Xi na karɓar baƙuncin taron SCO a China
Published: 31st, August 2025 GMT
Shugaban ƙasar China, Xi Jinping, na karɓar baƙuncin taron ƙungiyar Shanghai Cooperation Organisation (SCO) a birnin Tianjin, inda shugabannin ƙasashe kusan 20 daga yankin Eurasia suke halarta.
Taron, wanda zai gudana har zuwa Litinin, ana kallon sa a matsayin wani babban dandalin da ke ƙara tabbatar da matsayin China a tsakiyar harkokin siyasar ƙasashen Eurasia.
Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya isa Tianjin da manyan jami’an gwamnati da ’yan kasuwa daga ƙasarsa, inda kuma ya yi shirin gudanar da tattaunawa da shugabannin ƙasashe daban-daban a gefen taron.
Firayim Ministan Indiya, Narendra Modi, shi ma yana halartar taron, wanda ya kai ziyara ta farko zuwa China tun shekarar 2018.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin X, Modi ya ce: “Indiya za ta ci gaba da gina dangantaka da China bisa amincewa, mutuntawa da kuma fahimtar juna.”
Ya ƙara da cewa haɗin kan ƙasashen biyu zai amfanar da al’ummominsu da suka haura biliyan 2.8, tare da samar da ci gaba ga bil’adama gaba ɗaya.
Rahotanni sun nuna cewa tsohon rikicin iyaka tsakanin ƙasashen biyu da ya haddasa mutuwar sojoji a 2020, ya fara lafawa tun daga bara lokacin da shugabannin suka haɗu a wani taro a Rasha.
Daga cikin manyan shugabannin da suka halarci taron akwai shugaban ƙasar Belarus, Alexander Lukashenko, shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, da kuma shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, lamarin da ya sanya taron na bana zama mafi girma tun kafa ƙungiyar a 2001.
Masana sun bayyana cewa China da Rasha na amfani da SCO a matsayin wata hanya ta ƙarfafa tasirinsu a duniya a matsayin kishiyoyin ƙungiyoyin Yamma kamar NATO, musamman ganin yadda rikicin Ukraine da batun Taiwan ke jawo saɓani tsakaninsu da Turai da Amurka.
Bincike ya kuma nuna cewa Rasha na fatan amfani da SCO wajen samun goyon bayan ƙasashe masu tasowa, tare da ƙara kusantar Indiya a lokacin da take samun saɓani da Amurka kan batun shigo da mai daga Rasha.
Taron na Tianjin ya zo ne ’yan kwanaki kafin bikin gagarumin faretin soji da za a gudanar a birnin Beijing ranar Laraba, wanda zai ja hankalin shugabanni da dama daga sassa daban-daban na duniya, ciki har da Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Belarus Indiya Iran Koriya ta Arewa Kyrgyzstan Narendra Modi Rasha
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Taya Amusan Da Gumel Murnar Samun Nasarori A Ɓangarori Daban-daban
Shugaban ya yaba da abinda ya kira kwarewa da juriya irin na Amusan, tare da cewa aikinta ya sake misalta irin daukakar da yan Nijeriya za su iya samu ta hanyar aiki tukuru da nuna kwazo, Tinubu ya yi fatan Gumel da Amusan su ci gaba da samun nasara a ayyukansu tare da ba su tabbacin gwamnati za ta ba su cikakken goyon baya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp