Angola Zata Shiga Shirin ‘Yankunan Kasuwanci’ Na Kungiyar SADC
Published: 4th, March 2025 GMT
Kasar Angola ta bada sanarwan cewa, zata shiga shirin kungiyar kasashen kudancin Afirka SADC na yankunan kasuwanci, wanda hakan zai bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen yankin .
Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya bayyana cewa shigar Angola cikin tsarin yankunan kasuwanci, SADC kuma a matsayin mamba na 14 a wannan tsarin zai dauke kudin fito tsakanin kasashen 13 da Angolar.
Labarin ya kara da cewa bayan tattaunawa mai tsawo daga karshe Angola ta sami amincewar mafi yawan kasashen kungiyar ta SADC mai mambobi 16.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Rasha Ta Mayar Da Martani Ga Shugaban Amurka Kan Gindaya Wa’adin Kawo Karshen Yakin Ukraine
Martanin da Rasha ta mayar dangane da sabon wa’adin Trump na kawo karshen yakin Ukraine
Mataimakin shugaban kwamitin tsaron Rasha Dmitry Medvedev ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump game da takaita wa’adin tsagaita bude wuta tsakanin Rasha da Ukraine, yana mai cewa matakin kunna yaki ne.
Medvedev ya rubuta a kan dandalinsa na X cewa: “Trump yana wasa, irin wasan gargadi tare da Rasha: Na kayyade mata kwanaki 50 ko 10 … amma ya kamata ya tuna abubuwa biyu: Na daya Rasha ba Isra’ila ba ne ko kuma Iran. Na biyu. duk wani sabon gargadi yana matsayin barazana ne kuma matakin kunna wutar yaki ne. Ba tsakanin Rasha da Ukraine ba, amma tare da kasarsa. Amurka ta nshiga taitayinta!”
Da sanyin safiyar litinin ne shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da rage wa’adin kwanaki 50 da ya sanya a farkon wannan wata na tsagaita bude wuta a Ukraine zuwa tsakanin kwanaki 10 zuwa 12. Ya ce “ba ya ganin wani ci gaba wajen warware rikicin Ukraine” kuma “babu amfanin jira.”