Ban taɓa fuskantar tsangwama a Kannywood ba — Prince Aboki
Published: 26th, March 2025 GMT
Daraktan Fim ɗin Mai martaba, Prince Daniel (ABOKI), ya ce ba gaskiya ba ne batun da ake yaɗawa cewa yana fuskantar tsangwama a Kannywwod saboda bambancin addininsa.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Aboki ya ce shi ma batun cewa ana nuna masa bambamci a Nollywood saboda ɗan arewa ne ba shi da tushe balle makama.
“Wasu labarai da aka wallafa na nuna cewa wai masana’antar Kannywood ta ƙi amincewa da ni saboda addini na, ita kuma Nollywood saboda ni ɗan Arewa ne.
“Da farko dai ban yi hira da wata jarida ko kafar yaɗa labarai ba dangane da wannan batu. Amma duk da haka bari na ɗan yi ƙarin haske.
“Na halarci wani taron masana’antar Nollywood da Hollywood a birnin Los Angeles na Jihar California da ke Amurka a farkon wannan watan, inda a sashen tambaya da amsa na taron aka tambaye ni ƙalubalen da muka fuskanta lokacin fim ɗin Mai Martaba da gwagwarmayar da muka yi kafin kai wa matakin kambun fina-finan duniya na Oscar.
“Na faɗi abubuwa da dama da suka haɗa da fargabar matsalar tsaro da na masu ɗaukar nauyi kasancewar babu wanda yake son yin kasadar ba mu kuɗinsa, la’akari da cewa ni sabon darakta ne wanda ke aiki tare da sababbin jarumai.
“A wani lokacin ɓangaren masana’antar Kannywood na yi mana kallon ‘yan Nollywood, su ma Nollywood suna kallonmu a matsayin ‘yan Kannywood, saboda kawai ni ɗan Arewa ne.
“Na yi wannan bayanin ne da kyakkyawar niyya domin taimaka wa masu sauraro a cikin zauren su fahimci ɓangarorin masana’antar Fina-finai a Najeriya da kuma yadda yake da ƙalubale a gare mu a lokacin.
“Domin fayyace zahiri, masana’antar Kannywood ba ta taɓa nuna min ƙiyayya ba ta ƙabilanci ko addini.
“Hasalima, masana’antar ce babban ginshiƙin goyon bayan da na samu a matsayina na mai shirya fim.
“An nuna min ƙauna a fili ta hanyar babban goyon bayan da muka samu daga masu kallo da sauran al-umma a lokacin da muka nuna fina-finanmu a gidajen kallo, da kuma ƙarfafawa daga ƙwararrun ‘yan masana’antar tsofaffi da sababbin shiga,” in ji shi.
Fim ɗin Mai martaba dai an haska shi ne kimanin watanni takwas da suka gabata, kuma ci gaba ne kan wasan kwaikwayon gidan Rediyon Arewa da ke Kano mai taken ‘Kasar Jallaba”, inda Prince aboki ke aiki a matsayin jagoran sashin shirye-shirye.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: kannywood masana antar
এছাড়াও পড়ুন:
Ƙwallo ta kashe ɗan wasan Cricket
Wani haziƙin matashin ɗan wasan Cricket mai shekara 17 ɗan asalin ƙasar Australiya ya mutu a yau Alhamis bayan ƙwallo ta buge shi a lokacin wasa.
Ƙwallon ta bugi, Ben Austin a wuyansa ne duk da cewa yana sanye da hular kariyar kai (Helmet) a lokacin da yake ƙoƙarin kare ƙwallon da aka bugo.
Za a rataye wanda ya kashe ɗan uwansa a Ekiti Gobara ta tashi a babban kanti a AbujaNan take aka garzaya da shi asibiti cikin mawuyacin hali, daga bisani rai ya yi halinsa.
“Mun yi matuƙar baƙin ciki da rasuwar haziƙi Ben ɗinmu, wanda ya mutu da safiyar yau Alhamis,” in ji mahaifinsa Jace Austin a cikin wata sanarwa.
A cewar jaridar ABC News, matashin ɗan wasan bai sanya rigar da ke kare wuyansa ba, hakan ne ya sa ƙwallon ta dufafe shi.
Austin ya kasance ƙwararren mai buga ƙwallo, wanda ƙungiyarsa ta Ferntree Gully Cricket Club ta ɗauke shi a matsayin “ɗan wasan Cricket mai hazaka, babban jagora kuma matashi mai ban mamaki”.
‘Yan wasa daga ƙungiyoyin biyu na India da Australia a ɓangaren mata da ke buga wasan Cricket na duniya sun sanya baƙaƙen kambu domin alhinin mutuwarsa.
Yau dai kimanin shekaru 11 rabon da wani ɗan wasan Cricket ya mutu a lokacin wasa, tun bayan da shahararren ɗan wasan nan ɗan asalin ƙasar Australia Test Phillip Hughes ya mutu a 2014.