Leadership News Hausa:
2025-09-17@21:50:11 GMT

Antonio Guterres: Xi Jinping Shugaban Kasa Ne Mai Sanin Ya Kamata

Published: 1st, September 2025 GMT

Antonio Guterres: Xi Jinping Shugaban Kasa Ne Mai Sanin Ya Kamata

Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, wanda ya shigo kasar Sin don halartar taron koli na kungiyar hadin-kai ta Shanghai wato SCO na bana, ya zanta da dan jaridan babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a birnin Tianjin, inda ya ce, Xi Jinping shugaban kasa ne mai sanin ya kamata wajen tsara manyan tsare-tsare.

Guterres ya ce, akwai misalai da dama da suke iya tabbatar da haka. Alal misali, shugaba Xi ya taba sanar da burin gina na’urorin samar da wutar lantarki bisa makamashin da ake iya sabuntawa, wadanda karfinsu ya zarce kilowatt biliyan 1.2 zuwa shekarar 2030 a kasar Sin, wanda aka riga aka cimma shi.

Kazalika, ya yi alkawarin cimma nasarar kaiwa ga kololuwar fitar da sinadarin carbon a kasar Sin kafin shekarar 2030, wanda tuni aka cimma nasararsa. Har wa yau, yayin da kasashe da dama ke tunanin dabarun kyautata motoci dake aiki da man diesel, tun shekaru da dama da suka wuce kasar Sin ta kuduri aniyar kara raya kirar motoci dake aiki da lantarki, kuma a halin yanzu irin wadannan motocin na mamaye kasuwannin dukkanin fadin duniya.

Guterres ya kuma ce, yayin da duniyarmu ke fuskantar tarin yanayin rashin tabbas, abu ne mai wuya a iya tsara manufofi masu dorewa, don haka, sanin ya kamata da shugaba Xi ke da shi wajen tsara manufofi na da matukar muhimmanci. (Murtala Zhang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaban Kasar Iran Ya Gana Da Sarkin Kasar Qatar A Birnin Doha

Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan wanda yake halartar taron brinin Doha, na kasashen musulmi da larabawa, ya gaba da sarkin Qatar Tamim Bin Hamad ali-Thani, inda su ka tattaunawa halin da ake ciki a wannan yankin na yammacin Asiya.

Taron na Doha ne na gaggawa ne wanda aka shriya shi, domin tattauna harin wuce gona da iri da HKI ta kai wa kasar Qatar a wani yunkurin yi wa shugabannin Falasdinawa kisan gilla.

A yayin wancan harin dai, ‘yan sahayoniyar sun harba makamai masu linzami fiye da 10 akan wani gini wanda jami’an kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas suke taro a ciki.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka  Dan Kasar Iran Mai Kirkira Ya Sami Kyautar Yabo A Kasar China September 15, 2025 Fizishkiyan:  Wajibi Ne Musulmi Su Hada Kai Domin Dakatar Da Laifukan HKI September 15, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Qatar, Turkiyya, Pakistan Da Labanon A Doha September 15, 2025 Kwamitin Kolin Tsron Kasar Iran Ya Amince Da Yarjejeniyar Da Aka Cimma Da Hukumar IAEA September 15, 2025 Jami’in Kasar Yemen Ya Aike Da Sako Ga Mahalarta Taron Birnin Doha Na Kasar Qatar September 15, 2025 Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada Sakamakon Kisan Kiyashin ‘Yan Sahayoniyya A Gaza Ya Kusaci 65,000 September 15, 2025 Gwamnatin Sudan Ta Ce: Babu Sulhu Da ‘Yan Tawayen Kasar Na Kungiyar Rapid Support Forces September 15, 2025 Kasashen Larabawa da na Musulmi na taron gaggawa kan harin Isra’ila a Qatar September 15, 2025 Hamas ta bukaci kasashen musulmi da na Larabawa su dauki mataki mai tsari kan Isra’ila September 15, 2025 Rabin Sojojin Isra’ila da suka ji rauni a yakin Gaza na fama da ciwon damuwa September 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Har Kullum Burin Sin Shi Ne Wanzar Da Daidaito Da Cimma Moriya Tare Da Amurka
  • Guterres: Jerin Shawarwarin Da Sin Ta Gabatar Sun Cika Ka’idar Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya
  • Chadi:  Majalisa ta amince a baiwa shugaban kasa  damar ci gaba da Mulki har karshen rayuwa
  • Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
  • Pezeshkian: Ya kamata kasashen musulmi su yanke alaka da gwamnatin sahyoniya tare da kiyaye hadin kai
  • Mujallar Qiushi Za Ta Wallafa Sharhin Xi Jinping Mai Taken “Zurfafa Dunkulewar Kasuwannin Kasa Ta Bai Daya”
  • Fira Ministan Spain: Bai Kamata A Rika Barin “Isr’ila” Tana Shiga Gasar
  • Shugaban Kasar Iran Ya Gana Da Sarkin Kasar Qatar A Birnin Doha
  • Sin Ta Gano Wani Dutse Mai Sassaka Na Daular Qin A Kan Tsaunin Qinghai-Tibet
  • Kwamitin Kolin Tsron Kasar Iran Ya Amince Da Yarjejeniyar Da Aka Cimma Da Hukumar IAEA