “laifi na kai hari kan ministoci da ma’aikatan farar hula ya kara tabbatar da laifukan Haramtacciyar Kasar Isra’ila a yankin,” yana mai jaddada cewa dukkan wadanda suka yi shahada suna gudanar da ayyukansu ne a fagagen da ba na soja ba. Da yake mika ta’aziyyarsa ga iyalan shahidai, abokan aikinsu, da al’ummar kasar Yemen, ya tabbatar da cewa wuce gona da...
    ’Yar Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, Khadijah, wadda aka fi sani da Andijo, ta rasu. Ta rasu a Abuja tana da shekara 35, kuma ta bar ’ya’ya uku. Trust Radio za ta fara watsa cikakkun shirye-shirye a ranar Litinin Gwamnatin Sakkwato za ta fara biyan masallatan Juma’a kuɗi duk wata An yi jana’izarta a fadar Sarkin Katsina ƙarƙashin jagorancin Imam Mustapha Gambo. Ɗaruruwan mutane sun halarci jana’izar, ciki har da Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, sarakunan gargajiya, jami’an gwamnati da kuma al’ummar gari. Bayan kammala jana’izar, Gwamna Radda ya bayyana marigayiyar a matsayin uwa mai tausayi kuma mai son zaman lafiya. Ya roƙi Allah Ya gafarta mata, Ya kuma bai wa iyalanta haƙurin wannan rashi. Haka kuma, Gwamnan...
    Gidan rediyon Trust Radio mallakin kamfanin Media Trust Group, zai fara watsa cikakkun shirye-shiryenta a ranar Litinin, 1 ga watan Satumba, 2025. Wannan na zuwa ne bayan tashar ta kammala gwajin watsa shirye-shiryenta tare da samun amincewar Hukumar Kula da Watsa Shirye-shirye na Ƙasa (NBC). Kilishiyar Waja ta tallafa wa matan gidan yari da kayayyaki a Gombe Gwamnatin Sakkwato za ta fara biyan masallatan Juma’a kuɗi duk wata Babban Daraktan Kamfanin Media Trust, Malam Ahmed I. Shekarau ne, ya bayyana wannan ci gaba. Ya bayyana hakan a matsayin abin alfahari, inda ya ce Trust Radio za ta mayar da hankali kan yaɗa shirye-shirye na gaskiya, adalci da kuma abin da ya shafi jama’a. Za a riƙa watsa shirye-shirye daga Abuja...
      Shugaba Xi ya yi imanin cewa, kungiyar SCO za ta ba da karin gudunmawa wajen samun ci gaba, da kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe membobinta, da tara karfin kasashe masu tasowa, da kuma taimaka wa ci gaban wayewar kan dan Adam, a karkashin hadin gwiwa na dukkan bangarori.   Kafin liyafar maraba, Shugaba Xi da madam Peng Liyuan sun yi maraba da shugabannin kasashen waje da matansu cikin fara’a, inda suka mika musu hannu tare da gaisawa, kuma suka dauki hotuna tare da su.(Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kilishiyar Waja, Hajiya Rabee Abubakar Kulani, ta kai ziyara gidan gyaran hali na Gombe, inda ta raba mata fursunoni kayan tsaftar jiki domin su kula da kansu a lokacin al’ada. Ta ce ta kai wannan gudummawa ne domin tallafa wa mata fursunoni wajen kare mutuncinsu, ganin cewa sau da yawa ba su da damar samun irin waɗannan muhimman kayayyaki. Gwamnatin Sakkwato za ta fara biyan masallatan Juma’a kuɗi duk wata Zaɓen Ribas: APC ta yi nasara a ƙananan hukumomi 20, PDP ta samu 3 “Ina so su ji kamar sauran mata, su samu tsafta da mutunci duk da yanayin da suke ciki. “Shi ya sa na sayi kayayyakin da kaina domin na tallafa musu,” in ji ta. A yayin ziyarar,...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada muhimmancin aiwatar da yarjejeniyar bisa manyan tsare-tsare tsakanin Iran da China A daidai lokacin da shugaban kasar Iran ya kai ziyarar aiki zuwa kasar China, asusun kula da shafukan sada zumunta na ofishin kula da tsare-tsare da wallafa ayyukan Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya wallafa wani bangare na jawabinsa cikin harshen chinanci kan muhimmancin dangantakar Iran da China. Kididdigar ofishin kula da tsare-tsare da wallafa ayyukan jagoran juyin juya halin Musulunci ya wallafa bayanansa kan kasar Iran da kuma damar da kasar China ke da ita ta taka rawa a fagen duniya da kuma wajibcin aiwatar da yarjejeniyar tsare-tsare tsakanin kasashen biyu, wanda ya zo daidai da ziyarar...
    Mataimakin babban kwamandan “IRGC” ya bayyana cewa: Makiya sun kasa cimma wata manufa tasu a tsawon kwanaki 12 da suka yi suna yakar Iran Mataimakin babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ali Fadavi ya tabbatar da cewa: Makiya sun kasa cimma wata manufa tasu a tsawon kwanaki 12 da suka yi suna kai hare-haren wuce gona da iri kan kasar Iran. Duk da tsare-tsare masu yawa da kuma sanar da manufofinsu a baya, makiya sun kasa cimma wata manufa da suka ayyana a cikin yakin kwanaki 12 da suka kaddamar kan Iran, lamarin da ya tilasta musu amincewa da shan kashi ta hanyar amincewa da tsagaita bude wuta cikin hanzari. Fadavi ya kara da...
    Kenya ta tono gawarwakin mutane 32 a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna bacin ransu kan mace-macen ‘yan darikar addini masu tsattsauran ra’ayi Hukumomin kasar Kenya sun tono gawarwaki 32 a makon da ya gabata a kudu maso gabashin kasar, wani sabon bala’i da ya sake haifar da sukar gwamnatin kasar, wadda a baya ta yi alkawarin murkushe kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi bayan mutuwar daruruwan mabiya kungiyar asiri ta “Apocalypse” shekaru biyu da suka gabata. Gwamnatin Kenya da mazauna yankin sun danganta gawarwakin da aka gano a kauyen Kwa Binzaro da wata kungiyar kiristoci da ake zargi da hannu wajen kashe mutane fiye da 400 a dajin Chakahola da ke kusa a shekarar 2023. Babban likitan gwamnati a...
      A nata bangaren, darektar kula da yankin Asiya da Fasifik da Gabas ta Tsakiya a ma’aikatar kula da hadin kan Afirka da harkokin wajen kasar Senegal Cathy Diagne Thioye, ta bayyana dandalin FOCAC a matsayin abin koyi a bangaren hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Ta yi kira ga bangarorin biyu da su ci gaba da yin aiki tare don aiwatar da muhimman ayyukan da suka sa a gaba a karkashin tsarin dandalin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Jihar Sakkwato ta bayyana cewa za ta riƙa bai wa kowane masallacin Juma’a a jihar kuɗi daga Naira 300,000 zuwa 500,000 duk wata domin tallafa musu. Haka kuma gwamnatin za ta riƙa biyan limaman masallatan, na’ibansu da ladanai alawus na kowane wata domin sauƙaƙa wa hidimominsu. Zaɓen Ribas: APC ta yi nasara a ƙananan hukumomi 20, PDP ta samu 3 Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram 12, sun ƙwato makamai a Borno Mai magana da yawun gwamnatin, Abubakar Bawa ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa. Ya ce manufar shirin shi ne ƙarfafa karatun Alƙur’ani da koyar da ilimin addini ga yara da matasa a jihar. Gwamna Ahmed Aliyu, ya sanar da wannan mataki ne a ranar Asabar yayin...
      Ya tabbatar da cewa, an kwashe dukkan fasinjoji 618 da ke cikin jirgin cikin koshin lafiya. 20 sun samu kananan raunuka, yayin da bakwai ke kwance a asibiti amma tuni an sallame su, kuma NRC ce ta dauki nauyin biyan kudaden kiwon lafiyarsu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Dakarun Operation Haɗin Kai (OPHK) tare da Civilian JTF, sun yi nasarar kashe mayaƙan Boko Haram da ISWAP 12 a Jihar Borno. A ranar 29 zuwa 30 ga watan Agusta, sojojin sun kai farmaki ƙauyukan Tamsu Ngamdu, Dalakaleri, Gaza da Loskori Kura, inda suka yi artabu da ‘yan ta’addan. Tsohon Sufeto-Janar na ’yan sandan Nijeriya Solomon Arase ya rasu An ƙone wata mata ƙurmus kan yi wa Annabi ɓatanci a Neja A Loskori Kura, sojojin sun yi nasara, inda suka kashe ’yan ta’adda 12, suka kuma kwato8 bindiga ƙirar AK-47 guda shida, harsasai guda takwas da magunguna iri-iri. Majiyoyin tsaro sun ce wasu daga cikin ’yan ta’addan sun ji raunuka, bayan artabun da suka yi da sojojin. Wannan farmaki ya...
    135-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane, Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////…Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-mujtapa (a) jikan manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun bayyana yadda aka yi yaki kan ruwan furat, bayanda sojojin mu’awiya ya hana sojojin...
    135-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane, Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////…Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-mujtapa (a) jikan manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun bayyana yadda aka yi yaki kan ruwan furat, bayanda sojojin mu’awiya ya hana sojojin...
      A cewar majiyar, kwale-kwalen zai iya daukar fasinjoji 16 ne kacal, amma a zagaye na Uku cunkoson matafiyar ya yi yawa inda wasu mata biyu suka tilasta wa kansu afkawa cikin jirgin inda suka zama fasinjoji zuwa 18, ana kyautata zaton cewa, wannan ne ya yi sanadin kifewar kwale-kwalen. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    137- Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane, Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////…Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-mujtapa (a) jikan manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun bayyana yadda aka fara yakin gama gari tsakanin sojojin Imam Ali (a) da...
    136- Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane, Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////…Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-mujtapa (a) jikan manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun bayyana yadda aka fara yakin Siffin yakin da ya sauya tarihin musulunci, yakin...
    Mazauna sun lakaɗa wa wata mata duka sannan suka ƙone ta ƙurmus kan zargin yi wa fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (SAW) ɓatanci a yankin Kasuwan-Garba da ke ƙaramar hukumar Mariga ta Jihar Neja. Shaidu sun ce, lamarin ya faru ne a ranar Asabar lokacin da wata muhawara ta taso a cikin shagon matar inda take abincin sayarwa. Chelsea ta kammala ɗaukar Garnacho daga Manchester United Hamas ta tabbatar da mutuwar jagoranta a Gaza, Mohammed Sinwar Aminiya ta ruwaito cewa, wani daga cikin kwastomomin matar ne cikin raha ya ce yana so ya aure ta domin ta zamo matarsa kamar yadda sunnar Ma’aiki (SAW) da tanadar, amma daga bisani lamarin ya haifar da cece-kuce har aka yi zargin ta furta kalaman...
    Hadakar ta wuce batun tattalin arziki kadai, domin a bangaren tsaro ma, Rasha ta yi amfani da lalacewar alaka tsakanin kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar da kasashen yamma, inda ta samu kutsawa cikinsu.   Ganin yadda yankin ke fama da matsalolin tsaro, sai Rasha ta aika musu da sojojin haya na Wagner domin taimakon kasashen da makamai da horo.   Amma ganin yadda har yanzu kasashen ke ci gaba da fuskantar hare-hare, shin za a iya cewa alaka da Rasha ta yi musu rana?   Sababbin kawayen Moscow Tun a 2021 Rasha ke tura dubban sojoji da makaman da suka kai miliyoyin Dala zuwa Mali da Burkina Faso da Nijar. Tana haka ne domin taimakon kasashen wajen yaki...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta tabbatar da ɗaukar ɗan wasan gaban Manchester United, Alejandro Garnacho, kan kuɗin da ya kai kusan fam miliyan 85 (£85m). Rahotanni sun bayyana cewa ɗan wasan na ƙasar Argentina ya rattaba hannu kan kwantiragin zama a Stamford Bridge har zuwa shekarar 2032. Hamas ta tabbatar da mutuwar jagoranta a Gaza, Mohammed Sinwar Xi na karɓar baƙuncin taron SCO a China Garnacho, mai shekara 21, zai riƙa ɗaukar albashin fam 250,000 duk mako, kwatankwacin Naira miliyan 500 a kuɗin Nijeriya, lamarin ya sanya shi a sahun manyan ’yan wasa mafiya albashi a Stamford Bridge. A bara ne tauraruwarsa ta haska a Manchester United, bayan ya ci ƙwallo 11 ya kuma ba da gudunmawar zura wasu...
    Da ma can an yi ta ba da shawara cewa ya kamata Arsenal ta dauki danwasa mai buga gefen hagu kamar Gabriel Martinelli, amma ba ta ce komai ba har sai yanzu. Bayan da cinikin Eze ya fada, yanzu kuma kungiyar ta Arsenal ta sake mayar da hankalinta wajen sayan dan wasan baya daga kungiyar kwallon kafa ta Bayer Liberkusen, wato Piero Hincapie.   Chelsea Da alama har yanzu mai horarwa Enzo Maresca bai hakura da karin cefane ba kafin rufe kasuwar, yayin da yake neman Alejandro Garnacho na Man United da danwasan RB Leipzig Dabi Simons. Sai dai komai zai dogara ne da yawan ‘yanwasan da ta iya sayarwa kamar Nicolas Jackson da Christopher Nkunku da Tyrikue George, wadanda...
    Ƙungiyar Hamas ta tabbatar da mutuwar Mohammed Sinwar, wanda aka daɗe ana ɗauka a matsayin jagoranta a Gaza. Wannan tabbaci ta Hamas ta bayar na zuwa ne fiye da watanni uku bayan Isra’ila ta ce ta kashe shi a wani harin sama. Mutum 13 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Zamfara  Xi na karɓar baƙuncin taron SCO a China Hotunan da Hamas ta fitar ranar Asabar sun nuna Sinwar tare da wasu manyan shugabannin siyasa da na soji, waɗanda aka bayyana a matsayin “shahidan kwamitin soji.” Mohammed Sinwar, shi ne ƙanen Yahya Sinwar wanda Isra’ila ke zargi da jagorantar harin ranar 7 ga Oktoban 2023 a Isra’ila, rikicin da har yanzu wutarsa ke ƙara ruruwa. Kamfanin Dillancin Labaran...
    Ko Mbeumo zai dawo wa United da karsashinta? Dan wasan dan kasar Kamaru Bryna Mbeumo ya zama abin tattaunawa kuma mafi tsada a ‘yanwasan Afirka lokacin da ya koma Manchester United kan fani miliyan 65 daga kungiyar kwallon kafa ta Brentford. Dan kwallon mai shekara 25 ya ci kwallo 20 a gasar da aka kammala da kuma bayarwa a ci bakwai. Manchester United na tsaka da sake gina kungiyar karkashin mai horarwa Ruben Amorim bayan gama gasar a mataki na 15, wanda shi ne mafi muni a tarihin kungiyar na Premier League. Mbeumo zai fuskanci matsi nan take domin ya nuna kwarewarsa tare da Matheus Cunha da Benjamin Sesko wadanda duka kungiyar ta sayo a wannan kakar domin kara karfin...
    Shugaban ƙasar China, Xi Jinping, na karɓar baƙuncin taron ƙungiyar Shanghai Cooperation Organisation (SCO) a birnin Tianjin, inda shugabannin ƙasashe kusan 20 daga yankin Eurasia suke halarta. Taron, wanda zai gudana har zuwa Litinin, ana kallon sa a matsayin wani babban dandalin da ke ƙara tabbatar da matsayin China a tsakiyar harkokin siyasar ƙasashen Eurasia. Gwamnonin Arewa Maso Gabas sun yi taro kan tsaro da tattalin arziƙi a Taraba Ambaliya: NEMA ta raba kayan tallafi a Yobe  Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya isa Tianjin da manyan jami’an gwamnati da ’yan kasuwa daga ƙasarsa, inda kuma ya yi shirin gudanar da tattaunawa da shugabannin ƙasashe daban-daban a gefen taron. Firayim Ministan Indiya, Narendra Modi, shi ma yana halartar taron, wanda ya...
    Hakan yana faruwa ne saboda yawan hormones “progesterone” da yake taruwa a jikinta. A wannan gaban ana kiran yanayin da “luteal phase”. Shin wasu lokuta ne za ki tsammaci ganin farin ruwa a gabanki; Idan kin gani ba damuwa bane Yawanci mata suna iya samun bushewar gaba kamar na kwana 3 zuwa 4 kowane bayan yankewar al’adarsu. bayan wannan kwanakin, farin ruwa mai danko ya kan sake bullowa wanda zai yi kamar kwana 4 zuwa 5 kafin lokacin fitar kwayar alitta, alama ce ta kwayar alitta sun fara girma, ana kiransa da “follicular phase” that means a lokacin ne “eggs” (for obulation) suke kokarin girma. Idan kuma lokacin fitar ya yi, ruwan sai ya canza daga mai danko zuwa fari...
    Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki? An haife ni a garin Kano a Bichi LGA, na yi firamare a Bichi ‘Chiranci Primary School’. Amma ban cigaba ba da yake mu fulani ne, daga nan aka yi min aure. Bayan na fita daga gidan mijina, sai na fara koyan wasan dabe (Drama), daga nan ne dai na samu kaina a cikin wannan sana’ar.   Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma harkar fim? Abin da ya ja hankalina har na fara fim, bayan na yi aure na auri dan fim, Allah ya ji kanshi Rabilu Musa (Ibro). Bayan na fita daga hannunsa kawai sai na yi sha’awar ni ma na fara fim. To, akwai wacce nake so...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan kisan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi wa  wasu daga cikin manyan jami’an kasar Yemen, tare da yin kira ga al’ummar duniya da su tinkari irin wadannan munanan ayyuka  na rashin bin doka da oda. A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar ta yi tir da wadannan ayyuka na  ta’addanci, tare da jaddada bukatar  daukar matakin gaggawa daga kasashen duniya don dakile aniyar yahudawan sahyuniya ta kawo hargiti a gabas ta tsakiya, wanda kai tsaye yake shafar tsaro na kasashen duniya. Ta bayyana wannan munanan aiki da cewa, ba wai kawai laifukan yaki da laifin cin zarafin bil’adama ba ne, har ma  yana a matsayin ramuwar gayya...
    Gaskiya dai inda matsalar take shi ne, rashin wayewa da wasu mazan suke da shi, mafi yawa kuma mazan da suke da rashin ilimi su ke da wannan dabi’ar da take ba, dauwamammiya ba. Hakan gaskiya kwata-kwata bai dace ba, saboda an fi so namiji ya auri mai ilimi, wacce za ta tarbiyyantar da ‘ya’ya kan hanya ta gaskiya, da tarbiyya gurin rayuwa ta yau da kullum. Amma idan aka ce mace ba tada wani wayewa to, ba ita kadai za ta zauna cikin wannan rashin wayewar ba, har sai ya kai ga yaran da aka haifa suma su zama cikin duhun kai, su kasa mu’amala da al’umma. Saboda duk mutum wanda yake da rashin wayewa yana tare da tsatstsauran/baudadden...
    Fadar shugaban kasar Yemen a Sana’a ta sanar da shahadar firayim minista Ahmed Ghaleb al-Rahwi tare da wasu ministocin kasar, sakamakon harin da Isra’ila ta kai a ranar Alhamis din da ta gabata. Fadar shugaban kasar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta kara da cewa, wasu ministoci da dama sun samu raunuka sakamakon wannan ta’asa, kuma a halin yanzu suna samun kulawar lafiya. Duk da haka, fadar shugaban kasar ta ba da tabbacin cewa cibiyoyi za su ci gaba da gudanar da ayyukansu ga jama’a ba tare da wani tsaiko ba, duk kuwa da girman Rashin da aka yi. Dangane da matsayar kasar Yemen kan batun yakin  Gaza, fadar shugaban kasar da ke  birnin San’a ta jaddada wa...
    Shugaban mayakan RSF a Sudan Mohammed Hamdan Dagalo ya yi rantsuwar shugabatar gwamnati mai kishintar gwamnatin kasar. Sanarwar ta ce Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti, wanda kuma ba kasafai ake ganinsa a kasar Sudan ba tun bayan barkewar rikici na tsawon watanni 28 tsakaninsa da sojojin kasar, an rantsar da shi ne a yayin wani biki a birnin Nyala na kasar Sudan, ko da yake kamfanin dillancin labaran  Reuters ya kasa tabbatar da inda yake. Nyala, daya daga cikin manyan biranen kasar Sudan dake yankin Darfur, wanda kuma shi ne babbar tungar mayakan kungiyar RSF, kungiyar da ta nada nata firaminista da majalisar shugabancin karkashin jagorancin Dagalo. A ranar 16 ga watan Afrilu, Dagalo, kwamandan rundunar RSF  ya...
    Matsala ta farko na yi mata take da: 1. Sai Bango Ya Tsage….: Gaskiyar diyan Bawo, da yake cewa, ‘Sai bango Ya tsage, kadangare ke samun wurin shiga. Lallai babu yadda za a yi gwamnati da sauran manyan al’umma suna kallon harshen Hausa a matsayin wani harshe wanda nazartarsa koma baya ne ga al’umma kuma a samu wannan harshen ya ci gaba da yaduwa kamar wake dan arba’in. An taba yin wani shugaban kasa da ya ayyana nazartar wasu darussa a matsayin bata lokaci domin bai ma san a ina za su yi aiki ba. Duk kuwa da kasancewar duk kasar da ya ratsa a Arewacin kasar domin yakin neman zabe, da harshen Hausa yake magana. Abin da nake nufi...
    Gwamnonin Jihohin Arewa maso Gabas, sun koka kan matsalolin da suka shafi ayyukan jin-ƙai da kuma gina muhimman ababen more rayuwa duk da ci gaban da aka samu a yaƙin da ta’addanci a yankin. Wannan bayani ya fito ne daga sanarwar ƙarshen taronsu karo na 12 da aka gudanar a Jalingo, Jihar Taraba. Ambaliya: NEMA ta raba kayan tallafi a Yobe  An kama direban mota da jabun kuɗin N1m a Oyo Taron ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum. A yayin taron, gwamnonin sun nuna damuwa kan yiwuwar samun ambaliyar ruwa a wasu jihohin yankin. Don haka sun buƙaci a ɗauki matakan gaggawa da kuma neman taimakon Gwamnatin Tarayya da hukumar NEDC domin...
    Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta raba wa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Ƙaramar Hukumar Potiskum ta Jihar Yobe, kayan tallafi. Darakta Janar na hukumar, Zubaida Umar, ta amince da fara wannan tallafi a Potiskum, inda ta samu wakilcin Abdullahi Garba, ko’odinetan ofishin NEMA na Maiduguri. An kama direban mota da jabun kuɗin N1m a Oyo Mutum 13 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Zamfara  A cewarta, wannan mataki ya biyo bayan ambaliyar ruwa da ta auku a ranar 15 ga qatan Agusta, 2025. Ambaliyar ta shafi dubban jama’a kuma ta lalata gidaje da dama. Binciken da NEMA tare da wasu ƙungiyoyin agaji suka gudanar ya nuna cewa gidaje 2,557 ne abin ya...
    Gwamnatin kasar Denmark ta sanar da cewa: Tana goyon bayan dakatar da yarjejeniyar kasuwanci da haramtacciyar kasar Isra’ila Ministan harkokin wajen Denmark Lars Løkke Rasmussen ya fada a ranar Asabar cewa: Kasarsa tana goyon bayan dakatar da yarjejeniyar kasuwanci da haramtacciyar kasar Isra’ila da nufin kawo karshen yakin Gaza. Ya kara da cewa: Abin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi a Gaza ya wuce kare kai, don haka dole ne a matsa lamba kanta don kawo karshen yakin da kuma bala’in jin kai. Ya ci gaba da cewa gwamnatin mamayar Isra’ila na ruguza tsarin samar da kasashe biyu. A nata bangaren, jami’ar kula da harkokin wajen kungiyar tarayyar turai, Kaja Kallas ta bayyana cewa: Kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun dauki...
    Zanga-zangar adawa da kakaba yunwa da gudanar da kisan kare dangi da sojojiin mamayar Isra’ila ke yi a Gaza a biranen kasar Morocco Dubban al’ummar Moroko ne suka gudanar da zanga-zanga a garuruwa da dama na masarautar kasar a cikin jerin gwanon dare, domin neman kawo karshen yunwa da kisan kiyashin ga Falasdinawa a zirin Gaza. Zanga-zangar ta zo ne a daidai lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka tsananta kai hare-hare ta sama, da kasa da kuma ta ruwa a wasu unguwanni a cikin birnin Gaza, inda Falasdinawa kusan miliyan daya suke, tun da sanyin safiyar Juma’a. Wannan dai na daga cikin shirinta na mamaye birnin da kuma kammala kisan gillar da ta shafe watanni 23 tana yi wa Falasdinawa....
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo, ta kama wani direban mota ɗauke da jabun kuɗi har Naira miliyan ɗaya. Kakakin rundunar, CSP Adewale Osifeso ne, ya bayyana hakan a ranar Asabar cewa jami’an sintiri na Gwamnatin Tarayya ne suka tsayar da direban a kusa da gidan Guru Maharaji, kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan. Mutum 13 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Zamfara  Jigon jam’iyyar PDP a Gombe, Haruna Jonga, ya koma APC Direban mai suna Akande, ya fito daga Legas ne, kuma yana kan hanyarsa ta zuwa Osogbo, babban birnin Jihar Osun, kafin shiga hannu a ranar Juma’a. A cewar Osifeso, lokacin da aka tsayar da motar, direban ya fara rawar jiki abin da ya sa jami’an suka...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Aƙalla mutum 13 ne suka rasu, yayin da sama da 20 suka ɓace a Jihar Zamfara, bayan jirgin ruwan da suka hau domin tsere wa ’yan bindiga ya nutse. Mazauna yankin da wasu jami’ai sun tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Asabar. Jigon jam’iyyar PDP a Gombe, Haruna Jonga, ya koma APC Dokar ta-ɓaci: Fubara zai dawo ofis ranar 18 ga Satumba — Wike Harin ya faru ne a ranar Juma’a a yankin Birnin Magaji, inda ’yan bindiga suka kai wa ƙauyuka biyu hari. Mutane da dama ne suka tsere zuwa bakin kogi, inda suka riski jirgin ruwa guda ɗaya kacal. Hakan ya sa aka jirgin da mutane sosai, lamarin da ya sa ya nutse a cikin ruwa. “Babban yayana...
    Har ila yau, wannan ilhama ta tsotsar nonon uwa da ake haifar jarirai da ita, ana kiranta da ‘Sucking refled’, a turancin likita. Kazalika, ilhamar tana fara aiki ne gadan-gadan bayan haihuwa a duk lokacin da kan nonon uwa ya taba saman bakin jariri, wato hanka kenan.   Haka abin yake, idan aka sa wani abu makamancin kan nono; kamar kan yatsa ko kuma fasfaya (pacifier), haka za su rika tsotsa babu ji babu gani, saboda haka aka shirya wa kwakwalwarsu cewa; da zarar kan nono ya dunguri hanka, sai su kama tsotsa kai tsaye.   Don haka, su ma ba aikin kansu ba ne, haka kawai za su ji suna yi ba tare da wani kokari nasu ba, abu...
    Wakilin kasar Sin a fannin cinikayyar kasa da kasa, wanda kuma shi ne mataimakin ministan cinikayya na kasar, Li Chenggang, ya yi musayar ra’ayoyi da jami’an gwamnatin Amurka, dangane da alakar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin sassan biyu. Li, ya jagoranci tawagar kasar Sin yayin zantawa da jami’an ofishin baitulmalin Amurka, da na ma’aikatar cinikayya, da na ofishin wakilin cinikayyar kasar, tsakanin ranakun Laraba da jiya Jumma’a a birnin Washington. Wata sanarwa da ma’aikatar cinikayyar Sin ta fitar bayan ganawar, ta ce sassan biyu sun yi musayar ra’ayoyi dangane da yadda za a aiwatar da kudurorin da shugabannin kasashen biyu suka cimma, yayin zantawarsu ta wayar tarho a ranar biyar ga watan Yunin bana, da ingiza alakar tattalin arziki...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ɗan wasan ɗan shekaru 22 ya zura ƙwallaye 10 ne kawai a wasanni 52 da ya buga a United bara, kuma zuwan Sesko ya ka5ra rage masa damar zama a cikin ƙungiyar. Sha’awar Napoli kan Højlund ta ƙaru ne bayan Romelu Lukaku ya samu rauni a cinyarsa wanda zai sa ya daɗe a jinya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp