2025-09-20@11:01:58 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6194
«Najeriya da ke»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Aƙalla mutum uku ne sun rasu, yayin da wani ɗan sanda ya ji rauni a wani rikicin ƙungiyoyin asiri da ya auku a kasuwar Owode Onirin da ke Jihar Legas. Rundunar ’yan sandan jihar, ta bayyana cewa tana neman Abiodun Ariori, Shugaban Kamfanin Golden Venture Limited, bisa zarginsa da hannu a rikicin. HOTUNA: Tinubu ya dawo Abuja bayan ziyarar aiki a Japan da Brazil Kotu ta daure dan Shugaban Equatorial Guinea kan sayar da jirgin saman kasar Shaidu sun ce ƙungiyoyin asirin biyu sun yi artabu da bindigogi, adduna da kwalabe. Ɗan sandan da ya ji rauni an garzaya da shi asibiti, inda yake cikin mawuyacin hali. Kakakin rundunar, CSP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin. Amma ta ce...
Dukkan mambobin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, in ban da Amurka, sun goyi bayan ayyana bullar yunwa mafi muni a yankin zirin Gaza ta hanyar rahoton kungiyar Integrated Food Security Phase Classification (IPC), wata kungiya mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya. Kasashe 14 da daga cikin 15 da suka amince da hakan, sun ba da tabbaci a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka yi bayan taron da suka yi a wanann Laraba, kasa da mako guda bayan da hukumar ta IPC ta fitar da wani rahoto mai tayar da hankali game da halin da ake ciki na yunwa a zirin Gaza da kewaye. Sanarwar da Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar daga baya ta zo ne a daidai...
Ya ƙara da cewa jam’iyyarsu ta ADC za ta iya fito da ‘yan takara daga kowace shiyya, duk da cewa APC da PDP sun nuna cewa daga Kudu za su fito da ɗan takara a 2027. Duk da cewa wasu na ganin tasirinsa ya ragu a Jihar Ribas saboda rikicin siyasa tsakaninsa da Nyesom Wike, Amaechi ya ce har yanzu yana da goyon baya sosai. Ya bayar da misalin yadda aka tarbe shi a Jihar a baya-bayan nan ba tare da ya biya kowa kuɗi ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
Tawagar Sudan karkashin jagorancin babban daraktan hukumar leken asiri ta kasa (NISS) Manjo Janar Ahmed Mufadal ta isa Mogadishu babban birnin kasar Somalia a wata ziyarar aiki da ta kai kasar, inda ta gana da shugaban kasar Hassan Sheikh Mohamud a fadar shugaban kasa dake Mogadishu. Jagoran tawagar ta Sudan Mufadal Sheikh Mohamud ya aike da sako daga shugaban kwamitin rikon kwarya na kasar Sudan, Laftanar Janar Abdel Fattah Al-Burhan. Sakon ya hada da jaddada aniyar Khartoum na karfafa hadin gwiwa da Somaliya, musamman a fannin tsaro da leken asiri. Taron ya samu halartar babban daraktan hukumar leken asiri ta kasar Somalia (NISS), Mahad Mohamed Salad, wanda ya tattauna da Mufadal hanyoyin inganta hadin gwiwa domin tunkarar kalubalen da yankin...
Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya musanta rahotannin da ake na cewa sojojin kasarsa suna da hannu wajen ‘kashe-kashe’ a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo. Kagame, yayin da yake magana da jami’an soji da ‘yan sanda a wata cibiyar horaswa da ke gabashin Rwanda, ya ce, ‘yan tawayen FDLR, da mayakan gwamnatin Congo, da Azalendo, da kuma sojojin Congo ne suke aikata ta’asa a gabashin Kasar. Kagame ya ba da misali da Mozambique, da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, da Sudan ta Kudu, inda dakarun Rwanda ke jibge, ya kuma jaddada cewa “Rwanda ba ta yaki da wasu kasashe, sai dai tana goyon bayan wadannan kasashe bisa bukatarsu, wadanda ke fuskantar kalubalen tsaro.” Ya kara da cewa, “Ba za mu fara yaki...
Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), Farfesa Chris Piwuna, ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta aiwatar da ɗaya daga cikin yarjejeniyar da ta ƙulla da ƙungiyar ba. Farfesa Piwuna, ya ce ASUU a koyaushe na zaɓar tattaunawa da jami’an gwamnati a matsayin mafita. Amma duk da cewa sun cimma matsaya kan batutuwa masu muhimmanci kamar kuɗaɗen gudanarwa, albashi, ’yancin malamai, ‘yancin jami’o’i, da sake duba wasu dokoki, ba a ɗauki mataki kan kowanne ba. “Babu saɓani a tsakaninmu da tawagar gwamnati,” in ji shi. “Mun amince kan abubuwa da dama, sai dai shugabanninsu, Ma’aikatar Ilimi da Gwamnatin Tarayya ba su ɗauki mataki kan kowanne ba.” Ya danganta yawan ficewa daga Najeriya da malamai da likitoci ke yi saboda ƙarancin...
Shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja, bayan ya kammala ziyarar aiki a ƙasashen Japan da Brazil. Mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya ce jirgin shugaban ƙasa ya tashi daga filin jirgin sama na Brasília a ƙasar Brazil da ƙarfe 12:57 na rana a ranar Laraba. A cewarsa ya iso Abuja da safiyar ranar Alhamis. Ga hotunan yadda wasu manyan jami’an gwamnati suka tarbi shugaban:
A lokacin ziyarar, ya gana da Shugaban Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, da sauran manyan jami’an ƙasar. Ƙasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniya guda biyar da suka shafi sufurin jiragen sama, harkokin waje, kimiyya da fasaha, da kuma noma, da wasu muhimman fannoni a ci gaban Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
’Yan bindigar da suka sace wani mutum, matarsa da ’yarsu a Jihar Katsina, na neman Naira miliyan 600 a matsayin kuɗin fansa. Wanda aka sace sun haɗa da Anas Ahmadu mai shekara 33, matarsa Halimat, da kuma ’yarsu Jidda. Ba zan tsaya takarar kowanne irin mukami ba a 2027 – El-Rufai NAJERIYA A YAU: Matakan da ciwon suga ke bi kafin illata mai fama da shi An sace su ne a gidajensu da ke Filin Canada Quarters a Sabuwar Unguwa, cikin garin Katsina da safiyar ranar Talata. A yayin kai harin, wani ɗan sa-kai mai shekara 25 mai suna Abdullahi Muhammad, ya rasu lokacin da yake ƙoƙarin ceto su. Wani ɗan uwan ma’auratan ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar...
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya ce ba zai tsaya takarar kowanne irin mukami ba a zaben 2027, inda ya ce burinsa kawai ya samar wa jiharsa da Najeriya nagartattun shugabanni. Ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Kaduna, lokacin da ya karbi wasu matasa karkashin jagorancin Aliyu Bello da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar hadakar ’yan adawa ta ADC. NAJERIYA A YAU: Matakan da ciwon suga ke bi kafin illata mai fama da shi Ruftawar katanga ta yi ajalin uwa da ’ya’yanta 2 a Zariya El-Rufa’i ya kuma soki lamirin gwamnati mai ci, inda ya ce ’yan Najeriya na ganin gazawarta karara ba tare da wani ya musu karin bayani ba. “Ba abin da wannan gwamnatin ke...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mutane da dama ba sa sanin suna dauke da ciwon suga ballantana su san hanyoyin magance shi kafin ya yi tsanani. Sau da yawa ciwon sai ya kai wani matakin da zai yi wa mutum illa sannan yake sanin yana dauke da shi. NAJERIYA A YAU: Ci Gaban Da Harshe Da Al’adun Hausa Suka Samu A Shekaru 10 DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan matakan da ciwon suga ke bi kafin ya yi tsanani da kuma hanyoyin magance shi. Domin sauke shirin, latsa nan
Lardin Hubei shi ma ya bi sawu, inda ya bullo da nasa shirye-shiryen na raba takardun tallafin tare da mai da hankali musamman a kan bangaren da ya shafi cin abinci. Babban makasudin hakan shi ne a karfafa mutane su rika fita zuwa gidajen cin abinci. Wannan ya kara farfado da salon cin abinci tare a tsakanin Sinawa da kuma kwarya-kwaryan harkokin da ake yi a gefen wasu tituna bisa tsari. Baya ga bunkasa tattalin arziki, wannan dabara tana samar da yanayi mai dadi da faranta ran jama’a. Shi ma birnin Shanghai ba a bar shi a baya ba a kan wannan sabga, inda shi kuma ya mayar da hankali a kan nishadantarwa ta fuskar al’adu. Birnin ya...
Musiba da auka wa wani gida a Zariya da ke Jihar Kaduna, bayan da katangar wani kango da ke maƙwabtaka da su ta faɗa wa mazauna gidan suna tsaka da barci. Wakilinmu ya ruwaito cewa, ruftawar ginin wadda ta auku a safiyar wannan Larabar ta yi ajalin matar gidan, Habiba Nuhu da ’ya’yanta biyu, Hauwa’u da Aina’u Nuhu. Wani ɗan sanda ya harbe soja a Bauchi A ɗora min laifin hatsarin jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja — Shugaban NRC Sai dai mijinta, wanda shi ma ya samu rauni a sakamakon faruwar lamarin, tuni an sallamo shi bayan duba lafiyarsa a asibiti. Wani maƙwabcinsu, Malam Ahmed, ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4 na asubahi,...
Wannan na zuwa ne bayan samun labarin kama wata mai suna Maryam Hussain Abdullahi a Saudiyya da zargin fataucin miyagun ƙwayoyi a daidai lokacin da take aikin Umara. Da yake bayyana yadda aka bankaɗo harƙallar ta hanyar, wadda ke jefa mutanen da ba su ji, ba su gani ba cikin masifa, ya ce ‘yan uwan wadanda aka kama ne a Saudiyya ne suka kawo ƙorafi ga hukumar NDLEA cewa an kama ’yan uwan su a Saudiyya, inda cikin gaggawa hukumar ta ƙaddamar da bincike. “’Yan Nijeriya da aka kama a Saudiyya su ne: Maryam Hussain Abdullahi da Abdullahi Bahijja Aminu da Abulhamid Sadiq waɗanda suka hau jirgin Ethiopian Airline mai lamba ET940, wanda ya bar Kano a ranar...
Wani jami’in ’yan sandan kwantar da tarzoma (MOPOL) mai muƙamin Insfekta ya harbe wani soja har lahira a garin Futuk, da ke Ƙaramar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi. Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne bayan wata taƙaddama da ta taso kan wata mota mai ɗauke da ma’adinai da ake zargin ta wani kamfanin haƙar ma’adinai na ƙasar Sin ce. ASUU: Malaman Jami’ar FUK sun yi zanga-Zanga kan rashin cika musu alƙawura A ɗora min laifin hatsarin jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja — Shugaban NRC Mai riƙon muƙamin Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar soji, Laftanar Solomon Atang Hallet, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kama ɗan sandan da ake zargi, kuma ana ci gaba da...
A wata ziyarar da wata tawagar yan jarida daga Iran suka kai birnin Mosco, kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjeniyoyin habaka dangantaka na sardarwa tsakanin kasashen biyu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa hukumar tashoshin talabijin da Radiyo na kasar Iran da kuma na bangaren Rasha sun karan zurfafa dangantaka tsakaninsu a fagen yada labarai a yankin da kuma duniya gaba daya. Labarin ya kara da cewa wannan dangantakar zai sa fuskance labaran karya wadanda kafafen yada labarai na yamma suke yadawa. Har’ila yau yarjeniyoyin aiki tare tsakanin hukumomin watsa labaran kasashen biyu zai samar da labarai iri guda da kuma fadada hanyoyin samun labaran gaskiya a tsakaninsu. Daga cikin yarjeniyoyin dai akwai na tsakanin...

Jimilar Darajar Hada-Hadar Shige Da Fice A Fannin Bayar Da Hidimomi Ta Kasar Sin Ta Kai Yuan Tiriliyan 3.9 A Rabin Farko Na Shekarar Bana
Bikin CIFTIS na bana, zai kunshi nune-nune daga kasashe, da hukumomin kasa da kasa sama da 70. Kuma kusan kamfanoni 2,000 ne suka shirya shiga bikin a zahiri. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD (OHCHR) ta bayyana cewa sojojin HKI sun kashe Falasdinawa 982 a yankin yamma da kogin Jordan tun cikin watan Octb. Shekara ta 2023. Wannan banda wasu 42,000 da suka tilastawa barin gidajensu daga yankin. Banda haka sun rusa gidajen shaguna da sauran abinda Falasdinawa suka mallaka. Banda haka yahudawan da suke yankin suna kai farmaki kan Falasdinawa a yankin, inda suke kashe wasu Har’ila yau kungiyar red cross ta bayyana cewa ta sha jinyar wasu Falasdinawa a yankin Yamma da kogin Jordan wadanda suka sha hayaki mai guba wanda sojojin HKI suke jefa masu a yankin, Labaran sun kara da cewa a yau laraba sojojin yahudawan sun kai hare haren kan Falasdinawa a Nablus...
Ya yi alkawarin cewa, gwamnatinsa za ta kara hada kai da hukumomin tsaro domin dawo da zaman lafiya, tare da samar da kayayyakin agaji da tallafi ga wadanda abin ya shafa. Majiyoyin yankin sun ce al’ummar yankin sun sha fama da hare-hare akai-akai a ‘yan makonnin da suka gabata, lamarin da ya tilastawa mazauna yankin kauracewa gidajensu. Ku tuna cewa, Gwamna Radda a ranar 18 ga Agusta, 2025 ya bar kasar don hutun makonni uku domin duba lafiyarsa a kasar waje. Gwamnan ya samu rakiyar manyan jami’an gwamnati da shugabannin hukumomin tsaro na jihar da kuma kungiyoyin bayar da agajin gaggawa ga al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
Ƙungiyar Malaman Jami’a (ASUU) reshen Jami’ar Tarayya Kashere (FUK), ta yi zanga-zangar lumana, inda ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar da suka yi da sauran buƙatunsu da ba a cika ba. Zanga-zangar ta fara ne daga ofishin ƙungiyar, ta bi ta ginin shugaban jami’ar, sannan ta ƙare a bakin ƙofar shiga makarantar. Dilan ƙwaya ya shiga hannu a Borno Ambaliya: Gwamnatin Yobe ta samar wa magidanta 250 matsugunin wucin gadi Shugaban ASUU na jami’ar, Dakta Shehu El-Rasheed, ya ce gwamnati ta kasa cika alƙawuran da suka jawo yajin aikin watanni takwas a shekarar 2022. Ya ce har yanzu ba a biya malamai albashin baya ba, haka kuma babu ƙarin albashi na tsawon shekaru. Ya ja hankalin gwamnati cewa...
Ƙungiyar Malaman Jami’a (ASUU) reshen Jami’ar Tarayya Kashere (FUK), ta yi zanga-zangar lumana, inda ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar da suka yi da sauran buƙatunsu da ba a cika ba. Zanga-zangar ta fara ne daga ofishin ƙungiyar, ta bi ta ginin shugaban jami’ar, sannan ta ƙare a bakin ƙofar shiga makarantar. Dilan ƙwaya ya shiga hannu a Borno Ambaliya: Gwamnatin Yobe ta samar wa magidanta 250 matsugunin wucin gadi Shugaban ASUU na jami’ar, Dakta Shehu El-Rasheed, ya ce gwamnati ta kasa cika alƙawuran da suka jawo yajin aikin watanni takwas a shekarar 2022. Ya ce har yanzu ba a biya malamai albashin baya ba, haka kuma babu ƙarin albashi na tsawon shekaru. Ya ja hankalin gwamnati cewa...
Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawarin hanzarta aiwatar da ci gaban Nijeriya ta hanyar amfani da fasahar kere-kere da tattalin abinci don samun nasarori irin na sauran ƙasashe masu tasowa kamar Brazil. A yayin da yake jawabi a ranar Talata a lokacin da ya gana da wasu ‘yan Nijeriya mazauna kasar Brazil, shugaba Tinubu ya jaddada kudirin gwamnatinsa na kawo sauyi ta hanyar kere-kere, gyare-gyare, da kuma samar da ci gaba mai dorewa. Sin Da Kasashen Afirka Za Su Rubuta Sabon Babin Hakkin Dan Adam Bisa Ci Gabansu NRC Ta Dakatar Da Sufurin Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna Bayan Hatsarin Da Ya Yi “Dole ne mu sanya Nijeriya a gaba wajen ci gaban Afirka, ta hanyar amfani da fasahar kere-kere, tattalin abinci,...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta kama wani mutum da ake zargi da dillancin miyagun ƙwayoyi a Ƙaramar Hukumar Bayo. An cafke shi ne ranar 23 ga watan Agusta, 2025, yayin wani samame da ’yan sanda suka kai tare da haɗin gwiwar sashen leƙen asiri. DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Amurka ta ɗaure basaraken Osun kan zamba a tallafin COVID-19 Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce an kama wanda ake zargin mai suna Nasiru Ibrahim da fakiti 25 na tabar wiwi. Ragowar ƙwayoyin da aka samu a wajensa sun haɗa da fakiti 34 na ƙwayar Exzol, da kuma ƙwayar D5 guda 600. An miƙa shi tare da kayan da aka ƙwato...
Gwamnatin Jihar Yobe ta kwashe magidanta sama da 250 daga Garin Kolo da ke Ƙaramar Hukumar Nangere, zuwa sabon matsuguni bayan ambaliyar ruwa ta lalata musu gidaje. An ƙaddamar da sabon matsugunin ne ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni domin kare rayukan waɗanda abin ya shafa. Amurka ta ɗaure basaraken Osun kan zamba a tallafin COVID-19 Amurka ta ɗaure basaraken Osun kan zamba a tallafin COVID-19 Babban sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (YOSEMA), Alhaji Idi Jidawa, ya bayyana cewa an gina gidajen wucin gadi guda 22 domin amfanin mutanen. Haka kuma, an samar da rijiya, banɗakunan wucin gadi guda biyar, da motar ɗaukar marasa lafiya. Jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda da jami’an Sibil Difens...
’Yan bindiga sun kai hari garin Hunƙuyi da ke Ƙaramar Hukumar Kudan, a jihar Kaduna, inda suka kashe mutum ɗaya tare da sace wani ɗan kasuwa. Mutanen yankin sun ce maharan sun kai hari ne da misalin ƙarfe 12:30 na dare. ACReSAL ya tallafa wa manoma da buhunan iri 6,220 a Gombe Babu ɗaya daga cikin buƙatunmu da gwamnati ta aiwatar — Shugaban ASUU Maharan sun shiga yankin ne ta ɓangaren Katsina ɗauke da bindigogi, inda suka dinga harbi a sama. Sun harbe wani mutum mai suna Aminu Shehu har lahira, sannan suka yi awon gaba da wani ɗan kasuwa mai suna Alhaji Shehu Dakin. Majiyoyi, sun bayyana cewa maharan sun yi amfani da wayar Alhaji Shehu wajen kiran iyalansa,...
’Yan bindiga sun kai hari garin Hunƙuyi da ke Ƙaramar Hukumar Kudan, a jihar Kaduna, inda suka kashe mutum ɗaya tare da sace wani ɗan kasuwa. Mutanen yankin sun ce maharan sun kai hari ne da misalin ƙarfe 12:30 na dare. ACReSAL ya tallafa wa manoma da buhunan iri 6,220 a Gombe Babu ɗaya daga cikin buƙatunmu da gwamnati ta aiwatar — Shugaban ASUU Maharan sun shiga yankin ne ta ɓangaren Katsina ɗauke da bindigogi, inda suka dinga harbi a sama. Sun harbe wani mutum mai suna Aminu Shehu har lahira, sannan suka yi awon gaba da wani ɗan kasuwa mai suna Alhaji Shehu Dakin. Majiyoyi, sun bayyana cewa maharan sun yi amfani da wayar Alhaji Shehu wajen kiran iyalansa,...
Shirin Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (ACReSAL) ya raba wa ƙungiyoyin manoma 47 a Jihar Gombe, buhunan iri na zamani 6,220 don bunƙasa harkar noma. An gudanar da rabon ne yayin taron kwanaki biyar na masu ruwa da tsaki kan kula da manyan koguna na Gongola, Gali-Lamurde da Hawal-Kilunga, wanda yake ɗaya daga cikin muhimman ayyukan ACReSAL a Najeriya. Babu ɗaya daga cikin buƙatunmu da gwamnati ta aiwatar — Shugaban ASUU ’Yan bindiga sun sace ma’aurata da ’yarsu mai shekara ɗaya a Katsina Shugaban shirin a Jihar Gombe, Dokta Sani Adamu Jauro, ya ce Gwamna Inuwa Yahaya ya nuna jajircewa wajen tallafa wa manoma ta hanyar shirin. Ya ƙara da cewa an samu nasarori kamar shuka bishiyoyi a dukkanin ƙananan...
Ministan harkokin wajen Iran ya ce: A shirye Iran take ta gudanar da shawarwari da Amurka, amma kan sharudda Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya ce; kasarsa a shirye take ta dawo da tattaunawar makamashin nukiliya da Amurka, amma tare da ba da tabbacin babu batun kai hari kan Iran. Ya bayyana cewa ba za a cimma abin da Amurka ke so ba ta hanyar kai harin soji kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, kuma a duk wata tattaunawa dole ne Amurka ta kare sharuddan da Iran ta gindaya mata domin samun ci gaba mai daure wa. Araqchi wanda ya gana da Asharq Al-Awsat bayan halartar wani zama na musamman na ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi don...
Ministan harkokin wajen kasar Venezuela ya bayyana jin dadinsa ga hadin kai da goyon bayan Iran ga kasarsa A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Iran, ministan harkokin wajen kasar Venezuela ya yabawa irin hadin kai da goyon bayan Iran ga ‘yancin kai, yana mai jaddada aniyar Iran na kare ta daga barazanar Amurka. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya tattauna da takwaransa na kasar Venezuela Ivan Gil Pinto ta wayar tarho game da alakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma ci gaban da ake samu a yankin Caribbean. A cikin wannan kiran, Ministan Harkokin Wajen Venezuela ya ba da rahoto kan abubuwan da ke faruwa a yankin Caribbean bayan karuwar barazanar Amurka da...
Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), Farfesa Chris Piwuna, ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta aiwatar da ɗaya daga cikin yarjejeniyar da ta ƙulla da ƙungiyar ba. Ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin hira da gidan talabijin na Trust TV. ’Yan bindiga sun sace ma’aurata da ’yarsu mai shekara ɗaya a Katsina DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Farfesa Piwuna, ya ce ASUU a koyaushe na zaɓar tattaunawa da jami’an gwamnati a matsayin mafita. Amma duk da cewa sun cimma matsaya kan batutuwa masu muhimmanci kamar kuɗaɗen gudanarwa, albashi, ’yancin malamai, ‘yancin jami’o’i, da sake duba wasu dokoki, ba a ɗauki mataki kan kowanne ba. “Babu saɓani a tsakaninmu da tawagar...
Uzodimma ya ce ƙarin albashi zai inganta rayuwar ma’aikata, sannan ya bunƙasa tattalin arziƙin jihar. Ya kuma bayyana cewa kuɗaɗen shiga na cikin gida sun ƙaru daga Naira miliyan zuwa sama da Naira biliyan uku a kowane wata, yayin da bashin jihar ya ragu daga sama da Naira biliyan 280 a shekarar 2020 zuwa Naira biliyan 100. Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa cire tallafin mai, yana cewa duk da ya jawo tsadar rayuwa, amma ya ƙara yawan kuɗin da ake raba wa jihohi kuma ya bai wa gwamnati damar yin sauye-sauye. Gwamnan ya ƙara da cewa daga ranar 27 ga watan Agusta, gwamnati za ta fara biyan kashin ƙarshe na kuɗaɗen fansho da ake bai wa tsoffin ma’aikata,...
Maharan da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne a ranar Talata sun sace mata da miji tare da ’yarsu mai shekara ɗaya a cikin birnin Katsina. An dai kai harin ne a gidan ma’uratan, Anas Ahmadu, da matarsa Halimatu, da kuma ’yarsu Jiddah a Unguwar Kanada a yankin Ƙofar Ƙaura a Katsina. DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa NRC ta dakatar da jigilar jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja Rahotanni sun ce an kai harin ne wajen misalin ƙarfe 3:00 na daren Litinin inda maharan suka sace magidancin mai suna Malam Anas tare da matarsa mai suna Halimatu da ’yarsa. Bayanai sun kuma nuna wani dan bangar da yayi ƙoƙarin kai musu ɗauki ya rasa...
Haka kuma, a wani samame daban da rundunar ta kai a ranar 15 ga watan Agusta, 2025, ‘yansanda a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu sun yi artabu da ‘yan bindiga a kusa da garin Dankade. Sun ceto mutum biyu da aka sace; Tukur Bello da Isyaka Abubakar, waɗanda aka sace a dajin Gairi na Jihar Zamfara a ranar 9 ga watan Agusta yayin da suke kiwon shanu. ‘Yansanda sun ce sun ƙwato makamai da harsasai daga hannun ‘yan bindigar, tare da alƙawarin ci gaba da yaƙi da masu garkuwa da mutane a faɗin ƙasar nan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa dawowar Jonathan ko Obi na iya sauya tsarin PDP wajen fafatawa da jam’iyyar mai mulki ta APC. Jonathan na da magoya baya masu tsayi da suka daɗe a PDP, yayin da Obi kuma ya fi jan hankalin matasa. Sai dai har yanzu akwai tambayoyi kan ko za su amince da wannan kira, da kuma yadda PDP za ta shawo kan matsalolin cikin gida kafin zaɓen fidda gwani. Zuwa yanzu, babu wanda ya fito fili daga cikinsu ya tabbatar da komawarsa PDP. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta ce tana shirin kafa wata runduna ta dakaru 260,000 domin yaki da ta’addanci. Shugaban hukumar ta ECOWAS, Omar Alieu Touray ne ya bayyana haka a taron hafsoshin tsaron kasashen Afrika na shekarar 2025 a Abuja. Taken taron shi ne “Maganin barazana ga zaman lafiya da tsaro a Afirka a wannan zamani: muhimmancin hadaddiyar dabarun tsaro.” Touray wanda ya samu wakilcin kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro na kungiyar ECOWAS, Ambasada Abdel-Fatau Musah, ya ce hakan wani bangare ne na rage tushen ta’addanci da sauran nau’ikan rashin tsaro a yankin. Ya ce baya ga matakan yaki da ta’addanci, kungiyar tana kuma kokarin aiwatar da dabarun tsaron teku, yana mai cewa babu...
Shugaba Donald Trump, ya yi barazanar sauke Lisa Cook, Gwamnar Babban Bankin Amurka (Federal Reserve), yana mai sukar yadda ake tafiyar da harkokin bankin, musamman batun bayar da bashi da tsare-tsaren lamuni. A wata sanarwa da fadar White House ta fitar, Trump ya zargi Cook da gabatar da “bayanan ƙarya” kan sharuɗan bayar da lamunin gidaje (mortgage), yana mai cewa hakan ya jefa dubban Amurkawa cikin wahala sakamakon hauhawar kuɗin ruwa da kuma tsadar bashi. Sai dai Lisa Cook ta mayar da martani da cewa shugaban ba shi da ikon sauke ta daga muƙamin da take riƙe da shi, saboda dokar da ta kafa Babban Bankin Amurka ta tanadar da cikakken ’yanci ga ’yan kwamitin gudanarwarsa. Ta sha alwashin cewa...
Adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-hare biyu da Isra’ila ta kai a yankin Damascus ya karu zuwa 5, yayin da wasu ma’aikatan ma’aikatar tsaron kasar Syria suka samu raunuka, a cewar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Syria. Cibiyar sa ido ta kasar Syria ta sanar a yammacin jiya Talata cewa, hare-haren biyu an kai su ne a yankin al-Kiswah da ke yankin Damascus, kusa da hanyar Suwayda, tare da raunata wasu sojojin sabuwar gwamnatin kasar ta Syria, wanda suka kasance mambobin kungiyar Hay’at Tahrir al-Sham mai alaka da kungiyar da Aqaida. Majiyoyin cikin gida sun kuma tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari a wani shingen binciken sojojin sabuwar gwamnatin...
Cutar kwalara ta ɓarke a ƙananan hukumomin Gumi da Bukkuyum a Jihar Zamfara, inda ta kashe aƙalla mutum bakwai tare da kwantar da kusan mutum 200 a asibiti. Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar yankin, Hon. Sulaiman Abubakar Gumi, ya ce cutar ta fara tun 10 ga watan Agusta, kuma tana ƙara yaɗuwa. Gwamnati Ta Fara Aikin Gyara Na’urar Watsa Shirye-shirye Mai Gajeren Zango Ta Gidan Rediyon Muryar Nijeriya Hukumar NRC Ta Dakatar Da Zirga-zirgar Jiragen Kasa Na Abuja zuwa Kaduna Ya bayyana cewa rashin tsaftar muhalli da ruwan sama sun taimaka wajen yaɗuwar cutar, musamman a inda ‘yan gudun hijira suke zaune. Ya yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba, cutar na iya zama annoba. Daga...

Gwamnati Ta Fara Aikin Gyara Na’urar Watsa Shirye-shirye Mai Gajeren Zango Ta Gidan Rediyon Muryar Nijeriya
Idris ya gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa hangen nesan sa da jajircewar sa wajen zamanantar da kayan aikin yaɗa labarai a Nijeriya. A cewar sa: “Yayin da muke ɗaukar wannan babban mataki na ƙaddamar kwangilar gyara tiransimitar ‘shortwave’ ta Muryar Nijeriya mai ƙarfin kilowat 250, ya dace mu nuna ɗimbin godiyar mu ga Mai Girma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, bisa hangen nesa da jajircewar sa wajen farfaɗo da kuma zamanantar da kayan aikin yaɗa labarai na Muryar Nijeriya.” Ya kuma tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa wannan aikin zai sauya yanayin yadda ake yaɗa labarai a ƙasar nan. Ya ce: “Da zarar an kammala wannan aiki, na’urorin tiransimita na VON da aka...
Yakin duniya na II abu ne da ya keta kasashe da iyakoki da launin fata, wanda a karshe ya kawo hadin kai tsakanin kasa da kasa domin wanzar da zaman lafiya da ci gaban duniya. Shekaru 80 bayan samun nasarar yaki da masu danniya, ya kamata a yi waiwaye, a nazarci nasarar da aka samu da kyar, da tsamo hikimomi da dabaru da ma hanyoyin karfafa gina duniya cikin kawanciyar hankali da lumana. Yayin da al’ummomin kasashen duniya ke ganin wasu kasashe na kokarin lalata wannan nasara, ya zama wajibi a tsaya tsayin daka wajen bijire musu, don ganin ba a bar su sun mayar da hannun agogo baya ba. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
Fasinjoji na jirgin kasa wanda ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya sauka kan layin dogo da misalign karfe 11:00 nan safe kusa da garin jere. Da dama daga cikin fasinjojin suna cikin tashin hankali saboda matsalolin tsaro da ake fama da shi a kan hanyar. Amma Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa an kawo jami’an tsaro a yankin don tsaron fasinjojin. Kamfanin jiragen kasa na kasa wato ‘The Nigerian Railway Corporation (NRC) bai bada wani bayani kan al-amarin ba har zuwa lokacin bada wannan labarin. Saukan jirgin daga layin dogon dai bai jiwa wani rauni ba, kuma babu wanda ya rasa ransa. A cikin watan mayun shekara ta 2024 da ya gabata ma, an sami...
Fasinjoji na jirgin kasa wanda ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya sauka kan layin dogo da misalign karfe 11:00 nan safe kusa da garin jere. Da dama daga cikin fasinjojin suna cikin tashin hankali saboda matsalolin tsaro da ake fama da shi a kan hanyar. Amma Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa an kawo jami’an tsaro a yankin don tsaron fasinjojin. Kamfanin jiragen kasa na kasa wato ‘The Nigerian Railway Corporation (NRC) bai bada wani bayani kan al-amarin ba har zuwa lokacin bada wannan labarin. Saukan jirgin daga layin dogon dai bai jiwa wani rauni ba, kuma babu wanda ya rasa ransa. A cikin watan mayun shekara ta 2024 da ya gabata ma, an sami...
Akalla mutum daya ne ya rasa ransa a yankin Qunaitra na kasar Siriya a lokacinda HKI suka kai hare-hare a yankin da jirgin yaki wanda ake sarrafashi daga nesa wato Drons. Kamfanin dillancin labaran SANA na gwamnatin kasar Siriya ya bayyana cewa majiyar yankin wanda yake kudu maso yammacin duddan Golan wadanda HKI ta mamaye, ya bayyana cewa tun bayan kifar da shugaba Asad a shekarar da ta gabata, sojojin HKI sun kai hare-hare kan dukkan rumbun ajiyar makamai na sojojin Bashhar Al-asad, kuma su kan kai hare-hare da dare a kan yankun dukkan Golan na kasar siriya wanda yaejeniyar 1974 ya bayyana a matsayin yankin babu makamai. Sannan sukan kai hare hare kan yankin Suwaida su kashe wanda suka...
Ribadu ya yaba da jajircewar sojoji da ‘yansanda da sauran jami’an tsaro da suka gudanar da aikin, yana mai cewa, wannan wata nasara ce da za a yi alfahari da ita a tarihin yaki da ta’addanci. A Guji Siyasantar da Tsaro Sai dai Ribadu ya gargadi shugabannin siyasa da masu rike da madafun iko da su guji siyasantar da al’amuran tsaro, yana mai cewa: “Wannan ƙalubale na gama gari ne, ba wai na shugabanni kaɗai ba. Domin haka nake kira ga al’umma da shugabanni su daina siyasantar da tsaro.” Ribadu ya ƙara da cewa, gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu, za ta ci gaba da yin duk abin da ya kamata domin magance barazanar tsaro tare da kawo...
A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan suka gana da Sarkin Cambodia Norodom Sihamoni, da mahaifiyarsa Sarauniya Norodom Monineath Sihanouk a birnin Beijing. Xi ya yi kyakkyawar maraba da zuwan Sarki Norodom Sihamoni da mahaifiyarsa Sarauniya Norodom Monineath Sihanouk kasar Sin, kana ya yi lale maraba da halartar Sarki Sihamoni bikin da za a yi na cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiyar jama’ar kasar Sin kan zaluncin kasar Japan, da kuma yaki da mulkin danniya a duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
Hukumar Hisbah ta haramta karuwanci da duk wasu munanan ɗabi’u da ake gudanarwa a otal-otal, wuraren casu da duk wasu cibiyoyin nishaɗi a Jihar Bauchi. Babban Kwamishinan Hisbah, Barista Aminu Balarabe Isah, ya bayyana haka ne a yayin wani taron tattaunawa da masu otal-otal da wuraren shaƙatawa a Bauchi. Trump ya yi barazanar korar Gwamnar Babban Bankin Amurka Jirgin kasa dauke da fasinjoji ya yi hastari a hanyar Kaduna-Abuja Ya ce an haramta gudanar da al’adun gargajiya irin su Shadi, Sharo, Garaya da kuma shagulgulan wannan zamani kamar Kauyawa Day, Gala, DJ, Aloba da sauransu a bukukuwan aure. Isah ya ce an ɗauki waɗannan matakan ne bayan samun korafe-korafe daga jama’a kan yadda abubuwa na rashin tarbiyya da tayar da...
Har yanzu babu tabbaci ko zai iya buga wasan. Arsenal na fatan cewa Saka da Odegaard ba za su daɗe suna jinya ba. A kakar da ta wuce, Saka ya sha fama da rauni har ya yi watanni uku ba ya wasa. Sai dai a bana Arsenal ta ƙara wasu sababbin ‘yan wassan gaba kamar Viktor Gyokeres da Eberechi Eze, baya ga waɗanda ta ke da su kamar Gabriel Martinelli, Leandro Trossard, Ethan Nwaneri da Max Dowman don rage giɓin Saka da Odegaard. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe...
Jirgin kasa dauke da fasinjoji a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ya sauka daga kan titi. Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin tarogon jirgin kasan sun mirgina a yayin da fasinjoji suka shiga tashin hankali.
Kalli hotuna da bidiyo da sauran bayanai kai tsaye daga shafin Aminiya kamar kana wurin da ake gudanar da gagarumin bikin Ranar Hausa ta Duniya ta 2025.
A halin yanzu Sarkin Daura, ya hallara a filin gagarumin bikin Ranar Hausa ta Duniya da a bana ake gudanarwa a fadarsa, inda za a gudanar da hawan daba na musamman. Sarkin Daura ya karbi bakuncin Gwamnan Jihar Damagaram daga Jamhuriyar Nijar, Kanar Yosouf Labo da kuma Sarkin Damagaram, Aboubacar Sanda Oumarou a fadarsa, albarkacin bikin Ranar Hausa ta Duniya. Ga kadan daga cikin hotunan yadda kasaitaccen bikin ke gudana.
shafin Jagoran juyin juya halin Musulunci a cikin harshen Yahudanci ya bayyana cewa: ‘Yan sahayoniyya sune wadanda aka fi kyamata a duniya Shafin Jagoran juyin juya halin Musulunci na yaren yahudanci a shafin sada zumunta na X ya rubuta cewa: Makiyar al’ummar Iran na kan gaba a yau ita ce, gwamnatin ‘yan sahayoniyya wacce ita ce mafi kyamata a tsakanin al’ummar duniya. Shafin yanar gizo na KHAMENEI.IR na yaren yahudanci ya wallafa wani kaso na jawabin Jagoran a jiya litinin a wajen taron juyayin shahadar Imam Ali dan Musa al-Rida Jagoran shiriya na Iyalan gidan Manzon Allah {s.aw}. Sanarwar ta kara da cewa: “Makiyar al’ummar Iran a yau, ita ce gwamnatin ‘yan sahayoniyya, wacce duniya ta fi kyama a duniya....
Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka ta ECOWAS ta bayyana shirinta na kafa rundunar yaki da ta’addanci mai dauke da sojoji 260,000 domin tunkarar barazanar tsaro da ke kara ta’azzara a yankin. Shugaban ECOWAS, Omar Alieu Touray, wanda wakilinsa Abdel-Fatau Musah ya gabatar da jawabi a taron shugabannin rundunonin tsaro na Afirka da aka gudanar a Abuja, ya ce wannan mataki na daga cikin kokarin dakile ayyukan ta’addanci da sauran matsalolin tsaro da suka addabi yankin. “Babu wani yanki a Afirka da ya tsira daga ta’addanci, rikice-rikicen cikin gida da kuma koma-baya ta fannin ci-gaba,” in ji Musah. ECOWAS ta ce za ta bukaci dala biliyan 2.5 a kowace shekara domin tallafa wa rundunar da kayan aiki da kudaden gudanarwa....
Yau 26 ga watan Agusta take ranar murnar zagayowar bikin Ranar Hausa ta Duniya. A halin yanzu shirye-shirye sun yi nisa domin fara gagarumin bikin Ranar Hausa ta Duniya a birnin Daura, Jihar Katsina. An shirya gudanar da gagarumin bikin na bana a birnin Daura ne, kasancewarsa inda ake gani a matsayin asalin Hausawa, shekaru arau-aru. Mahaya dawaki da sauran mahalarta bikin daga sassa daban-daban na Najeriya da kasashen waje da mazauna garin Daura sun fara tururuwa zuwa filin bikin, wanda zai samu. An kuma shirya gudanar da gagarumin hawan daba a Fadar Sarkin Daura, albarkacin zagayowar bikin Ranar Hausa ta Duniya karo na 10. A wannan ranar ake cika shekara 10 da fara wannan gagarumin biki,...
Mataimakin Ministan harkokin wajen Iran da takwarorinsa na Faransa, Jamus, da Birtaniyya za su gudanar da wani sabon zagaye na tattaunawa a birnin Geneva na kasar Switzerland, a daidai lokacin da kasashen uku ke barazanar aiwatar da abin da ake kira tsarin dawo da takunkumin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a kan Iran. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya fada a ranar Litinin cewa, za a koma yin shawarwari tsakanin wakilan Iran da E3 a ranar Talata. Ya ce za a gudanar da taron ne a matakin mataimakan ministocin harkokin waje da daraktocin siyasa. Hakan na zuwa ne bayan wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da babban wakilin kungiyar EU mai...
Harin sama na Isra’ila kan cibiyar lafiya ta Nasser Medical Complex a Khan Younis ya kashe ‘yan jarida biyar ranar Litinin. Daga cikinsu akwai mai ɗaukar hoto Moaz Abu Taha da Mariam Abu Daqqa da mai ɗaukar bidiyon gidan talabijin na Palestine TV Hussam al-Masri, da kuma ɗan jaridar Al Jazeera Mohammad Salama da ma’aikacin kwantaragi na Reuters Hatem Khaled, in ji majiyoyin lafiya da kuma kafar watsa labaran da ke Qatar. Kashe-kashe na baya bayan nan sun nuna irin gagarumar ta’adin da yaƙin ya yi a kan ‘yan jaridan Gaza, lamarin da ya mayar da yankin wuri mafi hatsari ga ‘yan jarida a duniya. Daga farko a cikin ƙarshen mako, ƙungiyar ‘yan jarida ta Falasɗinu ta tabbatar da cewa...
A duk ranar 26 ga watan Agustan kowace shekara ake bukukuwan zagayowar Ranar Hausa ta Duniya. An fara wannan biki ne tun a shekarar 2015, inda wani tsohon ma’aikacin sashen Hausa na BBC kuma ma’aikacin TRT Hausa a yanzu, Abdulbaƙi Jari Aliyu ya ƙirƙiro tare da wasu masu amfani da shafukan sada zumunta. An ɓullo da ranar ce domin haɗa kan masu magana da harshen Hausa a faɗin duniya da nufin magance matsalolin da ke ci musu tuwo a ƙwarya. Da farko dai, an fara bikin wannan rana ce kamar wasa a shafukan sada zumunta, inda aka yi ta amfani da kalmar #RanarHausa. Zuwa shekara ta 2018 kuma aka fara yin bikin a zahiri tare da gudanar da tarurruka...
Na yi imani babu rayuwa ba tare da harshe ba, domin duk wata al’umma tana da buƙatar harshe domin gudanar da rubuce-rubuce, kimiyya da fasaha. Amma an yi sakaci da nazarin harshen Hausa, duk da cewa yana cikin manyan harsunan duniya masu ƙarfi da adabi. Don haka zan fara bayyana matsalolin, sannan in kawo shawarwari. Matsala ta farko: Sai Bango Ya Tsage… Idan gwamnati da manyan al’umma ba su ɗauki Hausa da muhimmanci ba, ba zai samu ci gaba ba. An taɓa samun shugaban ƙasa da ya ce nazarin wasu darusa ɓata lokaci ne, amma shi kansa a lokacin yaƙin neman zaɓe da Hausa yake magana. Gwamnati ta nuna rashin kulawa da harshen Hausa, tana ganin ba shi da amfani....
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan fara bikin harshen Hausa ta duniya shekaru goma da suka gabata ne dai manazarta suke bayyana irin cigaba da habbakar da yaren ya samu. Harshen Hausa ya samu zama a mataki na 11 cikin harsunan da ake amfani dasu a fadin duniya tare da fatan nan bada jimawa ba zai dara hakan. NAJERIYA A YAU: Ayyukan da fasahar AI za ta iya raba mutane da su a nan gaba DAGA LARABA: Yadda wasu tsare-tsaren ba da tazarar haihuwa ke yin illa ga mata Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan irin cigaba ko akasin haka da harshen Hausa da aladunta suka samu cikin shekara goma. Domin...
Matashin, wanda yake yin atisaye a makarantar Mount Kelly ta Birtaniya, ya nuna cewa Nijeriya na da ƙwarewa a harkar ninkaya, duk da cewa har yanzu babu ɗan wasan ninkayar Nijeriya da ya taɓa kai wa gasar Olympics. Nijeriya dai ta taɓa lashe lambobin yabo 27 a wasannin Olympics amma ba ta taɓa yin nasara a fannin ninkaya ba. Hukumar wasanni ta kasa ta taya shi murna, tare da hukumar kula da wasannin ruwa ta Najeriya. Darakta Janar, Bukola Olopade, a cikin sanarwarsa a ranar Lahadi, ya ce wannan babbar nasara ce ga wasannin Najeriya baki ɗaya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdel Aty ya tattauna da takwaransa na Tunisiya Mohamed Ali Nafti kan batutuwa da dama da suka shafi yankin gabas ta tsakiya a gefen taron majalisar ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC a birnin Jeddah na kasar Saudiyya. Dangane da ci gaban da halin da ake ciki a Gaza, Abdel Aty ya gabatar da kokarin Masar tare da hadin gwiwar bangarorin shiyya da na kasa da kasa, na cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ta ba da tabbacin sako mutanen da aka yi garkuwa da su da fursunoni da kuma bude hanyar shigar da kayan agaji. Ya lura da matsaloli na jin kai da suka biyo bayan manufofin Isra’ila na haifar...
Bikin ranar ba iya Nijeriya kawai ya tsaya ba. Ana gudanar da bikin a ƙasashe da dama irin su Ghana, Amurka, Turkiyya da kuma Dubai, inda al’ummar Hausawa ke yin rayuwa. A waɗannan wurare, ana shirya wasanni irin gargajiya kamar wasan Dambe, nuna abinci da kayayyakin al’adu, da kuma gudanar da taruka, tattaunawa kan harshen Hausa da tarihinsa. A Nijeriya, cibiyoyi da ƙungiyoyi masu zaman kansu sukan shirya taruka da laccoci. A jami’o’i irin su Jami’ar Bayero ta Kano da sauransu, masana da ɗalibai su kan tattauna kan ci gaban Hausa a fannin kimiyya da fasaha, da kuma ƙirƙiro sababbin kalmomi da ke dacewa da zamani. Haka kuma, jama’a na amfani da wannan rana a kafafen sada zumunta domin wallafa...
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM) ta bayar da rahoton a ranar Litinin cewa mutane sama da rabin miliyan ne suka koma Khartoum a cikin watan Yuli, wanda ke nuna karuwar komawa babban birnin Sudan da yaki ya daidaita. A cewar hukumar, kimanin mutane 500,074 ne suka koma birnin, wanda ya karu da kashi 400 cikin 100 idan aka kwatanta da alkaluman da aka samu a watan Yuni. Wannan ya biyo bayan kwato birnin ne da sojojin Sudan suka yi daga hannun mayakan Rapid Support Forces (RSF) a cikin watan Maris, a ci gaba da kokarin da gwamnatin kasar ke yi na kaddamar da shirye-shiryen sake gine-gine da kwantar da hankula. Hukumar ta IOM ta...
Kafar CGTN da jami’ar Renmin ne suka gudanar da nazarin ta hannun cibiyar inganta tuntubar juna tsakanin kasa da kasa a sabon zamani. An kuma gudanar da nazarin ne tsakanin mutanen manyan kasashen duniya da na kasashe masu tasowa. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A wannan Litinin ɗin Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sauka a Brasilia da ke ƙasar Brazil, inda ya fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu, domin amsa gayyatar da ƙasar ta yi masa. Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga shugaban Brazil, Inacio Lula da Silva, inda aka yi masa faretin ban girma irin na soji da ake karrama shugabannin ƙasashe. PDP ta miƙa wa kudancin Najeriya takarar shugaban ƙasa a 2027 Gwamnatin Kano ta musanta karkatar da N6.5bn daga baitul-malin jihar Ana saran shugabannin biyu da jami’ansu za su tattauna a kan batutuwa da dama da suka shafi sufurin jiragen sama da noma da harkar ma’adinai. Kazalika, shugabannin biyu za su tattauna inganta haɗakar diflomasiyya da sauran abubuwan da suka...
Albarkacin taron koli na Kungiyar Hadin Kan Shanghai (SCO) na 2025, an yi bikin kaddamarwa na kasashen SCO, da shiri mai taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” da CMG ta shirya a yau Litinin a nan birnin Beijing. Tun daga yau, za a fara watsa shirin a manyan gidajen talibijin na Rasha, Kazakhstan, Kyrgyzstan, Pakistan, Iran, da Belarus da sauransu. Shugaban CMG Shen Haixiong ya bayyana cewa, shirin ya zabi labarai masu ban sha’awa na yadda Shugaba Xi Jinping ke kula da al’adu da ci gabansu, don bayyana muhimman ra’ayoyinsa game da al’adu. A karkashin ruhin “Shanghai”, za a ci gaba da rubuta sabon labari na hadin kai da rabon makoma tsakanin al’adu, tare da kafa kyakkyawar makoma ta bil’adama...
Amma, a cikin wata sanarwa mai kakkausar murya da ya fitar a ranar Litinin, Daraktan Yada Labarai na Gidan Gwamnati, Sanusi Bature DawakinTofa, ya karya rahoton da cewa “aiki ne na tatsuniyoyi, wadanda abokan hamayyar siyasa suka shirya su, domin bata wa gwamnati suna don su samu madafun iko gabanin zaben 2027. “Kowane tsabar kudi da ke fita a cikin Ma’aikatun gwamnati a tsare suke yadda ya kamata a cikin kundin kasafin kudi na jihar. Don haka, babu wani mutum a cikin gwamnati da ke kula da kudaden jama’a ba tare da wata manufa ta musamman ba,” in ji sanarwar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
Har ila yau, rahoton ya ce, matakin na Amurka muradu da dabarunta na siyasar duniya kadai yake karewa, yayin da take dogaro da karfin soja wajen haifar da tsaiko ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankuna da ma tsarin harkokin tekun na duniya. Bugu da kari, ya soki ayyukan Amurka yana cewa, sun saba doka, ba su kamata ba, kuma suna nuna fuskoki biyu. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya, PDP, ta keɓe wa kudancin Nijeriya tikitin takarar kujerar shugaban ƙasa a Zaɓen 2027. Jam’iyyar ta tabbatar da haka ne a babban taron Kwamitin Zartarwa karo na 102 da ta gudanar ranar Litinin a Abuja. PDP ta tabbatar da Damagum a matsayin shugabanta na ƙasa Wata mata ta mayar da N4.8m da aka yi kuskuren tura wa asusunta a Maiduguri A baya-bayan nan dai wasu masu ruwa da tsaki kan sha’anin siyasa sun zafafa kiraye-kiraye ga tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya yi wa jam’iyyar takara a Zaɓen 2027. A yayin taron na yau ne kuma PDP ta tabbatar da Umar Damagum a matsayin shugabanta na ƙasa a hukumance. Damagum wanda ya shafe fiye da...
Ministocin harkokin waje na Iran da Saudiya sun bukaci hadin kan kasashen musulmi don magance matsalolin da al-ummar falasdinu take faskanta a gaza. Sun bayyana cewa akwai bukatar kasashen musulmi su san yadda zasu yi don nisar da abinci zuwa yankingaza da kuma kawo karshen kissan kiyashin da HKI take yi a yankin. Tashar taabijin ta Presstv ta bayyana cewa Abbas Aragchi ya tattauna da tokwaransa na kasar Saudia Faisal bin Farhan al-Saud ne a gefen taron ministocin harkokin waje na kasashen musulmi OIC na gaggawa wanda aka gudanar a birnin Jidda na kasar Saudiya . Banda haka ministocin sun yi maganar karfafa dangantaka tsakanin kasashen wadanda suka hada da kasuwanci, yawon shakatawa, da kuma al-adu. Sun kuma ya magana...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wata ƙungiyar siyasa da ke goyon bayan masu fafutikar nan ta “Bring Back Our Goodluck” ta buƙaci tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, da ya tsaya takara a Zaɓen 2027. Ƙungiyar ta ce a Zaɓen 2015 an yaudari ‘yan Najeriya da suka dage wajen ganin bai yi nasara ba a ƙoƙarinsa na neman wa’adi na biyu, lamarin da yanzu kowa yake nadama saboda an jefa ƙasar cikin tsanani da tsadar rayuwa da rashin tsaro. Za a yi amfani da Hausa wajen samar da zaman lafiya — Abdulbaqi Jari Jiragen yaki sun kashe ’yan ta’adda 35 a iyakar Najeriya da Kamaru A yayin wani taro na Arewa maso Yamma da aka gudanar ranar Lahadi a Kano, madugun ƙungiyar na ƙasa, Dokra...

Sin Ta Shiga Jerin Kasashe 3 Dake Sahun Gaba Wajen Gudanar Da Cinikayya Da Kasashe Da Yankunan Duniya 157
Shugabar hukumar kwastam ta kasar Sin Sun Meijun, ta ce Sin ta shiga jerin kasashe uku dake sahun gaba wajen gudanar da cinikayya da kasashe da yankunan duniya 157. Sun Meijun, ta bayyana hakan ne a Litinin din nan yayin taron manema labarai da ta gudana, inda ta ce a shekarar 2024 darajar hada-hadar cinikayya tsakanin Sin da kasashen da suka shiga shawarar ziri daya da hanya daya ta kai yuan tiriliyan 22, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan uku, ciki har da wadanda suka hada da sama da kaso 50 bisa dari na jimillar hada-hadar shige da ficen hajoji. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
Za a yi amfani da harshen Hausa a matsayin hanyar samar da zaman lafiya a yayin bikin Ranar Hausa ta Duniya karo na goma (10), wanda za a gudanar a Daura da ke Jihar Katsina, a ranar Talata, 26 ga watan Agusta, 2025. Jagoran taron, Abdulbaqi Aliyu Jari, wanda shi ne ya ƙirƙiri wannan rana, ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Katsina. Jiragen yaki sun kashe ’yan ta’adda 35 a iyakar Najeriya da Kamaru Jami’an tsaro sun tsare jagoran Falasdinawa mazauna Najeriya Ya ce dukkan shirye-shirye sun kammala, kuma manyan baƙi daga ciki da wajen Najeriya tuni sun fara isowa domin halartar bikin. Jari ya ce an tsara taron ne domin baje kolin al’adun Hausawa...
Sojojin Najeriya sun kashe ’yan ta’adda kimanin 35 da ake zargin mayakan kungiyar ISWAP ne a kusa da iyakar Najeriya da Kamaru. ’Yan ta’addan sun taru a yankin Kumshe, wani gari da ke kan iyaka a Jihar Borno, da safiyar Asabar domin kai hari kan sansanin sojoji da ke yankin. Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa bayan samun bayanan sirri, sojojin kasa sun nemi taimakon rundunar sojin sama, inda jiragen yaki suka kai hare-hare a wuraren da aka gano ’yan ta’addan sun taru. “Ranar Asabar, 23 ga Agusta, sojojin runduna ta 21 sun dakile wani hari da ’yan ta’adda suka kai da daddare, inda jiragen yaki suka ragargaza ’yan ta’addan,” in ji wata majiya. Binciken bayan harin ya nuna cewa an...
Jami’an tsaron Najeriya sun yi awon gaba da Shugaban al’ummar Falasdinawa mazauna Najeriya, Abu Ramzi Ibrahim, a birnin Abuja Rahotanni sun suna jami’an tsaro sun kama Abu Ramzi Ibrahim me a gidansa da ke Abuja tun ranar Juma’a. Majiyoyi daga cikin al’ummar Falasɗinu sun ce Ibrahim, wanda dasn Bafalasɗine ne kuma ya yi karatu a jami’ar Najeriya, yana tsare har zuwa yanzu. Wakilinmu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin Jakadan Falasɗinu da ke Najeriya amma hakarsa ta cin ma ruwa ba. Rushe Kasuwar Alaba Rabo: Mun yi asarar fiye da N20bn — ’Yan Arewa Yau Shugabannin Tsaron Afrika 54 ke taro a Abuja Ibrahim ya shahara wajen kare muradun Falasɗinawa ta kafafen yaɗa labarai, musamman a ’yan watannin nan da...
’Yan Arewa a Kasuwar Alaba Rago, shahararriyar kasuwar ’yan Arewa a Jihar Legas sun roki gwamnatin jihar ta biya su diyya kan asarar da suka yi sakamakon rushe kasuwar da gwamnati nta yi. Sun bayyana cewa asarar da suka tafka ta haura Naira biliyan 20 bayan Gwamnatin Legas ta rusa masallatai sama da 40 da shaguna kimanin 3,000 a Kasuwar wadda suka kafa shekara 45 da suka gabata a jihar. A karo na biyu a ’yan kwanakin nan mahukunta a Jihar Legas suka rushe sassa da dama na kasuwar, wadda ta yi fice da kasuwancin kayan abinci da dabbobi da karafa da sauran kayan masarufi, wacce Hausawa suka kafa a shekarar 1979. A cikin watan Mayun 2024, jami’an hukumar ’yan...
Kwamandan sojojin Iran ya yi barazanar mayar da martani mai muni da zai haifar da nadama ga makiya Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya jaddada cewa: Sojojin kasar Iran da jarumtarsu suna tsayawa da dukkan karfinsu wajen fuskantar barazanar makiya. A yayin ziyarar da ya kai Jami’ar Kimiyyar Sojin Ruwa ta Imam Khumaini (RA) da ke tashar jiragen ruwa ta Noshahr ta arewacin kasar Iran a jiya Lahadi, Manjo Janar Hatami ya bayyana cewa: “A yau Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da matsayi na musamman a tsakanin kasashen yankin, ya kamata makiya su sani cewa al’ummar kasar na kwarai a cikin sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye suke, kamar yadda suka saba a baya, da...
Kafofin yada labarai na yahudawan sahayoniyya sun yarda da gazawar dakile Yemen daga ci gaba da ayyukan soji kan Isra’ila Kafofin yada labaran Isra’ila, wadanda tashar 12 da tashar ta 13 ke wakilta, sun amince da cewa: Hare-haren da makiya ke kaiwa kasar Yemen, ya gaza hana sojojin Yemen harba makamai masu linzami zuwa yankunan Isra’ila da aka mamaye. Waɗannan tashoshi na yahudawan sahayoniyya sun yi imani cewa; Da’awar iya dakile hare-haren sojojin Yemen kan yankunan Isra’ila, rudu ne kawai na jami’an haramtacciyar kasar Isra’ila ganin tsawon lokacin da za a iya dauka domin hana kai waɗannan ayyuka saboda “haɗarinsu.” Tashar talabijin ta yahudawa ta 13 ta yarda cewa harin na baya-bayan nan da aka kai kan kasar Yemen ba...
Wani babban kusa a kungiyar Hamas ya yi Allah wadai da kin amincewar firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu na kin amincewa da sabuwar shawarar da masu shiga tsakani suka yi na tsagaita bude wuta a Gaza. Mamban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Bassem Naim, ya fada a ranar Lahadin da ta gabata cewa da gangan Netanyahu ya dakatar da tattaunawar sulhun Gaza don kare kansa da kuma majalisar ministocinsa na masu tsattsauran ra’ayi, da kuma zafafa yakin da ake yi kan al’ummar Gaza. Ya bayar da misali da rahotannin da kafafen yada labarai na baya-bayan nan da ke nuni da cewa gwamnatin kasar ta yi watsi da yarjejeniyar wani bangare da Hamas, yana mai cewa Tel Aviv na son cimma cikakkiyar...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk wanda ya shekara arbain zuwa sama ya san irin tarbiyyan da ya samo daga wurin iyayen sa a da baya can, irin mu’amalan dake tsakanin sa da iyaye har ma da shakuwan dake tsakanin ‘ya’ya da iyaye. A yanzu kuwa abubuwa sun canza daga yadda aka san su, inda abubuwa suka rincabe sukayi wa iyaye yawa. Daya daga cikin manyan sauyin da aka samu sun hada da aikin gwamnati ko aikin wata da iyaye mata suke yi a wannan zamani wanda hakan a wasu lokuta ke barazana ga irin kulawan da ‘ya’ya suke samu. NAJERIYA A YAU: Ayyukan da fasahar AI za ta iya raba mutane da su a nan gaba...
A nasa ɓangaren, Farfesa Usman Yusuf Bugaje ya gargadi gwamnati cewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba, matsalar za ta iya bazuwa zuwa manyan birane a jihar. A ƙoƙarin gwamnati, rundunar sojin Nijeriya ta sanar da shirin kafa sabuwar bataliya a ƙaramar hukumar Malumfashi domin ƙarfafa yaƙi da tashe-tashen hankulan ƴan bindiga a jihar Katsina. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian yayin da yake jinjinawa bayanan goyon bayan da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi a ranar Lahadin da ta gabata ya rubuta cewa: “Ina mika godiya ta musamman ga Jagora bisa kyakkyawan ra’ayi da goyon bayan da yake bayarwa, mu saurari shawararsa ta hadin kai da hadin kan kasa daga gare shi.” Shugaba Masoud Pezeshkian yayi wannan jinjina ne biyo bayan jawabin goyon bayan da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya baiwa yunkurin hadin kan kasa da hadin kan al’ummar kasa. Pezeshkian ya rubuta a cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadin da ta gabata cewa: “Bisa da kokarin ganin...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya isa kasar Saudiyya domin halartar wani babban taro na majalisar ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi. A yayin da yake jagorantar tawagar diflomasiyya ta kasar Iran, Araghchi ya isa birnin Jeddah na kasar Saudiyya a jiya Lahadi domin halartar taron kungiyar OIC da za a bude a wannan Litinin bisa bukatar da Iran da kuma wasu kasashe gabatar na yin hakan. A yayin taron na kwanaki biyu, mahalarta taron za su tattauna kan matsalolin jin kai a zirin Gaza, da yiwuwar kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa al’ummar Palastinu, da kuma gurfanar da ‘yan sahayoniya masu laifi a gaban kotu. Kungiyar ta OIC ta ce taron zai mayar...
A yau ne babbar jam’iyyar adawa ta PDP za ta gudanar da zama na 102 na Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC), inda ake sa ran ta yanke hukunci kan wasu jiga-jiganta da ake zargi da cin dunduniyarta, ciki har da Ministan Abuja Nyesom Wike da tsohon Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom. Majiyoyi a jam’iyyar sun ce a yayin taron, za a gabatar da rahoton kwamitin ladabtarwa ƙarƙashin jagorancin Tom Ikimi, wanda ya ba da shawarar ɗaukar mataki a kan waɗanda ake zargi da yi wa jam’iyyar zangon ƙasa. Har ila yau, taron zai tattauna shirin gudanar da babban taron jam’iyya na ƙasa a Ibadan a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba, inda za a zaɓi sababbin shugabanni. Kazalika rahoton...
Malaman addinin Musulunci da shugabannin al’umma sun buƙaci matasan Najeriya da su rungumi rayuwa mai ma’ana bisa koyarwar addini, suna gargaɗi cewa watsi da tarbiyyarsu na iya jefa makomar ƙasa cikin haɗari. An yi wannan kira ne a taron ’Light of Guidance Youth Conference 2025’ da aka gudanar a Abuja, wanda ƙungiyoyin Light of Guidance Foundation da Ma’aruf Foundation suka shirya. Uwargidan Gwamnan Jihar Yobe, Hajiya Hafsat Kollere-Buni, ta shaida wa mahalarta taron cewa matasa su ne “kadarar ƙasa mafi daraja,” don haka dole a jagorance su da koyarwar Musulunci domin su jagoranci al’ummarsu cikin mutunci. “Idan muka jagorance su bisa koyarwar Musulunci, za su kai al’ummarmu gaba cikin martaba da mutunci. Amma idan muka yi watsi da su, muna...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A ranar 27 ga watan nan na Agusta, za a bude cibiyar tattarawa da watsa labarai game da bukukuwan cika shekaru 80 da samun nasara a yakin turje wa harin Japan da karshen yakin duniya na II. Cibiyar wadda take hotel na Beijing Media Center, za ta bayar da shaidar watsa labarai da shirya damarmakin hirararki ga ‘yan jarida na kasar Sin da na ketare. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ɗariƙar Tijjaniyya a Jihar Gombe, ta yi babban rashi bayan rasuwar ɗaya daga cikin fitattun malamanta, Sheikh Umar Bojude. Sheikh Bojude shi ne babban limamin Masallacin Juma’a na Alhaji Gidado Dalibi Yahaya (AG Dalibi). Japan za ta bai wa Najeriya rancen $190m don inganta wutar lantarki Rikici ya kunno kai a jam’iyyar ADC a Gombe Malamin ya rasu a ranar Lahadi, kuma an yi jana’izarsa a unguwar Jan Kai da misalin ƙarfe 5 na yamma. Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya aike da saƙon ta’aziyyarsa ta bakin Daraktan Yaɗa Labaransa, Isma’ila Uba Misilli. Ya bayyana rasuwar malamin a matsayin babban rashi ga ɗariƙar Tijjaniyya, iyalansa da kuma al’ummar jihar. “Ina miƙa ta’aziyyata ga iyalan marigayi, ɗariƙar Tijjaniyya, Fityanul Islam...
Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa Najeriya za ta karɓi rancen dala miliyan 190 daga Ƙasar Japan domin inganta wutar lantarki. Wannan na cikin wata sanarwa da ma’aikatar lantarki, yayin da ake gudanar fa taron ƙasashen Afirka da ke gudana a birnin Yokohama na Ƙasar Japan. Mutum 6 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Sakkwato An harbe masu garkuwa da mutane 3 a Kebbi Tawagar Najeriya ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu ta halarci taron. Rancen zai fito ne daga hukumar Japan International Cooperation Agency (JICA), kuma ana sa ran zai taimaka wajen samar da wutar lantarki mai ɗorewa a yankunan da ba su da isasshiyar wuta. Ma’aikatar ta kuma ce wannan lamuni ya zo ne a matsayin ƙari...
Jam’iyyar ADC a Jihar Gombe, ta sanar da korar tsohon ɗan takarar gwamnanta na shekarar 2015, Nafiu Bala, bisa zargin yi mata zagon ƙasa. Shugaban ADC na jihar, Auwal Abba Barde, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudana a Gombe. An harbe masu garkuwa da mutane 3 a Kebbi Mutum 6 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Sakkwato A cewarsa, kwamitin ladabtarwa na unguwar Nasarawo ya binciki Bala, inda ya same shi da laifukan cin amanar jam’iyyar wanda hakan ya saɓa wa dokokinta. Ya ce an gayyaci Bala domin ya kare kansa a gaban kwamitin amma ya ƙi bayyana. Barde ya ƙara da cewa kwamitin zartarwa na jihar, ya tabbatar da wannan hukunci,...
’Yan sanda sun samu nasarar kashe wasu mutum uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, tare da ƙwato bindigar AK-47 bayan musayar wuta da su a yankin Shanga na Jihar Kebbi. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, CSP Nafiu Abubakar, ya fitar. Mutum 6 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Sakkwato An tsinci gawar saurayi a gefen kudiddifi a Kalaba Sanarwar ta bayyana cewa lokacin da lamarin ya faru, DPO na Shanga ya gaggauta haɗa jami’an ‘yan sanda da ‘yan sa-kai waɗanda suka fafata da ‘yan bindigar, inda aka kashe uku daga cikinsu, sauran kuma suka tsere cikin daji. Kakakin ’yan sandan ya ce wannan nasara na da nasaba da...
Aƙalla mutane shida sun rasa rayukansu, yayin da har yanzu an nemi wasu uku an rasa, sakamakon kifewar kwale-kwale a Garin Faji na Ƙaramar Hukumar Sabon Birni da ke Jihar Sakkwato. Lamarin ya faru ne lokacin da mazauna yankin ke tsere wa wani harin ‘yan bindiga da misalin ƙarfe 5:30 na safiyar Alhamis, 21 ga watan Agusta. An tsinci gawar saurayi a gefen kudiddifi a Kalaba Sarkin Musulmi ya ayyana Litinin 1 ga watan Rabi’ul Awwal Wannan shi ne karo na biyu cikin kasa da mako guda da irin wannan ibtila’i ya faru, domin a kwanaki shida da suka gabata, mutane huɗu sun mutu a hatsarin kwale-kwale makamancin wannan a Ƙaramar Hukumar Goronyo ta jihar. Aminiya ta ruwaito cewa, waɗanda...
An tsinci gawar wani saurayi mai suna Daniel Ekanen, mai kimanin shekaru 18, a gefen wani kudiddifi da ke unguwar Ikot Effanga a Ƙaramar Hukumar Kalaba, Jihar Kuros Riba. Lamarin ya jefa firgici a zukata da kuma zaman dar-dar a cikin mazauna yankin, inda aka ruwaito cewa an kawo marigayin ne wurin dangin mahaifinsa daga ƙauyen Ikot Offiong da ke ƙaramar hukumar Odukpani a jihar. Sarkin Musulmi ya ayyana Litinin 1 ga watan Rabi’ul Awwal Dangote ya ci gaba da zama attajiri mafi arziƙi a Afirka — Forbes Rahotanni sun nuna cewa ana zargin masu tsafi da sassan jikin ɗan adam ne suka yi kisan, domin kuwa an yanke kansa kafin a jefar da gawarsa a gefen kudiddifin. Wani daga...
Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya tabbatar da cewa gobe Litinin, 25 ga watan Agusta, 2025, ita ce za ta zama 1 ga watan Rabi’ul Awwal, 1447 bayan hijira. Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin shugaban kwamitin kula da harkokin addini a majalisar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaid, wanda ya bayyana cewa ba a samu labarin ganin sabon wata na Rabi’ul Awwal a ranar Asabar, 29 ga Safar ba. Dangote ya ci gaba da zama attajiri mafi arziƙi a Afirka — Forbes An haramta bukukuwan aure a Taraba Farfesa Sambo wanda kuma shi ne Wazirin Sakkwato, ya ce saboda haka, Lahadi, 24 ga watan Agustan 2025, za ta zama 30 ga watan Safar, sannan kuma bisa...
Fitaccen attajirin nan, Aliko Dangote ya ci gaba da riƙe kambinsa na mutum mafi arziƙi a nahiyar Afirka, inda dukiyarsa ta kai dala biliyan $24.4, a cewar sabuwar ƙididdigar da mujallar Forbes ta fitar a bana. Wannan ya sanya shi zama mutum na 88 a jerin masu kuɗin duniya, inda ya rike wannan matsayi da tazara mai nisa a kan sauran attajiran Najeriya. An kama matashi kan zargin kashe matar ɗan uwansa mai juna biyu An haramta bukukuwan aure a Taraba Abdulsamad Rabiu wanda ya mallaki rukunin kamfanin BUA, shi ne ya biyo bayansa da dukiyar da ta kai dala biliyan $7.2, wanda ya sa shi zama attajiri na 516 a duniya. Sai kuma Mike Adenuga da dukiya mai darajar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wannan yana samar da lantarki da rage asarar makamashi da kuma samar da kaso 25 na bukatun makamshi na ginin. Haka kuma zai kai ga rage fitar hayakin Carbon tan 500 a shekara. Baya ga haka, ginin na amfani da tsoffin baturan motoci masu amfani da lantarki, wajen adana makamashi. Ana amfani da irin wadannan batura guda 14 wajen adana rarar makamashin da ake samu daga bangon gilas mai zukar hasken rana da samar da makamashi mai tsafta a lokaci mafi samun hasken rana, a farashin yuan 0.22 kwatankwacin $0.031, kan kilowatt 1 a kowacce sa’a. Kuma za a yi amfani da makamashin da aka adana a lokacin da ake bukatar lantarki mai yawa ko kuma lokacin da...
Amma abin takaici, duniya ba ta san laifukan da Japan ta yi wa kasar Sin a lokacin yakin ba sosai. Har yanzu gwamnatin Japan ba ta nemi afuwar Sin da sauran kasashen Asiya da ta jefa cikin ukuba ba. Har ma, ‘yan siyasar Japan masu tsattsauran ra’ayi na ci gaba da gurbata wannan tarihi, a yunkurin gujewa hukunci da al’ummar duniya za su yi musu. Mace macen da aka samu a yakin duniya na 2, abun bakin ciki ne ga dukan bil’adama. Al’ummomin kasashen duniya suna da makoma da tarihi na bai daya, wanda ba za a iya mantawa da shi ba, balle a gyara shi. A bana ake cika shekaru 80 da nasarar yakin kin harin...