HausaTv:
2025-09-17@21:50:55 GMT

Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 136

Published: 31st, August 2025 GMT

136- Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane, Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana jalaluddin Rumi.

Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

////…Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-mujtapa (a) jikan manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun bayyana yadda aka fara yakin Siffin yakin da ya sauya tarihin musulunci, yakin da, da ba’a ya shi ba da duniyar musulmi da kuma sauran mutane ba haka zai kasance ba. Sabu a siffin ne aka kulla makirce-makirce wadanda suka sauya fuskan addinin All..zuwa addinin sarakunan banu umayya da Abba siyawa daga bayan.

Bayan da Imam Ali (a) ya debe kauna dawowan Mu’awiya, sai ya kulla tutoci, ya bawa kwamandojin sojijinsa wadanda suka hada da Malikul Ashtar, Ammar dan yasir, Ash’ash dan kais alkindi Abdullahi dan Abbas da sauransu, haka ma mu;wiya ya rarraba tutocinsa ga kwamandujikinsa, Ubaidullahi dan Umar Abdullahi dan Amru dan Ashi, da Dhahaak da sauransu.

Imam (a) yayi masu khuduba wanda ya saba yi kafin yaki, kamar yadda yayi A jamal musamman sanin wannan yaki tsakanin musulmine, don haka ya bayyana musu, sabbin dokokin yaki wadanda basu taba saninsu, wadanda suka hada da, cewa kada su bi wanda ya juya baya daga yakin, kada su karasa wanda yi rauni, kada su shiga tentunansu na tafiya, kada su daga labule kada su shiga wani gida ba tare da sallama ba, kada su dauki wani abu daga wajensu sai abinda ya shafi yaki wato kamar takobi ko dawakansu na yaki, amma duk sauran gado ne ga magadansu.

Sannan aka fara yaki jefi jefi saboda Imam (a) yana fatan mu’awiya ya dawo daga dagawarsa ya tuba. Suna cikin wannan halin har watan muharram ya shigo, suna daina yaki. Na wata guda, sannan a cikin wannan lokacin sukan shudanya da juna babu fada a lokacinda Safar ya shigo sai suka koma yaki. Ana cikin wannan halin ne,  Mu’awiya ya aiki Ubaidullahi dan Umar ya je ya kodaitar da Imam Hassan (a) ko muce ya yaudare shi, kan ya dawo bangaren su ya bar babansa Immam Ali (a), saboda ya kashewa kuraishawa iyayensu a yake-yaken da yayi tare da manzon All..(s), sai Imam hassan ya ce babansa yayi dai dai tunda a kan tafarkin All..ya kashe su. A nan ne sai  yace masa mu’awiya ya yi alkawalin zai bashi khalifanci idan ya koma bangarensa. A lokacin Imam Hassan (a) ya ji wadannan kalaman, sai ya daka masa tsawa, ya kuma bayyana masa cewa hakan ba zai taba yi yu wa ba.

Sai Imam yayi masa wani kallo, na fushi a fuskansa, sai yace masa nan gaba kadan za’a kashe ka wannan yakin. Ya kara da cewa:

{Sai dai ina son sanar da kai, za’a kashe ka yau ko gobe. Imma shaitan ya kawata maka, ya yaudareka, sai da ya fito da kai, kana dauke da wannan halin, matan sham zasu ga matsayinka da , kuma All..zai turbude fuskanka matacce.)

Sai Ubaidullah ya koma wajen Mu’awiya ya kuma fada masa abinda ya fada da martanin da ya mayar masa. Sai Mu’awiya ya ce: Lallai shi dan babansa ne.

Daga nan sai Ubaidullah ya fita yaki tare da makiya, sai ya gamu da wani mutum wanda ake kira Fazza Nabil daga Hamdan, sai ya kashe shi, sannan ya zauna a wurin, ya jingina da gawar Ubaidullahi dan Umar, sannan ya daura dokinsa a kafar gawar.

Sai Imam Hassan (a) ya zo wurin tare da wasu daga cikin  magoya bayansa. Sai ya masu ku duba waye yake jingine da gawannan ?  sai suka je suka gani suka dawo suka fada masa,  wani mutumin Hamadan ne kuma gawar ta Ubaidullahi dan Umar ne, sai Imam ya yi farinciki da hakan. Ya fadi hakan yana mai murmuci: {Godiya ta tabbata kan Hakan.}

Don haka daga karshe dai Ubaidullahi dan Umar ya hadu da ajalinsa yana mai yakar All..da manzonsa (s). kuma mai zaluntar musulmi, kuma a matsayin dan tawaye ga shugaban musulmi Aliyu dan Abitalib(a).

Daga nan sai yaki na gama gari, ko gaba daya. A lokacin da Imam (a) ya ga cewa babu alamun mu’awiya zai dawo sai ya sake tsara sojojinsa ta yadda za’a shiga yakin yaki n agama gari. Bayan da Mu’awi ya ga haka shi sai ya sake tsara sojojinsa.

Ana cikin wannan halin sai Imam al-Hassan (a), ya fara kaiwa sojojin Mu’awiya hare-hare, a lokacinda Imam ya ga haka sai ya damu sannan ya fadawa wadanda suke kusa da shi,

{Ku kama mani wannan yaron, kada ya halakani, don ni ina matukan kare wadan nan –Al-hassan da al-Al-hussain (a) daga mutuwa, don kada zuriyyar manzon All..(s) ya yanke a kansu}.  

Don haka yaki ya barke tsakanin rundunonin biyu, har saida mutane kowa ya ji tsoron mutuwa, kowa yana iya mutuwa a ko yaushe, sai an kutsa cikin bangaren damar sojojin Imam (a). tsakiyar rundunarsa ta yi rauni. Kuma faduwa ta bayyana a wajenta.

Sai ya kira Sahal dan Hunaif, a lokacinda ya zo, sai yace masa ya koma ta dama tareda wadanda suke tare da shi. Da suka isa, sai sojojin sham suka far ma su, sai suka tare su suka kuma tarwatsu. Sai suka koma ta hagu.

Imam (s) da kansa yana shiga yakin , sannan yayansa suna tare da shi suna tare masa duk wasu makaman da suke zuwa kansa. Sai wani mai suna Ahmar Kisan daga cikin bayin Banu Umayya, ya nufi Imam (a), yana cewa sai ya kasashe, ya yi ta kutsawa har ya zo kusa da Imam (a) sai ya kamashi ya daga sama ya jefa shi a kansa yakarya masa ya karya kafadu da hannayensa, Imam Hussain (a) da Muhamm dan Hanafiyya suka karasa shi.

Sai wasu Jama’a daga sojojin sham sun zo kusa da Imam (a) Sai Imam Hassan (a) Yace masa: Da ka dan gushe zuwa kusa da sojojimmu (wato Bani Rabee,) daga cikin mutanemmu. Sai  Imam Ali (a) ya fahinci abinda yake nufi: Sai ya fadawa Imam Hassan a hankali yana cewa

{Ya da na, babanka yana da wata rana, wanda ba zai ketareta ba, kuma kokari ba zai nesantata daga gareta ba, kuma takwa ba zai jinkirta zuwanta gareshi  ba, Lalle wallahi  Babanka bai damu da fadawa mutuwa ba ko mutuwa ta fada masa ba}  

Don haka bayan da sojojin Imam suka tarwatse suka bar Imam (a) tare da yayansa, sai Malik dan Ashtar, yayi sauri ya zo wajensa don kada makiya su kashe shi, a lokacinda ya iso sai Imam (a) ya ca masa

{Ya Maliku, sai ya masa –labbai-Ka je wajen wadan nan mutane, ka fada masu cewa: Ina ne gudunku daga mutuwa, Wanda rayuwa  bazaku taba gagareta zuwa rayuwa ba, , wacce itama ba zata rege kowa daga cikinku ba.?}.

Sai Malik ya je wajen wadanda suka tarwatse a gaban Imam suka barshi a cikin makiyansa, ya kirasa ya fada masu sakon Imam, sannan yayi ta masu jawabi, masu nishadantarwa, wanda kuma ya sake basu karfin giwa, sai kuma suka dawo wajensa, ya sake nanata masu kan cewa shi ne Malik dan Ashtar, wansa suka sani da jarunta da kuma iya yaki.

Sannan da ya samu ya sake tarasu, suka tunkari sojojin Mu’awiya saida suka dangana da haimarsa, mu’awiya ya fara shirin gudu. Don kada Malik ya riske shi.

A lokacinda Mu’awiya ya ga raunin da ya bayyana a sojojinsa, ya kira masu shawara da shi wato Amru dan Asee, don sanin abinda zasu yi.

A dayan bangaren kuma Ammar dan yasir ya ga yadda kawukan mutane suke fadawa a cikin yakin, kasar Siffin gaba daya y ajika da jinin mutane, daga cikin muminai da Fasikai. Ko azzalumai. da kuma tsananin da ake ciki sai ya fada cikin tunani yana cewa:

Manzon All..(s) yayi gaskiya…wannan itace ranar da manzon All..(s) ya yi masa bushara da shahada,. Yana cewa tabbas wadannan suke azzalumai (kamar yadda manzon All..) ya kirasu. Wannan it ace ranar da manzon All..(a) yayi mani alkawali, gas hi na kusan shekara 90 a duniya me neke jira. ? Rahamarka ya Ubangiji! Hakika ni ina shaukin haduwa da yan’uwana wadanda suka rikani a Imani, ..da sannu zan hadu da Ubangijina, ina mai jihadi da makiyansa, a  gaban waliyyinsa kuma wasiyin manzonsa, (s),kuma khalifansa a bayansa.To lalle ina ganin yau ce ranar da manzon All..(s) yayi mani alkawali.

Daga nan yayi ta kallon tutocin a yakin sai ya ga cewa, tutocinsu sun yi kama da tutocin manzon All…(s) a badar da uhudu da kuma Hunain, a yayinda dayan bangaren kuma ya yi kama da tutocin  mushrikai da rundunoni.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu wassalamu Alaikum wa vrahamatullahi wa barakatuhu.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Sami Nasarar A Kan Amurka A Gasar Volleyball Na Kasa Da Kasa August 31, 2025 Rasha Tace: Masu Son Yaki A Turai Suna Zangon Kasa Ga Kokarin Trump Na Kawo Karshen Yaki A Ukraine August 31, 2025 AU Da WHO Zasu Hada Kai Don Yakar Cutar Kolera  A Nahiyar Afirka August 31, 2025 Almashat: Yemen Za Ta Dauki Fansar Jinin Shahidanta A Kan Sahyuniyawa August 31, 2025 Iran ta yi Allawadai da kisan jami’an gwamnatin Yemen da Isra’ila ta yi August 31, 2025 Yemen: Firayi Ministan da wasu ministoci sun yi shahada a wani harin Isra’ila August 31, 2025 Argentina: Lauyoyi sun bukaci a cafke Netanyahu a kan laifukan yaki August 31, 2025 Sudan: Hamedti ya yi rantsuwar shugabantar gwamnati mai kishiyantar gwamnatin kasar August 31, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Ce: Ba Za Su Kyale A Lalata Alakar Iran Da Armeniya Ba August 30, 2025 Larijani: Iran Tana Adawa Da Juya Akalar Siyasar Yankin Daga Wasu Masu Son Baba-Kere August 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Ubaidullahi dan Umar a cikin wannan Masu sauraro wadanda suka wannan halin masu sauraro mu awiya ya Mu awiya ya

এছাড়াও পড়ুন:

NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025

A cewarsa, ɗalibai 1,367,210 ne suka yi rajistar jarrabawar; maza 685,514 da mata 681,696.

Daga cikinsu, ɗalibai 1,358,339 ne suka rubuta jarrabawar, waɗanda suka haɗa da maza 680,292 da mata 678,047.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
  • NECO ta saki sakamakon jarabawar 2025
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025
  • Chadi:  Majalisa ta amince a baiwa shugaban kasa  damar ci gaba da Mulki har karshen rayuwa
  • Sowore Ya Maka DSS, Meta da X A Kotu Kan Take Masa Haƙƙi
  • Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
  • NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano
  • Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 
  • An kama mabaraci da kuɗaɗen ƙasar waje a Ilorin