Kotu ta tsige Ohinoyi na Ƙasar Ebira
Published: 4th, February 2025 GMT
Babbar Kotun Jihar Kogi ta tsige Alhaji Ahmed Muhammed Tajani Anaje daga kujerarsa ta Ohinoyi na Ƙasar Ebira.
Kotun ta soke naɗin Alhaji Ahmed Muhammed ne a ranar Litinin, shekara guda bayan fara aikin basaraken.
Alƙalin kotun, Mai Shari’a Salisu Umar, ya kuma dakatar da basaraken daga gabatar da kansa matsayin Ohinoyi, har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukuncin ƙarshe.
Kotun ta bayar da umarnin ne bayan ƙarar da Dakta Barnabas Adeku Ojiah da wasu mutum biyu suka shigar.
Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Kano Mai gari ya tsere bayan mazauna sun cinna wa gidansa wuta a Kano NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Noma Ba Tare Da Kashe Kuɗi Da Yawa BaSun shigar da ƙara ne suna ƙalubalantar naɗin da Gwamnan Jihar Kogi ya yi wa Alhaji Ahmed Muhammed Tajani Anaje a matsayin Ohinoyi na Ƙasar Ebira.
A watan Disamban 2023 ne tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ne ya naɗa Alhaji Ahmed Tijani Anaje a matsayin Ohinoyi na Ƙasar Ebira a yayin da tsohon gwamnan ke shirin sauka daga mulki.
A ranar 8 ga watan Janairun 2024 ne dakataccen sarkin ya fara aiki.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
DSS Ta Maka Sowore, Facebook Da X A Kotu Kan Wallafa Rubutu Game Da Tinubu
Ta kuma ba shi umarnin ya goge rubutun da ta ce ya ci zarafin shugaban ƙasa.
Sai dai Sowore ya ƙi sauke rubutun da ya wallafa.
Ya rubuta a shafinsa na X cewa: “DSS ta shigar da ƙara mai tuhuma biyar a Babbar Kotun Tarayya a Abuja a kaina, X da kuma Facebook.
“Sun ce wai na aikata wasu sabbin laifuka saboda na kira Tinubu ‘ɓarawo’. Duk da haka, zan halarci kotu duk lokacin da aka fara shari’ar.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp