Babban Sakataren MDD: Sin Ta Taka Rawar Gani Sosai Wajen Cimma Nasarar Yakin Duniya Na Biyu
Published: 3rd, September 2025 GMT
Babban sakataren MDD António Guterres, wanda ya halarci taron kolin kungiyar hadin gwiwar Shanghai wato SCO da aka gudanar a birnin Tianjin dake kasar Sin, ya bayyana cewa, Sin ta taka rawar gani sosai wajen cimma nasarar yakin duniya na biyu. Kuma gudummawar da Sin ta bayar ita ce mabudin nasarar da kawancen kasashen duniya suka samu a yakin duniya na biyu.
Bugu da kari, Guterres ya jaddada ta hanyar nuna batutuwan tarihi cewa, babbar mamayar da Japan ta yi wa Sin ita ce farkon yakin duniya na biyu na gaskiya. Guterres ya yi imanin cewa, tsayin daka da kasar Sin ta yi wajen yin tir da hare-haren Japan, ya taka muhimmiyar rawa a tsawon shekaru da dama, tare da ba da muhimmiyar gudummawar raunana Japan, kuma a karshe hakan ya kai ga murkushe Japan a karshen yakin duniya na biyu. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: yakin duniya na biyu
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
Daga Usman Muhammad Zaria
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi sabbin motoci 10 kirar Toyota Hilux da Gwamna Umar Namadi ya bai wa rundunar a Dutse, babban birnin jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, CP Dahiru Muhammad ya yaba da jajircewar Gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa hukumomin tsaro domin sauke nauyin da ke kansu a jihar.
Ya bayyana cewa, wannan gudummawa ta nuna cikakken kudirin gwamnatin Gwamna Namadi na ƙara inganta harkokin tsaro da kuma tallafawa Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya wajen aiwatar da aikinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.
Kwamishinan ya nuna cewa, waɗannan sabbin motoci 10 za su taimaka matuƙa wajen rage lokacin da ake ɗauka kafin amsa kiran gaggawa, tare da ƙara inganta aikin rundunar a fadin jihar.
Ya ƙara da cewa, za a yi amfani da motocin yadda ya kamata, tare da kula da su don tabbatar da ingantaccen tsaro.
CP Dahiru Muhammad ya kuma sake jaddada aniyar rundunar wajen ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, doka da oda, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki.