Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Kwalejin Koyon Tukin Jiragen Sama
Published: 19th, February 2025 GMT
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Dokta Danjuma Adamu Ismaila a matsayin shugaban kwalejin koyon tukin jiragen sama ta Najeriya (NCAT) da ke Zariya.
Sanarwar da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce Dakta Ismaila, kwararre kan harkokin sufurin jiragen sama, da manufofin tattalin arziki, ya kammala karatunsa na digiri a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya samu digiri a fannin kimiyyar lissafi a shekarar 1989.
Ya kuma yi babbar Difloma ta a fannin Sufuri sannan ya halarci kwasa-kwasan da dama, da tarukan karawa juna sani.
Hakazalika memba ne na kungiyar masana harkar sufurin jiragen sama ta Birtaniya, wato Aeronautical Society, UK, da Ƙungiyar Binciken Sufurin Jiragen Sama, da sauransu.
Kafin nadin nasa, Dr. Danjuma Adamu Ismail malami ne a jami’ar sufuri ta tarayya dake Daura.
Daga Bello Wakili
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kwalejin Koyon Tukin Jiragen Sama
এছাড়াও পড়ুন:
PLA Reshen Kudancin Kasar Ta Yi Sintiri Na Hadin Gwiwa A Tekun Kudancin Sin
Kakakin yada labarai na rundunar sojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin ko PLA reshen kudancin kasar, babban kanar na sojojin sama Tian Junli, ya bayyana cewa, jiya Asabar rundunar sojin ta gudanar da sintiri na hadin gwiwa a ruwan teku da kuma sama a yankin tekun kudancin Sin.
Tian ya kara da cewa, sitirin hadin gwiwa a teku da sama da Philippines ta gudanar tare da wasu kasashen duniya, ya kawo barazanar tsaro ga yankin tekun kudancin Sin, kuma ya lalata zaman lafiya da kwanciyar hankali na yankin. Don haka, rundunar za ta ci gaba da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana tare da kiyaye ikon mulkin kan kasar Sin, da hakki da moriyarta a tekun.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp