Maduro: Aikewa da sojojin ruwan Amurka a yankin Caribbean babbar barazana ce ga yankin
Published: 2nd, September 2025 GMT
shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana cewa, Aikewa da sojojin ruwan Amurka a yankin Caribbean itace barazana mafi girma ga al’ummomin yankin a cikin wannan karni.
Da yake magana a wani taron manema labarai, Maduro ya ce an jibge jiragen ruwan sojan Amurka guda 8 dauke da makamai masu linzami 1,200 da kuma na nukiliya a gabar tekun Venezuela.
Maduro ya zargi Washington da aiwatar da manufar matsin lamba ta soja a kan Caracas, wanda ya tilasta wa Venezuela ayyana cikakken shirin tsaron kasa.
“Venezuela kasa ce mai zaman lafiya, amma al’ummarta mayaka ne kuma ba za su taba yin watsi da barazana ko cin zarafi a kan kasarsu ba,” in ji shugaba Maduro.
A cikin watan Agustan 2025, Washington ta tura wasu manyan jiragen ruwa masu daukar makamai masu linzami guda uku, wato USS Gravely, USS Jason Dunham, da USS Sampson, kusa da yankin ruwan Venezuelan. Tare da sojoji da yawansu ya kai 4,000, lamarin da ya fuskanci tofin Allah tsine a fadin Latin Amurka.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Araghchi : China da Rasha sun bi sahun Iran wajen kin amincewa da yunkurin E3 na dawo mata da takunkumai September 2, 2025 Guterres: Hakkin Iran Ne Ta Mallaki Fasahar Nukuliya Ta Zaman Lafiya September 2, 2025 Pezeshkian: Dole Ne Kungiyar Hadin Gwiwar Shanghai Ta Zama Hanyar Sanar Da Zaman Lafiya A Duniya September 1, 2025 Shawarar Iran A Taron Shanghai Zai Durkusar Da Darajar Dalar Amurka A Duniya September 1, 2025 Baqa’i Ya Ce: Iran Zata Kare Muradunta A Zaman tattaunawanta Da Tawagar Kasashen Turai September 1, 2025 Adadin Mutanen Da Suka Mutu A Girgizar Kasar Afganistan Ya Karu Zuwa 800 September 1, 2025 Dakarun Kai Daukin Gaggawar Kasar Sudan Sun Kai Hari Kan Birnin El Fasher Da Ke Darfur September 1, 2025 Ana Fargaban Daruruwan Mutane Sun Rasa Rayukansu A Girgizan Kasa A fganistan September 1, 2025 An Gudanar Da Jana’ar Jami’an Gwamnatin Kasar Yemen Da Suka Yi Shahada September 1, 2025 Sojojinn Yemen Sun Kai Hari Kan Wani Jirgin Daukar Mai Na Haramtacciyar Kasar Isra’ila September 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya
Hukumar zaben kasar Tanzaniya ta bayyana shugabar kasa mai ci Samia Suluhu Hassan a matsayin wadda ta lashe zaben shugaban kasar.
Shugaban hukumar zaben ya ce Shugaba Samia ta yi nasara a zaben da kashi 98% na jimillar kuri’un da aka kada.
Bayanai sun ce manyan ‘yan takarar adawa ba su shiga ba, wasu kuma an tsare su ko kuma an hana su tsayawa takara, wanda hakan ya haifar da tashin hankali.
Jam’iyyar adawa ta kasar ta ce daruruwan mutane ne suka mutu sanadiyyar zanga-zangar da aka kwashe kwanaki ana yi tun bayan zaben na ranar Laraba.
Wani mai magana da yawun jam’iyyar adawa ta Chadema ya shaida wa AFP cewa kimanin mutane 700 ne suka mutu, a alkalumman da aka tattara daga asibitoci.
Gwamnatin Shugaba Samia ta musanta duk wani “yin amfani da karfi fiye da kima,” yayin da Ministan Harkokin Waje Mahmoud Thabit Kombo ya shaida wa Al Jazeera cewa babu “bayani” kan adadin wadanda suka mutu.
Hukumomin sun katse hanyar intanet, sun sanya dokar hana fita, kuma sun takaita ‘yan jarida, wanda hakan ya takaita samun bayanai.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar November 1, 2025 Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific November 1, 2025 Israila Ta Kai Hari Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A November 1, 2025 Amurka Na Shirin Kai Hari Kan Kasar Venzuwela A Kowanne Lokaci November 1, 2025 Iran Ta Sanya Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3 October 31, 2025 Isra’ila Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza October 31, 2025 An Tube Yarima Mai Jiran Gado Na Birtaniya Bayan Da Aka Tabbatar Da Laifinsa October 31, 2025 Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta October 31, 2025 M D Duniya Tayi Gargadi Game Da Gwajin Nukiliya Da Amurka Ta Sanar Za ta yi October 31, 2025 Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda October 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci