Shugaban Zimbabwe Ya Sauka Beijing Domin Halartar Bikin Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Mamayar Dakarun Japan
Published: 2nd, September 2025 GMT
A yau Litinin shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya iso birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin domin halartar bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin mamayar dakarun Japan, da yakin kin tafarkin murdiyya na duniya.
Shugaba Mnangagwa ya sha ziyartar kasar Sin, inda a shekarar da ta gabata ma ya zo birnin Beijing domin halartar taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC tare da gudanar da ziyarar aiki a kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ya Kamata A Kiyaye Nasarorin Da Aka Cimma A Shawarwarin Sin Da Amurka
Daga ranar 14 zuwa 15 ga wata, an gudanar da sabon zagayen shawarwari kan harkokin tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka a birnin Madrid, babban birnin kasar Spaniya, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra’ayoyi a kan harkokin cinikayya da ke janyo hankalinsu, tare da cimma daidaito ta fannin daidaita batutuwan da suka shafi Tiktok, da rage shingayen zuba jari, da sa kaimin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu.
Taron shawarwarin ya kasance zagaye na hudu da sassan biyu suka gudanar cikin watanni biyar da suka wuce. Kwatankwacin shawarwarin da aka gudanar a baya, a karo na farko, an sanya Tiktok cikin batutuwan da aka tattauna a shawarwarin na wannan zagaye. Yadda Sin da Amurka suka cimma daidaito a kan batun, ya kuma sake shaida cewa, samun moriyar juna shi ne tushen huldar kasashen biyu ta fannin tattalin arziki da cinikayya.
Hada karfi da karfe shi ne mafita daya tilo, a yanayin da ake ciki na karancin karfin bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Ba za a rasa samun sabanin ta fannin tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka ba, amma duk da haka, akwai mafita idan sun dinga yin shawarwari da juna. A gaba, ya kamata sassan biyu su tabbatar da daidaito da shugabannin kasashen biyu suka cimma, musamman ma ya kamata Amurka ta samar da yanayin kasuwanci mai adalci ga kamfanonin kasar Sin, ciki har da Tiktok, kuma ta yi hadin gwiwa da kasar Sin, don su kiyaye nasarorin da suka cimma a shawarwarin, don tabbatar da hada-hadar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu yadda ya kamata. (Lubabatu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp