Dalilin da Tinubu ya ƙi amincewa da ƙudirin kafa Jami’ar Ilimi a Adamawa
Published: 4th, February 2025 GMT
Shugaba Bola Tinubu ya ƙi rattaba hannu kan ƙudirin kafa Jami’ar Ilimi ta Tarayya a Numan da ke Jihar Adamawa.
Hakan na ƙunshe cikin wata wasiƙa da ya aike wa Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas wadda mataimakinsa, Benjamin Kalu ya karanta a yayin zaman majalisar na yau Talata.
Alakarmu da El-Rufai na nan babu matsala —Uba Sani HOTUNA: Hatsarin tirela ya yi ajalin mutum 4, shanu 15 da awaki 20 a NejaWasiƙar shugaban ta kare matakin da ya ɗauka na ƙin amincewa bisa la’akari da tanadin da sashe na 22 da ke cikin ƙudirin kafa jami’ar ya yi.
Ya yi bayanin cewa sashen ya yi tanadin cewa filin da za a gina jami’ar zai kasance a ƙarƙashin ikon Gwamnatin Jihar Adamawa wanda ya saɓa wa ƙa’idar kasancewa a ƙarƙashin ikon Gwamnatin Tarayya.
Kazalika, wasiƙar ta Shugaba Tinubu ta kafa hujjar cewa sashe na 25 (b) da ke ƙunshe a cikin ƙudirin bai bayyana cewa jami’ar tana da hurumin da za ta riƙa bayar da shaidar karatun digiri ba.
Idan ba a manta ba, a shekarar da gabata ce Majalisar Wakilan ta amince da ƙudirin kafa Jami’ar Ilimi a Numan da ke Jihar Adamawa kuma ta miƙa wa shugaban ƙasar domin neman sahalewarsa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jami ar Ilimi ta Tarayya Jihar Adamawa
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya janye dokar ta-ɓaci da ya ayyana ta tsawon watanni shida a Jihar Ribas.
Tinubu, ya ayyana dokar tun a ranar 18 ga watan Maris, 2025, saboda rikicin siyasa da ya haifar da tsaiko a harkokin mulki tsakanin ɓangaren Zartarwa da Majalisar Dokokin jihar.
NECO ta saki sakamakon jarabawar 2025 Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyiA jawabin da ya gabatar a Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Laraba, Tinubu ya ce matakin dokar ta-ɓacin ya cimma manufarsa, kuma ba za a tsawaita ba ƙarewar wa’adin da aka gindaya.
“Ina farin ciki yau game da bayanan da ke hannuna, an samu yanayin fahimta a tsakanin dukkanin masu ruwa da tsaki a Jihar Ribas domin dawo da mulkin dimokuraɗiyya cikin gaggawa,” in ji Shugaban Ƙasa.
Gwamnan Jihar, Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu, tare da ‘yan majalisar dokokin jihar, za su koma kan kujerunsu daga ranar Alhamis, 18 ga watan Satumba, 2025.
Tun da farko, dokar ta-ɓacin ta dakatar da manyan jami’an gwamnati da masu madafun iko na jihar sakamakon rikici da aka daɗe ana yi a jihar.
“Da ban ayyana wannan dokar ta-ɓacin ba, da hakan ya zama babbar gazawa a wajena a matsayina na Shugaban Ƙasa.
“Amma yanzu da zaman lafiya da doka suka wanzu, al’ummar Jihar Ribas za su sake cin moriyar dimokuraɗiyya,” in ji Tinubu.
Ya kuma yi kira ga gwamnoni da majalisun dokokin jihohi na faɗin Najeriya da su ci gaba da wanzar da zaman lafiya da haɗin kai tsakanin ɓangaren zartarwa da na majalisa.
Har ila yau, ya jaddada cewa zaman lafiya da kyakkyawan shugabanci su ne tubalin kawo ci gaban dimokuraɗiyya ga al’umma.