2025-09-17@21:55:48 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6135
«kasashen musulmi su yanke»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Masu lura ko sa ido kan harkokin ilimi sun ce biyan kuɗaɗen cikin lokaci za su taimaka matuƙa wajen samun matsin da takurar da ƴan makaranta ko Iyayensu ke fuskant, bugu da ƙari kuma za su kasance a wuraren da suke karatu domin maida hankali kan abinda ya sa suke a makarantar ko kwalejin Hukumar ta kafar sadarwar zamani duk waɗanda suke amfana da tsari da su tabbatar da bayanan Banki da suka bada da na makaranta daidai suke domin hakan ne zai bada dama ta ci gaba da samun kuɗin duk lokacin da aka tashi biya ba ater da ɓata lokaci ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
Cikakkun bayanai kan halartar Iran zuwa taron shekara- shekara na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya na kasar Iran Muhammad Islami ya yi karin haske kan yadda Iran za ta halarci taron shekara -shekara na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA. Mohammad Eslami ya bayyana dangane da cikakkun bayanai na halartar taron shekara- shekara na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA inda ya ce: A gobe ne za a fara taron shekara- shekara na hukumar IAEA karo na 69 a birnin Vienna. Ya kara da cewa: “Iran zata tsara tare da gabatar da wani kuduri na yin Allah wadai da harin da aka kai kan cibiyoyin nukiliyarta na zaman lafiya...
Kabiru Abubakar Aliyu, wanda aka fi sani da Nakwango, ɗaya ne daga cikin jiga-jigan da aka kafa masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood da su. A cikin wannan tattaunawar, ya bayyana cewa bai taɓa yin da-na-sanin shigarsa sana’ar ba, sannan ya bayyana dalilin da yanzu ba a cika ganin sa sosai a fina-finai ba, da ma yadda ya ce fim ɗin Hausa ya taɓa zama silar sasanta wasu ma’aurata da aurensu yake tangal-tangal. Tun yaushe ka shiga harkokin fim ɗin Hausa? Ai harkar fim ɗin Hausa daga baya ta fito, a da wasan kwaikwayo ake yi. Na fara wasan kwaikwayo na rediyo wajen 1970, lokacin ina ƙarami. A lokacin rikoda ta fito. To a sannan na fito a matsayin mace...
Kamar yadda Oche, wadda ‘ya’yan ‘yar’uwarta suke zuwa makarantar Reno ta Oluwami da Firmare , da take Abuja inda shekarun baya suke biyan wajen Naira 600,000 ko wane zangon karatu, saboda wasu haraje- harajen da aka haɗa da su ciki. “Maganar gaskiya kowace shekara idan za’a shiga sabon zangon karatu, makarantu su kan ƙara kuɗin makaranta, su ƙara wasu sabbin abubuwa, kamar su kuɗin ICT, wasanni tsaro. Sai dai ƙarin da akwai matuƙar matsala.” A makarantar( Prime School ) da ke, Karu,inda aka ƙiyasta ana biyan kusan Naira 300, 000, kowane zangon karatu,wani Malamin da baya son a ambaci sunansa ya ce, akwai ƙarin kuɗin makaranta waɗanda suna da alaƙa ne da lamarin daya shafi kayn zuwa makaranta, bunƙasar makaranta,...
Kungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa (NARD) ta sanar da janye yajin aikin gargaɗi da ta fara bayan kwanaki biyu kacal. Sai dai ƙungiyar ta sake bai wa Gwamnati Tarayya mako biyu ta biya buƙatunta ko ta sake tsunduma yajin aiki. Shugaban ƙungiyar, Dakta Tope Osundara ne ya bayyana haka a ranar Asabar tare da umartar ɗaukacin mambobinsu da su koma aiki a yau Lahadi. Osundara, ya ce gwamnati ta biya musu wasu daga cikin buƙatunsu, tare kuma da alƙawarin duba sauran batutuwan da suke yajin aiki akan su. Tun a daren Juma’a ne likitocin masu neman ƙwarewa suka tsunduma yajin aikin na gargaɗi, bayan ƙarewar wa’adin da ƙungiyar ta ba Gwamnatin Tarayya kan batutuwan da suka shafi albashi, alawus, da...
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya buƙaci ƙasashen da ke cikin ƙungiyar tsaro ta NATO da su dakatar da cinikin mai da Rasha tare da sanya takunkumi, kafin Amurka ita ma ta bi sahu da irin nata takunkuman. Trump ya wallafa wannan bayani a shafinsa na Truth Social, wanda ya bayyana a matsayin wasiƙa ga dukkanin mambobin NATO da ma duniya baki ɗaya. Mun kori Falasɗinawa sama da dubu 250 daga Gaza — Isra’ila ’Yan rakiyar amarya 19 sun mutu a hatsarin mota a Zamfara Shugaban Amurkan ya ce ƙasarsa a shirye take ta sanya gagarumin takunkumi ga Rasha kan yaƙinta da Ukraine muddin ƙasashen NATO suka fara sanya irin nasu takunkumin da kuma dakatar da sayen mai na ƙasar. “A...
ADC ta ce, “APC tana tsoron ƙaruwar shaharar ADC a faɗin ƙasar nan ne, kuma yana bayyana cewa shi ne kawai hanyar da za su iya bi wajen tarwatsa ƴan adawa a ƙasar nan. “An fara ne a Jihar Edo da gargaɗin shugabannin ADC kan ka da su ziyarci jihar, sannan Kogi ta biyo baya, tare da rufe tashar rediyo ta kashin kai a Jihar Neja, kafin ya ƙaru zuwa ga kai hare-haren da aka ɗauki nauyi kan taronmu na Kaduna, sannan kuma da hare-hare a kan ayarin motocin shugabannin ADC a Kebbi. “Haka kuma an kai hari a wurin taron ADC a Alimosho a Jihar Lagos, wannan yana nuna cewa APC ta ji kunya kuma ba ta girma ko...
Aƙalla mutane 19 ne suka mutu a yayin da suka ɗauko wata amarya zuwa ɗakin mijinta bayan motarsu ta faɗa a ƙarƙashin gadar Gwalli da ke yankin Fass a Ƙaramar Hukumar Gummi a Jihar Zamfara. Lamarin ya faru ne da yammacin Asabar da misalin ƙarfe 4:45 na yamma, lokacin da motar, da ke ɗauke da maza da mata da yara ta faɗo daga saman karyayyiyar gadar, ta nutse a cikin ruwa. Wani ɗan uwan amaryar, Babangida Halifa Ibrahim Fass, wanda ya rasa ’yan uwa a cikin hatsarin, ya ce hatsarin ya faru ne a lokacin da ake kai ’yar uwarsa amarya gidan mijinta da ke Jega a Jihar Kebbi. Ya ce, “Motar ta faɗo ne daga kan gada ta nutse...
Wani mutum mai shekara 67 aka kai asibiti da raunuka masu barazana ga rayuwa, abin takaici kuma ya rasu a asibiti a ranar Juma’a, 5 ga Satumba. An bayyana sunansa da James Gbadamosi.” Bayan faruwar lamarin, ƴan sanda sun bayyana cewa sun kama Wright-Walter mai shekaru 37, suka gurfanar da shi bisa laifin kai hari a watan Agusta, amma aka ba da belinsa. Sai dai an sake kama shi a ranar Asabar bayan rasuwar Gbadamosi, sannan aka gurfanar da shi a gaban kotun majistare a ranar Litinin. Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Andre Wright-Walters, mai shekaru 37 (05.02.1988) na Aɓery Hill, Greenwich, an gurfanar da shi a ranar Lahadi, 7 ga Satumba. Ya bayyana a gaban kotun majistare ta...
Haka kuma, kamfanonin gwamnatin tarayya da suka durƙushe a jihar sun haɗa da: Nigeria Paper Mill, Jebba; Nigeria Sugar Company, Bacita; da Nigeria Yeast and Alcohol Manufacturing Company, Bacita. Yadda Tinubu Ya Shawo Kan Gwamnonin Arewa Wajen Amincewa Da Kafa Ƴansandan Jihohi Yadda Tinubu Ya Shawo Kan Gwamnonin Arewa Wajen Amincewa Da Kafa Ƴansandan Jihohi Jaridar LEADERSHIP Sunday ta gano cewa wasu kamfanonin gwamnati na jihohi sun riga sun durƙushe tun kafin zuwan tsarin mulkin dimokuraɗiyya na yanzu a Nijeriya a shekarar 1999. Haka kuma, an gano cewa wasu kamfanonin masu zaman kansu sun durƙushe ne sakamakon manufofin gwamnati marasa kyau, mawuyacin yanayin tattalin arziƙi, wutar lantarki mai yawan ɗauke wuta, shigowar kayayyaki marasa inganci, hauhawar farashin kayayyaki, tashin farashin...
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce Najeriya ta daɗe tana fama da shugabanni waɗanda ba su da nagarta. Ya bayyana haka ne a bikin “Kano International Poetry Festival” da aka yi a Kano a ranar Asabar. Gini mai hawa 3 ya rufta kan mutane a Legas HOTUNA: Mahaifiyar Dangote ta halarci gasar karatun Alƙur’ani ta Shetty a Kano Sarkin ya ce matsalolin ƙasar nan sun samo asali ne daga rashin shugabanci na gari. “Ƙasar nan tana tashi da faɗuwa bisa ingancin shugabanni. Najeriya ta daɗe tana fama da shugabanni marasa nagarta. “Kowace rana kuna gani a jaridu da labarai, ’yan majalisa suna ɓata lokaci kan abubuwan da ba su da amfani, yayin da sauran ƙasashe suke tattauna abubuwa kamar...
Wani gini mai hawa uku da ake ginawa ya rufta kan mutane a unguwar Yaba, da ke Jihar Legas. Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta ce ginin ya rufta ne da misalin ƙarfe 8 na dare. Gwamnatin Kuros Riba ta bankaɗo ma’aikatan bogi 800 HOTUNA: Mahaifiyar Dangote ta halarci gasar karatun Alƙur’ani ta Shetty a Kano Shaidu sun ce akwai mutane biyar zuwa shida a cikin ginin lokacin da abin ya faru. NEMA ta ce ta ceto mutum huɗu, kuma an garzaya da su asibiti domin kula da lafiyarsu. Sai dai hukumar ta ce ba a tabbatar da adadin waɗanda har yanzu suke ƙarƙashin ginin ba, yayin da ake ci gaba da aikin ceto.
A yau Asabar aka kaddamar da tashar watsa labarai ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) ta Sichuan, tare da kaddamar da wasu jerin ayyuka na CMG din a Chengdu babban birnin lardin Sichuan. Daraktan CMG Shen Haixiong ya halarci taron, inda a ciki jawabinsa ya ce kafar CMG za ta kara lalubo albarkatun dake bangarorin al’adu da yawon bude ido na Sichuan, da gabatar da kyawun al’adun Bashu da karfafa aikin sadarwa cikin ci gaba mai inganci na lardin Sichuan. Har ila yau, an kaddamar da cibiyar kirkire-kirkiren kimiyya da fasahohin bidiyo na ultra HD da na daukar murya da dakin gwaje gwajen ayyukan watsa labarai na kasa a birnin na Chengdu. (Mai fassara: Fa’iza...
Yau Asabar, an gudanar da taron dandalin tattauna al’adu na kasa da kasa na Golden Panda na 2025 a birnin Chengdu. Li Shulei, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan sashen fadakar da al’umma na kwamitin kolin JKS, ya halarta tare da sanar da bude taron. Mahalarta na kasar Sin da na kasashen waje da suka halarci bikin bude taron sun bayyana cewa, ba za a iya raba tinkarar kalubale da samun kyakkyawar makoma, da karfin al’adu da wayewar kai ba. Sun jaddada muhimmancin zurfafa hadin giwwar al’adu na kasa da kasa a fannonin raya ilimi, kimiyya da fasaha, al’adu, da kafofin watsa labarai don kara inganta hadin kan al’adu da mu’ammalar jama’a. Dandalin...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa alakar iran da Tunusiya wani babban misali ne na irin yadda kasar iran ke son su fadada dangantaka da sauran kasashen musulmi bisa girmamawa da mutunta juna. Haka zalika Araqchi ya jinjinawa kasar Tunusiya game da irin matakin da ta dauka musamman a lokacin harin wuce gona da iri da hki takai a kasar iran a watan yuni, yace wannan goyon bayan ya nuna irin zurfin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Kuma ya bayyana cewa iran a shirye take ta yi aiki da kasar tunusiya a bangarorin daban-daban wajen musayar kwararewar da suke da shi a bangaren kimiya da fasaha da dai sauransu. Ana ta bangaren kasar Tunusiya tace tana...
Rahotanni sun bayyana cewa babban zauren majalisar dinkin duniya ya amince daftarin kudirin dake nuna goyon bayan kafa kasar falasdimu mai cin gashin kanta, inda ka samu kasashe 142 suka kara kuri’ara amincewa yayin da kasashe 10 kuma sun nuna rashin amincewa sai kuma guda 12 da suka kauracewa kada kuria. Wannan daftarin kudurin ya nuna irin yadda duniya ke goyon bayan kafa kasar palasdinu adaidai lokacin da Isra’ila take ci gaba da kisan kare dangi a Gaza, yayin da duniya ke ci gaba da yin tir da cin zarafi da take hakkin dan adam a gazan, Duk da yake cewa wannan daftarin kudurin ba dole ba ne amma ya kara wa matakin kima a siyasance, kuma ya kara jan...
Shugaban kasar Serbia, Aleksandar Vucic, ya ce kasarsa na goyon bayan Shawarar Kula Da Harkokin Duniya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar. Shugaba Vucic ya bayyana haka ne yayin da yake hira da wakilin CMG a birnin Beijing na kasar Sin a kwanan baya, inda ya ce tsarawa da gabatar da wannan shawara mai ma’ana, ya zama wani abun da ya wajaba, saboda da farko, a zamanin da ake ciki, ana bukatar samar da karin ikon wakilci ga kasahe masu tasowa a fannin kula da al’amuran kasa da kasa. Kana na biyu, yanzu sannu a hankali ana lalata sakamako da nasarorin da dan Adam ya samu ta fuskar dokoki da ka’idoji na kasa da kasa, yanayin dake bukatar...
Ya ƙara da cewa: “Don haka taya ɗaya daga cikin shugabannin Nijeriya mafiya sauƙin kai, masu karamci da jarumtaka, murnar zagayowar ranar haihuwar sa, da roƙon Allah ya ci gaba da yi masa jagora a babban nauyin shugabanci na ƙasar Nupe da jama’ar ta, ya kuma ƙara masa ƙarfi don ci gaba da aiki wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai, da cigaban Nijeriya.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar ’yan sandan Jihar Anambra, ta fara bincike kan kisan wasu mutum huɗu da ’yan bindiga suka yi lokacin da suke zaman makoki. Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun buɗe wa masu makokin wuta ne a ranar Alhamis a garin Ogidi, da ke Ƙaramar Hukumar Idemili. Hilda Baci ta kafa tarihin dafa shinkafa buhu 200 a tukunya guda Abba ya tarbi tagwayen da aka raba da juna bayan yi musu tiyata a Saudiyya Harin ya yi sanadin mutuwar mutum huɗu tare da jikkata aƙalla mutum 15. Kakakin rundunar, Tochukwu Ikenga, ya ce suna zargin harin ya shafi rikicin ƙungiyoyin asiri ne. Ya ƙara da cewa jami’an tsaro da suka isa wajen sun gano harsasai 16, kuma za su yi amfani...
Dokar ta ba da damar dakatarwa na ɗan lokaci ko kuma cire rajistar Tax ID gaba ɗaya idan mai riƙe da shi ya daina gudanar da kasuwanci. A gefe guda, Dokar Kafa Hukumar Haraji ta Nijeriya, 2025, ta ba Shugaban Zartarwa na Hukumar babban ikon, wanda zai kasance shugaban Kwamitin Gudanarwa na hukumar. Kwamitin zai haɗa da wakilai daga Ma’aikatan Kuɗi, Tsare-Tsaren Ƙasa, Shari’a, Man Fetur, Babban Bankin Nijeriya, Haraji da Kwastam, Hukumar Kula da Harkokin Kamfanoni, da sauran muhimman hukumomi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga...
Shugaban rikon kwaryar Siriya ya bayyana cewa; Babu sabani na dindindin da Iran Shugaban rikon kwarya na Siriya Abu Mohammed al-Jolani ya yi magana kan alakar Siriya da sauran kasashe, inda ya mai da hankali kan Rasha, Iran da Masar. Ya kuma yi jawabi game da zaben Siriya da ayyana kundin tsarin mulkin kasar da kuma abubuwan da suka faru a lardin Suweida na kasar. Shugaban rikon kwaryar ya fada a jiya Juma’a cewa: Kasarsa ta yi saurin sake gina huldar dake tsakaninta da kasa da kasa, kana ta samu goyon baya daga galibin kasashe musamman na yankin. Ya yi nuni da cewa, ba za a so a kasance cikin halin damuwa da wata kasa ba, kuma kwallon tana cikin...
Wike ya goyi bayan Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a wani mataki da ya samu matsayin ministan Babban Birnin Tarayya Abuja. Duk da yake har yanzu shi mamba ne na PDP, Wike ya kasance yana bayyana cewa zai ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyar yayin da yake kuma yin aiki don sake zaɓen Tinubu, wani matsayin da yawancin mambobin PDP ba sa jin daɗinsa. Kafin yanzu, jam’iyyar ta shiga cikin wata babbar matsala kan matsayin sakatare jam’iyyar na ƙasa, tsakanin Samuel Anyanwu, wanda Wike yake goyo baya, da Sunday Ude-Okoye, wanda yake samun goyon bayan Gwamnan Jihar Inugu, Peter Mbah. Mafi yawancin shugabannin jam’iyyar sun yi tunanin cewa idan har Anyanwu ya dawo a matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa zai...
Chef Hilda Baci mai shekara 28 ta kama hanyar kafa sabon tarihin girka shinkafa dafa-duka (Jollof) ’yar Najeriya mafi yawa a duniya. Hilda Baci ta kafa wannan sabon tarihi ne inda ta girka shinkafa basmati buhu 200 a wata katafariyar tukunya a bainar jama’a. Ta yi wannan sabon abin bajinta ce shekara biyu kacal bayan ta shiga kundin tarihi na duniya na Guinness a matsayin wadda ta shafe awanni mafiya yawa tana girke-girke a duniya. A ranar Juma’a ta fara girkin a otel ɗin Eko Hotel & Suites, da ke Legas, kuma sama da mutum 20,000 mashahurai da sauransu sun yi rajista don halarta. An kama buhun tabar wiwi 150 bayan hatsarin mota a Kano Abba ya tarbi tagwayen da...
“Haka zalika, shi ma matuƙin babur ɗin; ruwan ya yi awon gaba da shi,” a cewar tasa. Ganau ɗin ya ci gaba da cewa, wani ƙwararre a fannin iya ruwa; nan da nan ya garzayo tare da yin sufa a cikin ruwa, domin ƙoƙarin ceto su, amma tuni ruwan ya riga ya yi awon gaba da su. Limamin da ya jagoranci sallar jana’izar gawar da aka samu a kwarin Dangoma, Mallam Musa Umar Al mishawi ya bayyana cewa; marigayin ya samu rauni a goshinsa. “Marigayin, mazaunin Unguwar Gidan Dangoma ne da ke tudun jukun ta garin Zaria, sannan kuma an yi jana’izarsa kamar yadda a safiyar yau kamar yadda addinin musulunci ya tanada,” in ji shi. Kazalika, har zuwa lokacin...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhakan, sharbin bayan labarammu a yau zasu yi magana dangane da ‘yiyuwar gwamnatin kasar Qatar ta nemi maye gurbim Amurka a bangaren tsaron kasarta, bayan cin amanan da Amurka ta yi a ranar talatan da ta gabata. Kamfanin dillancin labaran Parstoday, ta nakalto wani shafin labarai na yanar gizo a Amurka ‘Axios’. A ranar Alhamis da ta gabata ce, shafin yanar gizo na Acios na labarai ya nakalto Firay ministan kasar Qatar tana fadawa fadar white House kan cewa, bayan saba alkawalin da Washington ta yi, dangane da hare-haren da HKI ta kaiwa birnin Doha, Qatar zata sake duba yarjeniyar tsaron da ke tsakaninta da Amurka ta kuma nemi sabon abokin aiki a wannan...
Akalla Falasdinawa 64,756 sukayi shahada a kisan kiyashin da Isra’ila ta yi a Gaza tun daga watan Oktoban 2023, in ji ma’aikatar lafiya a yankin Falasdinawa da ke kewaye. Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce an kawo gawarwakin mutane 38 da suka hada da biyu da aka zakulo daga baraguzan gine-gine a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, yayin da mutane 200 suka samu raunuka, wanda ya kawo adadin wadanda suka jikkata zuwa 164,059. Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa, hare haren Isra’ila sun kashe Falasdinawa 14 tare da raunata wasu 143 yayin da suke neman agaji a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, lamarin da ya kai adadin Falasdinawa da aka kashe yayin da suke neman agaji zuwa 2,479,...
A cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14, kasar Sin ta samu ci gaba a bangaren sufurin jiragen kasa na cikin birane, da motocin bas na zirga-zirgar yau da kullum, da zirga-zirga cikin aminci. A halin yanzu, akwai layukan dogo 331 a cikin birane 54 dake fadin kasar, inda jimilar tsawonsu ta kai kusan kilomita 11,000, wanda ke matsayi na farko a duniya. Babban rukunin gidajen rediyo da talabin na Sin wato CMG, ya samu wannan kididdiga ne daga ma’aikatar kula da sufuri da jigilar kayayyaki ta kasar a kwanan nan. A yanzu haka, sama da mutane miliyan 200 a kasar Sin sun zabi hanyoyin sufuri masu kiyaye muhalli a kowace rana, wadanda suka hada da miliyan 100 da suke hawa jiragen kasa masu inganci...
Ma’aikatar kula da cinikayya ta Sin ta sanar a yau Juma’a cewa, biyo bayan amincewar kasashen Sin da Amurka, He Lifeng, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS kuma mataimakin firaministan kasar, zai jagoranci wata tawaga zuwa Spaniya daga ranar 14 zuwa 17 ga watan Satumba, domin tattaunawa da tawagar Amurka. A cewar ma’aikatar, bangarorin biyu za su tattauna kan haraje-harajen Amurka da yadda aiwatar da matakan kayyade fitar da kayayyaki da batun manhajar TikTok da sauran batutuwan tattalin arziki da ciniki. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tarbi tagwayen da aka haifa manne da juna, inda aka raba su da juna ta hanyar yi musu tiyata a Ƙasar Saudiyya. Tagwayen waɗanda ’yan asalin Najeriya ne, sun iso filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, inda tawagar Saudiyya ta tarbe su. Ambaliya: SEMA ta raba kayan tallafi ga gidaje 90 a Gombe ’Yan bindiga sun harbi fasinjoji 2, sun sace makiyaya a Neja An yi musu tiyata a Asibitin Ƙwararru na Yara King Abdullah da ke Riyadh, bisa umarnin Sarki Salman bin Abdulaziz Al-Saud da Yarima Mohammed bin Salman. Hassana da Husaina sun tafi Saudiyya tun a watan Oktoban 2023, inda likitoci suka gano cewa suna manne da juna ne ta...
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Gombe (SEMA) ta raba kayan tallafi ga al’ummar Jalingo-Kamo da ambaliyar ruwa ta shafa a Karamar Hukumar Kaltungo, inda iftila”in ya shafi gidaje kimanin 90. Rabon kayan ya biyo bayan umarnin Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, wanda ya amince da bayar da kayan abinci da na masarufi domin rage raɗaɗin da jama’ar da abin ya shafa suke ciki. NAFDAC ta kama jabun maganin maleriya na ₦1.2bn a Legas Harkar tsaro a gabashin Sakkwato na ƙara taɓarɓarewa — Sanata Lamiɗo Yayin rabon kayan a fadar Hakimin Jalingo-Kamo, Sakataren Hukumar SEMA, Alhaji Abdullahi Haruna Abdullahi ya ce sun gudanar da cikakken bincike da ƙirga waɗanda abin ya shafa kafin rabon. Abdullahi ya bayyana lamarin...
Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta kama jabun magungunan zazzaɓin cizon sauro (maleriya) da darajarsu ta kai sama da Naira biliyan ₦1.2bn a Legas. Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a a shafinta na sada zumunta X, inda ta ce jami’anta sun kai samame a wani ɗakin ajiyar kaya da ke yankin Ilasa-Oshodi, inda aka gano katan 277 na jabun magungunan maleriya nau’in Malamal Forte. Harkar tsaro a gabashin Sakkwato na ƙara taɓarɓarewa — Sanata Lamiɗo ’Yan bindiga sun harbi fasinjoji 2, sun sace makiyaya a Neja NAFDAC ta ƙara da cewa, “Ta kama katan 277 na jabun magungunan zazzaɓin cizon sauro na Malamal Forte...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sanarwar ta ƙara da cewa, SABER wani shiri ne na shekaru biyar, wanda ya dogara da aiki, wanda Bankin Funiya ke tallafawa, wanda aka tsara shi cikin tsanaki domin wargaza shingayen faɗuwar jari, da zaburar da sana’o’i masu zaman kansu, da samar da ayyukan yi masu ɗorewa ga al’ummar Zamfara. Za a raba Naira 150,000 ga mutum 2,000 a faɗin jihar domin tallafa wa ƙananan sana’o’i. Bugu da ƙari, mutane 1,000 a ƙanana da matsakaitan sana’o’i za su karbi Naira 500,000 kowanne. Haka kuma, mutane 60 daga matsakaita da manyan ‘yan kasuwa za su ci gajiyar tallafin Naira miliyan biyar kowannen su. A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa, SABER ba wani abu ba ne na yau...
Mai ba da shawara ga Jagora kan harkokin kasa da kasan ya jaddada ccewa; Dole ne duniya ta daina yin shiru game da zaluncin ‘yan sahayoniyya Ali Akbar Velayati mai ba da shawara ga jagora kan harkokin kasa da kasa ya yi Allah wadai da wuce gona da irin da yahudawan sahayoniyya suka kai a kasar Qatar, yana mai cewa: Dole ne duniya ta daina yin shiru kan zaluncin yahudawan sahayoniyya saboda ba su san iyaka kan laifukansu ba. Velayati ya bayyana a shafinsa na twitter game da harin da gwamnatin ‘yan sahayoniyya suka kai wa kasar Qatar yana mai cewa: Keta dokokin kasa da kasa da keta alfarmar kasashe ya zama al’ada ga ‘yan sahayoniyya, kuma dole ne duniya...
Akalla Falasdinawa 48 ne suka yi shahada a harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a zirin Gaza tun daga wayewar garin yau Juma’a Falasdinawa 48 ne suka yi shahada a ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan zirin Gaza tun daga wayewar garin yau Juma’a. Majiyoyi a asibitocin Gaza sun bayyana cewa: Shahidai 27 ne a kai zuwa asibitin Al-Shifa, shahidi daya zuwa asibitin Al-Ma’amoudiya, shahidai uku zuwa asibitin shahidan Al-Aqsa, da shahidai biyar zuwa asibitin Nasser. Wani Falasdine ya yi shahada kana wasu kuma suka jikkata lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai hari a wani gida da ke unguwar Sheikh Radwan da ke arewacin birnin Gaza. Share 0...
An kammala taron baje kolin zuba jari na duniya na Sin karo na 25 (CIFIT) a jiya Alhamis 11 a birnin Xiamen. A yayin taro na wannan karo, an kulla yarjejeniyoyin ayyukan zuba jari guda 1,154, inda jimillar kudin dake kunshe a ciki ta kai kudin Sin Yuan biliyan 644 (kwatankwacin sama da dala biliyan 90.5 ). An kuma fitar da rahotanni masu inganci guda 21. Taron mai taken “Hadin kai da Sin don zuba jari ta yadda za a samu bunkasa nan gaba,” ya gudana ne a fadin filin baje koli da ya kai murabba’in kilomita 12. An gudanar da ayyukan habaka zuba jari sama da dari, kuma tawagogin kasashe da yankuna fiye da 120 sun halarta, tare da...
Wani dalili da ba zato ba tsammani ya janyo gazawar kashe manyan shugabannin Hamas a Doha Kafofin yada labarai sun bayyana wani dalili na bazata a ranar Laraba da ya biyo bayan gazawar da Isra’ila ta yi na kashe manyan shugabannin Hamas a Doha babban birnin Qatar. Kamfanin dillancin labaran RT ya nakalto tashar talabijin ta Channel 12 cewa, kwana guda bayan kaddamar da shirin kawar da ofishin siyasa na kungiyar Hamas a birnin Doha, rahotanni na nuni da cewa harin bai yi nasara ba, sakamakon matakin da shugabannin Hamas suka dauka na yin sallar azahar tare da ficewa daga dakin tattaunawar. Wani abin ban mamaki shi ne, shugabannin Hamas sun bar wayoyinsu a cikin dakin tattaunawar, lamarin da ya...

Korafin Philippines Ya Tabbatar Da Halascin Matakan Da Sin Ke Dauka Na Kare Muhalli a Tsibirin Huangyan
Bugu da kari, kafa wurin kare muhalli na kasa da kuma tsara ayyukan kamun kifi a tekun tsibirin Huangyan na da matukar muhimmanci ga ci gaban masana’antar kamun kifi a yankin. Matakin da Sin ke dauka a wannan karo ya nuna iyakoki da manufofin da aka tsara a karkashin doka, ya kuma fayyace iyakokin ayyukan da suka kamata a yi a tekun tsibirin Huangyan, kana ya bullo da shiri mai ma’ana domin rigakafin barkewar rikice-rikice. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A yau da safe, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya gudanar da jerin tarukan manema labarai mai taken “Kammala shiri na 14 na shekaru biyar-biyar na raya kasa mai inganci”, inda aka yi karin haske kan ci gaban da aka samu a fannin kafa tsarin shari’a a kasar Sin a wa’adin gudanar da shirin. An bayyana yayin taron cewa, a wa’adin shirin, hukumomin shari’a sun ci gaba da inganta tsarin kasuwanci bisa shari’a, da cibiyoyin kula da lafiyar jama’a a matakin gundumomi, kuma sun fara aiki gaba daya, kana an hukunta manyan laifuka bisa doka. Taron ya kuma bayyana kasar Sin a matsayin daya daga cikin kasashen da aka amince da su a duniya a...
’Yan bindiga sun kai wa wata mota hari a kan hanyar Tegina zuwa Kontagora a Jihar Neja, inda suka jikkata mutum biyu. Harin ya faru ne a Tudun-Fulani bayan direban motar ya ƙi tsayawa lokacin da ’yan bindigar suka buƙaci ya tsaya. ’Yan Najeriya sun kusa fara shan wutar sa’o’i 24 babu ɗaukewa — Minista Jonathan ya tattauna da Peter Obi kan tsayawa takara a 2027 Rashin tsayawarsa ya sa maharan suka buɗe wa motar wuta, inda suka jikkata fasinjoji biyu da ke zaune a kujerar gaba. Wannan lamarin ya faru ne bayan sa’o’i da ’yan bindigar suka sace wasu makiyaya a garin Usalle da daren ranar Laraba. Rahotanni sun nuna cewar ’yan bindigar sun tura makiyayan bakin hanya sannan...
Hukumar Binciken Hatsari ta Najeriya (NSIB) ta fitar da rahotonta na farko, inda ta tuhumi wani matuƙin jirgin sama na Air Peace da kuma wani ma’aikacin jirgin da laifin shan miyagun ƙwayoyi da barasa. Masu binciken hatsarin sun gwada ma’aikatan jirgin cewa suna amfani da abubuwan da ake zargin su bayan da jirgin su da ya yi yunƙurin sauka tare da kauce hanya ba tare da izinin hakan ba a titin jirgin sama na filin jirgin sama na Fatakwal a ranar 13 ga Yuli, 2025. ’Yan Najeriya sun kusa fara shan wutar sa’o’i 24 babu ɗaukewa — Minista Likitoci sun tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya Hakan na ƙunshe ne a cikin wani rahoto na share fage mai ɗauke da...
Hukumar Binciken Hatsari ta Najeriya (NSIB) ta fitar da rahotonta na farko, inda ta tuhumi wani matuƙin jirgin sama na Air Peace da kuma wani ma’aikacin jirgin da laifin shan miyagun ƙwayoyi da barasa. Masu binciken hatsarin sun gwada ma’aikatan jirgin cewa suna amfani da abubuwan da ake zargin su bayan da jirgin su da ya yi yunƙurin sauka tare da kauce hanya ba tare da izinin hakan ba a titin jirgin sama na filin jirgin sama na Fatakwal a ranar 13 ga Yuli, 2025. ’Yan Najeriya sun kusa fara shan wutar sa’o’i 24 babu ɗaukewa — Minista Likitoci sun tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya Hakan na ƙunshe ne a cikin wani rahoto na share fage mai ɗauke da...
Hukumar Binciken Hatsari ta Najeriya (NSIB) ta fitar da rahotonta na farko, inda ta tuhumi wani matuƙin jirgin sama na Air Peace da kuma wani ma’aikacin jirgin da laifin shan miyagun ƙwayoyi da barasa. Masu binciken hatsarin sun gwada ma’aikatan jirgin cewa suna amfani da abubuwan da ake zargin su bayan da jirgin su da ya yi yunƙurin sauka tare da kauce hanya ba tare da izinin hakan ba a titin jirgin sama na filin jirgin sama na Fatakwal a ranar 13 ga Yuli, 2025. ’Yan Najeriya sun kusa fara shan wutar sa’o’i 24 babu ɗaukewa — Minista Likitoci sun tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya Hakan na ƙunshe ne a cikin wani rahoto na share fage mai ɗauke da...
Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce nan ba da jimawa ba Najeriya za ta fara samun wutar lantarki ta tsawon sa’o’i 24 ba tare da ɗaukewa ba. Ya bayyana haka ne a Abuja lokacin da ya ƙaddamar da sabbin ɗakunan horo da ɗakin kwana a Cibiyar Horas da Ma’aikata ta Ƙasa (NAPTIN). Gwamna ya aike wa majalisa dokar haramta auren jinsi ɗaya a Kano Likitoci sun tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya Adelabu, ya ce gwamnati ta samu nasarar samar da wutar lantarki da rarraba ta a matakin da ba a taɓa samu ba a tarihin ƙasar. Ya bayyana cewa bunƙasa wutar lantarki shi ne ginshiƙin ci gaban ƙasa, domin tana tallafa wa makarantu, asibitoci, masana’antu da kasuwanci. Ya...
A yayin da suka yi alƙawarin yin adawa da aiwatar da harajin, ƙungiyar ta ƙara da cewa: “Yajin aiki na kan tebur idan gwamnati ta yi ƙoƙarin watsi da wannan gargaɗi ta ci gaba da aiwatar da waɗannan manufofi. Don haka, TUC ta umarci dukkan kwamitocin jihohi, rassan ƙungiya, da tsarin ta a faɗin ƙasa da su kasance cikin shiri, sanya ido, kuma su jira ƙarin sanarwa wanda zai iya kai wa ga ɗaukar mataki mai ƙarfi idan gwamnati ta ƙi sauraron muradin jama’a.” Ƙungiyar ta kuma kira ga abokan hulɗarta – ƙungiyoyin farar hula, ƙungiyoyin ƙwararru, ɗalibai, ƙungiyoyin kasuwa, shugabannin addini da duk ƴan Nijeriya masu kishin ƙasa – da su tsaya tare da ita a wannan gwagwarmaya. “Tare,...
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da mika kudirin dokar haramta auren jinsi daya, luwadi da madugo ga Majalisar Dokokin Jihar domin amincewa da shi a matsayin doka. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Juma’a, ya ce gwamnan ya bayar da umarnin ne yayin zaman majalisar zartarwar jihar karo na 31 da aka gudanar a reshen gidan gwamnati da ke Kwankwasiyya City a Kano. Likitoci sun tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya Ambaliyar ruwa ta tsayar da ababen hawa cak a tsakiyar birnin Abuja Gwamna Yusuf ya ce gwamnatinsa ba za ta sassauta kan koyarwar addinin Musulunci ba, yana mai jaddada cewa dole ne Kano ta ci gaba...
Ƙungiyar Likitocin Masu Neman Ƙwarewa a Nijeriya (NARD) ta tsunduma cikin yajin aikin ƙasa baki ɗaya, bayan gwamnatin tarayya ta kasa cika mafi ƙarancin bukatun da ƙungiyar ta gabatar cikin wa’adin sa’o’i 24 da ta sanya. Wannan mataki ya zo ne bayan kammala taron gaggawa na Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (E-NEC) ta yanar gizo a ranar Laraba, 10 ga Satumba, 2025. Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Dakta Osundara Tope Zenith, ya tabbatar da hakan, inda ya ce yajin aikin ya zama dole bayan shiru daga bangaren gwamnati. Ƙungiyar ta jaddada cewa rashin biyan Kudaden Tallafin Koyan Aiki (MRTF) ga wasu asibitoci, tare da rashin biyan alawus na watanni biyar daga karin kaso 25% da 35%, da sauran hakkoki da aka dakatar...
Kungiyar Likitocin Masu Neman Kwarewa ta Najeriya (NARD) ta umurci mambobinta da su dakatar da aiki a dukkan asibitocin gwamnati da ke fadin Najeriya daga yau Juma’a. Wannan mataki ya biyo bayan karewar wa’adin sa’o’i 24 da kungiyar ta bai wa Gwamnatin Tarayya don cika bukatunsu da ba a biya ba. Wa’adin ya biyo bayan karewar wani wa’adin na kwanaki 10 da ya kare a ranar 10 ga Satumba ba tare da an biya wa likitocin bukatun nasu ba. Ambaliyar ruwa ta tsayar da ababen hawa cak a tsakiyar birnin Abuja Jonathan ya tattauna da Peter Obi kan tsayawa takara a 2027 A ranar daya ga watan Satumba, NARD ta gargadi gwamnati cewa za ta fara yajin aikin sai baba...
Firaiministan Qatar, Mohammed bin Abdulrahman Al-Thani Ya bayyana shugabannin Isra’ila a matsayin masu tsattsauran ra’ayi da ke kishirwar jefa duniya cikin rikici. Al-Thani, ya bayyana hakan ne a birnin New York, inda ya halarci taron gaggawa na kwamitin tsaro kan harin da Isra’ila ta kai Qatar. Qatar ta yi lale marhabun da matakin kwamitin sulhu na Majalisar na yin Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai wa shugabannin Hamas a birnin Doha, Kuma ya ce hakan ba zai hana su ci gaba da jagorantar yunkurin cimma yarjejeniya don wanzar da zaman lafiya a Gaza ba. Nan gaba a yau Juma’a ne dai firaministan zai je Washington domin tattaunawa a fadar White House. Kungiyar Hamas ta ce shugabanninta sun tsira...
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya yi wata tattaunawa ta wayar tarho a daren jiya Alhamis da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi, inda suka mai da hankali kan shirin nukiliyar Iran da batutuwan da suka shafin yankin. tattaunawar na zuwa ne bayan da Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA suka cimma matsaya ta hadin gwiwa a nan gaba. Tehran ta dage kan kare hakkinta a karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT), yayin da ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta dauki wani mataki mai karfi kan ayyukan sojan Isra’ila a yankin. Manyan kasashen yammacin duniya sun yi barazanar maido da takunkuman kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da aka dage a...
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya sha alwashin dakile kafa kasar falasdinawa yayin da ya sanya hannu kan yarjejeniyar gaggauta ci gaba da ginin matsugunan yahudawa a yankin El, na yamma da kogin Jordan da Isra’ilan ta mamaye. A jiya Alhamis ne Netanyahu ya sanya hannu kan yarjejeniyar, duk da kashedin da sassan kasa da kasa suka jima suna yi, cewa hakan zai gurgunta damar falasdinawa ta kafa kasa mai cin gashin kai. Yankin da Isra’ila ke fatan ginawa, mashigi ne a bangaren gabashin birnin Kudus, tsakanin birnin da yankin unguwar Ma’ale Adumim, ana kuma ganin gina shi zai haifar da mummunan tasiri, kasancewar hakan zai raba gabashin birnin Kudus da arewacin gabar kogin Jordan, wanda hakan zai dakile damar samar da dunkulalliyar kasar falasdinawa a nan...
Ya ce a halin yanzu kamfanin na samar da kimanin ganga miliyan 1.6 na mai a kowace rana (bpd) tare da burin haɓaka samarwa zuwa miliyan 2 bpd nan da shekara ta 2027 da miliyan 3 bpd nan da 2030. Ya haskaka ayyukan da ake gudanarwa a halin yanzu, ciki har da bututun iskar gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano (AKK), faɗaɗa West African Gas Pipeline zuwa Morocco da Turai, da kuma haɓaka aikin Nigeria LNG. A cewarsa, Nijeriya tana samar da kashi 60 cikin ɗari na LNG ga Portugal da Sipaniya, kuma a halin yanzu tana kan Train 6, tana gina Train 7 wanda za a kammala a shekara ta 2026, tare da shirin gina Trains 8 da 9. “Nijeriya na ɗaya...

Rashin Wutar Lantarki: Masana Sun Nuna Damuwa Kan Asarar Dala Biliyan 29 Da Ƙananan Masana’antu Ke Yi
Masanan sun yi gargaɗi yayin da Shugaba Bola Tinubu ya sake tabbatar da ƙudurin gwamnatinsa na sake fasalin ɓangaren lafiya na Nijeriya, inda ya bayyana cewa babu wani ɗan ƙasa da ya kamata ya rasa rayuwarsa saboda rashin wutar lantarki a cibiyoyin lafiya. Yayin da yake jawabi a Taron Tattaunawar Masu Ruwa da Tsaki na Ƙasa kan Wutar Lantarki a Ɓangaren Lafiya, a Ladi Kwali Hall na Continental Hotel, Abuja, Shugaban ƙasa, wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya wakilta, ya lura cewa rashin wutar lantarki da ke ci gaba a asibitoci na rage ingancin kulawa da kuma jawo asarar rayuka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
Ya kamata a kafa hukumar musamman da za ta kula da gano mutane da suka ɓace tare da bata ƙarfi don gudanar da bincike. Kaso 68 cikin 100 na masu neman ƴaƴan da suka ɓace iyaye mata ne, amma da dama suna dawowa hannu rabbana saboda rashin tsari daga mahukunta. A jihar Yobe kaɗai, yara 2,500 ne aka ce sun ɓace, mafi yawan su a Gujba, abin da ya nuna gazawar gwamnati wajen kare rayuka a Arewa maso Gabas. Yakuma zama wajibi a samar da tsare-tsaren gwamnati da za su kare haƙƙin ƴanuwa waɗanda suka rasa nasu, musamman a jihohin da ake fama da tashe-tashen hankula. Waɗannan tsare-tsaren za su yi aiki kaf shoulder da al’ummomin yankuna, sarakunan gargajiya, malaman...
Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, sun gana ranar Alhamis a Abuja, a yayin da ake ci gaba da hasashen kafa kwakkwaran kawancen adawa gabanin zaben shugaban kasa na 2027. Manyan ’yan siyasar na Kudancin Najeriya dai sun mamaye tattaunawa a bakunan jama’a a baya-bayan nan a matsayin wadanda za su iya kalubalantar Shugaba Bola Tinubu na jam’iyyar APC. Kodayake har yanzu Peter Obi yana cikin LP, amma yana mu’amala da jam’iyyar kawancen adawa ta ADC ke jagoranta. NAJERIYA A YAU: Masu Nau’in Jinin AS Sun Fi Masu Nau’in AA Lafiya 2027: Malamai sun gudanar da addu’o’in nasarar Tinubu-Barau a Kano Jonathan kuwa, wanda har yanzu dan jam’iyyar...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Araghchi ya yi Allah-wadai da matakin da kasashen Turai uku suka dauka na yin biris da batun harin da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran a baya-bayan nan, da kuma barazanar da suke yi na maido da kudurorin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da aka soke, lamarin da yake ganin zai kara ta’azzara halin da ake ciki. Araghchi ya bayyana hakan ne a daren Alhamis a wata tattaunawa ta wayar tarho da babban sakataren MDD Antonio Guterres. Ya jaddada aniyar kasar Iran na kare hakki da muradun al’ummarta bisa yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya. Ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya da kasashe mambobinta da su yin da Allawadai da hare-haren da Amurka...
A cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Alhamis, kwamitin sulhu na MDD ya yi Allah wadai da harin da aka kai a Doha babban birnin kasar Qatar, ba tare da ambaton sunan Isra’ila ba. TY kuma jaddada wajabcin daina kai irin wadannan hare-hare da kuma nuna cikakken goyon baya ga ga ‘yancin kasar Qatar. A nata bangaren, mataimakiyar Sakatare-Janar ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi wa kwamitin sulhu bayani kan koken na Qatar, inda ta jaddada cewa, harin na Isra’ila ya bude wani babi ne mai hadari a cikin wannan rikici mai muni. Mataimakin Sakatare-Janar ta kara da cewa “dole ne dukkan bangarorin su dauki matakin kiyaye yunkurin da ake yi na samo hanyoyin tsagaita bude wuta,” tana...
Shugaban kungiyar Ansar Allah, Sayyed Abdul-Malik al-Houthi, ya tabbatar da cewa hare-haren da Isra’ila ta kai kan kasar Yemen a ranar Laraba ba ta nuna wata nasara ba, sai dai yana nuna rashin bin dokokin kasa da kasa wajen ci gaba da aikata laifukan yaki. A cikin jawabinsa na mako-mako a wannan Alhamis, yayin da yake magana kan sabbin abubuwan da suka faru dangane da hare-haren wuce gona da iri kan zirin Gaza da kuma abin da ya biyo bayan hakan, Sayyed al-Houthi ya bayyana cewa, kasar Yemen, a hukumance da kuma a matsayi na al’ummar kasar, tana a kan matsaya ta gaskiya, tana taka muhimmiyar rawa, kuma tana da cikakkiyar fahimtar abin da take aiwatarwa na sadaukarwa domin al’ummar...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Sau da dama wadanda ke dauke da nau’in jini na AA na bayyana cewa sun fi kowa lafiya. Suna bayyana cewa basa rashin lafiya kamar yadda masu sauran na’ukan jini ke yi. NAJERIYA A YAU: Rayukan Da Aka Rasa Sakamakon Ambaliyan Wannan Shekarar DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Uku Shirin Najeriya A Yau na wanna lokaci zai yi nazari ne kan ko da gaske ne masu nau’in jini na AA sun fi sauran masu nau’ukan jini lafiya. Domin sauke shirin, latsa nan
Ministan harkokin wajen Tunisiya Mohamed Ali Nafti ya ce kasarsa da Iran sun amince da karfafa hadin gwiwa tare da shirya taron komitin hadin gwiwa, yayin da yake maraba da sabuwar yarjejeniyar da Tehran ta kulla da hukumar IAEA. A cikin rubuce-rubuce uku na X a jiya Alhamis, ministan harkokin wajen Tunisia ya bayyana cewa, an cimma yarjejeniyar fadada huldar dake tsakanin kasashen Tunusiya da Iran a yayin ganawarsa da takwaransa na Iran Abbas Araghchi a birnin Tunis. Nafti ya ce, “Ina mai farin cikin maraba da takwarana Araghchi, ministan harkokin wajen Iran, a ziyarar aiki da ya kai kasar Tunisiya, mun gudanar da tattaunawa mai zurfi don tantancewa da kuma inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, domin samun...
Kasar Sin ta kasance kan gaba a duniya a yawan hakkokin mallakar fasaha, a masana’antun dake karkashin bangaren tattalin arziki na fasahohin zamani ko dijital a shekarar 2024, inda karuwar da ta samu ya zarce na matsakaicin adadin na duniya A cewar hukumar kula da hakkin mallakar fasaha ta Sin, adadin hakkokin mallakar fasahar kirkire kirkire a wadannan masana’antu ya kai 500,000 a bara, adadin da ya karu da kaso 23.1 kan na mizanin shekara-shekara. An fitar da wadannan alkaluma ne yayin taron shekara shekara kan hakkin mallakar fasaha na kasar Sin da aka yi wa taken “Hakkin Mallakar Fasaha a Zamanin Fasahohi da Na’urori.” (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
Har ila yau, karkashin wadannan shawarwari, kasashe membobin BRICS za su ci babbar gajiya daga fifikonsu, da ma alfanun dake tattare da hadakarsu wuri guda. Zage damtse da kasashe membobin BRICS ke yi wajen karfafa cudanya, da hadin gwiwa na zuwa ne a wani muhimmin lokaci da duniya ke fuskantar karin rashin tabbas, ake kuma kara fuskantar koma baya ta fuskar jituwa tsakanin wasu sassan kasashen duniya. Don haka, dandalin BRICS karin dama ce ga duniya ta rungumar juna, don kare cudanyar mabanbantan sassa, da tsarin cinikayya mai game dukkanin bangarori, har a kai ga cimma nasarar kafa al’ummar duniya mai makomar bai daya ga kowa da kowa. Tarihi ya sha nuna yadda cudanyar sassa daban daban ke...
“Gwamnatin Jihar Kaduna ta shirya tsaf domin ɗaukar matakin gaggawa kan kowanne yanayi da ka iya tasowa sakamakon wannan hasashen yanayi. An umurci KADSEMA da ta yi aiki tare da dukkan hukumomi masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cikakken shiri. Ana roƙon jama’a da su bi dukkan umarnin kariya, su share magudanan ruwa, kuma su guji wuraren da ambaliya ke yawan faruwa a wannan lokaci,” in ji Maiyaki. Hakazalika, sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KADSEMA), Dakta Usman Hayatu Mazadu, ya jaddada muhimmancin kasancewa cikin shiri da kuma bin matakan kariya da ke cikin sanarwar. “Hasashen yanayi ya nuna cewa za a samu guguwar iska da ruwan sama mai yawa musamman a ranakun Laraba...
Gwamnatin jihar ta sha alwashin bayyana sakacin aikin da Kwamishinan ya yi da zarar ta kammala bincike. Don haka, an umurci babban jami’i a ma’aikatar da ya ci gaba da jan ragamar ayyukan ma’aikatar har zuwa lokacin da za a fitar da wata sabuwar sanarwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Da safiyar yau Alhamis ne aka gudanar da taron manema labarai game da taron tattaunawa karo na 12 na dandalin Xiangshan wanda za a gudanar a nan Beijing daga ran 17 zuwa 19 ga watan Satumban nan a cibiyar taro ta duniya ta Beijing, bisa taken “Hadin kai don kare tsarin duniya, da habaka ci gaban zaman lafiya”, inda za a gudanar da cikakken zama har sau 4 tare da kuma tarurruka 8 na rukuni-rukuni, da kuma taron shugabanni, da taron tattaunawa tsakanin matasan jami’an soja da masana, da na tattaunawa tsakanin manyan masana na Sin da na kasashen waje. Wakilan da za su halarci taron sun hada da na kasashe masu arziki, da manyan kasashe masu tasowa, da kananan...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa makiya suna son cusa gaba a tsakanin kasashen musulmi don su sami damar sace arzikin makamashin da sunke da shi da kuma jawo hankalin kwararrun da kasashen musulmi suke da shi don amfanin kansu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalyo shugaban kasar yana fadar haka a safiyar yau Alhamis, a birnin Ardabil da ke kusa da ke iyaka da kasar Azarbaijan daga arewacin kasar. Masoud Pezeshkian ya je landin ne don kaddamar da ayyukan ci gaban kasa da ayyukan raya kasa wadanda aka kammala a yankin har guda 72. Shugaban ya kara da cewa, da wadannan kasashe basu da kome ba zasu zo su nemi wani Abu a wajemmu...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa makiya suna son cusa gaba a tsakanin kasashen musulmi don su sami damar sace arzikin makamashin da sunke da shi da kuma jawo hankalin kwararrun da kasashen musulmi suke da shi don amfanin kansu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalyo shugaban kasar yana fadar haka a safiyar yau Alhamis, a birnin Ardabil da ke kusa da ke iyaka da kasar Azarbaijan daga arewacin kasar. Masoud Pezeshkian ya je landin ne don kaddamar da ayyukan ci gaban kasa da ayyukan raya kasa wadanda aka kammala a yankin har guda 72. Shugaban ya kara da cewa, da wadannan kasashe basu da kome ba zasu zo su nemi wani Abu a wajemmu...
Gwamnatin kasar Qatar ta yi tir da fray ministan HKI Banyamin Natanyahu, kuma ta bukaci a gurfanar da shi a gaban kuliya, saboda hare-haren ta’addanci da kai birnin Doha babban birnin kasar a ranar Laraban da ta gabata . Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Firay ministan kasar Qatar yana fadar haka a yau Alhamis a birnin Doha ya kuma mkara da cewa, duk da cewa dama ana nemansa a kotun ICC saboda laifukan yaki, kasar Qatar tana bukatar a gaggauta kaishi gaban kuliya. Hare-haren dai sun jawo tir da allawadai kan HKI a mafi yawan kasashen Duniya, da kuma manya-manyan kungiyoyi na kasa da kasa. Musamman ganin cewa kasar Qatar ce babbar mai tsiga tsakani don...
Kungiyar Hamas ta bayyana cewa hare-haren da HKI ta kai shuwagabannin kungiyar masu tattaunawa a doha a ranar talatan da ta gabata, ba zai sauya kome a abinda kungiyar zata gabatar na sulhu a Gaza ba. Shafin yanar gizo na labarai “Arab News” ya nakalto Fawzi Barhoum yana fadar haka a wani faifen bidiyo da aka watsa a kafafen yada labarai a yau Alhamis. Hamas ta bayyana cewa tana da tabbaci kan cewa gwamnatin kasar Amurka, ko kuma shugaba Trump yana da hannu a cikin wannan makircin na kokarin kashe shuwagabannin Hamas a Doha. A ranar talata ce HKI ta yi kokarin kashe tawagar tattaunawar sulhu da kuma zaman Lafiya na kungiyar Hamas a binin Doho wanda bai sami nasara...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hukumar makamashin nukliya ta Duniya IAEA ta amince da sabuwar yarjeniya tsakaninta da Iran ta yadda ma’amala tsakanin bangarorin biyu zata kasance. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Laraba a birnin Tunis babban birnin kasar Tunisia. A lokacinda yake jawabin hadin guiwa ta tokwaransa na kasar ta Tunisia. Kafin haka dai Aragchi ya yada zango a birnin Alkahira na kasar Masar inda ya gana da Rafael Grossi shugaban hukumar IAEA, suka kuma rattaba hannu kan sabuwar yarjeniya da hukumar, ta yadda hulda tsakaninsu zata kasance bayan hare-haren da HKI da Amurka suka kai wa cibiyoyin sarrafa makamashin nukliya na kasar ta...
Zanga-zangar ta biyo bayan kashe jami’an ‘yansanda uku da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi a wani shingen bincike a cikin garin Egbe. Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kogi, SP William Ovye Aya, ya shaidawa manema labarai a Lokoja cewa, harin ya faru ne da sanyin safiyar Laraba. Ya kara da cewa kwamishinan ‘yansanda, Miller Dantawaye, nan take ya tura rundunar ‘yansanda zuwa yankin domin fatattakar maharan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
An kafa MDD ne shekaru 80 da suka gabata yayin da ake cikin burbishin yakin duniya II. Kuma yanzu bayan shekaru 80, duniya tana kan wata muhimmiyar gaba ta shawo kan matsaloli. Sake tasowar yakin cacar baka da amfani da ka’idojin duniya wajen cimma muradu na kashin kai da rashin daidaito ta fuskar ci gaba a duniya, tsarin da ake bi a baya, ba zai iya shawo kan sabbin matsaloli ba. Bayan shawarwarin raya duniya da ta tabbatar da tsaro da ta wayewar kai, kasar Sin ta sake gabatar da wata mafita, wato shawarar jagorantar harkokin duniya. Wadannan manyan shawarwari 4 sun kunshi cikakken tsarin tafiyar da harkokin kasa da kasa, tare da samar da daidaitacciyar alkibla ga duniya mai...
Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta bai wa Gwamnatin Tarayya sabon wa’adin kwana ɗaya domin ta cika buƙatun da take nema. Hakan dai na zuwa ne bayan wa’adin farko na kwanaki 10 da suka bayar, wanda ya ƙare a ranar Talata, 10 ga Satumba. An saki fursunonin siyasa 52 a Belarus Daruruwan magoya bayan NNPP sun tarbi Kwankwaso a Kalaba Matakin da ƙungiyar ta ɗauka na zuwa ne a ƙarshen wani taron gaggawa da shugabanninta suka gudanar a ranar Laraba, domin nazarin ci gaban da aka samu tun bayan bayar da wa’adin farko. Shugaban ƙiungiyar Dr. Tope Osundara ya ce sun saurarin alƙawurran da gwamnatin Najeriya ta yi masu game da buƙatun nasu amma suna neman a...
Gwamnatin Belarus ƙarƙashin jagorancin Shugaba Alexander Lukashenko ta saki fursunoni siyasa 52 ciki har da fitaccen ɗan adawa, Mikola Statkevich da kuma ɗan jarida Ihar Losik, a wani yunƙuri da aka danganta da ruwa da tsakin Amurka. Shugaban Lithuania, Gitanas Nauseda, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X (Twitter), yana mai cewa: “Mutum 52 da aka daure bisa dalilan siyasa sun tsallako kan iyaka daga Belarus zuwa Lithuania lafiya.” Daruruwan magoya bayan NNPP sun tarbi Kwankwaso a Kalaba Kotu ta yanke wa jagoran Ansaru hukuncin ɗaurin shekaru 15 Ya ce yana “matuƙar godiya” ga gwamnatin Amurka da Shugaba Donald Trump bisa rawar da suka taka wajen sasantawa da cimma wannan matsaya. Daya daga cikin wadanda aka sako shi ne...
A cewarsa, kudaden fansa da ake yawan ji ana biya yawanci iyalan wadanda abin ya shafa ko al’ummarsu ne ke tarawa. Ya kuma bayyana cewa rahotanni sun nuna ’yan bindiga sun karɓi sama da Naira biliyan 2.5 a shekarar 2025 kadai, adadin da ya ce babu wata gwamnati da za ta iya ɗauka. Masanin tsaron ya ce matsalar tsaro a Najeriya ta fi ƙarfin dabarun soja kaɗai, inda ya danganta ta da cin hanci da rashawa wanda ya kira “babban mai ba da damar ayyukan ta’addanci.” Ya yi gargadin cewa ya zama dole a guji yin zarge-zargen da ba su da tushe kan shugabannin da ke kan karagar mulki, yana mai tunatar da cewa irin wadannan maganganu...
Al’amari mai rikitarwa Hakikanin gaskiya ya fi an rikitarwa. Bisa al’amari, ana kiyasta cewa mutane kimanin 15,000 zuwa 20,000 ne suka mutu a sakamakon kashe-kashen da suka shafi ‘yan bindiga da ta’addanci a Arewa maso Yamma kaai cikin shekaru 10 da suka wuce. Wannan adadi yana daidai da yawan rayukan da aka rasa a Yakin Kosobo, ko kusan kashi 40 cikin ari na asarar rayuka a Yakin Basasar Saliyo na tsawon shekaru 10, duk da cewa ba gwamnati ba bace ke yakar ‘yan bindiga, sai dai ‘yan ta’adda ne masu zaman kansu. Wannan kididdigar ba ta bayyana irin wahalar da dubban yara ke sha ba, waanda aka kashe iyayensu, gidaje marasa uwa ko masoya, mutane da suka ji rauni...
Daruruwan magoya bayan jam’iyyar NNPP ne suka taru a birnin Kalaba na Jihar Kuros Riba, domin tarbar jagoran jam’iyyar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, a wata ziyarar sada zumunta da ya kai a jihar. Kwankwaso ya fara irin wannan ziyarar ce daga yankin Kudu maso Gabas, kafin ya wuce zuwa Kudu maso Kudu, inda ya sauka a Kalaba domin ganawa da mambobin jam’iyyar. Kotu ta yanke wa jagoran Ansaru hukuncin ɗaurin shekaru 15 Trump ya tiso ƙeyar rukunin farko na ’yan Najeriya daga Amurka A yayin da yake jawabi ga taron magoya bayan jam’iyyar a Kalaba, tsohon Gwamnan Kano, ya bayyana cewa wannan ziyara ba ta da alaƙa da yaƙin neman zaɓe. Sai dai ya ce uzuri ne ya kai shi...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wata babbar kotu a Abuja ta yanke wa Mahmud Muhammad Usman (Abu Bara’a), ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar Ansaru hukuncin ɗaurin shekaru 15 a gidan kaso. Abu Bara’a wanda Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta gurfanar a ranar Alhamis, ya amsa laifin gudanar da harkokin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, lamarin da ya ba shi damar mallakar makamai da aikata ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane. Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya bayar da umarnin a ajiye Mahmud Usman a ofishin Hukumar DSS har zuwa lokacin da za a kammala shari’a kan sauran zarge-zargen da ake masa guda 31. A lokacin gabatar da ƙarar, an tuhumi Mahmud Usman da Abubakar Abba da aikata ta’addanci a 2022, ta hanyar...
Diphtheria cuta ce mai saurin yaɗuwa wadda ke shafar maƙogwaro da hanyoyin numfashi, kuma tana iya hallaka mutum idan ba a yi saurin ɗaukar mataki ba. Rigakafi shi ne babban mataki wajen hana yaɗuwar cutar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rukunin farko na ’yan Najeriya da aka tsara korar su daga Amurka a karkashin Shugaba Donald Trump sun bar kasar. Shugaban Ghana, John Dramani Mahama, ne ya bayyana hakan ga ’yan jarida a daren Laraba. “Rukunin mutane 14 da aka kora daga Amurka, ciki har da ’yan Najeriya da wani dan kasar Gambiya, sun iso Ghana, kuma gwamnati ta taimaka wajen mayar da su kasashensu,” in ji Mahama a wani taron manema labarai. Budurwa ta mutu a ɗakin saurayin da ke shirin auren ta a Abuja Mota ɗauke da tabar wiwi ta yi hatsari a Kano, ta faɗa hannun jami’an NDLEA Ya ce Ghana ta riga ta shirya jigilar ’yan Najeriya zuwa kasarsu ta mota, yayin da ake ci gaba...
Wata budurwa mai shekaru 24 mai suna Kelechi Ebubechukwu, ta rasu a cikin wani yanayi da mai daure kai a gidan saurayinta da ke Gwagwalada, Babban Birnin Tarayya Abuja. Wani ƙwararren masani kan tsaro, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba. A cewarsa, lamarin ya faru ne a ranar Talata. Mota ɗauke da tabar wiwi ta yi hatsari a Kano, ta faɗa hannun jami’an NDLEA Likitoci sun bai wa gwamnati sa’o’i 24 kafin tsunduma yajin aiki Majiyoyin ’yan sanda sun ce binciken farko ya nuna cewa marigayiyar na fama da zazzabin cizon sauro kafin rasuwarta. A cewar mjiyoyin, an samu takardar da ke dauke da rubutun magungunan da...
Hukumar Hana da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), reshen Jihar Kano, ta cafke buhuna uku da kuma sinki 150 na tabar wiwi mai nauyin kilogiram 112. Bayanai sun ce an kama kwayoyin ne bayan wani hatsarin mota da ya faru a Gadar Tamburawa da ke kan hanyar Zariya zuwa Kano. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Sadiq Muhammad-Maigatari, ya fitar a ranar Alhamis a Kano. Likitoci sun bai wa gwamnati sa’o’i 24 kafin tsunduma yajin aiki Tinubu ya bayar da umarnin a sake karya farashin kayan abinci Ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:00 na safiyar ranar Asabar, lokacin da jami’an hukumar da ke sintiri suka...
Rahotanni sun bayyana cea Shugaban nigeria Bola Tinubu ya umarci wani kwamiti na Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) da ya dauki matakai don karya farashin abinci a fadin Nijeriya. Sanata Sabi Abdullahi, Ministan Noma ne, ya bayyana hakan a lokacin wani taron horaswa na kwana daya ga ‘yan jarida a Abuja ranar Laraba. Ya ce shirin rage farashin kayan abinci ya hada da tabbatar da cewa kayan noma suna tafiya cikin tsari da farashi mai sauki. Sanata Abdullahi ya kara da cewa, tsadar jigilar kayan amfanin gona shi ne daya daga cikin dalilan da ke sanya abinci ya yi tsada a kasuwanni. Ya ce kwamitin na FEC yana aiki don tabbatar da jigilar kayan amfanin gona sun zama masu sauki,...
Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Sanin Makamar Aiki ta Najeriya (NARD), ta bai wa Gwamnatin Tarayya sa’o’i 24 don ɗaukar mataki game da buƙatunsu, ko kuma su tsunduma yajin aiki. Wannan matakin ya biyo bayan cikar wa’adin gargaɗin kwanaki 10 da suka bayar a baya. Gwamnatin Tarayya za ta gurfanar da shugabannin Ansaru 2 a kotu Tinubu ya bayar da umarnin a sake karya farashin kayan abinci Tuni wasu likitoci a Abuja da Jihar Oyo suka tsunduma yajin aiki. Likitocin, waɗanda yawancinsu ke aiki a Asibitocin Koyarwa da na Ƙwararru, suna yawan tafiya yajin aiki saboda rashin biyan wasu haƙƙoƙinsu. A halin yanzu, suna neman a biya su kuɗin horon 2025 da bashin albashin da suka bi, sannan sun buƙaci a...
Ya ƙara da cewa wannan mataki yana cikin hangen nesan Shugaba Tinubu a kan abinci, wanda ke nufin samar da abinci mai sauƙi ga kowa. Ministan ya kuma ambaci shirye-shiryen da ake shirin aiwatarwa, kamar Shirin Lafiyar Ƙasa na Manoma, waɗanda ke nufin inganta rayuwar manoma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugabannin kasashen Afirka sun kammala taron kwanaki 3 kan sauyin yanayi na Afirka a babban birnin kasar Habasha a jiya Laraba tare da amincewa da sanarwar Addis Ababa, inda suka yi alkawarin mayar da nahiyar ta zama cibiyar samar da makamashi mai safta da kuma hanyoyin magance sauyin yanayi a yayin da suke neman kudade na gaske. Shugaban kasar Habasha Taye Atske Selassie, wanda ya rufe taron, ya ce taron ya nuna cewa Afirka ba ta shiga cikin rikicin da ba ta haifar da shi ba. ” Mun himmatu wajen samar da wata nahiya mai wadata,” in ji shi. “Zalunci ne cewa sama da ‘yan Afirka miliyan 600 har yanzu suna rayuwa ba tare da samun wutar lantarki ba. Dole...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban Kasa Bola Tinubu ya umarci Kwamitin Majalisar Zartarsa ta Kasa da ya dada aiwatar da matakan da za su kara karya farashin kayan abinci a fadin Najeriya. Karamin Ministan Noma da Samar da Abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ne ya bayyana hakan ranar Laraba a Abuja. EFCC ta tsare Mele Kyari kan binciken matatun mai Macron ya karɓi baƙuncin Tinubu a Fadar Elysee Ya ce umarnin ya shafi tabbatar da cewa an rage farashin sufurin kayan amfanin gona ba tare da kashe makudan kudade ba. “Shugaban Kasa ya bayar da umarni ga Kwamitin Majalisar Zartarsa ta Kasa wanda dama yanzu haka yana nan yana kokarin ganin an saukaka hanyoyin sufurin amfanin gona a fadin kasar nan, da su dada...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk shekara rayuka da dukiyoyi na kara salwanta sakamakon ambaliyar ruwa. Duk da jan kunne da hukumomi a matakai daban-daban keyi, rayukan mutane da dukiyoyi na kara salwanta. NAJERIYA A YAU: Tasirin Takaddamar NUPENG Da Dangote A Kan Tattalin Arzikin Najeriya DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Uku Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan rayukan da suka salwanta a damunan wannan shekarar. Domin sauke shirin, latsa nan
Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), ta tsare tsohon Shugaban Hukumar Man Fetur ta Ƙasa (NNPC), Mele Kyari kan zargin karkatar da kuɗaɗen gyaran matatun man Najeriya. Kyari na cikin jerin waɗanda ta hukumar ta sanya ido a kansu, kuma ta isa ofishin EFCC da misalin ƙarfe 2:30 na ranar Laraba. Macron ya karɓi baƙuncin Tinubu a Fadar Elysee Masu zanga-zanga sun ƙone matar tsohon Firaministan Nepal Majiyoyi, sun bayyana cewar ya isa ne don bayar da bayanai kan batutuwan kuɗi da aka ware don gyaran matatun man fetur a Najeriya lokacin da yake shugabantar NNPC. Wani majiya ta shaida wa Aminiya cewa: “Eh, yana ofishinmu. Za a kai shi ɗaki inda masu bincike na...
A yau Laraba kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda ya bayyana cewa, kasar Sin ta soki lamirin harin da aka kaddamar a birnin Doha, fadar mulkin kasar Qatar a jiya Talata, tana kuma adawa da matakin Isra’ila na cin zarafin ikon mulkin kasa da tsaron kasa na Qatar. Lin Jian ya ce kasar Sin na kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa, musamman Isra’ila, da su kara kokari wajen dakile rikicin, da sake fara tattaunawa maimakon akasin hakan. Dangane da sanarwar da Isra’ila ta gabatar wa Amurka kafin ta kaddamar da harin ta sama, Lin Jian ya bayyana cewa, matakin da Isra’ila ta dauka na da...
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya karɓi baƙuncin Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a Fadar Elysee da ke birnin Paris. Wannan dai wani ɓangare ne na hutun aiki da Tinubun yake yi a ƙasashen Turai da ya tafi a makon jiya. INEC ta amince da jam’iyyar haɗaka ta ADC Yadda zanga-zangar adawa da rashawa ta rikiɗe zuwa tarzoma a Nepal Hakan na ƙunshe cikin wani saƙo da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya wallafa tare da hotunan ganawar a ranar Laraba. A cewar sanarwar, “Shugaba Macron ya karɓi baƙuncin Shugaba Tinubu domin cin abincin rana a fadar Elysee da ke birnin Paris.” Tinubu ya fara hutun kwanaki 10 daga cikin hutun shekara da ya dauka wanda ya soma...
Haka zalika, Ministan Ilimi, Dakta Olatunji Alausa , shi ma ya jinjinawa rawar da Gwamna Sani ya taka wajen sauƙaƙa bikin kaddamar da Cibiyar Horar da Sana’o’i da Kwarewa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gudanar, yana mai cewa yanzu haka ana sake fasalin makarantun fasaha na ƙasa baki ɗaya domin su mai da hankali kacokan kan darussa masu amfani da tasiri. Shettima ya bukaci mambobin NCS da su hada kai bayan wani tsari guda na juyin-juya halin Nijeriya, yana mai gargadin cewa “ba za mu iya gina ma’aikata da za su yi shiri a nan gaba kan tushen rarraba.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
Za a kuma ƙaddamar da sabon shiri, Nigeria@65 Compendium, wanda zai zayyano ci gaban ƙasa a fannoni kamar shugabanci, tattalin arziƙi, da ci gaban ƙasa a tsawon shekarun. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Zaɓen Nijeriya INEC ta amince da jam’iyyar ’yan haɗaka ta ADC, ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Majalisar Dattawa, David Mark. Wannan tabbaci na zuwa ne bayan hukumar ta wallafa sunayen shugabannin jam’iyyar a shafinta na intanet, abin da ya kawo ƙarshen dogon jira da aka yi tun bayan ayyana ta a matsayin jam’iyyar haɗin kan ’yan adawa a ranar 2 ga Yuli. Masu zanga-zanga sun ƙone matar tsohon Firaministan Nepal Yadda zanga-zangar adawa da rashawa ta rikiɗe zuwa tarzoma a Nepal Tun a watan Yulin ne dai gamayyar ’yan adawa suka ayyana David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar, tare da tsohon Gwamnan Osun, Rauf Aregbesola, a matsayin sakatarenta na ƙasa. Sai dai kafin yanzu, INEC ba ta sanya sunayensu a...
A halin yanzu, sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a cikin karni guda suna ci gaba da habaka cikin sauri, yayin da mulkin kama-karya, son kai, da kuma kariyar tattalin arziki suka kara yawaita. A wannan yanayi, a wajen taron yanar gizo na shugabannin kasashen BRICS da aka gudanar a ran 8 ga watan nan da muka ciki, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da shawarwari uku don karfafa “hadin kan kasashen BRICS” da kuma kafa kyakkyawar makomar bil’adama ta bai daya. Wato na farko nacewa ga kasancewar mabambantan bangarori a duniya. Bugu da kari, a kare adalcin duniya domin ci gaba da bude kasuwanci don samun nasara ga kowa, da kuma kiyaye tsarin tattalin arzikin duniya....
Shaidu sun ce yawancin ‘yan kasuwar sun gudu cikin daji, domin tsira da rayukansu. Maharan sun kashe sojoji biyar da ‘yan kasuwa kusan 10. Al’ummar sun roƙi gwamnati a matakan ƙananan hukumomin, jiha da tarayya su tallafa musu wajen tsaro, ilimi, lafiya, da samar da hanyoyi. Kakakin sojojin, Kyaftin David Adewusi, ya ce bai san da labarin harin ba amma zai yi bayani daga baya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Jami’ar MAAUN Da Kwalejin Seneca ta Canada Sun Yi Haɗin Gwiwa Domin Samar Da Damarmaki Ga Ɗalibai A Duniya
A yayin taron rattaba hannun, Farfesa Gwarzo ya bayyana manufar wannan yarjejeniya, inda ya ce hadin gwiwar za ta bai wa dalibai da ma’aikata damar cin moriyar albarkatu da kwarewa daga kasashen waje. “Wannan hadin gwiwar alama ce ta jajircewarmu wajen hada jami’o’inmu da manyan cibiyoyi na duniya domin bunkasa kirkire-kirkire da bincike a rukunin jami’o’inmu na MAAUN,” in ji shi. A karkashin wannan yarjejeniyar, cibiyoyin biyu za su rika raba kwarewar su tare da tallafa wa juna don cimma manufofi na bai daya. Muhimman bangarorin hadin gwiwar sun hada da samar da koyarwar harshen Turanci ta yanar gizo ga daliban MAAUN, samar da hanyoyi don ci gaba da karatu a Seneca, da bayar da shawarwari kan harkokin...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa takaitacce hadin kai ta bawa hukumar IAEA a yarjeniyar da ta cimma da Gorris a birnin Alkahira. Ya nuna irin hakurin da JMI ta nuna bayan hare-haren da aka kai mata kan cibiyoyin Nukliyar kasar . Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana fadar haka a yau a shafinsa na X kan cewa, Iran ta amince da takaitaccen aiki da hukumar IAEA ne saboda dole ne ya zamanto ana kula da ayyukan nukliyar kasar ko da takaitacce ne. Sannan ya ce kasar tana son ci gaba da raya yarjeniyar JCPOA na shekara ta 2015. Ya ce, Iran ta amince da wannan takaitaccen yarjeniya ne bayan ta...