2025-08-01@20:53:05 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6008

«kasuwa»:

    Bayan shekar 22 da kuɓutar da Nijeriya daga mulkin soja, dimokuraɗiyya na ci gaba da fama da rauni mai tsanani. Alamun cutar sun bayyana ne a cinikin baragurbin wakilai (delegates), amfani da kuɗin ƙasa da aka wawure ta hanyar haram wajen gudanar da yaƙin neman zaɓe, maƙudan kuɗin da ake ware wa Hukumar Zaɓe ta...
    Asusun kula da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, ya ce Najeriya ce ƙasa ta biyu da aka fi samun ɓullar cutar kwalara a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka. Darektan Hukumar UNICEF mai kula da yammacin Afirka da Afirka ta tsakiya, Gilles Fagninou  ne ya bayyana hakan tare da cewar annobar kwalara ta zama...
    An yi balaguro na cikin gida sama da biliyan 3.28 a kasar Sin a rabin farko na shekarar 2025, adadin da ya karu da kashi 20.6 cikin dari a mizanin duk shekara, bisa bayanan da ma’aikatar al’adu da yawon bude ido ta fitar a yau Jumma’a. Masu yawon bude ido na cikin gida sun kashe...
    A daren Juma’a ne dab da wayewar gari wata motar tirela ɗauke da awaki da kaji wadda ta taso daga Gwauron Dutse a Jihar Kano ta yi haɗari. Motar tirelar wadda take ɗauke da dakon awaki da kuma kwandunan kaji mai yawa a samanta baya ga mutane da ta ɗauko ta yi haɗarin a kusa...
    Kafin ya yi ritaya daga Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya, AVM Kaita ya riƙe muƙamai da dama, ciki har da Daraktan Tsare-tsare a Hedikwatar Tsaro da kuma Shugaban Sashen Kirkire-Kirkire na tsaro. Ana girmama shi saboda gudunmawar da ya bayar wajen horarwa da inganta ayyukan rundunar sojin sama. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
    Majalisar Dokokin Jihar Sokoto ta umarci Kwamishinan harkokin makamashi da albarkatun man Fetur, Hon. Sanusi Danfulani, da ya bayyana a gabanta ranar Talata, 5 ga watan Agusta, saboda gazawarsa wajen halartar ziyarar duba aiki da kwamitin majalisar mai kula da kimiyya da fasaha ya gudanar. Ziyarar da aka shirya a ranar Alhamis ta sami tsaiko...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Matukar dai Trump ya bukaci dakatar da inganta sinadarin Uranium gaba daya a Iran, to ba za a cimma wata yarjejeniya ba Ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Araqchi ya jaddada a wata hira da jaridar Financial Times cewa: Iran na neman a biya ta diyya kan...
    Kungiyar Ma’aikatan jinya da Ungozoma ta Ƙasa (NANNM) ta mayar wa da gwamnati martanin cewa har yanzu tana ci gaba da gudanar da yajin aikin da take yi. Ministan Lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Ali Pate, ne dai ya bayyana cewa ƙungiyar ta janye yajin aikin gargaɗin. An ceto mutum uku da aka yi garkuwa...
    Slovenia ta kasance Ƙasar Turai ta farko da ta ba da sanarwar hana tura makamai zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila Kasar Slovenia ta sanar da haramta musayar zirga-zirgan kayayyakin kasuwanci tsakaninta da haramtacciyar kasar Isra’ila musamman safarar makamai da kayan aikin soji zuwa Isra’ila, inda ta zama kasa ta farko ta Turai da ta dauki wannan...
    Kasar Spain ta bayyana abin da ke faruwa a Gaza a matsayin abin kunya ga bil’adama Ministan harkokin wajen kasar Spain José Manuel Albares ya yi kira ga mahukuntan Isra’ila a ranar Alhamis da su bude mashigar ruwa na dindindin domin ba da damar kai agajin jin kai zuwa zirin Gaza, yana mai gargadin cewa;...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta ce ta ceto wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su, bayan sun yi artabu da wasu da ake zargin sun yi garkuwa da su a wani mummunan musayar wuta da aka yi a tsaunin Shanga. Waɗanda aka yi garkuwan da su sun haɗa da: Muhammad Nasamu Namata...
    Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), za ta fara rajistar ƙuri’a ta intanet a ranar 18 ga watan Agusta, 2025, domin tunkurar zaɓen 2027. Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar ban girma da Hukumar NOA ta masa a hedikwatar INEC da ke Abuja. Rundunar sojin ruwa za...
    A kwanakin baya, an bude tashar jirgin ruwa ta fasinja ta kasa da kasa ta kasar Sin ta farko, wato tashar jirgin ruwa ta Shekou dake birnin Shenzhen. ’Yan kasuwa daga Argentina, da Chile, da Brazil sun shiga kasar Sin ta tashar bisa sabuwar manufar shiga kasar Sin ba tare da biza ba, inda aka...
    Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyar ta na hadin gwiwa da Cibiyar Binciken Cututtuka ta Jihar Kano(KIRCT) a fannonin bincike, samar da rigakafi, habaka magunguna da kuma yaki da cututtuka masu nasaba da zafi (tropical diseases). Darakta Janar na Hukumar Binciken Harkokin Halittu ta Kasa (NBRDA), Farfesa Abdullahi Mustapha ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar...
    Rundunar sojin ruwan Najeriya ta bayyana aniyar kafa sansaninta a Ƙaramar Hukumar Yauri ta Jihar Kebbi a wani mataki don bunƙasa harkokin tsaron iyakokin ruwa. Hakan na zuwa ne bayan da wata tawagar manyan jami’an sojojin ruwan suka kai ziyara gidan gwamnatin Jihar Kebbi. Ɗaliban da aka sace a Binuwai sun kuɓuta  ’Yan Najeriya miliyan...
    Jami’an tsaro sun tabbatar da kuɓutar wasu ɗalibai shida na Makarantar Horon Ilimin Shari’a ta Najeriya da aka sace. Rundunar ’yan sandan Jihar Binuwai ce ta bayyana hakan a ranar Juma’a. ’Yan Najeriya miliyan 34 na cikin barazanar yunwa Mun ci ribar Naira biliyan 414 a cikin wata 6 a Najeriya – Kamfanin MTN Kakakin...
    “Kiyasin ƴan Nijeriya miliyan 20 ke rayuwa da cutar hanta, kuma mutum miliyan 18.2 sun kamu ne da cutar rukunin B, sannan wasu mutum miliyan 2.5 sun kamu da cutar rukunin C. Abin takaici, ƴan Nijeriya 4,252 ne ke mutuwa a duk shekara sakamakon ciwon hanta da aka kasa maganceta ke haifarwa,” ya shaida.  A...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana naɗin Saidu Yahya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a da yaƙi da cin hanci da rashawa (PCACC), bayan ƙarewar wa’adin tsohon shugaban, Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado, a watan Yuni. Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta...
    Gwamnan Jihar ta Gwambe, ya tunatar da cewa; a lokacin da Bola Ahmed Tinubu ya tsaya a gabanmu a matsayin ɗan takara a yaƙin zaɓen 2023, ya yi wa Arewacin Nijeriya alƙawura na musamman. Kazalika, Arewa ta amince da manufofin shugaban ƙasar, ta kuma yi tsayin daka wajen zaɓensa, inda suka bayar da gudunmawa na...
    Iran ta yi watsi da zarge-zargen marasa tushe balantana makama da kasashen yammacin duniya ke yi a kanta, kan cewa tana yunkurin kashe wasu mutane a cikin kasashensu. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya yi Allah wadai da ikirarin da ya kira  na kin jinin Iran da Amurka da Canada da wasu kasashen...
    Akalla ’yan gudun hijira miliyan daya da dubu 400 da ke Arewa maso gabashin Najeriya ne suke fuskantar barazanar yunwa bayan yanje tallafin da Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ke bayarwa. Wani rahoton majalisar a kan abinci da tsaro wanda gwamnatin Najeriya, Shirin Kula da Abinci na Majalisar (FAO) da sauran masu ruwa da tsaki a...
    Ministan kasuwanci na Afirka ta Kudu Parks Tau ya fada jiya Alhamis cewa kasarsa na shirin yin shawarwarin kasuwanci da nufin kaucewa harajin kashi 30% na Amurka a kan kasarsa, wanda  zai fara aiki daga wannan Juma’a. A farkon watan Mayu ne Afirka ta Kudu ta gabatar da wani shirin  yarjejeniya ta kasuwanci ga gwamnatin...
    Gidan rediyon sojojin Isra’ila ya bayar da rahoto a wannan  Alhamis cewa, wani soja ya kashe kansa bayan ya kwashe fiye da kwanaki 300 a cikin sojojin wucin gadi. Jaridar Haaretz ta Isra’ila ta bayar da rahoton cewa, adadin sojojin da suka kashe kansu a wannan watan kadai ya kai bakwai. A cikin wannan yanayi,...
    Ya nuna rashin jin daɗinsa da rabon ayyukan tituna kamar yadda aka samu a cikin wata sanarwa da ma’aikatar ayyuka ta fitar a watan Mayun 2025, wanda a cewarsa, an ware Naira tiriliyan 1.394 wa yankin Kudu-maso-Yamma, yayin da ɗaukacin yankin Arewa-maso-gabas suka samu Naira biliyan 30, sai kuma yankin Arewa-maso-Yamma Naira 105 biliyan. “Rashin...
    Sai dai girma, kima da ɗaukakar da matasa ke da ita ga al’umma ta ja baya ƙasa sosai a bisa ga yadda rayuwarsu ke iyo da ninƙaya a kogin  zubar da mutunci ta hanyar aiwatar da abubuwan da ke da alamar ayar tambaya. Matasa da dama a yau ba su ganin kowa da gashi, ba...
    Jim kadan bayan da kungiyar kai Dauki Gaggawa ta kasar Sudan ta sanar kafa gwamnatin mai mambobi 15, kungiyar tarayyar Afirka ta mayar da martanin kin amincewa da ita. Bugu da kari kingiyar ta tarayyar Afirka ta kira yi  kasashen  da suke mambobi a cikinta da kuma kungiyoyin  kasa da kasa da kar su amince...
    Dangote Ya Bada Shawarar Samar Da Gidaje Masu Rahusa Da ‘Yan Nijeriya Za Su Iya Mallaka Majalisar Dattawa Ta Yi Allah-wadai Da Zanga-zangar Ƙin Jinin ’Yan Nijeriya A Ghana Sai dai, abin dubi a nan shi ne, yadda kusan yanzu a kasar, tabbatar da doka da oda, a cikin kasar, ya koma kachokam, a huunun...
    Kamfanin sadarwa na MTN ya sanar da cin ribar Naira biliyan 414 a watanni shida na farkon shekarar 2025 a Najeriya. Kamfanin ya bayyana hakan ne a rahotonsa na karshen wata shidan da ya gabatar a gaban Hukumar da ke Kula da Kasuwar Hannun Jari ta Najeriya a ranar Alhamis. Za a kashe biliyan 712.26...
    Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince da kashe Naira biliyan 712.26 don yi wa wani sashe na filin jirgin saman a Murtala Muhammad da ke Legas garambawul. Hakan dai ya biyo bayan zaman majalisar wanda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta a Abuja ranar Laraba. NAJERIYA A YAU: Me dokar kasa ta ce kan...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Karin wa’adin aiki da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Kwanturola Janar na Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kasa, Bashir Adewale Adeniyi na ta shan suka daga mutane daban-daban. Yayin da wasu ke ganin abin da shugaban ya yi da cewa ya dace, wasu kuwa na...
    Mujallar Qiushi ta kasar Sin za ta wallafi jawabin shugaban kasar Sin Xi Jinping gobe Jumma’a 1 ga watan Agusta, wanda Xi ya taba gabatarwa a gun babban taron kiyaye muhallin halittu na kasar Sin a ranar 17 ga watan Yulin shekarar 2023. Jawabin ya bayyana cewa, bunkasar tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar Sin...
    Gwamnatin Nijeriya ta bayanna cewa za ta soma yi wa ɗaliban jami’o’in ƙasar nan gwajin miyagun ƙwayoyi a wani mataki na daƙile yaɗuwar ta’ammali da ƙwayoyin. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito cewa, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya tare da haɗin gwiwar Hukumar Yaƙi da Fataucin Miyagun Kwayoyi NDLEA ne za su jagoranci aikin....
    Ruwan sama kamar da bakin kwarya tare da iska mai karfi da aka tafka a kwanan nan ya yi sanadin mutuwar mutane 44, yayin da wasu tara suka bace a birnin Beijing, kamar yadda aka bayyana a wani taron manema labarai da ya gudana a yau Alhamis. A yayin taron manema labarai da gwamnatin birnin...
    A wani yunkuri na yaki da rashin abinci mai gina jiki da kuma karfafa tattalin arzikin mata a jihar Jigawa, Gwamna Umar Namadi ya jagoranci bikin yaye mata 600 da suka samu horo kan yadda ake sarrafa abincin yara mai gina jiki daga kayayyakin da ake samarwa a gida, wanda aka fi sani da “Tom...
    Allah Ya yi wa Mai Martaba, Sarkin Gudi Alhaji Isa Bunuwo Ibn Khaji rasuwa a asibitin Nizameye da ke Abuja ranar Alhamis. Mai martaba Sarkin wanda ke garin Gadaka a Ƙaramar hukumar Fika cikin Jihar Yobe ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya. Gwamnatin Jigawa ta horas da malamai 20,000 fasahar sadarwar zamani Peter...
    Gwamna Zulum ya nuna jin dadinsa ga kwamishinonin biyu, tare da yi musu fatan alheri a cikin ayyukansu na gaba.   Sai dai ya sanar da nadin Engr. Mohammed Habib da Ibrahim Hala Hassan domin maye gurbin kwamishinonin biyu da aka sauke.   A halin da ake ciki, Gwamna Zulum ya kuma amince da nadin...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta horas da Malaman makarantun sakandare kimanin dubu 20 ilimin fasahar sadarwar zamani (digital). Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawaga daga Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta ƙasa (NITDA) da Cibiyar Zaman Lafiya ƙarƙashin jagorancin Farfesa Hauwa Ibrahim da take Amurka, a...
    A wani ɓangare na shirin gudanar da zaɓen cike gurbi na Babura/Garki a Majalisar Tarayya, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) reshen Babura ta shirya muhimmin taron masu ruwa da tsaki domin tabbatar da sahihin zaɓe mai inganci da haɗin kai.   A jawabinsa yayin taron, jami’in zaɓe na ƙaramar hukumar Babura, Malam...
    Ɗaya daga cikin jigo da suka kafa Jam’iyyar PDP, Farfesa Jerry Gana ya yi iƙirarin cewa tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi zai kayar da duk wani ɗan takara a jihohin Arewacin Najeriya idan ya tsaya takara a PDP. Da yake bayabni a tashar talabijin ta Arise TV a ranar Laraba, Gana ya ce, “Ni...
    Gwamnatin Amurka ta bada sanarwan kakabawa gwamnatin jeka na yi ka ta Falasdinawa takunkuman hadawa jami’anta visar shiga kasar a safiyar yau Alhamis. Shafin yanar gizo na labarai ‘abrabNews’ na kasar Saudiya ya bayyana cewa majiyar fadar white House ta bayyana cewa gwamnatin Palasdinawa musamman Mahmood Abbas suna zagon kasa ga kokarin da kasar Amurka...
    Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah ta Nijeriya reshen Jihar Benuwe, a ranar Alhamis, ta bayyana cewa aƙalla shanu 340 na mambobinta ne aka sace a cikin watan Yuli na 2025. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren ƙungiyar na jiha, Ibrahim Galma ya fitar kuma aka rabawa manema labarai a Makurdi. Tinubu...
    Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙarin wa’adin shekara guda ga shugaban hukumar Kwastan ta Nijeriya, Bashir Adewale Adeniyi. Kafin wannan ƙarin wa’adin, aikin Adeniyi zai kare ne a ranar 31 ga Agusta, 2025. Sai dai sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya...
    Tsohon ɗan wasan tsakiyar Barcelona, Carles Perez, yana kwance a asibiti a ƙasar Girka bayan da wani kare ya cije shi a al’aurarsa yayin da yake yawo da nasa karen a Thermi, a wata unguwa a Thessaloniki, ranar Talata. Perez, mai shekaru 27, yana ƙoƙarin raba karensa da wani da suke fada lokacin da ya...
    Shugaba Bola Tinubu ya ƙara wa Bashir Adeniyi, Shugaban Hukumar Kwastam ta Ƙasa, karin shekara ɗaya a kan wa’adin da ya kamata ya yi na shugabancin hukumar. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Alhamis. Mutum 9 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa NNPCL...
    Shugaba Bola Tinubu ya ƙara wa Bashir Adeniyi, Shugaban Hukumar Kwastam ta Ƙasa, karin shekara ɗaya a kan wa’adin da ya kamata ya yi na shugabancin hukumar. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Alhamis. Mutum 9 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa NNPCL...
    Shugaban kasar Lebanon wanda ya gabatar da jawabi da safiyar yau ya ce; A cikin sakwannin da mu ka aike wa Amurka, mun bukaci ganin an kawo karshen hare-haren da Isra’ila take ci gaba da kawo wa Lebanon, ta sama, kasa da ruwa, haka nan kuma kisan gillar da take yi wa mutane a cikin...
    Binciken likitoci da ‘yansanda ya tabbatar cewa gubar ce ta yi sanadin mutuwarsa. Haka kuma, kotun ta yanke wa wani mutum mai suna Sani Sa’adu hukuncin ɗaurin shekara biyar saboda ɓoye gaskiya da ya yi dangane da wata Gift Bako, wadda ake zargi da hannu a kisan. Lauyoyin waɗanda aka yanke wa hukunci sun nemi...
    Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ya sanar da sake haka sabbin rijiyoyin man fetur guda hudu yankin Kolmani na jihar Bauchi, kamar yadda Darakta a kamfanin, Yusuf Usman ya tabbatar. Daraktan ya kuma sake jaddada aniyar kamfanin ta ganin ya fara aikin hako danyen man fetur a Arewacin Najeriya. Samar da makamashi mai tsafta na...
    Aƙalla mutum tara ne suka rasu, yayin da wani kwale-kwale ɗauke da fasinjoji 17 ya kife a Jihar Jigawa. Yawancin fasinjojin da hatsarin ya rutsa da su ’yan mata ne. Kamfanin NNPCL ya sake haka sabbin rijiyoyin man fetur 4 a Kolmani Samar da makamashi mai tsafta na zamani shi ne fatanmu — Guterres Lamarin...
    Abdullahi ya ce tun kafin a kafa haɗakar, wasu sun riga sun fara yaɗa cewa an shirya ta ne domin Atiku. Ya ƙara da cewa: “Ni ina da shekara 56, wa ya ce ba zan iya tsayawa takarar shugaban ƙasa ba?” Da aka tambaye shi game da Peter Obi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na...