HausaTv:
2025-11-02@12:26:24 GMT

Kasar Denmark Tana Goyon Bayan Dakatar Da Yarjejeniyar Kasuwacin Da Isra’ila

Published: 30th, August 2025 GMT

Gwamnatin kasar Denmark ta sanar da cewa: Tana goyon bayan dakatar da yarjejeniyar kasuwanci da haramtacciyar kasar Isra’ila

Ministan harkokin wajen Denmark Lars Løkke Rasmussen ya fada a ranar Asabar cewa: Kasarsa tana goyon bayan dakatar da yarjejeniyar kasuwanci da haramtacciyar kasar Isra’ila da nufin kawo karshen yakin Gaza.

Ya kara da cewa: Abin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi a Gaza ya wuce kare kai, don haka dole ne a matsa lamba kanta don kawo karshen yakin da kuma bala’in jin kai.

Ya ci gaba da cewa gwamnatin mamayar Isra’ila na ruguza tsarin samar da kasashe biyu.

A nata bangaren, jami’ar kula da harkokin wajen kungiyar tarayyar turai, Kaja Kallas ta bayyana cewa: Kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun dauki mataki kan gwamnatin mamayar Isra’ila.

Ta kara da cewa, akwai rashin jituwa tsakanin kasashe mambobin kungiyar kan yadda za su tunkari gwamnatin mamayar Isra’ila, amma za a ci gaba da tattaunawa kan zabin da ya fi dacewa.

Kallas ta ci gaba da cewa, ba zai yiwu a samar da hanyoyin soji a Gaza ba, kuma matakin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi na ayyana birnin Gaza a matsayin yankin yaki ya sa al’amuran jin kai suka yi muni.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Moroko: Zanga-Zangar Rashin Amincewa Da Kisan Kiyashi Da Kakaba Yunwa A Gaza August 30, 2025 Guinea: An Fara Tattaunawa Kan Zaben Raba Gardama Na Sabon Kundin Tsarin Mulki August 30, 2025 Turkiyya Ta Bukaci A Dakatar Da Isra’ila (HKI) Daga Majalisar dinklin duniya August 30, 2025 Iran: IRGC Sun Kama Ma’aikatan Mosad A Arewa Maso Gabacin Kasar August 30, 2025 Iran Ta Yi Watsi Da Shirin ‘SnapBack’ Na Kasashen Turai August 30, 2025 E3 sun gindaya sharudda 3 kan dakatar da dawo da  takunkuman MDD a kan Iran August 30, 2025 Amurka ta hana izinin shiga kasarta ga shugaban Falastinawa don halartar taron MDD August 30, 2025 Rwanda ta dauki bakin haure kashi na farko da aka kora daga Amurka August 30, 2025 Jami’in Sojin Isra’ila: Masu Tunanin Hizbullah Ta Yi Rauni Suna Mafarki Ne August 30, 2025 Mali: Kungiyar Al-Qaeda ta kwace iko da garin Farabougou da ke tsakiyar kasar August 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: gwamnatin mamayar Isra ila

এছাড়াও পড়ুন:

Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan

Isra’ila ta amince da gina sabbin gidaje 1,300 a yankin Gush Etzion, kudu da Gabashin Urushalima da ta Mallake, wanda hakan ke nuna wani sabon ci gaba da fadada matsugunai ba bisa ka’ida ba a fadin Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye.

A cewar tashar talabijin ta Isra’ila Channel 14, Kwamitin tsare-tsare da Gine-gine na musamman da ke kula da matsugunan da ke Gush Etzion ya amince da wannan shawara a farkon wannan makon, inda ya shafi unguwar Har HaRusim, wadda ke kusa da matsugunan Alon Shvut, kudu maso yammacin Gabashin Urushalima da aka Mallake.

Shirin bai shafi gidaje ba kawai, har ma da gina makarantu, wuraren jama’a, wuraren shakatawa, da kuma babbar cibiyar kasuwanci da aka yi niyya don yi wa al’ummomin da ke makwabtaka hidima.

Majalisar Yankin Gush Etzion ta yi maraba da wannan mataki, tana mai ganin hakan a matsayin martani ga karuwar bukatar mazauna yankin.

Wannan sanarwar ta zo ne kwanaki kadan bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da damuwar da ake da ita game da ayyukan Isra’ila a Yammacin Kogin Jordan.

Jawabin Trump ya zo ne a daidai lokacin da majalisar dokokin Isra’ila ta Knesset ta amince da wasu kudirori biyu da nufin hade Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye da kuma yankin Ma’ale Adumim.

Irin wadannan matakai za su ware Gabashin Kudus daga yankunan Falasdinawa da kuma raba Yammacin Kogin Jordan zuwa yankuna biyu daban-daban, don haka za su kawo cikas ga yiwuwar hadewar kasar Falasdinu.

Majalisar Dinkin Duniya da yarjejeniya kasa da kasa sun sha nanata cewa matsugunan Isra’ila a yankin Falasdinawa da aka mamaye haramtattu ne a karkashin dokokin kasa da kasa, gami da Yarjejeniyar Geneva ta Hudu.

Bugu da kari, kungiyar kare hakkin dan adam ta Peace Now ta bayyana shirin E1 a matsayin “mummunan rauni” ga samar da Falasdinu, tana mai jaddada cewa aiwatar da shi zai kawo cikas ga yunkurin kafa kasar Falasdinawa.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 An Kafa Dokar Ta Baci A Darul-Salam Saboda Tarzoman Zaben Shugaban Kasa A Tanzania October 30, 2025 Rasha Da Amurka Sun Sake Dawo Da Gwaje-gwajen Makaman Nukiliya October 30, 2025 Kasar Czech Ta Hana Wa Wani Sojan HKI Shiga Kasar Bisa Gargadin  Faransa October 30, 2025  Sojojin HKI Sun Kutsa Kudancin Lebanon October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza
  • Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon
  • MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania
  • Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara
  • HKI Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza Inda Take Kashe Falasdinawa
  • An Tube Yarima Mai Jiran Gado Na Birtaniya Bayan Da Aka Tabbatar Da Laifinsa
  • Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta
  • Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar
  • Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Duk Wani Kutse Na Isra’ila A Kudancin Kasar
  • Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan