Girgizar ƙasa ta kashe mutum 610 a Afghanistan
Published: 1st, September 2025 GMT
Aƙalla mutum 610 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu sama da 1,300 suka jikkata sakamakon girgizar ƙasa mai ƙarfi da ta afku a ƙasar Afghanistan.
Rahotanni daga hukumomi da kafafen watsa labarai na duniya sun ce ibtila’in ya auku ne a yankin gabashin ƙasar Afghanistan, kusa da iyakarta da Pakistan.
Rahoton Hukumar Binciken Ƙasa ta Amurka (USGS) ya bayyana cewa ƙarfin girgizar ƙasar ta kai matakin 6.
An gano cewa girgizar ta afku a zurfin kilomita takwas kacal daga saman ƙasa, wanda hakan kan ƙara tsananta illarta.
Rushe Kasuwar Alaba Rago: Ya kamata shugabannin Arewa su sa baki An ƙone wata mata ƙurmus kan yi wa Annabi ɓatanci a NejaKamfanin Dillancin Labarai na AP ya rawaito cewa akwai yiwuwar adadin mutanen da suka mutu zai ƙaru yayin da ake ci gaba da binciko gawarwaki da kuma ceton waɗanda ke cikin ɓaraguzan gine-gine.
Haka zalika, New York Times ta ce an ji girgizar a Kabul — babban birnin Afghanistan — da ke tazarar kilomita 160 daga Jalalabad, duk da cewa ba a tabbatar da samun mace-mace a can ba.
Mai magana da yawun gwamnatin Taliban, Zabihullah Mujahid, ya wallafa a shafinsa na X cewa, “Muna cikin alhini kan asarar rayuka da asarar dukiya da wannan girgizar ƙasa ta haddasa a wasu yankunan gabashin ƙasarmu. Jami’ai da mazauna yankin suna ci gaba da aikin ceto.”
Me ke kawo yawon girgizar ƙasa a Afghanistan?Afghanistan na fuskantar yawan girgizar ƙasa saboda matsayinta na tectonic.
Wannan yanayi ne da ke haifar da fashewar ƙasa akai-akai, musamman a yankunan tsaunuka da ke gabashin ƙasar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Girgizar ƙasa girgizar ƙasa
এছাড়াও পড়ুন:
Hauhawar farashi ya ragu a watan Agusta — NBS
Hukumar ƙididdigar a Najeriya NBS ta bayyana cewa an samu raguwar hauhawar farashin kaya a watan Agusta idan aka kwatanta da watan Yulin da ya gabace shi.
Cikin sabbin alƙaluman da NBS ta fitar a ranar Litinin sun nuna cewa an samu raguwar kashi 1.76 a watan Agustan saɓanin watan Yulin, wanda ya nuna karo na hudu ke nan a jere hauhawar farashin yana sauka.
NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas Kundin Bajinta na Guinness ya taya Hilda Baci murnaRahoton na hukumar NBS na zuwa ne kwanaki bayan da Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin karya farashin kayan abinci ƙasar.
A watanin baya-bayan an riƙa samun raguwar hauhawar farashin kayyaki a ƙasar.
Ko alƙaluman da NBS ta fitar a watan Yuni, ta bayyana cewa hauhawar farashi a Najeriya ya sauka zuwa kashi 22.22 daga 22.97 da aka samu a watan Mayu.
A baya dai dai an yi ta kiraye-kirayen gwamnatin ƙasar ta ɗauki matakan rage hauhawarar farashi domin magance tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar.