Habasha da Dangote sun rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa ta dala biliyan 2.5
Published: 3rd, September 2025 GMT
Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa ta dala biliyan 2.5 da gwamnatin kasar Habasha, domin gina daya daga cikin manyan masana’antun takin zamani a duniya a garin Gode.
An rattaba hannu kan yarjejeniyar tsakanin rukunin Dangote da kamfanin zuba jari na Habasha (EIH), wanda zai baiwa rukunin Dangote damar rike hannun jarin kashi 60 cikin dari, yayin da EIH zai rike kashi 40 cikin dari.
Ana has ashen cewa idan an kammala aikin, zai kasance cikin manyan masana’antun samar da takin zamani guda biyar na duniya, wanda zai rika samar da takin zamani ton miliyan uku a kowace shekara.
A cewar EIH, za a kammala aikin a cikin watanni 40 kuma zai hada da bututun jigilar iskar gas daga filayen gas na Calub da Hilala na Habasha.
Firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed wanda ya halarci rattaba hannu kan yarjejeniyar, ya bayyana aikin a matsayin wani muhimmin mataki na samun ‘yancin cin abinci daga kokari da gumin ‘yan Afirka.
A nasa bangaren, Aliko Dangote ya ce hadin gwiwar ya nuna hangen nesa domin kara habaka masana’antu a Afirka da kuma inganta samar da abinci a fadin nahiyar.
“Mun kuduri aniyar kawo kwarewarmu na shekaru da dama a manyan ayyukan masana’antu don tabbatar da cewa wannan kamfani ya zama ginshikin sauye-sauyen masana’antu na Habasha da kuma hanyar samar da amfanin gona a duk fadin yankin,” in ji Dangote.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Jami’an Iran sun yaba da nasarorin da aka samu a yayin halartar Pezeshkian a taron SCO September 3, 2025 Sojojin Yemen sun kai hare-hare a kan babbar hedikwatar tsaro ta Isra’ila September 3, 2025 Masar ta yi watsi da wasan sada zumunta da Zambia kan Isra’ilawa na horar da ‘yan wasan kasar September 3, 2025 Pezeshkian: Idan Ba A Hada Kai Ba, Munanan Manufofin Amurka Zasu Hada Har Da Kasar China September 2, 2025 Baqa’i: Tawagar Turai Sun Fara Amfani Da Tsoffin Takunkumai Kan Kasar Iran September 2, 2025 Majalisar Shawarar Musulunci Ta Yi Zaman Na Musamman Kan Shirin Tawagar Turai September 2, 2025 Batun Kwance Makaman Kungiyar Hizbullahi Kokarin Kunna Wutar Fada Ne A Kasar Lebanon September 2, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Aiwatar Da Kisan Kiyashi A Zirin Gaza Cikin Sa’o’i 24 Kacal September 2, 2025 Aragchi Yayi Tir da Kissan Firaiministan Kasar Yemen Da Wasu Ministocinsa September 2, 2025 Fiye Da Mutane 1000 Ne Suka Rasa Rayukansu A Yammacin Sudan Saboda Zaizeyar Kasa September 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: rattaba hannu kan
এছাড়াও পড়ুন:
Rabin Sojojin Isra’ila da suka ji rauni a yakin Gaza na fama da ciwon damuwa
Ma’aikatar tsaron Isra’ila ta ce fiye da sojojin kasar 20,000 ne suka ji rauni tun farkon yakin da aka fara a Gaza a watan Oktoba 2023, inda fiye da rabinsu ke fama da matsalolin lafiyar kwakwalwa, ciki har da ciwon damuwa.
A cewar sashen bayar da shawarwari na ma’aikatar, kusan kashi 56 cikin 100 na wadanda suka ji rauni sun kamu da wasu matsalolin lafiyar kwakwalwa, wanda ke nuna irin tasirin matsalar kwakwalwa da wannan rikici ke haifarwa.
Ma’aikatar ta kara da cewa kusan kashi 45 cikin 100 na wadanda suka ji rauni suna fama da raunuka a jiki, yayin da kashi 20 cikin 100 na sojojin ke fama da matsalolin kwakwalwa da na jiki a lokaci guda.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sudan ta soki takunkuman da Amurka ta kakaba mata September 15, 2025 Dakarun Sojin Yamen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Ramon Na Isra’ila. September 14, 2025 Isra’ila Za ta Gamu Da Mummunar Martani Idan Tayi Gigin Afkawa Iran September 14, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Larabawa Da Na Musulmi Sun Fara Taro A Qatar. September 14, 2025 Gwamnatin Najeriya Ta Sanar Da Sabon Sharadi Na Bude Asusun Banki September 14, 2025 An Zabi Issa Tchiroma A Matsayin Dan Takara Daya Tilo A Kamaru September 14, 2025 Kasar Iran Ta Yi Fatali Da Zarge-Zargen Da Kungiyar G7 Da Kawayenta Suka Yi Kanta September 14, 2025 Iran Ta Bayyana Shirinta Na Halartar Taron Shekara-Shekara Na Hukumar Makamashin Nukiliya September 14, 2025 Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Bayyana Rashin Halarta Tawagarta A Kada Kuri’a Kan Batun Falasdinu September 14, 2025 Tsananin Masifar Da Falasdinawa Ke Ciki A Gaza Saboda Hare-Haren Gwamnatin Mamayar Isra’ila September 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci